chapter 21&22
_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
ƴan uwa mu yawaita yin istigfari,Allah ya yafe mana baki ɗaya.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️21& 22
…………………ina juyawa mamaki ya kusa kashe ni saboda ganin Ammina,da sauri naje na rungumeta ina kuka me tsuma zuciya.
na ce"Ammi wai mi yasa su Mama basa jin tsoron Allah?yanzu safiya ta kirani take shaidamin wai mamansu ta ce idan mun tsallake wannan ba lallai ne mu tsallake wani ba".
Ammi ta shafa kai na sannan ta ce"Adawiyya yadda muka tsallake wannan shima wancan ɗin zamu tsallake,hankalina ne ya kasa ƙwanciya har sai dana je wajen oganku ta ƙwatantamin nan nazo".
Tausayin Ammi ya kamani sosai,me yasa tun daga kan haihuwata har zuwa yanzu ya zame mata mabuɗin wahala? tun kafin ta haifeni ma tasha faɗawa wahalhalu kala kala,amman haihuwata sai ya ƙara wutar tsana tsakaninta da mama uwar gida da kuma Mama safiya,tun haihuwata har zuwa yanzu bazan taɓa tuno rana ɗaya da sukaji tausayina ba,ko amsa gaisuwata basa yi ni sai nake ganin ta wani ɓarin kamar gwara mama uwar gida akan mama safiya,sam ta tsaneni ni da Ammi na wai har cewa take ita da Ammi kishiyarta ce da ta daɗe da korarta,duk iya asirinta na sadaka yallah to ita ta dame ta ta shanye.
muna gama decoration ɗin mukayo hanyar gida ni da Ammi,muna zuwa gida muka tarar da wata masifar wacce tafi ta ɗazu yawa,don mama uwar gida ce xaune tana zuga baba,wai dama kusan ƙwana biyu haka Ammi take yi tana fita ba tare da sanin Abba ba,ina jiyo karaɗin miryarta tana ce wa"yo barewa za tayi gudu ne ɗanta yayi rarrafe? kaga tare ma suka tafi yawon,yo da haka ne ma fa zata koya mata yawon,daga haka sai kaji abu yayi girma ya girmi ne tarin tunani da kuma dattaku irinka,kai da ake ganinka malami ana ganin girmanka da ƙimarka duk sai ta zube saboda mummunan tsiron daya fito daga bara gurbi".
Duk bahaushe yasan abinda take faɗa,wato ni ce ma mummunan tsiron kenan? lallai tana son ta kaini maƙura wataran in kasa sarrafa jikina da harshena in faɗa mata maganar da har ta mutu ba zata taɓa mantawa dani ba.
Ammi ta kasa yin shiru har sai da ta ce"haba mama Uwar gida,me yasa kike haka ne? ai idan baki kare ni ba bai kamata kuma ki nemi tona asiri na ba,nasan ban kyauta ba dana fita ba tare da saninsa ba,amman ko menene ku kuka janyosa ke da mama safiya".
a'i da sauri ta ce"ke zulaiha uban me mukayi miki ni da mama safiyar? wani sharri kuma zaku ƙullamin? to duk sharrinki da tsanar da kike mana baki isa ki haɗa mana sharri ba,ƴar baƙin haure kawai".
Don kar a tona mata asiri sai ta shige ɗaki,Umma dake tsaye tana kallon ikon Allah ta ce"Zulaiha kinsan mlm baya son fita ba tare da an sanar dashi va,ki kiyaye ko don nan gaba".
tana faɗar hakan ta shige ɗakinta,shi kuwa Abba tuni ya shige ɗakinsa bai ƙara cewa komi,kamar yadda na faɗa muku a baya shi Abbana mutum ne mara son hayaniya,musamman akan matansa kowaccensu baya faɗa ta faɗa duk rashin kunyar mama uwar gida,saboda shi bai taso yaga ana haka agidansu ba,sannan ga iliminsa wanda shima ya ratsashi sosai.
