FACALA

chapter 19&20

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_Wattpad✅_*

***


*_𝘼rewabooks✅_*

 https://arewabooks.com/user/rabiattu0444


*Sirrinmu➡️*

ƴan uwa mu dena gaba,don duk mutumin dake gaba wutarsa daban ce.


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️19& 20

…………………Fulani na ganin Aamiru awani hali ta sallami bayinta,waɗanda ke tayata hira da bata labari don Fulani ba tada girman kai ko kaɗan ita da bayinta suna hira sosai kuma tana musu ihsani sosai.


 Aamiru ya zauna yana ɗan buga hannunsa cikin ɗayan hannun,Fulani ta tsorata sosai ta ce"yaron albarka wai lafiya kuwa"?.

kallonta yayi da jajayan idanuwansa sannan ya ce"Fulani aƙwai gagarumar matsala arayuwar galadima,bansan me yasa kullum yake janyowa kansa damuwa sannan muma ya dinga son ya janyo mana ba,gaskiya indai haka ta cigaba da faruwa zan cire hannuna akansa,saboda abin ya yi yawa gwara tun wuri mu yiwa tufkar hanci,idan ba haka ba zai janyo mana masifar da bazamu iya fita daga ciki ba,sannan mu rasa ruwan kogin da zai wanke wannan mummunan ɗauɗar".

har lokacin fulani bata gane inda ya dosa ba,cikin hargagi ta ce"haba Aamiru wannan wacce irin magana kake? ban gane wata masifa bace? don Allah ka fito dani acikin tafkin duhun daka jefa ni".

share wani gumi me ɗumi yayi sannan ya ce"Fulani ina zargin fa Galadima yana da ɗa".


  wani irin mugun zaro ido tayi,tana dafe ƙirjinta alkyabbar dake jikinta taji ta jiƙe sharkaf da gumi,kanta yayi mata wani irin mugun nauyi tamkar an ɗaura dutse,jiri da juwa ta faraji taga garin ya zama kala biyu,kai hatta Aamirun ma koma mata yayi gida biyu ta dafe goshinta tana salati.

 Ganin hakan yasan Aamiru ya tsorata sosai,ya ƙaraso inda take amman kafin yazo ta zauna,tana ɗan ɗaga masa hannu alamar yaja da baya bata buƙatar taimakon,ta danne dai dai saitin zuciyarta tana kiran sunan Allah,kuka take so tayi amman ta kasa kukan hankalinta da nutsuwarta,duk suna kan ɗantw namiju tilo wato galadima ɗa namiji tilo me martaba sarkin Babbar masarauta.

cikin matsanancin ɓacin rai ta ce"Aamiru kasan bana son zancen daba na gaskiya bane,shiyasa duk inda ƙarya take bana zama awajen,saboda haka ka faɗamin gaskiyar lamarin abinda ya faru"?.

   

   Duk abinda ya faru tun fitarsu har zuwa rabuwarsu babu abinda ya ɓoyewa Fulani,da kuma ɓoyayyan sirrin daya gani da idanuwansa duk sai daya bata labari bai rage mata ko A ba.

sosai gabanta ya tsananta faɗuwa ta dafe ƙirjinta,lokacin ne kuma ya ciro wayarsa ya nuna mata hoton yaron.

hannunta na kakkarwa ta amshi wayar,ta tsurawa yaron ido tamkar me son gano wani ɓoyayyan lamari,kuka ta fashe dashi tana ce wa"shikkenan Galadima ya cucemu ya cuci kansa,yanzu bayan ta asar daya tafka abaya bai tsaya haka ba har ciki ya yiwa wata ta haife masa ɗan? innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya Allah idan mafarki nake Allah kasa in daina".


  kuka take sosai na tashin hankali,Aamiru yayi dana sanin faɗa mata don baya son ciwonta na hawan jini ya tashi,amman yasan babu yadda zaiyi dole sai ya faɗa mata ɗin,don idan bai gaya mata yanzu ba duniya ta sani sai ɓacin ran yafi wanda take ciki ayanzu.


  ɓacin rai ya hango ƙarara a fuskarta sannan ta ce"Aamiru kiramin shi awaya kace masa duk abinda yake yazo ina jiransa".

