1
by @hafnancy
.....Zub'ewa nayi bisa lallausar katifata irin sakko mu gaisan nan ina fadin"Washh Allahna yau na kwaso gajiya wallahi.." daga kwancan na soma k'ok'arin cire bak'ar suit d'ina bayan na kwab'e karamin Farin hijabin kaina.Sai ya rage daga ni sai bak'ar doguwar wandona da kuma farar shirt d'ina na ciki.Gani nayi kwanciyar bai mun ba, sai kawai na tashi zaune na jawo jug d'in ruwa da kuma kofi wanda k'anwata Sakina ta tarbeni dashi, Tsiyaye ruwan nayi acikin kofin kana na kafa kai na kwankwad'e tass na sake karawa dan ba karamin rana ake kwalawa agarin ba dake haifar da tsananin kishirwa, balle garin Sokoto ma ranarmu daban yake.
Ina gama shan wannan ruwan nasa hannu na rik'e kaina jin yadda yake barazanar Fashewa gashi kuma na kara assasawa kaina ciwon adalilin ruwan sanyin dana sha.Acikin wannan halin ne Addah ta shigo ta sameni, Tun kan ta karaso inda nake take"Rahama Sai yanzu? Sakina ce ta tasheni take fad'amun wai kin dawo, ammh fa kun dad'e sosai wai dama haka abun yake da wahala ne ?." Da sauri nace"Oh ya rabbi ni wallahi ban san randa Sakina zatayi hankali ba, yanzu sai da ta tasheki bayan na gargad'eta akan hakan ?" Addah tace"A'a kar ki ga laifinta, wannan umarnina ne, ni dakaina nace ta tasheni in kin dawo, tun bayan da aka idar da sallar azahar nake ta tsumayen ganinki ammh shiru shiru dai, shine bacci ya kwashe saman sallaya, toya akai ne ? Ya orientation d'in ?"d'an guntun tsaki na sakar kana nace"Ke dai bari kawai Addah munci kwal ubanmu yau, Ni takaicina ma inda akai posting d'ina ne akwai wahala, Sun daukeni as theatre Nurse {Nas na b'angaren daya shafi dakin aiki}, dad'in abun kawai buri ya cika kuma Alhamdulillah, Addah shikenan fa yanzu idan baku da lafiya kuka zo UDUTH sai kukace anemo muku Nurse Rahama Abdulmalik, Cike da takama zanzo inda kuke ina wasu Feeling kaina d'innan." Na karashe zancena ina mai kashe mata ido daya, Kallon sha'awa ta bini dashi kan tace"Rahama kar dai ki kasance cikin sahun malaman asibitin nan masu wulak'anta mutane, idan hakan ta faru bazan yafe miki ba kinji dai na gaya miki, kiyi k'ok'ari ki zamo mai tausayi dan ita 'ya mace da rauni aka santa bada taurin zuciya ba, kuma ayanzu ne zaki soma cud'anya dak'yau da mutane daban daban masu banbancin kabila, Rahama ina mai zaburar dake da kiji tsoron Allah akodayaushe, karki sake ki bari wani Fajirin ko Fajira su doraki kan turba mara k'yau, Kiyi k'ok'arin tuna daga irin gidan mutuncin da kika Fito, Ki tuna tarbiyar da muka baki dan girman Allah karki sa kafa ki tattakeshi, wannan shine jawabin da nake yawan miki tun kina karamarki har kawo yanzu da kika zama cikakkiyar mutum, To ki tabbata kina amfani dashi kar da ki kuskura ki bamu kunya."
