chapter 9-10
by @ummuaffan
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 9-10*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba! Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT ***
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka *** Tana Bauchi tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa ko wanne da farashinsa. Na gode.
A ɓangaren su Abba kuwa Sakinaa na ganin su Mubarak sun tafi ta saka kuka, da yaja motar kuwa bin bayansu tayi Hamma Umar ne ya kamota, kuka take sosai da haka suka shiga cikin gida.
Umma saboda takaici rufe Sakinaa tayi da bugu Abba kuwa zurum ya yi yana tunan. Bai taɓa hasaso ko tunanin Sakinaa za tayi haka ba, ɗan yau kenan da baka shaidar shi, sai ya baka kunya a idon duniya. Yanzu ga shi ya ɗau alkhawarin bai ma Umar ita ga shi za ta ba shi kunya. Babu wanda ya kai Umar tashin hankali don suna shugowa ya musu sallama ya tafi gida kawai.
Allah ne ya kai sa gida lafiya domin gudun da yake ya wuce ƙa'ida ga shi baya cikin haiyacinsa, bai san ma ya aka yi yazo gidan ba, domin tunaninsa fita ya yi a ƙwaƙwalwarsa, yana parking ya fito ko motar bai iya rufewa ba. Yana shiga Parlour kuwa ya zube yana wani irin numfashi da kakarin amai.
Su Dad daga sama suka farajin kakarin aman sa sun ji tsayuwar motarsa amma suka ji shi shuru bai hawo sama ba. Da sauri suka fito ai hango sho su ka yi zube yana amai, da sauri suka ƙarasa, tuni Mummy ta ruɗ nan ta fara kuka ganin aman jini yake. Dad ma hankalinsa ya tashi rungumesa ya yi yana tambayarsa abinda ya faru, ya kasa magana sai saitin zuciyarsa da yake nuna musu zuwa can ya yi luww! Ya zube jikin Daddy a sume.
Mummy ta saki wani rikitacciyar ƙara mai haɗe da sautin kuka ta kurma ihuw. Daddy ne ya yi ƙarfin halin ɗauko ruwan sanyi ya zuba masa amma ko ɗan yatsansa bai yi motsi ba, nan fa suka sake ruɗewa, Da ƙyar Daddy ya iya cicciɓar Umar don shiɗin cikakken namiji ne ga tsayi ga shi kuma ƙaƙƙarfa, sai da Mummy ta riƙe ƙafafuwansa shi kuma ya riƙe can wajenuwar jikin da kai sannan suka nufi harabar gidan, cikin mota suka saka shi Mummy ta shiga bayan tare da ɗaura kansa bisa cinyarta tana ta kuka shi kan sa Daddy ƙarfin hali yake da haka yaja motar suka nufi asibiti.
Suna isa aka ɗauko irin kujerar nan ta tura marasa lafiya a kai aka ɗaurasa suka nufi ciki, nan fa Lokitoci suka fara ba shi taimakon gaggawa.
A gidansu Sakinaa kuwa rigima sabuwa domin haƙiƙancewa tayi ita fa Mubarak take so. Umma dukanta take amma bakin yaƙi mutuwa don Umma ba ta da haƙurin irin haka.
"Don ƙaniyarki mu muka haifeki ba ke ki ka haifemu ba, da zaki ce ba zaki bi umarninmu ba." Cikin kuka ta ce, "Wallahi Umma ko kashe ni zaki yi bazan daina ce miki Mubarak nake so ba." Saitin bakin Umma ta buga nan kuwa ya fashe Sakinaa ta saki wani gigitaccen kuka duk da haka ba ta fasa cewa Mubarak take so ba.
Abba ne ya jenye Umma daga bugun da takewa Sakinaa ya ce, "Rabu da ita Hadiza kanta tamawa mu dai take gayawa irin waɗannan kalaman ko, duk wanda yaƙi ji ai ku to ba zai ƙi gani ba, duniya ce ta ishi kowa riga da wando."
Bayan wucewarsu Zaliha ta din ga kallon Sakinaa rai ɓace ta ce "Yanzu Sakinaa saboda wani banza can ki ke wa iyayenki wannan cin mutuncin? Abinda baki taɓa ba, duk gatan da iyayenki ke miki ki rasa da abinda zaki saka musu sai na butulcewa ina ji miki tsoran wataran ki girbe abinda kika shuka."
