AZAAD JUNAID

005

by @jeeddah3256

*AZAAD JUNAID*

   (The young Billionaire)

SECOND EDITION.


Na

Jeeddah Aliyu


© HASKE WRISTERS ASSOCIATION.



005.



Koda Aslamiyya ta kammala shara zuwa lokacin ta jigata matuƙa, ga yunwa ga azabar zogi da hannunta ke mata kamar zai tsinke. Duk da halin da take ciki bata fasa tattaro tulin wanke-wanke wanda ba na Dadda kaɗai bane hadda na surukarta.Tun daga lokaci da ta fara wanke kwanuka har ta kammala kuka take yi idanuwanta sun yi luhu-luhu.

Amrah tai ido biyu da mai provision store da ya tare ƙofar fita, gabanta ya yi mummunar faɗuwa gani yadda mutumin ya murtuƙe fuska yasa cikinta murɗawa "Ke! uban me ya shigo dake shagona?"

Yadda ya daka mata tsawa yana zare idanu ta daburce ta rasa abin faɗa jikinta ya fara mahaukacin rawa. Gani haka ya fahimtar dashi bata da gaskiya musanmman da ya shiga ƙare mata kallo hannuwanta cikin hijabinta tana kiciniya ɓoye wani abu. "Mene ne a cikin hijabinki me kika sata fito dashi don ubanki?"

Kusan a tare ya watsa mata waɗannan jerin tambayoyi, tsora ne ya ƙara lullu6eta. Ta tabbata yau dubunta ya cika, mai kwatar ta hannun wannan mutumin mai zubin samudawa sai Allah. Ta shiga yawo da idanuwanta lugu da saƙo na shagon ko Allah zai sa taga hanyar fita kafin ta gama dube-dubenta ta ji an finciko ta da ƙarfi bai tsaya wata-wata ba ya cire mata hijab sai ga bread sakaɗe a hamanta ta. Ta saki bread ɗin ya fado ƙasa. "Don Allah malam kayi haƙuri wallahi ba halina bane yunwa da rashin gata ya saka ni satar maka bread...

Tun kafin ta ƙarasa magana ya kifa mata mari, wasu jajayyen taurari suka ma-maye ganinta cike da rashin imani ya shiga jibgarta kamar ya sami sa'anshi. Ya sukunce ta ya fito da ita waje yana mata ihun ɓarauniya kafin kace me wurin ya cika da mutane har da yara 'yan makaranta sa'o'inta sai kallonta suke yi. Baki da hancinta na zubda jini Amrah bata ƙara shiga tashin hankali ba sai da taga mutumin yana faɗawa mutane wai ko jiya ya gannta ta shigo mishi shago tana fita, ya nemi kuɗinsa dubu ɗari ya rasa saboda haka ta fito mishi da kuɗinsa ko ya miƙa ta hannun hukuma. Sosai take kuka tana mishi magiya mutane da ke kallo abin da ke faruwa sai la'antar ta suke yi, gata ƙaramar yarinya ace tana sata. Tana ji tana gani ya kwashe ta zuwa police station, tana kallonshi ya ba wa 'yan sanda false statement wai ta satar mishi dubu ɗari.

Ba tare da duba da ƙaranci shekarunta ba suka jefa ta cell cikin muryarta da ta gama disasshe saboda kuka tace."Ku dubi girman Allah da manzonsa ku yi min rai wallahi azim ban ɗauki kuɗinsa ba. Biredi na sata kuma tun a shago na ajiye mishi abinsa...

"Ke! Rufe mana baki ɓarauniyar banza da wofi daga ni idanuwanki za ki aikata, iri-irinku ne idan kuka girma ku ke zama shahararrun 'yan ta'adda.

Wani dogon ɗan sanda ne ya ke magana har yana nuna ta da kulkin hannunshi. Tun Amrah tana kuka da hawaye har ta dawo kukan zuci ga yunwa na nuƙurƙusar hanjinta ga ɗan banza duka da tasha hannun mutumin. Ga kuma tsoro shigowarta hannun police domin abu ne da bai taɓa faruwa da ita ba. Dukka ƙanana sace-sace da take yi cikin gidaje da shaguna ne kuma ba a taɓa kamata ba sai akan wannan.