ni da Ammi muka shige ɗaki muma,duk hankalinmu ba a ƙwance ba don indai Abbana yayi shiru to tabbas shirun nasa ka iya zuwa ya dawo,don kuwa ɗauke musu wuta yake baki ɗaya ya fita daga sabgarki,yanzunma hakan ce ta kasance don kuwa ɗaukewa Ammi wuta yayi baki ɗaya,sai da ƙer suka shirya don abinda na lura dashi Ammi ta riga da ta kanainaye Abbana,ko yayi fushi da ita baya iya yin nisa kuma tsantsar kulawa ce kawai ba wai asiri ba,don ko da Ammi ta haifeni ba zakace ita ce ta haifi ƴar budurwa me shekara 13 ba,sai ka ɗauka wata ƴar budurwa ce sabida tsantsar gyara da sanin ƙimarta na ƴa mace,shiyasa baya gajiya da ita sam tasan takan gyara jiki ta ko ina don har gyaran jiki tana yiwa amare,musamman ma awajen aikinta na ƴan hisba tana samun costumer sosai,don mata da yawa kan kawo mata koke koke akan mazajensu na wulaƙantasu a shimfiɗa,sai kiga nan da nan ta baki shawararwari sannan ta haɗa miki haɗin ƴar gata,wanda nima da kaina nasan wasu daga ciki.
an sanya rana ta da yaya Ahmad,amman shekara guda aka sanya Hajiya kamar za tayi hauka don cewa tayi babu wanda ya isa ya ɗaurawa ɗanta aure da ɗiyar mayu shuwa arab.
abu yayi tsamari sosai,don a yanzu haka ko gaisuwata ma Hajiya bata amsawa,ban damu da hakan ba don dama ko acan baya ba kullum ne take amsa sallamar tawa ba.
Yaya Zubair yana son Baby ƙawata sosai,amman ko da Hajiya tasan da hakan cewa tayi indai ya aure ta babu shi babu ita,don dama ita a yaranta tafison Ahmad,don duk abinda yace tayi shi take yi,saboda haka shiyasa ta sanya masa ido akan aure na don ba zata iya magana ba kamar ma tsoronsa take.
rana ɗaya Yaya Zubair ya juyawa Baby baya,duk da dama ta ɗan girme min amman al'adar gidansu ma da wuri suke aurar da ƴaƴansu tunda fulanin usul ne su.
Hajiyarsa tace indai matar aure ce zata nemo masa wacce take so,haka kuwa akayi don tuni ta nemo masa ƴar ƙawarta ashe dama ta daɗe tana sonsa me suna Balaraba,Hjy ta sani sarai kaf ƴan gidansu Balaraba ba suda tarbiyya ko kaɗan,yara ne masu bala'in jin kai da kuma yawon tsiya,ina ga gidan biki ko paty ga bin bokayen tsiya,don mahaifiyarsu ta koya musu duk halinta,ita da kanta idan ta fita tun safe sai dare take dawowa tana can tana yawon ta zubar,sannan uwa uba mahaifinsu bai isa yayi ko da tari ba don yana masifar tsoron matarsa,duk abinda tayi me kyau ne ko mara kyau ne haka yake haƙuri yaja bakinsa yayi shiru,don idan safiya tayi duk ƴammatan gidan da samarin gida ficewa suke daga su har uwar,shine yake zama agidan yana ɗan yi musu aikatau tun daga kan wanke wanke da shara,wankinsu duk shine ke yi idan kika shigp gidan kika ga aikin da yake yi sai kin zubar masa da hawaye tsabar takaici,kuma ahaka Hajiya ta rufe idonta tace dole sai Zubairu ya auri Balaraba,idan baiyi haka ba zata cire ta cikin ƴaƴanta,babu yadda ya iya da ita don Zubairu mutum ne me matuƙar biyayya ga iyayensa,don dole ta sanya shi sintiri hanyar gidansu Balaraba,amman duk sanda zaije sai ya yi azkar saboda wani turare da yake sanyawa sam bata sanshi,yaya Zubair likita ƙwararre na mata yana kallon Balaraba yasan ta gama yawon ta zubar ɗinta tun da kuwa gashinan har da tsarabar ciki.
