Chapter 11
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*11*
*Zariya*
Laraba.
Abubuwa biyu ne suka min tsaye a kahon raina a kwanaki nan.
Na farko yau kwanaki biyar cur mutumin da ke siyan Danwaken Sannan kuma ya kuma bar min chanjin naira na gugan naira har Dari biyu ya daina zuwa.
ina lissafe tun Alhamis da ya aiko aka siya masa bai kara dawowa ba har ga shi yau talata. Tun safe na ke duban hanya ammh shuru har su datti na kira na tambaye su sukace suma sun daina ganinsa yana zuwa. Acikin raina na ke ta faman wasi wasin to lafiya?
Wata zuciyar kuma ta kwab'eni da cewa"Hasiya kada zak'ewar ki ta cika yawa fa."
Nima sai daga baya naga na zak'en gaskiya mutumin da ban taba sani ba me yasa zan damu kaina Saboda shi? Sai wata zuciyar tace min ko ban san shi ba Cinikayar ya had'amu kuma sanin Mu'malace ka yi cigiyar abokin Cinikaryar ka.
Tun Safe da na zauna kujeran saka Danwake a tsakar gida na ke ta famam duba kofar gida da naga yaro ya shigo sai na Dauka shine, ammh kuma rashin ganin yar kular da ya saba aikowa ke sakarmin da gwiwa.
Maganar gaskiya ina cikin zullumi Ajiyar rai na sauke lokacin da Goma ta gota na gama Saka Danwake gabadaya har ya kare iya wanda zan ci kad'ai na rage.
Shi kuma abu na biyun da ke damuna Salisu ne! Ya na yawan Fad'omin a rai a kwanaki nan jiya har mafarkin sa nayi. Wai mun had'u na gaishe shi ya ki amsawa naga Musabahu a wajen da ya ce masa"Salisu Hasiya ce fa ke gaisheka ka yi kamar baka ji ba."
Kai tsaye naji muryan Salisu na Fad'in"Bazan amsa mata ba Musbahu koma miye faru. Bai kamata na kwanta Jiya Hasiya taki gaisheni ba."
Daganan na farka ina ta faman zufa. Tun daga lokacin zullumi na ya karu akan na baya. A bakin Mamam boy nake jin sun koma asibiti an kara Dubashi an ce sai karfen jikinsa ya shekara za'a cire masa.
Maman boy Idon gari ce ka rasa ina take samun wasu labaran, ko da ya ke Gantali ce da ita ba inda kafarta baya shiga da mijinta ya fita itama ta ke saka kafa ta fita kusfa kusfa a samaru nan anguwar Tsamiya Da'i da'i kun gidaje ne Maman boy ba ta shiga ba. shiyasa akwai labaran gidajen mutane da dama abakinta.
Nasan ko giyan wake na sha ban isa na dauki Siraran kafafuwana zuwa gidan Salisu da sunan gaishe shi ba. na tabbata Sahura sai ta kasheni kamar yadda ta kudurta in kuma ban mutu ba to tabbas zan samu manyan Rauninka da zan jima cikin Doguwar suma. tuna haka kad'ai kan kwabar da Niyyata ko Amma na kasa gayamata zuciyata duk da ta ganni suku suku da ta tambayeni sai na ce mata ban jin dad'i da Safen ne.
Amma na da wani irin hali ko ya ya na ke cikin damuwa ta sani sai da ta kalleni cikin Nazarina kafin ta kad'a kai tana fadin"Ko ulcer d'in ki ce zata tashi?
Kai tsaye nace mata"In ma itace ina da Sauran magunguna na ruwa da na kwayar sai na sha."
Kai tsaye itama tace min"In bazaki Jefa Danwaken nan ba a hakura yau Hasiya."
Ban bari ma na ja mganar da ita ba. Taga na mike na fara had'a kayan yin Danwaken sai ba ta kara mgana ba Ammh ta jima ta na kallona ta kuma san tabbas wani abu na Damuna to ta ina ma zatayi Tunanin bazan damu ba. Damuwa a gareni ta zama Tilas ko domin yadda na zama abun gudu da kyama wajen jama'a.