Sosai gaban Aamiru ya faɗi don ganin irin halin da take ciki,sai kuma tausayin amininsa ya tsarga masa don bai san wani irin hali zai shiga ba idan yaga ya tona masa asiri.


 Bugu biyu ya ɗauki wayar,daga yadda Aamiru yayi masa magana ya tabbatar aƙwai gagarumar matsala me numfashi,ga kuma matsalar da Gwaggwala take neman jefa sa aciki,wai dole sai yayi aure shi ya rasa wacce irin tsohuwa ce wacce bata son azauna lafiya.

da matsanancin fushi ya fito daga sashen gwaggwala,sai ihu take tana cewa"to duk fushinka aure de anyi an gama kuma da ƴar uwarka sai inga yadda za kayi dani,mutum sai baƙar zuciya tamkar sarkin micizai".

tana ta sababinta, jakadiyarta kuwa nata dariya har su Amira da autar momma suka dawo daga laɓen da suka yiwa Galadima.








***       ***        ***


........daga wajen Abba muka fito ni da yaya Ahmad,sai zolayata yake yana ce wa"taɓ autar Abba kinga kuwa yadda kika koma"?.

sunkuyar da kaina nayi na ce"ai kaima ka girma yaya Ahmad gashi kayi wani ƙwanji kamar ɗan dambe".

murmushinsa yayi minme ƙayatarwa,ya gaida mama uwar gida wacce ba tada wata sana'a sai ta zaman tsakar gida duk me fitowa ta sanya wa mutane ido.

sai kuwa ta ce"au yanzu Ahmad ace ka dawo kaƙi leƙowa inda nake? sai dai kaje inda ake mararin mutum yazo a cinyesa har kuruwarsa"?.

kasa magana yayi saboda mamaki,ko da yake dama ba abin mamaki bane don dama can halin mama uwargida ne zagi da kuma cin mutuncin ɗan adam.

kuɗi ya ciro a wallet ɗinsa masu ƴan yawa ya miƙa mata,ai kuwa sai ta washe baki tana yi masa addu'ah sannan ta ce ya faɗawa hajiyarsa an jima zata shigo ƙwance jaka.

ni kuwa tuni nayi gaba don ban manta ranƙwashin dana awajenta da mama safiya ba.


muna fitowa ya kalleni ya ce"wai Adawiyya haryanzu gidanku bai koma normal bane? ni dai aganina ya kamata Mama ta saduda haka,kishi ai ba hauka bane ni dai zan yiwa hajiya magana tayi mata faɗa".

da sauri na ce"a a yaya, yanzu idan kayi mata magana a'i sai ta ɗauka maganarta mukayi,ƙarshe kuma laifin ya ƙare akaina da kuma Ammina".

Shiru yayi baice komi ba,alamar yaji amman ba lallai ne yayi amfani da abinda yaji ɗin ba.

muna shiga gidan na su,na tarar da Babansu da yaya Zubair suna magana yaya zubair yana tsugunne alamar magana suke.

na gaishesu su duka,Baba ya ce"to daman dai dana ce yanzu zaka ganshi da Adawiyya,ashe kuwa banyi ƙarya ba ni yaushe za ayi auren ne autarmu?".

Rufe fuskata nayi saboda kunya,yaya Zubair ya ce"to Baba ai ni ina ganin gwara a sanya ranar kawai,idan taɗan ƙara ƙwari sai asha buki ko"?.

Baba ya ce"yo wani ƙwari kuma? ni dana auri uwarku shekararta 12 aka auramin ita,ta haifeka kai Zubairu tana da shekara 19".

dukkanmu dariya muka sanya,don Baba aƙwaishi da raha sannan yana jana ajiki sosai wai ni auta ce kuma ina da sunan mamansu,wato mahaifiyar Abbanmu da yake kusan itace ta riƙi Bbansu ya Ahmad.