ranar daya san tana da ciki ya yi nadamar fara zuwa wajenta sosai,ya rasa wanda zaiyi shawarar dashi,ranar muna falon Abiey sai ga yaya Zubair ya shigo,muka gaisa mu dukanmu amman da yake lokacin muna ɗaukar karatu ne awajen Abiey ɗinmu,ni da Baby sai kuma Rabia,ƴar gidan maka uwa gida don kaf cikin ƴaƴanta ita kaɗai ce muke ɗinya sosai,ma ana munfi shiri da ita don ita ce tayo zyciyar Abiey a yaranta.
ina kallon Baby tana kallonsa tana hawaye,don har ga Allah tana sonsa sosai kuma shima yana sonta don dai anyi musu fin ƙarfine kawai.
bayan mun gama karatun ya gaida sauran matan Abiey sannan ya shigo ɗakin Ammi,alokacin tana kan injin saƙarta tana yi,ya samu waje ya zauna ni kuma na kawo masa zoɓo rodon da Ammi ke siyarwa don rufawa kai asiri,na haɗa masa har da fankasau ɗin da tayi.
ya yimin godiya,ina shiga ɗaki naji yana faɗa mata abinda ya sanyani firgita sosai,na sakko daga kan gadon Ammi gabana yana faɗuwa sosai,duk da ba nida wayo amman ai muna karanta komi a makaranta sannan tun ina shekara goma na fara haila,saboda haka Ammina ta sanar min da komi,na in kula da maxa kada na zama me wasa dana miji ko da kuwa wanda zan aura ne,hakan yasa na zama me taka tsantsan da kuma kula da kai,amman duk da haka ya Ahmad na ƙoƙarin taɓa jikina ni ce dai me kiyayewa ammanshi awajensa sai naga kamar wata wayewa ce.
sosai na tausayawa ya Zubair,Ammi ma ta tayasa jajan abin sosai ina juyota tana ce wa"sai haƙuri ɗana,nasan abin da zafi kuma da muni kuma ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya,in sha Allah zaka zama me nasara arayuwa,sannan kafin ka aureta ka ɗauketa kuje ayi muku gwaji,don gudun faɗawa cikin matsala hakan kuma zai zamar maka kariya don ita guguwa idan ta taso babu me iya kareta sai Allah,hannu ko waji mahuci ba zai taɓa yi maka garkuwa ba,sai dai ka nemi zaɓin Allah sannan ka dage da nafilfilu da kuma roƙon Allah shima wata madogara ce".
murmushi yake me haɗe da ƴar dariya,duk da ba wai zuciyarsa tayi 100%100 ba amman kuma yana jin kaso hamsin ya tafi,don tun da ya fara neman shawarar Ammi bata taɓa jefasa acikin matsala ba,sai dai ta fito dash dumu dumu aciki.
*** *** ***
Fulani ta kallesa cike da takaici,hawaye wasu na bin wasu ta nunasa da ƴatsanta ta ce"haƙiƙa Haidar da haihuwarka gwara ɓarinka,tabbas sa nasan zaka shigo cikin duniya ne don ka ruguzawa al'umma tarihi da kuma jin daɗi da na hanaka zuwa,sai dai ba nida wani ikon yin hakan baka taɓa faɗamin abinda ya zama na ƙarya ba,amman a wannan karon ka yimin ƙarya mafi muni arayuwa,bana son inyi maka mummunan fata,amman inason ka gaggauta barin garin nan don wallahi idan ina kallonka zan iya tsine maka kabi duniya".
sosai yake kallon mahaifiyarsa cikin mamaki,don gani yake tamkar de ba ita bace canja masa ita akayi,sai dai ganin Aamiru da yayi awajen ya tabbatar masa da cewa tabbas Aamiru ya sanar da mahaifiyarsa komi,takaici da kuma nadamar ɗaukar Aamiru amatsayin abokin sirri shiya ƙara haɓaka adadin ɓacin ransa,ya tako cikin takunsa me matuƙar sare zuciyar ƴammata,ya riƙe hannayenta duka biyu ya kalli cikin ƙwayar idonta waɗanda suka cika da hawaye sannan ya ce"Nisful hayat,me kuma nayi? waɗannan wasu zantuka ne suke fitowa ta bakinki me albarka? menene ya zafafa zuciyar da take cikin sanyi da sanyayawa? ki faɗamin Nisful .............."