Ramatu na ke son gani ko zan gayamata cikina ta ba ni shawara, Shiyasa ina gama wanke wanken kayan da na bata, bayan na kai Daki na zo na saka ruwan zafi a rushin da na rage na leka Dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta zan kira Ramatu.
Kai tsaye tace min"Gaskiya ba kudi acikin wayar"
Cikin mamaki nace mata"Ba kud'i? Ba shekaranjiya na saka Dari da zan kira Adda Fati ba? Kuma ba mu jima mu na mgana ba. Na dai san ban isa cinye wannan Darin ba."
Cikin tabe baki tace"To ni dai bansani ba, ban kira kowa da shi ba."
Ban kara mgana ba Na karb'i wayar na juya ban ko tsaya duba kudin wayar ba na leka kofar gida na kira Salihi na Dauki Naira dari da goma cikin cinikin Danwake na ce ya ruga ya siyomin Katin Mtn ya yi Sauri.
Sanin Halin Salihi da aikensa da sai ka mamta da shi ya ke dawowa yasa na koma Daki na fara kanta shi zan gyara Amma na saman gadonta barci ya kwasheta itama duk sai a hankali kwanaki nan da zazzabi ta ke kwana.
Har sai da na gama na share daki na wanke bayi saboda bazan iya shigarsa haka batare da na wanke ba. Na juye ruwa na yi wanka na fito na sauya kaya sannan Salihi ya dawo, Allah ya taimakeni ma ya kawomin katin lafiya.
Ina gama Loda katin na kira Ramatu daman na Haddace lambarta bayan ta Dauka mun gaisa da tambayan su Amma da Noor nace"Ke ina son ganinki kina gida gobe..?
Da zumud'i tace"To ni kuma ai goben nake shirin zuwa miki Yini ni da Noor. Gidan Inna zan kwana da Sassafe tahowa kawai zan yi"
Cikin jin dad'i nace"To shikenan ma sai kin zo d'in. Ki gaida inna Talatu"
Kai tsaye tace"Zata ji nima ki gaidamin da Amma da Habi auta."
Daganan muka yi sallama. Jin tace zata zo sai naji dadi a raina.
Ban koma na zauna ba sai da na Mayar ma Maman boy wayarta sannan na dawo na saka Danwake da manja da maggi naci.
Ganin Amma nata barci yasa na kwashe yan kayanta da suka yi datti na Daureye mata da nawa na aikin Danwake. Kayan ba su da yawa tunda wanchan Sati Habi ita tayi mana wankin kayan duka ranar Sati tunda ba makaranta.
Su datti na bama goma goma suka Debemin ruwa a waje. Ina mamakin yadda matan gidanmu ba su damu da sanya yaransu a makaranta ba sai dai su bar su su yi ta gararamba a gari ba arabi ba boko. Na taba yin musu mgana Maman Salihi tace min da na abinci za su ji ko da na kudin makarantarsu daganan sai na Rufe bakina. Duk da sai ayi abu Dari ban saka bakina ba yanzu sai kiji gori na tashi ni da ke da ababen gori gasusan kaca kaca.
Kwanakin nan ma da na ga Kaltume na jin Haushina daga ni har Amma bata kulamu kawai saboda mijinta na son Danwake na,ya kan siya ya ci kafin ya fita sai ta fara adawa da ni kai Tsaye kuma ta same ni ta min mgana cewa bata son na kara saida ma Mijinta Danwaken mu in tace bata so kawai a barshi kada rayuka su baci.
Amma na jin haka tace a barshi kawai saboda Kaltume ba ta tsoron Tijara Tundaga ranar ban kara saida masa ba ko ya aiko zan ce gabadaya an siye shi ba bu. Daganan na samu lafiya,ammh har alokacin bata daina min gani gani ba ita a tunaninta kada Mijinta yace ya na sona na saka ta uku ni kam a raina nace ta ya ya zai ce ya na sona? Shi kan shi ai baya so ya shiga cikin ukun ba.
*****
Washegari saboda zuwan Ramatu sai ban kwab'a danwake da yawa ba. Tunda tace min sabon gari ta kwana kenan zata iso nan da wuri, shiyasa tun safe na tashi na fara aikin Habiba ta taimakamin da wura gawayi ni har ta sakamin tukunyar Farko.