Hannu nasa ina share hawayen Fuskata wanda ya safko babu shiri kana na kamo hannayenta ina d'an murzasu kan nace"Addah na dau miki alkawari in sha Allahu Rahama Abdulmalik bazata tab'a baku kunya ba, Zanyi k'ok'ari naga na zame muku d'iyar da zakuyi Alfahari da haihuwarta bi'izinillahi ta'ala, Kuma zanji tsoron Allah aduk inda nake akuma duk halin dana tsinci kaina, Snn Zanyi namijin k'okari wajen k'are muku mutuncin kaina, ayadda baku tab'a kuka dani ba har kawo yanzu, to insha Allahu nayi muku alk'awarin bazaku tab'a Zubar da tsadaddun hawayen naku bane akaina, Addah nagode kwarai da gaske da kuka cika mun burina ta kasancewa malamar asibiti, Allah ya biyaku da gidan aljanna" Amsa min tayi da "Ameen Allah miki albarka, Allah kuma ya nuna mana na kannenki haka, muga watarana suma sun zamo wasu mutane arayuwa wa'enda za'ai alfahari dasu." Nace"Ameen Addata." Mik'ewa nayi ina tikar dariyar dole hadda rik'e ciki ina Fadin"Addah 'yarki wai 'yar sanda take san ta zama wannan shine burinta arayuwa." Gwalalo idanu tayi tana Fadi cike da mamaki"Wa kenan ? Ba dai Sakina ba dai ko ?" Nace"Ita d'in fa."
Tafa hannaye Addah ta shiga yi tana salallami, Sai juya abun take tana wak'a dashi"Yar sanda ? In banda abinta me ake tsinta acikin aikin 'yan sanda in banda cin hanci da rashawa ? Hakan take san ta zama kenan ko ? To kuwa zan kwab'eta tun wuri gwara ta canza ra'ayi dan kuwa ni ba bari zanyi tayi aikin 'yan sanda ba, 'ya mace da aikin kaki ina wani abun burgewa ma anan." Cike da rashin jindadin maganarta nace"Haba Addah ina nema ba'a yin cin hancin da rashawar ? Na 'yan sandan ne kawai ake gani ammh kowa da nashi kawai ki bita da fatar alkhairi kar kice zaki kawo cikas a cikar burinta, addu'a kawai muke bukata daga wurinku akodayaushe dan samun haske acikin lamuran rayuwarmu, Addata ina k'aunarku matuk'a keda Papa da Uncle Yusuf."
Nasa hannu ina d'an jan kumatunta da murmushi akan fuskata, ita ma d'in murmushin ne ta mayar mun kan ta sauke ajiyar zuciya tace"To shikenan Allah yayi albarka, yanzu dai tunda naki burin ya cika dan Allah kiyi k'ok'ari ki tsayar da mijin aure dan ba yarinya kike kara zama ba, Rahama kinja shekaru sosai, idan ban manta ba shekarunki talatin da biyu, ganinki haka babu aure abun yana mun ciwo sosai, Sai mutane ke ganin kamar munki aurar dake ne muna jiran muyi auran jari dake ga wanda ya dace, dan Allah Rahama ki taimaka kema ki cika mana burinmu tunda kinga mu mun cika miki naki."
Idanunta k'yam acikin k'wayar idanuna tana shirin soma tsiyayar da ruwan hawayenta, asanyaye nace"Addah kul karki soma, karki kuskura hawayen nan ya zubo kasa akaina, insha Allahu zanyi aure domin kuma in cika muku burinku akaina, ammh ki sani Addah Ni Rahama bazan tab'a auran wanda banaso ba sai wanda ya gameni ya kuma kwanta mun arai sannan kuma bana son wanda keda mata agida, kuma kinga yawancin masu matan ne ke yawan zuwa suna nuna suna sona, Ni kuma bani da ra'ayin auran irinsu, acikin samarin kuma har yanzu ban ga wanda dacewarsa tazo daidai da nawa rayuwar ba dan ina son mijin da zan aura ya Kasance wayayye mai aji mai kuma addini, sannan d'an dangi gaba da baya, mai kuma nagartattun halaye, Wannan shine ake kira da Miji na gari, Addah kimun addu'a Allah yasa in samu irinsa."