kamar in tsaya awajen don sam bana son shiga wajen hajiyarsu ya Ahmad,don macece mara mutunci bata san darajar ɗan adam ba baki ɗaya,haka kishiyarta ke shan wahala da ita don irin mutanen nanne waɗanda ba a iya musu duk ta inda ka ɓullo musu sai su ɓullo maka,kuma amaryar hajiyarsu y Ahmad ƙawar Ammi ce sosai,sai dai fa suna fuskantar ƙalubale sosai awajen uwargidajen na su,don sunsha haɗa musu sharri suna tsallakewa don bazan taɓa mantawa aƙwai ranar da suka je suna,sai basu dawo da wuri ba mijin ƙawar tasu ya kawo su a mota har ƙofar gida,Abida ƴar gidan mama uwargida na ƙofar gida da gdu taje ta faɗawa mama uwar gida,ai kuwa sai cewa tayi yawon bin maxa suka tafi tunda gasu can namiji ya saukesu,ranar basu Ammi kaɗai ba hatta nima sai dana shiga cikin tashin hankali,don ranar Ammi bata ƙwana agida ba,itama mamansu Khadija wato kishiyar mamansu ya Ahmad bata ƙwana gidan ta ba,don sun haɗa musu sharri kuma sun faɗa ciki,don sam iyayenmu maza sunƙi jinin mace ta fita daga gida ta kai dare,shiyasa ma suka horasu akan hakan ba don zuciyoyinsu suh yadda da zasu iya bin mazan ba.



  Hajiya na ganina ta ce"a uxubillahi minasshaiɗanurrajim,Ahmad me yasa ka shigomin da wannan mayyar yarinyar ɓangarena? me yasa bata tafi sashen mayun data saba shiga ba? daman nasan kana dawowa da masifar wannan yarinyar zaka dawo,don dama tun kana can ka dameni da zancenta daka samu ban haɗaku awayar ba,shine yanzu daka dawo ka kawomin ita sashe na,su zuƙemin jini ita da uwarta sadaka yalla ko? to wallahi kuruwata kurrrr".


  ta faɗi hakan tana kallona da fici ficin idanuwanta.



da sauri na janye idanuwa na daga gareta,ji nake tamkar xan fasa ihu saboda haushi ina da mugun rauni akan mahaifiyata,naƙi jinin inga ana cin mutuncinta ballantana wannan kalma ta mayya da suke jifanta dashi,ban ƙara tsayawa jin sauran zagin da take min ba na fice baki ɗaya daga falon.


  Haushima yasa ko jiransa banyi ba,don biyoni yayi yana ta kirana ni kuwa nayi banza dashi nayi wucewata zuwa gida.


  ina shiga na faɗa kan cinyar Ammi,wacce ke ta saƙa da injin yin saƙa kayan sanyi,ɗan tureni tayi tana ce wa"ke fa wannan taɓarar taki ƙara yawa take,ke kullum baki girma ne wai? sai ki shigo kullum kina kuka tamkar ƴar yaye?".

 Goge hawayena nayi sannan na ce"to Ammi ba Hajiya bace take zagina,wai har da cewa ni ƴar mayu ce".

Ammi ta ce"to ni aikenki nayi? kuma kada ki ƙara kawomin ƙara,na faɗa miki ki kasance me shanye magana ba komi ake faɗawa iyaye ba,sai ke ki manta iyayenki kuma basu manta ba,sai su riƙe abin a zuƙatansu ke kuma tuni kinyi biris da al'amarin kin manta dashi,Adawiyya inason ki zama mace me zurfin ciki,nan gaba fa aure za kiyi kina son duk abinda aka yi miki ki zama me kai ƙara? to bana son wannan halin ki kula ki kuma mai da hankalinki,sannan duk lokacin da na faɗa miki magana ki dinga amfani da ita yin biyayya ga iyaye yana sanyawa ka zama ɗawisu me walainiya acikin ɗibban jama'ah sannan ka gyara duniyarka ka gyara lahirarka".


 kai na bisa cinyarta gashina yayi yala yala har bacci ya fara ɗaukata,ina kallonta tana murmushi tare da shafa ƙwantaccen yalwataccen gashina sannan ta ce"Allah ya karemin ke ƴata,Allah ya tsare gabanki da bayanki Allah ya baki miji nagari abin tinƙaho".

a zuciyata na amsa da Amin.

alokacin ya Ahmad ya shigo,duk ina jinsu har ya canja kayansa zuwa shadda fara sol tayi masa kyau sosai ya samu waje ya zauna,a ɗaya daga kujerun falon Ammi two seater,ya ce"Ammi nasan Adawiyya tazo ta baki labarin abinda Hajiya tayi mata,nima banji daɗi ba amman in sha Allah zan faɗawa Alhaji yayi mata magana,don sam bana son irin wannan halin ga wani ma ba mahaifiyata ba".