Daga baya na amsheta ta shiga wanka Saboda tafiya makaranta.
Cikin ikon Allah yau sai ga Mutumin ya aiko Datti da gudunsa ya zo min da kular ya na washe baki ya ce"Adda Hasiya ga Mutumin nan ya zo"
Bansan dalili ba sai da naji wani sanyi a raina na karbi kular da Sauri tare da dubu d'ayan da ya ke ba ni.
Ga mutane na layi ammh sai da na saka masa sannaan na mika ma Datti ina Fad'in"Ka ce masa mai Danwake tace lafiya kwana biyu bai zo ba?
Sai Faman mirmishi na ke yi ni kadai Har sai da Datti ya Dawo yana cemin"Yace tafiya ya yi shiyasa."
Kad'a kaina na yi a fili nace"Haba shiyasa naji sa shuru ashe.."
Har Datti ya juya na sake kwalamasa kira ya dawo na kallesa kafin nace"Tambayarka zan yi. Mutumin nan da ke aiko ka yaro ne ko babba?
Da Sauri Datti yace"Kai Babba ne fa."
Ya fad'a cikin nuna yarintarsa.
Da gudu kuma ya fita ya barni ina mamakin kaina na miye nawa na son sanin yaro ne ko Babba?.
Yau cikin Nishad'i na cigaba da Saka Danwake na zuwa tara na gama komai na share wajen, sannan na wanke kwanukan da na taba girki zan yi saboda zuwan Ramatu. Ammh sai nace bari sai tazo kada na Dafa ya yi sanyi.
Amma na fara saka ma ruwan wanka na juye mata ta yi tunda jiya bata samu yi ba, kokon da na Dama mata na sha nima tunda ba shi da Tsami sai waken da na saka masa manja kadan naci saboda kumburin ciki.
Kafin ta fito wanka na gyara dakin na Share ta na fitowa nima na shiga na yi, koda na fito na isketa ta shirya ta na zaune ta na shafama kafafuwanta man zafi.
Cikin yanayin mganarta tace"Hasiya nace ki siya ko karamar waya ce. Ta na da amfani tunda ga shi ina ta son na kira Adda mu gaisa ba wayar da zan kirata."
Ina shafa ma jikina Vaselin nace"Amma zan siya. Ki bari riban ya kara taruwa ba na so na taba ne kuma mu shiga har uwar kudin"
Amma ta yi mirmishi kafin tace"Hasiya ina zaki kai wannan tattalin naki?
Dariya na kyalkyalce da shi kafin nace"Amma rayuwar nan sai mutum ya iya tattali ballatana yadda Tsadar rayuwa ya kara Hauhawa."
Amma ta jinjina kai kafin tace"Hakane ina miki Fatan watarana mijinki ya Mori wannan Tattalin naki da hangen nesan da Ubangiji ya mallaka miki su Hasiya."
Na ji add'aunta acikin raina na amsa da Ameen batare da na ji acikin raina hakan zai iya kasancewa ba.
Na riga na Sadakar na gama aure a Duniya baxan kara yarda na auri wani ba. Ballatana nazo na zame masa matsala a rayuwarsa. Iya bakin Fentin da shafa ma kaina Dalilin Aure ya isheni ba na kuma Bukatar karin wani Tozarcin.
Amma itama ta Fahimceni sai ta sauya Hirar zuwa ta Adda Fati ta na Fadin"Oh Fati shuru kwana biyu bata zo ta dubamu ba."
Ina Zura Doguwar riga a jikina nace"kinsan ta yi ta fama da Zazzabi ita da yara. Ta na samun Sarari zaki ganta, Adda Rukayyace ma naga kwana biyu yan ganin Damanta ba su turo ta zo ba."
Amma tace"Itama sai da nayi mganarta a raina. Allah yasa suna lafiya su da iyalansu"
Ina Daura Dankwali nace"Amma lafiya ke shuru fa. Suna nan lafiya da wani abu ya faru da mun sani."
Amma na shirin mgana mukaji sallamar Adda Fati suna gaisawa da su Maman Boy.