"To ameen ameen."kayan jikina na tub'e na daura towel, Addah dai nata bina da ido, ko ba'a fad'a ba kasan tafi k'aunata aduk cikin ya'yanta."Addah bari in watsa ruwa sannan in Fito inyi sallah, Allah yunwa nake ji gashi yarinyar nan bata gama girki ba." Daga murya nayi sosai yadda nasan zata jini"Wai Sakina abincin ne har yanzu ? Ko dutse kike dafa mana ne yau agidan ?" Ji nayi ta bani amsa itama d'in da k'arfi"Yi hakuri Anty Nurse ta kusa tsotsewa" Wanka na shiga nabar Addah nan zaune ta buga uban tagumi tana tunani.Ni nasan rashin aurena na daya daga cikin abun dake damunta kuma ni bada gangan naki yi ba kawai ina da ra'ayi da kuma dogon buri ne. ina tunanin hakan na cikin dalilin dayasa na dad'e agida.
**
Saida nayi sallolina hadda na la'asar Kafin na zauna cin abinci, su Addah na gefena sun tasani gaba da kallo, sai wahala nake wajen cin indomie dan arayuwata ina bala'in sonta, su kuma sai dariya suke mun, Nace"Yanzu Addah na musamman kenan kika sa aka dafa mun favourite d'ina hadda yankamun kaza papa yasa akai, ga lemu mai sanyi, Allah sarki Addata da papana ina sonku matuk'a." Murmushi Addah tayi tace"ai kin cancanta ne, munyi hakan ne dan kema mu faranta miki kamar yadda kike ta faranta mana da maida hankali da kikai wajen neman ilimi, gashi buri ya cika." Nace ina mai yagar cinyar kazata"Addah addu'arku da kuma tsayamun da kukai ne yasa har na taka wannan matsayi" kafin wani ya sake magana wayata ta shiga k'ara, Kai tsaye na daga wayar ina murmushi"Ubaida ya akai ne ? Kin ga wallahi dawowata kenan, dama so nake idan na gama cin abinci in shigo in fesa miki daddad'ar labari..." Kukanta ne ya dakatar dani, nan take fara'ata ta dauke, wani irin faduwar gaba ne ya ziyarceni, cike da rauni nace" Ubaida what happened ? Me aka miki kike kuka ? ina fatar dai wannan karon ba Umar bane dan na rantse da Allah bazamu kwashe da dad'i ba ?"
Jan majina tayi tana fad'i awahalce"Haba Rahama ya kike abu tamk'ar yau ne kika fara sanin matsalata ? Ke kin san Ubayda bata da matsalar data wuce ta Umar, Umar shine damuwata, tashin hankalina da kuma hawan jinina, Rahama Wallahi abun na yau yayi kamari, yafi na kullum d'an belt yayi amfani dashi ya zaneni abunda bai tab'a yi ba, iyakacin ya tsaya akan zagi, amma yau Umar yasa hannu ajikina da sunan duka" Ta rushe da kuka, mik'e wa nayi da wayar akunne ina fad'in" Duka fa kika ce ? Ubaida wai shi mijinki wani irin mahaukaci ne ? Wani irin dabba ne wanda ko kadan bai san darajar 'ya mace ba ? Wannan magana bata waya bace ina zuwa" kit na katse wayar ina huci, jifa nayi da wayar akan kujera na hau sintiri acikin falon, hannayena harde da juna ta baya, sam nama manta dasu Addah afalon, hawaye nake sosai ina tunanin irin rayuwar auren wulak'ancin da makobciyarmu Ubaida take Fuskanta agidan auranta, Arayuwata na tsani in ga ana wulak'anta 'ya mace, 'ya macen daya kamata ace ana daukaka darajarta amma shine wasu ke wulak'antasu ? Musamman Umar wallahi ba mijin arzik'i bane.