Miƙewa Sakinaa tayi cike da bala'i.
"Ina ruwanki, me ya shafeki? Nayi ɗin iyayenki ne ko nawa? Daƙiƙiya wawiya kawai." Zaliha ta ce, "Kai ni ki ke zagi haka Sakinaa? Ai gaki nan babbar daƙiƙiya marajin maganar iyayenta, akwai wawiya da ta fiki?" Ai kafin ta rufe baki Sakinaa cikin zafin nama ta kai mata bugu a baki Zaliha ma ta ce ba ta isa ba nan suka fara danbe na bala'i.
Sai da Abba ya shugo ya raba su ya ce, "Zaliha rabu da ita ai abinda mutum ya shuga shi yake girba, tayi lokacinta ne, wata rana sai labari, waɗanda suka yi abin da yafi nata ma yanzu ina suke?" Haka ya kama Zaliha suka fita, Sakinaa kuwa ko ajikinta wai an tsikari kakkausa, zama tayi tana zan tsaki Mtsuw ta ce A bayyane "Wallahi ba wanda ya isa ya raba ni da Mubarak ina son sa kuma sai na aure shi."
A can asibiti kuwa an samu Umar ya farfaɗo sai dai da sunan Sakinaa a bakinsa, ita kawai yake kira Likita ya sanar da Daddy tabbas a kawo Sakinaa domin sun masa allurar bacci suna so da ya farko ya ganta idan ba haka ba kuwa akwai matsala. Hankalin a tashe Daddy ya nufi gidansu Abba, ya sanar masu duk kan abinda ya faru. Umma kuka kawai ta fara Abba ya fara sallallami hawaye kwance a idonsa.
Ɗkin Sakinaa Abba ya nufa, kwance ya isketa tana hawaye tana ganinsa ta juya masa baya cike da mamaki Abba yake kallonta kafin ya ce, "Sakinaa Umar yana asibiti babu lafiya shi ne na ce ki shirya muje."
Turo baki gaba tayi cikin halin ko in kula ta ce, "Ni Abba babu inda zani." Buɗe ido ya yi yana kallonta kafin ya iya furta. "Sakinaa ni mahaifinki Mamal Abdullahi Bakanike ki ke faɗawa wannan maganar mai zafi da ɗacin furzarwa, kina da hankali kuwa?"
Banza ta masa tana ƙunƙunai abin ya ɓata wa Abba rai bai san lokacin da ya kwasa mata mari ba, riƙe kuncinta tayi tare da sakin wani rikitaccen kuka ta ce, "Ni wallahi babu inda zan je."
Jin kukanta Daddy da Umma suka shugu. Daddy da bai san wainar da ake toyawa ba ya yi tambaya, nan suke sanar ma sa duk abinda ya faru, kallonta ya yi "Sakinaa me ke damun ki iyaye ba abin wasa ba ne, sam."
Ko ƙala ba ta ce ma sa ba, sai harare-harare da take. Daddy ne ya ce, "Tunda ba za ta ba shi ke nan." Lallaɓa ba irin wacce Abba baiwa Sakinaa ba taƙi, mai haƙuri bai iya fushi ba haka ya rufeta da bugu amma ko gezai ba tayi ba, akan bata zuwa. Daddy ne ya bawa Abba haƙuri sannan suka tafi duka asibitin.
Ko da Umar ya farfaɗo ya ga su Abba kuka ya saka ya ce, "Abba ka mini alk'awarin zaka ba ni Sakinaa don Allah ka bata haƙuri kar ta guje ni ita ce FARIN CIKINA."
Abba da Umma me za su yi ba kuka ba. Abba ya ce, "Umar tabbas na maka alƙawarin baka Sakinaa amma ban taɓa tunanin ko kawo za taƙi bin umarni ni ba ɗan yau ne ka haifesa amma baka haifi halinsa ba tabbas Sakinaa ta ba ni mamaki amma duniya ce ta isheta riga da wando har da zanin ɗaurawa."