Na kalli Ammi ta kalleni kafin nace"Amma Muryan Adda Fati ce fa."
Amma tace"Baiwar Allah ina ta zencen ta sai ga ta"
Ta na ko dago labule ta shigo nace"Kinsan yanzu Amma ke mganar ta ji ku shuru ke da Adda Rukayya Allah yasa kuna lafiya"
Ta na Sauke goyon Hanifa da ke bayanta gefen Amma lokaci daya ta na Fadin"Zazzabin da muka sha ne da yara duk jikina ba Dadi. Babansu ma sai yau ya fara fita aiki. shi har da Basir ne ya tasar masa."
Ni da Amma muka had'a baki wajen fadin"Subhanallah." Na dauki Hanifa sai naga barci take yi na mikama Amma ina Fadin"Habi ai tace har Hanifa ta sha Zawon hakuri."
Adda Fati tace"Sosai ammh duk mun samu sauki su har sun tafi makaranta shima yau ya tafi na gaji da zaman gidan nace bari na biyosa ya saukeni agida kawai na duba ku."
Ledan da ta shigo da shi ta mikama Amma tana fadin"Sabulai ne da Manshafawa Amma. Ba kudi ne duk mun cinye a asibiti"
Amma tace"Bakomai Fati. Allah ya yi albarka ya azurta mijinki da kudin Halal ya shirya muku zuru'a."
Muka amsa da Ameen Ameen.
Kallona ta yi kafin tace"Hasiya wlh rashin wayarki na damuna kana son mgana da ku ammh sai ka kira makota."
Amma tace'Nima tsiyar da na ke mata ko da yaushe kenan. Kinsan ta da rashin son kashe kud'i ba Dalili."
Adda Fati tace"Kamar wata ma'aikaciyar gwammati ba. Komai ace sai an yi shi cikin Tsari."
Dariya kawai na yi bance komai ba.
Ina kusa da Amma ina kallon Hanifa da ke hannunta ta na barci.
Adda Fati ashe kallo na ta ke yi sai da na Dago muka had'a ido cikin ware mata ido nace"Na yi miki kyau ne wannan kallon fa Adda Fati"
Adda Fati tace"Kin kara fari ne sannan atamfar nan ta na yi miki kyau in kika sakata"
Na bi Atamfar jikina da kallo wata Bakar Atamfa ce Chiganvy baka da Fara ce tun ta akwatin aurena da Abubakar ne. Ba tun yau ba in dai na saka Atamfar ne sai mutane sun ce ta na yi mini kyau.
Dukkansu ni suka bi ni da kallo, ni kuma tuna Abubakar yasa yanayi na kawai ya sauya Amma ce ta ce"ki gayamata ta rage tunani baki ga ta na ta ramewa ba ne"
Adda tace"Amma Hasiya fa daman ka shi da rai ne. Tunanin rayuwa kuma Dole ne Amma. hasiya ki yi hakuri In sha Allahu Mijinki na Har Abada ya kusa zuwa. Wanda zaki Daura kayansa ki yi ta Daurawa har Abada."
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana Ameen din ma wannan karon ban ce ba.
Hira Amma da Adda Fati suka cigaba da yi ni kuma sai na jingina da Bango na fada kogin Tunanin irin Rayuwar da muka shinfida da Abubakar. Sai ga shi cikin wattani uku komai ya zama Sai Tarihi. Tunanin da na lula yasa ko sallamar Ramatu ban ji ba sai da naji Challara kukan Noor sannan na san har ta iso. Na bita da kallo har ta zauna kusa da ni ta na gaida Amma Noor kuma na Hannun Adda Fati har ta fara kuka.
Cikin kasalan da ya Rufeni nace"Yaushe kika shigo.?
Tana mirmishi ta kalleni kafin tace"Lokacin da kika shiga kogin Tunani mana"
Sai kawai na yi mata mirmishi. Ta shi nayi na je na Debo musu ruwa. Na Dauki Dubu daya na fita tsakar gida ba yaran sai na leka waje Hamisu na gani yayan Salihi shi na ba ma wa nace ya siyomin lemun panta guda Biyu.