"Ke wai meye haka ne ki natsu man dan Allah" firgigit na dawo cikin hayyacina, kallan Addah nayi hankali tashe nace ina shirin sakin kuka"Addah wallahi Umar ba mijin arzik'i bane, da irin Umar amatsayin miji gara in mutu babu aure" Da sauri ta tari numfashina"A'a kul, kar in sake jin irin wannan zance ya fito daga bakinki, Ki sani kowa da irin tasa kaddarar, Wani kaga Allah ya jarabceshi ta hanyar samun dukiya, ko talauci, ko rashin lafiya, wani kuma rashin dacen mata ko miji na gari, misali ki Fara ta kanki, ke kina cikin jarabawar rashin samun tsayayyen mijin aure ne, kuma muna rok'on Allah yasa jinkirin ya zame miki alkhairi" sauke Ajiyar zuciya tayi kan tacigaba"Hak'ik'a ita Ubaidar Allah ne ya jarabceta da rashin dacen miji na gari, Rahama abunda nakeso dake kawai ki tayata da addu'a amma karki kuskura ki shiga cikin lamarin aurensu d'an mata da miji sai Allah, daga gyara kayanka zai zamo sauke mu raba ne kar daga baya su koma ganin bak'inki" hannu nasa ina share hawaye daya wanke mun Fuska kan nace"Yanzu Addah shikenan sai mu zuba idanu muna kallonsa babu wani matakin da zamu dauka ?" a harzuk'e tace"To Rahama me zaki iya yi ? Ina jin mantawa kike da cewar zumuncin makobtaka ce kadai ta had'a mu dasu ko ? To wallahi ki cire idonki akansu na dai gaya miki d'an naji kina Fadin ke da mijin nata zaku kwashi 'yar kallo, Rahama ki kiyaye ban san ki shiga lamarin abunda bai shafeki ba karki jawa kanki matsala" Nace"Maa abunda nakeso kema ki fahimta shine, hakk'in makobtaka na rataye a wuyanmu, kin ga kuwa ya zama dole mu shiga lamarinsu ba wai mu zuba idanu muna kallo ba, ko ba hakk'in makobataka ba ma, yadda Ubaida ta daukeki amatsayin mahaifiya ya kyautu ace kin taimaka mata" Wani irin kallo ta watso mun kan tace"In taimaka ? Mutanenta fa ? Inace haka suke son ganinta shiyasa suka banzantar da al'amarinta ? tunda su basu damu da ita ba, to ke meye naki aciki ? Me kika had'a da ita da har zaki tada hankalinki akan lamarin auranta ?" Nace"Sabida ba makobciya kadai na dauketa ba, na dauketa ne tamk'ar yar'uwata wacce muka Fito ciki daya da ita, Addah ki Fahimta man"
Na lura jikinta yayi sanyi sosai da zancen Nawa, Tana kallo na dauki hijabin da nayi sallah da ita na zura, Kana na fice da sauri sauri.
Tun daga tsakar gidan na soma jiwo hargagin Umar"Ubayda wallahi aurenki bai tsinamin komai ba illa bak'in ciki, amaimakon in sami Farin ciki da kwanciyar hankali, a'a akullum bak'in ciki nake kwasa awajenki, baki iya girki mai dad'i na zamani ba, baki iya kwalliya ba, baki iya kula da bukatun mijinki ba, Kai komai ma baki iya ba, gaki nan ne dai, acikin gidadawan ma kece shugabarsu, abun karin takaicin ma ba d'a ba jika balle asamu salama ta wannan b'angaren, Shekararmu shidda da aure amma har iyau kin kasa k'yankyashewa, gaskiya na gaji da zama da wacce bata da rabo, adalci d'aya zan miki kuma shine bazan sakeki ba, amma zan karo aure, zan auro wahayyiya 'yar boko, yarinya 'yar zamani kamar ni" Cikin toshewar murya naji tana fad'i awahale"Wallahi Umar kai ba mijin aure bane, amma ban ga laifinka ba, nafi dora laifin akan mahaifina wanda shine ya daukeni ya baka, Ka sani duk wani azzalumi mai zaluntar matarsa bazai tab'a gama da duniya lafiya ba, k'arshensa bazai yi dad'in kallo ba, kuma ita haihuwar da kakemun gori akanta Umar ina mai Farin cikin shaida maka cewa ni Ubaida ina dauke da juna biyu, sati hudu da dorin kwanaki biyar, kuma yau kwanak'i hudu kenan da Rahama tamin test da tsinken gwajin ciki ta kuma sake tabbatar da Lallai ina dauke da juna biyun" Cike da mamak'i yayi saurin katseta.."Da gaske Ubaida cikina ne ajikinki shine amatsayina na uban d'an ban cancanta in sani ba sai wata banza can awaje ? 4weeks, 5days pregnancy ace banda masaniya ? Kodayake baki daukeni abakin komai ba shiyasa baki damu in sani ba, to yanzu in nace ba nawa bane fa ? Akwai yadda zakiyi ne ?"