Hawaye Umar yake yana danne saitin zuciyarsa tabbas Allah ne ya dasa masa ƙaunar Sakinaa ba shi ne ya sawa kan sa ba.
Haka Umar ya yi jinyar kwana biyu yaji jiki sosai, amma Sakinaa ba ta zo ba, Zaliha tana zuwa tare da Umma ta tausayawa Umar sosai har kuka take idan suka je.
Bayan sun koma gida. Daddy ya ɗauki Mummy da Umar suka je gidan Abba, don Umar ya matsa yana son ganin Sakinaa. Ranar da suka je suka iske durama domin Mubarak ne yazo Abba yanawa Sakinaa magana taƙi ji wai lallai sai tabi Mubarak, wasu zafafan hawaye ke zubowa a fuskar Hamma Umar, ganin yadda Abba yake dukan Sakinaa yasa yaje ya riƙeshi ya ce, "Please Abba rabu da ita indai don ni ne wallahi daga yau na haƙura da Sakinaa ka bata wanda take so, ba zan so na auri Sakinaa amma zuciyarta tana gurin wani ba, na haƙura Abba."
Gabaɗaya zuba ma sa ido su kai cike da tausayi kowa na hawaye, ɗaga Sakinaa ya yi ya ce, "Sorry Princess Abba zai baki wanda ki ke so, kwantar da hankalinki ƙanwata."
Daddy ya ce, "Allah na gode maka da ka ba ni yaro adali wanda yasan ya kamata, tabbas abinda kayi shine daidai Umar masoyin gaskiya shine ke iya sadaukar da farin cikinsa domin farin cikin abinda yake so, wannan shine so na haƙiƙa wanda babu gauraye ko algus a cikinsa."
Abba ya dafa Umar ya ce, "Allah ya maka albarka Umar tabbas Sakinaa ta ba ni kunya, amma kan ta tabawa ina roƙon Allah ya baka juriya da hakurin rashinta ya kuma zaɓa maka mata ta gari." Hawaye ne suka gangaro a fuskarsa ya ce "Amin Abba."
Juyowa Abba ya yi ya kalli Mubarak Ya ce, "Ina so ka turo iyayenka yau ɗin nan su kawo sadaki kawai nake buƙata dubu Ashirin gobe Juma'a a masallaci za a ɗaura muku aure. Ba na ƙaunar wannan butulun yarinyar ta ƙara wuce gobe a gidana."
Ai daga Sakinaa har Mubarak murmushi a ka ga suna yi. Mubarak ya ce, "To na gode bari naje na sanar musu." Ya kalli Sakinaa suka sake yin murmushi ya fice. Dukansu kasa magana su ka yi abin ya ba su al'ajabi haka Sakinaa ta wuce ɗakinta cikin murna har da tsalle.
Daddy suka musu sallama jiki a sanyaye suka fita. Abba da Umma ba wanda ya iya magana dukansu sun yi jigum-jigum.
Zaliha ce ta nufi ɗakin Sakinaa wacce ke ta faman haɗa kayanta waje guda na tafiya ɗakin miji, don har a zuciyarta ta ƙosa safiyar gobe ta waye.
Kallonta tayi galala ta ce, "Sakinaa wai kan ki guda kuwa?" Ba ta waigo ba ta ce, "To duba da ƙyau dai, idan kuma na haɗa shi da naki ne to?" Zaliha ta riƙe baki cike da mamaki kafin ta ce, "Sakinaa zaki yi kuskure babba kuwa kinƙi bin umarnin iyayenki ba abu me sauƙi ba ne, ki dawo haiyacinki Sakinaa. Tsuwww Sakinaa taja tsaki ba ta kuma tanka mata ba. Zaliha ta zuciya sosai ta ce, "Sakinaa tabbas zaki ga ne kuranki, masoyinki na haƙiƙa Hamma Umar sai Allah ya saka masa haka iyayenki ma."
Cikin tsananin fushi Sakinaa ta ce, "Wai Zaliha ina ruwanki ne? Iyayenki ne ko nawa? Idan kin ji haushi ki auri Hamma Umar ɗin mana.