Ban dawo ba sai da na jirasa ya dawo sannan na Dawo Dakin. Na ijiye mata a gabanta duka ta kalleni ta na fadn''Ji don Allah kamar wata bakuwa."
Ina Hararanta nace"Eh mana ke ai bakuwa ta ce mana ko Amma?
Amma tace"Ni ma Ramatu bakuwatace. Ammh kuma yar gida ce Tunda diyata ce"
Adda Fati tace"Kwarai kuwa. Hasiya karbi yarku mai kiyuya."
Ina Dariya na karbi Noor ina mata wasa. Fita na yi waje in da su Maman Salihi suke ganina da Noor yasa maman Boy ta karbeta tana Fadin"Yarinyar ta yi yawo fa".
Yake nayi kafin nace"In ba damuwa zamu zauna a dakin ki ni da Ramatu maman boy."
Cikim Fara'a tace"Haba Hasiya me zai hana? Na taba miki shamaki da Dakina ne?
Karaf Maman Salihi ta karbe da Fadin"Ballatana ni. Ko ya'yana ban muku shamaki da su ba, aike ko gaban anguwan nan ne ta aike su zasu je."
Mirmishi nayi kafin na karbi Noor ina Fadin"To nagode"
Na juya naji Kaltume da ke jajjagen kayan miya tace"Uhm ku dai bi a Hankali kada mu ji gobara ta fara bin Dakuna."
Ina mamakin meyasa Kaltume ta ke wasa da Kaddara ta? Ko don ita yarinyace domin ko haihuwa bata tabayi ba shekararta daya ne da wani abu a gidan bata wuce sa'ata ba ga rawan kai ga munafunci ga Gulma.
Ni dai shigewata daki nayi ban biye mata ba na iske Ramatu da Adda Fati na ta Hira. Zani na Dauka na goya Ramatu na Dauki mata lemonta nace tazo muje Dakin Maman Boy.
Ba musu ta taso ta na ce ma su Amma'"Adda bari mu je"
Suka amsa mana da Toh.
Dakin Maman Boy muka shige na saki Labule na san su da Dabi'an labe.
Daman mun shige mun bar su da mgana a bakinsu.
Zama muka yi a kujera d'aya ina ta kallon Ramatu ta yi kiba kamar ba ita ba Taga kallon ya yi yawa ta Zungureni ta na fad'in"Kallon fa kinga na sauya miki ne?
Kai Tsaye nace"Kin yi kiba Ramatu kin yi fari sosai ma sha Allah."
Ramatu tace"Alhamdulillah. Ammh kinsan har da Jego ko?
Ina Hararanta nace"Wani jegon? Mata kina neman wata biyar da Haihuwa kina kiran Jego kawai dai yayana ya iya kiwo ga Noor ma ta yi bulbul ta yi yawo."
Ramatu tace"Gaskiya kam baza'a raina ma yayanki ba. Yana ji damu sannan ya na kula damu yace na gaisheki ma sosai."
Ina mirmishin jin dadi nace mata ina amsawa. Nan muka shiga Hira har da Shewa sallah kadai ya tadamu girki ma Adda tace na bari zata girka.
Me zata Dafa? Nace muna da Sauran Taliya ta Dafa mana Amma na son ta da wake ta manja.
Tace to kafin ma ta Dora Biyu tayi sai ga Habiba ita ta karbi girkin. Cikin lokaci ta gama sai da muka ci muka natsa Noor ma Habiba ta karbeta mayya yara ne ina ta mata Fad'an ina zata kai yara har Biyu ga Hanifa ga Noor ta na Dariya tace"Kai Adda na iya fa renon yara kema ki bari ki Haihu ni zan renan miki ya'yan ki."
Mirmishi kawai na yi kafin nace"Habi ni ai bazan haihu ba ballatana ma ki renin ya'ya na ammh dai ga na su Adda da su Ramatu sun isheki Reno."
Ba Ramatu kadai ba Hatta Habiba sai da ta tsaya ta na kallona.
Ramatu ne tace taje kawai ta na Fita ta juya kaina ta na min Fad'a cikin Masifanta tace"Haba Hasiya. Shikenan sai ki cire rai da Rahmar Allah? Wa ya fada miki bazaki yi aure ba? Sannan wa ya fad'a miki ke ma bazaki Haihu ba?