Dakatawa nayi daga bak'in kofar apartment d'insu ina sauraron maganganun da suke jifan juna dashi daga can cikin uwar dak'a, Tabbas naji zafin zagina da yayi amma halin da matarsa take ciki yafi komai daga hankalina, ina jinta tace"Babu yadda zanyi dakai in har kace ba naka bane, amma ai shi Allah baya bacci, yana kallon mai gaskiya, San nan kuma kana wani hayagaga akan ban sanar dakai ba, da'ace ka damu dani ne ai acikin kwanak'in nan idan ka lura bani da wani isassahen lafiya, amma dake ni d'in bani gabanka shiyasa baka damu da lafiyata ba balle har kayi tunanin kaini asibiti adubani, hakan yasa nima na zab'i binne abun acikin raina, idan cikin ya bayyana ai zaka gani da idonka, kaicona ayanzu bai wuci yadda zan haihu da mutumin da bai san darajata ba, ban san taya zai karbi d'an dazan haifa masa ba, zai gwad'a masa So da k'auna ne ko kuwa shima d'in zai wulak'anta rayuwarsa ne kamar yadda ya mayar da mahaifiyarsa wata aba mara daraja awajensa ?" Kan ta karashe maganarta taji zazzafar mari akan k'uncin, Cike da d'acin rai yake Fadin"Lallai Ubaida kinyi k'aurin wuya ? Wai har nine zaki tsaya agabana har ki kalli cikin k'wayar idanuna kina gayamun bak'aken maganganu ? Da alamun dukan dana miki bai gamsheki ba, kari kike nema to yanzu zan miki dukan kawo wuk'a, Kuma ki bud'e kunnuwanki ki saurareni dak'yau, listen and listen good, Ni Umar ban shirya ma haihuwa da kazama irinki ba, kuma bana jin zan tab'a haihuwar dake , Zan nemo wacce zata haifamun ya'ya daga tsatso mai k'yau, Ki sani ba sai munje asibiti an zubar dashi ba, da hannuna zan barar da dan iska yanzu nan take"
Wani irin bugawa ne zuciyata tayi jin abunda ya fad'a, arikice na soma bugun k'ofar ina fad'in"Kai Umar karka kuskura ka aikata hakan, in ba haka ba kotu ce zata rabamu dakai, mugu azzalimi wanda bai san darajar 'ya mace ba, kazo ka bud'e kofar nan in ba haka ba zan nemi abu in ballata"Kuka nake sosai ina bugun k'ofar da aka kulle, ko yaji abunda na fad'a ko bai ji ba ban sani ba, amma tuni har ya soma dukanta tana ihu da kururuwa, babu abunda kake ji baiwar Allahn na fad'i illa"Umar kaji tsoron Allah karka zubar mun da ciki, ina son kayana ahakan, ka tuna fa mun dad'e muna son wannan haihuwar amma bamu samu ba, sai ayanzu ne Allah ya k'arbi kukanmu ya azurtamu da samun rabo, shine kake neman butulce masa ayau ? Amaimakon kayi farin ciki da hakan sannan ka amsheshi da hannu bibbiyu ?" Azafafe yace yana cigaba da kai mata naushi aciki"Wallahi sai ya zub'e d'an ke baki cancanci da ki zama uwar ya'yana ba, Kina dai amsa sunan matata ne amma ban dai tab'a gaya miki bane bani son in haihu dake"Izuwa yanzu Ubaida ta soma galabaita da irin bugun da Umar yake mata, awahalce tace"Umar kayiwa Allah ka rabu dani hakan, nayi maka alk'awari zanje da kaina asibiti afitar da cikin ba sai ka azabtar dani har ka illatani ba......