********************

Madam Salima tare da ƙawarta Hafsah Shinkafi suna zaune a office ɗinta dake cikin kamfaninta, asalin Hafsah Shinkafi 'yar jahar zamfara ce aure ne ya kawo ta Kano mijinta ya rasu ya barta da yara 4 bata sake yi aure ba, a ganinta aure zai takura ta ya hanata neman kuɗi, a ganinta yanzu tafi ƙarfin kowanne ɗan namiji duk abinda namiji zai iya idan ta fanni kuɗi ne ita ma za ta iya saboda haka babu amfani namiji ya sake shigowa rayuwarta. Duk wani gantali neman duniya tare suke yi abinsu. Dabi'unta da na Madam Salima sak iri daya babu bam-banci shiyasa ƙawance su ya yi lasting.

"Salima duk laifinki ne sau nawa ina faɗa miki ki fitar da yaranki ƙasar waje su yi karatu za su fi samun cikakkiyar kulawa, dukiyar nan Allah ya ba ki ita kina sarrafa ta iya son ranki gashi kullum cikin nema kike kina tarawa, to miye amfanin nemanki idan 'ya'yanki ba su sakata suka wala ba?"

Sai da Madam Salima ta shaƙi iska kana ta fesar ta ƙofufin hancinta kafin tace. "Ba wai naƙi shawara ki bane Hafsah kema kinsan kafiya da taurin kai irin na Azaad ba zai taɓa bari yaranshi su yi nesa da gida ba. Yanzu ɗin ma kullum a cikin tuhumata yake akan tarbiyyarsu. Ina gaya miki jiya da haukar shi ya motsa cewa ya yi sai na ajiye business ɗina ko uban me zan masa idan na zauna gida?"

"What! Ki ajiye business ɗinki for what reason?"

"Wallahi kuwa haka ya faɗa. Sai dai ko kusa maganganunsa ba su yi tasiri akaina ba.

"Zance gaskiya Salima ki tashi tsaye domin sare-sarin hauka aka ce zubda miyau. Na fahimci manufar Azaad Junaid guda biyu ne dole ɗaya daga ciki ya kasance gaskiya na ɗaya kodai so yake ya rusa ki yana baƙin ciki da yadda duniya ta fara haska tauraronki. Saboda ya ga kin fara kamo ƙafarshi a arziki shine yake so yai miki ƙafar ungulu. Na biyu Ko so yake ya ƙaro aure....

"Dallah ya isa Hafsah haka! hasashen ki ne ya ba ki hakan. Azaad ba haka yake ba, kawai dai yana so na karɓi ragamar kula da gidana saboda yaranmu sun fara girma.

"Matsalarki kenan Salima har yau kin kasa buɗe idanuwanki ki fahimci gaskiya, kin yarda da Azaad ɗinan shi kuma sam bai yarda dake ba, kin ɗauki soyayyar duniya kin ɗora mishi shi Kuma ya gaji da zama dake duk wannan salo ya fito miki da shi ne saboda kin kasa haifa mishi ɗa namiji wanda zai gaje shi, shiyasa ya fito miki ta wannan siga.

"No....no...please Hafsah don't say that me ya kawo zance haifar namiji da rashin haifarsa?" Kar ki saka min shakku akan mijina mana. Ina miki ƙorafi ne akan rashin jituwa da muke fuskanta a koda yaushe ke kuma kina neman shigowa da wani sabon al'amari.

"Ba sabon al'amari bane Salima kece kika kasa gano hakan da kanki, ki yarda dani Salima akwai  ƙamshin gaskiya a cikin abubuwan da na lissafa miki. Shi zama yake yi ne a gida naga kullum yana yawo a sama kamar tsuntsu yau yana wannan ƙasar gobe yana waccan. Yana ƙara habbaka kasuwancin sa, ko kuma ke kaɗai Allah ya ɗorawa nauyin tarbiyyar yara?" Ki yi amfani da kwa-kwalwarki mana.