Kai Tsaye nace"Komai a bayyane ya ke Ramatu kada ki yi kokarin Lullube abunda bazai taba lullubuwa Saboda ina taki ba. na sani kin sani, Ba bu wani Namijin da zai so ya aure ni ya auri Bala'i masifa da shiga uku da kudinsa ba Ramatu, ba bu wannan Namijin"
Kai Tsaye Ramatu tace"Akwai shi. akwai shi Hasiya."
Cikin Idanuwana da suka cika da kwallah na kalleta kafin nace"Akwai shi fa kika ce? To in akwai shi yana ina?
Shuru ta yi cikin wani yanayi kafin tace"Ya nan a inda Allah ya ijiyesa Hasiya. Kila kusa dake ko kuma nesa da Duniyarki. Ammh tabbas nasan akwai wannan Namijin. Namiji irin Salisu sannan wanda ya fi Abubakar Jarumta da Tausayi namijin da yasan Babu mai yi sai Allah ya kuma san Kaddara ce ke bibiyan Rayuwarki ba Canfi ba"
Kalamanta suka sakani sai da na Murmusa kai tsaye nace"Kada mu yaudari kanmu Ramatu ba bu wannan Namijin. ko zai amince da ni Ahalinsa bazasu taba bari D'ansu ya auro Jaraba da kudinsa ba."
Ramatu tace"ni kuma ina ji ajikina Hasiya bazaki Dauwama ahaka ba. Namijin da na Fada miki koma waye zai zo. Zai zo in sha Allahu"
Cikin Sauri nace"Zai zo? Yaushe..?
Ramatu ta kalleni cikin Rauni kafin tace"Bansani ba Hasiya.. ammh nasan Allah zai kawo sa."
Ina jin kalamanta sai nima nawa kalaman bakin suka kare cigaba da bani baki tayi ta na ta faman Lallashina.
Shine ma na sake har na gayamata mafarkin da nayi na Salisu. Kai Tsaye tace"Kada ki damu Salisu bazai taba Zargin ki ba ai yasan abubuwan da suka Faru ya tabbata ke ma kina kokarin kokuwa da Kaddaran ki ne."
Sai na gyad'a mata kai alamun gamsuwa shiyasa ta cigaba da Fad'in"Saboda haka ki kwantar da Hankalin ki Salisu zai warke kamar wani abu bai taba samunsa ba."
Da Sauri nace"In sha Allah.."
Muna nan muna mgana sai da aka kira la'asar muka koma Dakin Amma muka yi sallah mun idar kenan sai ga Kiran Adda Rukayya ta wayar Adda Fati bayan sun yi mgana aka bama Amma suka gaisa suka yi mganan da za su yi sannan suka yi sallama.
Sai alokacin Adda Fati ke fad'amana Ranat asabar Adda Rukayya zasu tare a Sabon gidan da Mijinta ya gida anan Gaskiya. Sannan tare da Birthday din Cikar Amna shekara Shidda Shine ta ke fad'ama Adda Fati tace ta fad'amana jin ma tana gidan sai tace ta bama Amma ta yi mata mganar Habiba tazo Ranar Jumma'a ta tayata parking.
Dukkanmu mun yi mata Murna. Adda Fati tace"Ramatu ki fad'ama Inna Talatu Ranar sati sai mu je mata Murna."
Ramatu tace"Zan fad'a mata Hasiya ki shirya muje.."
Zan yi mgana kenan in ce bazan je ba Amma ta yi saurin cewa"Zaki je mana Hasiya. Yanzu ma sai da tace na fad'a miki tana jiran ki."
Na sha mamakin wai Adda Rukkaya na jira na, matar da Tsoron fad'an mijinta ta ke yi sama da ni yar'uwanta.
Ganin yadda na yi ne yasa Adda Fati da Ramatu suka rika Tausana da kada na Damu yar'uwata ce Rukayya ban isa na sauya ma wannan alakar tamu suma ba jinina ce.
Da kalaman bakinsu yasa nace na amince zan ce batare da Tunanin wani irin Tozarci ke jirana in na shiga cikin sha'anin da ban saba shiga ba.