"Ni bazan auresa ba, amma ina son ki sani sai na rama masa abinda ki ka masa ni Zaliha Shehu nayi alkhawarin sai nasa kin yi da nasanin abinda kika yi, daga ke har wannan shegen Mubarak ɗin." Kuka Sakinaa ta kama "Allah ya isa tunda ki ka kira sa, shege wallahi da ki zagi Mubarak gara ki zage ni shi ba shege ba ne da ubansa."
Baki da hanci da kuma kunne sai ido Zaliha ta saki tana kallon Sakinaa a mamakance, nan take wani tunani ya faɗo mata anya kuwa Sakinaa cikin haiyacinta take? Domin biri ya yi kama da mutum abin ya yi yawa." Fita tayi amma tasa a zuciyarta ko ta halin ƙaƙa sai ta ceto ƙawarta daga wannan halin, sai ta nuna mata abinda tayi babban kuskure sai ta nuna mata zaki ko a dawa shi ne sarki.
Mubarak kuwa cike da murna ya shiga cikin gidansu, tun daga harabar gidan yake kwalawa Hajiya kira.
Da sauri Hajiya ta fito tana cewa "Mubarak lafiya kuwa?" Domin ta zaci ko wani abin ne ya faru da shi, jikinta ya faɗa yana cewa "Hajiya mun ci su da yaƙin, Abban Sakinaa ya ce a kai sadaki gobe za a ɗaura mana aure."
Wani irin shu'umin murmushi tayi "Wa ya faɗa musu barno gabas take? Daman me na faɗa maka?"
"Hajiya kizo muje kawai a kai sadakin." Murmushi ta kuma, wayarta ta ciro ta kira ƙaninta Buhari ta ce, "Kazo yanzun nan ina son ganinka."
Ba a yi cikakken awa ba sai ga shi bayan sun gaisa take sanar da shi kuɗin auren Mubarak za su kai kuma gobe ne bikin.
Cike da mamaki yake kallonta ya ce, "Kuɗin aure kuma Hajiya? Goben nan biki amma ba mu ji ba sai yau?"
"Abin ne yazo na gaggawa yanzu iyayen yarinyar mu ma suke sanar mana, ka ga indai maganar kuɗi ce mu ba mu da haufi, don haka ka tashi muje mu kai kuɗin." Zaro ido ya yi "Hajiya mu zamu kai kuɗin? Ina su Alhaji Sani da Alhaji Lawan ƙannan mahaifinsa? Ai su ya dace su kai komai dangin ubansa."
Harara ta banka masa ta ce, "Kasan dai ni da yarana ba shiri muke da su ba, don haka bazan bari su shaga maganar yarana ba yanzu kuɗi suke magana ko ba dangin uba?" Zai yi magana ta katse shi "Ka ga Buhari idan kai ma ba za ka je ba, ni kaɗai sai inje tunda ƙafa gare ni.
Saboda yana matuƙar jin tsoranta yasa shi ammasawa da "To idan kin shirya sai mu wuce." Amma shi dai ai ya san da uba ake ado.
Mayafi da jaka ta ɗauko suka fita Mubarak ya kai su gidansu Sakinaa, bayan sun gaisa da Malam Abdullahi suka masa maganar sun kawo kuɗin auren ne.
Daga Umma har shi suka kalli juna cike da al'ajabi, to ya suka iya 'yarsu ce ta musu wannan kwashe-kwashen wai uwar yaro da kawo kuɗin auren ɗanta ba su taɓa gani ba. Ko a garin mahaukata.
Dubu ɗari biyu ta ba da ta ce, "wannan kuɗin nagani ina so, ta bada wasu ɗari biyar ta ce na sadaki ta bada ɗari uku ta ce na uwa da na uba. Harararta ita da kuɗinta Abba ya yi ya ce, "Ki kwashe abin ki ba su muke buƙata ba abinda kawai nake so dubu ashirin sadakinma don ya wajabta da bazan amsa ba.
Ta ce, "Shi ke nan, kayi wa kan ka, amma ba ma so ku kawota da komai ita kaɗai muke so." Haushi ya cika Abba ya ce"Idan mun kawota da su sai ku zubda, sannan ya tashi ya fita. Zuciyarsa na suya kamar an ɗaurata a tukumar tsure...
***
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUuku
#LabarinSakina