Har Hafsah ta dasa aya a zance ta idanuwan Madam Salima na lumshe tana girgiza kanta, ta ɗauki lokaci a haka kafin da sauri ta buɗe idanuwanta gabanta na mugun faɗuwa miƙewa tayi da sauri tare da harɗe hannuwanta a ƙirji ta shiga safa da marwa sai ta kai bangon farko na office ɗinta ta dawo na ƙarshe. Hafsah sai bin ta da kallo take gani safa da marwan nata ba mai ƙarewa bane yasa ta miƙe ta kamo hannunta

"calm down ƙawata..

Ta fincike hannunta da ƙarfi ta ja da baya tana wani girgiza kai, cikin kaushin murya take faɗin "Kina faɗar min mijina zai ƙaro aure kuma kina gaya min I should calm down as how Hafsat tell me as how?"

"Ni ban ce dake zai ƙara aure ba kawai I'm trying to get your brain clean up.

Ajiyar zuciya tayi ta dako cike da izzarta da taƙama ta iso gaban Hafsah ta dafa kafaɗarta, tace. "Hafsat a rayuwata abu biyu nakeso neman kuɗi da Azaad. Haka zalika abu biyu na tsana talauci da kishiya. Ki sani Azaad ba shida ra'ayi mace fiye da ɗaya haka zalika yana matuƙr so 'ya'yanshi fyye da son da ni nake musu, bai taɓa nuna min yana son haifar ɗa namiji ba. Da mace da namiji there are all equal to him ko yanzu ya bijiro da zance na ajiye business ɗina dalilin dambe da Aneesa tai da schoolteacher ɗinsu. Saboda haka tun wuri mu ajiye wannan zance, kafin maganganunki su yi tasiri a zuciyata"

"Kenan kin amince za ki bi abin da yake so za ki mika ragamar kamfaninku ga 'yan uwanki, burinki na mallakar kamfanin ke Kaɗai ya rushe ya bi iska?"

Yatsine fuska tayi kana cikin zallan izgilanci tace.

"Bari ki ji Hafsah ko ubana Kabir Dala da shine silar arziki na da ace zai baro lahira ya zo duniya ya nemi na ajiye business ɗina billahil-azim ba zan masa biyayya ba, balle wani Azaad Junaid da yake tamkar steering mota sai yadda na juya shi.

Lokaci ɗaya suka kwashe da dariyar sheƙinyaci tare da tafawa, Hafsah ta shiga koɗata tana zuba mata kirari.

******************

Fitowar Azaad Junaid da Abdulhakeem Daura daga meeting wayar Abdulhakeem tai ringing, ya ɗaga tare da karawa a kunnenshi. Muryar ƙanwarsa Zainab ya ji tana rera kuka.

"Will you shut up and tell me what exactly happened?"

Shiru ya yi yana sauraren bayani da zainab take mishi, ya shiga furta

"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Zainab sau nawa zan faɗa miki ki daina tafiya mai nisa ba tare direba har sai kin kware da driving,da yake kunnen ƙashi ne dake ki ka ƙi ji. Shi Kenan ganina zuwa.

Ya kashe waya ya mayar da dubanshi kan Azaad wanda ya tsare shi da idanuwa.

"Zainab ce ta kirani wai ta buge wani ɗan achaɓa tana police station.

"Subhanalillah!Allah yasa da sauƙi ka je kawai za mu yi waya.

Cikin sauri Abdulhakeem ya fice kaitsaye police station ɗin ya nufa, cikin yarda Allah ɗan achaɓa bai ji ciwo sosai ba machine ɗinsa ne ya yi damage cikin ƙanƙani lokaci Abdulhakeem ya biya kuɗin machine ɗin ya kuma yi belin ɗin ƙanwarsa. Tun yana cikin office ɗin inspector ya ke ji kukan Amrah da magiyar da take wa 'yan sanda.