Ammi ta girgiza kanta cikin sanyi ta ce"a a kada ka faɗa masa Ahmad,ba a haka sai ya zama kamar haɗi ne kai dai ka zama me biyayya ga iyayenka musamman ma mahaifiyarka,ka bita asannu da kuma addu'ah in sha Allah zata gane".


  hurarsu suka cigaba dayi har aka kira sallah ya fita yana cewa Ammi ta tashe ni inyi sallah.




washe gari da wuri na shirya cikin uniform ɗina na wajen aiki,don ayanzu muna lokacin hutu ne babu boko,Ammi ta ce"Adawiyya idan kinje kice ogan naku ta bugomin waya aƙwai maganar dana ke so muyi,yanzu ba nida numba ɗinta ne".

na amsa mata lokacin dana ke saka ƙaton hijabina,wanda nake rufe doguwar rigar da take jikina ta aiki.


  ina fitowa kuwa mukayi kiciɓis da ya Ahmad,ya riƙe baki yana kallona ya ce"a auta aikin kenan aka tafi? gaskiya an kusa fa a dena aikin nan,don nifa inada kishi wallahi".

ɗan murmushi nayi ina wasa da ƴan yatsun hannuna,sai kuwa ya ce"to muje in rakaki inga wajen na ku".

muna tafiya muna hira har muka iso,ya riƙe baki yana cewa"la la la ashe wajen naku na manya ne?".

muka shiga ya gaida oganmu wacce ta kasance macece,sannan gata da kirki sosai duk da yare ce ita.

bayan ya tafi na faɗa mata saƙon Ammi,ta kuwa kira sukayi maganar da zasuyi sannan ta kashe,kai tsaye na fara wucewa don lokacin dana bawa amaryar da zan yiwa ƙwalliya ya yi.

tana zuwa kuwa nayi mata,sosai tayi kyau ai kuwa ƴan uwanta ma waɗanda ba anan za a yi musu ƙwalliya ba suka biya kuɗinsu me tsoka aka rangaɗa musu tasu,har da cewa in basu lambar waya ta sai na sanya musu ta Ammina.



ina gama musu oganmu ta kirani,ina zuwa ta ce"Adawiyya an fasa yin decoration ɗin nan a unguwar shanu,a unguwar malali za ayi saboda haka yanzu zaku tafi,kuma ke na sanya shugabarsu ke zaki tsara komi,don naga sauran girma suka fiki amman kin fisu brain(ƙwaƙwalwa)".

na murmusa ina ɗan sanya lipstick a leɓena na bita muka fito compound,muka shiga motar baki ɗayanmu mukayi gaba.


muna kan hanya Ammi ta kirani,ta ce"yauwa ko da mama uwargida zata kiraki ta tambayeki a ina za kuyi aiki,kada ki yarda ki ɗaga wayar".

nace mata "to".

azyciyata ina ta mamakin abinda yasa Ammi ta kirani,ina cikin mamakin sai kuwa ga kiran mama uwar gida don daman kaf ƴan gidanmu suna da numbar wayar wajen aikinmu,kuma idan muka fita aiki nike riƙe da wayar wajen aikin a hannu na.

mamaki nake sosai,amman sai naƙi ɗagawa ta kira yafi sau goma amman ban ɗaga ba,da ta gaji sai ta turomin saƙo.

dariya nayi bayan na karanta saƙon sannan na ajje wayar ma baki ɗaya.



****muna cikin haɗa wajen decoration ɗin sai ga kiran safiya,wato ƴar gidan mama safiya itace autarta.

ina ɗagawa ta ce"Adawiyya yanzu naji mama da mamansu Badi 'a suna waya,wai tunda kinƙi faɗa musu inda kuke walimar zasu biyo muku ta wata hanyar ke da Amminki".


  kasa ce mata komi nayi,jikina yayi sanyi ƙalau,ina mamakin hali irin na waɗannan miyagun mutanen waɗanda basa tsoron Allah,na rasa mi yasa suka tsanemu haka? hawaye suka fara ƙwaronyomin sai naji ana kirana na juya don ganin waye............soon➡️

***

ga masu son joining ɗin grp faccala,zasu iya bin wannan link ɗin na ƙasa bana son maza a grp sannan bana son ƴan masu turo ba tsa.


***

L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


*MRS GREEN CE✅*