A'i bai ƙarasa faɗar abinda zai faɗa ba,ta turesa gefe har sai daya kusa haɗuwa da tibin bangon da ta kusa cika tamkeken falon,Aamiru ya taho da sauri zai taimaka masa,ai kuwa shima da sauri ya cakumo sa ya shaƙesa sosai,asalin kalar Galadima ta fito ya ce"Aamiru ayau ne nasan dawa nake xaune? ayau ne nasan kai munafuki ne wanda ba a sirri dashi,lallai ka cika maha'inci kuma mayaudari,amman abinda nake son ka sani ni nawa sirrin daka bayyana cike take da securities da kuma ikon Allah,kai kuma naka sirrim a hannuna yake ko yanzu nayi niyya zan tona maka asiri za kuma kayi dana sanin wannan abin da kayi min".
yana faɗar hakan ya fice fu,don yasan halin mahaifiyarsa indai tayi fushi alokacin babu me rarrashinta sai me martaba,zai je ya tonawa kansa asiri awajen mahaifinsa,ya kuma buɗe masa cikinsa wanda dama acan baya damar hakan yarasa ko Allah zai sa ya samu me jin tausayinsa.
yana fita Aamiru ya rasa yadda ze yi,don kamar yadda Galadima ya faɗa nasa sirrin yana tafin hannunsa wanda kuma ya tabbatar da nasa yafi na galadiman,amman ya ze yi da rayuwarsa? wani mataki zai ɗauka don kada hakan ya tabbata? idan kuwa ya tona masa asiri ya gama dashi.
*** *** ***
uwar gidan sarki,ta miƙe tsaye asanda take kallon wani bidiyo awayarta,ta tuntsire da dariyar cikakkiyar ƙeta tana ce wa"good! tabbas yanzu ne na samu wani makami da zan fito yaƙi dashi,ba tare dana ji wani ɗarr ko tunanin komi ba kyauta, inason ki ɓoye wannan bidiyon kamar yadda zan ɓoyesa,nayi hakanne don ki zamar min shaida don kuwa me martaba baya komi sai da shaida".
wacce aka kira da kyauta,ta ɗan murmusa gami da tsugunnawa ta ce"an gama ranki shi daɗe duk yadda kika ce haka za ayi,kuma ina yi miki albishir da zan dinga bankaɗo miki wasu sirrikan da suka fi waɗannan,ke de kawai ki zama me bani goyon baya ɗari bisa ɗari".
Murmushin gefen baki tayi,irin na cikakkun sarakai sannan ta ce"kyauta,kina yi mana gandarki ne akan bama baki goyon baya? nada ma da kika saba bincikomin basu yimin bane sai yanzu ne kika ganomin wanda nake so".
ta ɗakko bandir ɗin kuɗi masu yawan gaske,ta sanya mata akan mayafinta sannan tayi mata nuni da hannu alamar ta fita,babu musu kuwa ta amsa ta fice da sauri har tana haɗawa da ɗan gudu don yau bokanyarta zata samu kyakkyawan labari.
tana fita ta kyalkyale da dariya tana ce wa"Fulani ke da ɗanki kun shigo hannuna,sai na tarwatsa muku dariya kun zamo tamkar baku wanzu ba a doron duniya,sai na shayar dake baƙin cikin da kika shayar dani ni da ƴaƴa na"...........soon➡️
***
ga masu son joining ɗin grp faccala,zasu iya bin wannan link ɗin na ƙasa bana son maza a grp sannan bana son ƴan masu turo ba tsa.
***
XEN6TlUzv4BA
*MRS GREEN CE✅*