Ba fata ake ba amma in hakan ta kasance kai zaka iya samun rabo da wata amma ni fa ? Watakila har abada, wallahi ban san da cewa cikinka dana dauka zai zo ya zama babban laifi bane agareka, ban san baka k'aunar ka haihu da Ubaida ba ai dana sani da tuni na dad'e da tsarin iyali"
Sulalewa nayi na zub'e akasa ina rusar kuka, ji nake kamar in fita inje in nemo mutane d'an akawo mata taimakon gaggawa amma sai kawai naji bani da wannan sauran kuzarin, gabak'i daya lakar jikina yayi sanyi, ban san ko tsawon yaushe ne ya dauka yana dukanta ba d'an ban sake jin muryarta ba, Can na mik'e hankali tashe ina shesshek'ar kuka, na shiga k'wala mata k'ira"Ubaida!.." Shiru kake ji hakan yasa hankalina sake tashi na shiga bugun k'ofar da iya k'arfina ina fad'in"Ubaida kina jina ko dai ya kashe mun ke ne ?" Na sake cewa"Kai Umar azzalumi, mai dauke da tambari na gidan wuta ka sani in har ka aikata abunda nake hasasowa ne, to ni Rahama Abdulmalik nayi maka alk'awarin kasheka da hannuna bibbiyu"
Adaidai lokacin naji ana k'ok'arin zare sakatar k'ofar, tsit nayi ina jiran naga fuskar dazan soma yin ido hudu dashi, gabana ne ya cigaba da bugawa, bud'o k'ofar akai, mukai ido hudu da Ubaida wacce gabaki daya ta gama fita daga hayyacinta, da alamun ma jan jiki tayi tazo ta bud'e mun k'ofar, sabon kuka nake shirin sakewa amma bata bani damar hakan ba tace tana murmushin yak'e"Rahama shigo daga ciki ki ga abunda azzalimin yamun, Rahama Umar bashi da imani ya rabani da gud'an jinina kuma gud'an jininsa ta k'arfi da yaji, cikin k'eta da kuma rashin imani" kuka yaci mugun k'arfinta, Wani irin kara na sanya tare da sanya hannu aka, Cike da tashin hankali na ratsa ta gefenta na wulla idona daga inda take har zuwa can hanyar dakin baccinsu, jini ne malale ya b'ata tiles, da alamun tun daga can daki ne ta soma jan jiki har ta karaso falon cikin k'arfin hali irin nata d'an bud'emun k'ofar...
Kuka nake sosai mai daga hankali ina jimanta al'amarin, "How can a man be so wicked to his wife like this ? Aure da aka sani ana yinshi ne d'an soyayya da kuma samun zuri'a dayyaba amma ku d'in kamar mak'iya ? Menene laifinta d'an ta dau cikin d'anka dake kwance amahaifarta ? Zaka iya biyanta wahalhalun da zata sha ne akansa har zuwa sanda zata haifesa ko kuwa zaka iya biyan taka mahaifiyar dawainiyar da ita ta sha akanka ? Umar ka fito ka bani amsar tambayoyina"
Rungumeta nayi muna kuka sosai, sai k'arar ruwan wanka kawai muke ji na zuba akasa daga can bandak'i, da alamun daya gama aikata wannan ta'adin fad'awa bandak'i yayi d'an tsaftace jikinsa sannan ita kuma ya barta cikin wannan mawuyacin halin.....
_KU GYARA ZAMA WASA FARIN GIRKI_
*Amma kafin nan, ina barar kuri'oinku ta hanyar danna tauraron nan na kasa, lol what am simply trying to say is pls vote this page and comment line by line, ku sani sai na samu yawan comments akan page d'in nan kafin in cigaba sabida in san littafi ya samu karbuwa awajenku*
#OneLove
#KT
#HafnancyCe
#UltimateWriter
#IWrite4rmTheHeart❤️
#AnaTare
#Nagode🤝
Follow my account pls.