Sai Yamma Adda Fati ta tafi, Ramatu ta riga ta tafiya tunda ita gida zata koma.
Naji dadin zuwan Ramatu ko banza ta Debemin kewa tare da Shawarwarinta masu amfani.
****
Tahir bai dawo ba sai Ranar Jumma'a Da Safe ya je wajen aiki ko da ya dawo ya iske shi.
Ya san muhimmamcin sallama a musulunci an kuma ce in kai kaje to kayi ma wanda ka iske sallama. Shiyasa ya yi masa sallama ya kuma ba shi Hannu suka yi musabaaha. Yadda Tahir bai sakar masa Fuska ba shima haka ya yi masa gim da ransa.
Abu d'aya ya Kudurta ko kwashe kayansa Tahir ya yi zai sauya wajen zama bazai taba ce masa don me ba? Saboda sanda ya zo suka zauna Tare ba shi ya Kirasa ba Ra'ayinsa ne yanzu ma in yace zai sauya wajen zama bazai taba zama Takura ga Ra'ayin Tahir ba. Shi dai hakkin zaman tare ya Cire sannan ba zai fasa gayama Tahir gaskiya ba.
Duk da yasan shakuwa da Amintar da ke Tsakaninsu bazai saka su yi nesa da juna ba. Dole daya zai nemi daya kuma ya na Tabbacin ko kwashe kayansa Tahir ya yi ya na da tabbacin sai ya Dawo Domin bai saba da kowa ba sama da shi shiyasa bai damu ba ya shiga Harkan gabansa.
Yau da Danwakensa yaje wajen aiki ya ci a chan bai dawo da Saura ba Duka ya cinye. Ya ji kimar mai Danwaken nan ta karu a idonsa Matar mai mutumci ne tasan Daraja Costumominta tunda har ta iya lura da ya yi kwanaki bai zo siyan Danwake ba har ga Allah abun ya yi mishi dadi a ranshi.
Wata zuciyar ta fad'a masa ka sani ko itama ta na da manyan ya'ya dole ta damu da ya'yan wasu. Kawai Tunaninsa ya fi ba shi mai Danwaken nan Dattijuwa ce uwa kuma Rayuwa da yanayin da ake ciki ballatana ga ire iren anguwan nan sai a hankali zaka ga kowa na sana'a domin Dogara da kansa.
Kuma a tunanin Sadiq a irin su Sana'an Danwake, Kuli abinci haka na Dattijai ne yara kuma sai dai in su awara, Dankali da Sauransu. Bai taba kawo ma kansa matashiyace ke Danwaken da ke siya ya na jin Dadinsa ba.
Tahir da kansa tun a daran ya gaji da cin mganinsa ya sauko ya na masa mgana bai kuma tambayeshi ba ya fad'a masa kano yaje gidan Jb.
Sadiq bai yi mamaki ba daman ya na kallon Wani Turkish Drama ne a laptop dinsa ya Tsaida yana Sauraransa Tahir din.
Cikin Tattausan lazafi yace"Fatan ya na lafiya..?
Tahir ya sauke wayar Hannunsa ya na Fadin"Uhm kai kasan me? naga abunda ka ke gayamin Jb fa ya lalace mata haka ya ke kawowa gidan ana shaye shaye ana lalacewa."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ba sabon abu ba ne."
Tahir yace"Ni ai ban zata haka ya lalace ba. Wlh da gudu na had'o kayana na dawo nima ya fara kokarin Tusamin lalacewarsa har da cewa zai kawomin yan mata Biyun da zasu rika tayani kwana kafin na dawo."
Sadiq ya gyada kai ya na kallon Tahir kafin yace"Me yasa baka karbi' tayinsa ba.?
Tahir ya harareshi kafin yace"Ni dan iska ne Sadiq? Haba haba dai."
Sadiq ya ce"Ok ashe yanzu ka Fahimci mganata. Da nace ba matsayin ku d'aya da Jb ba."
Tahir yace"Na Fahimta. Sorry Abokina Sharrin Shedan ne."
Sadiq yace"Is ok.."
Daga haka ya cigaba da kallon Tahir kuma ya Dauki wayarsa ya na Fadin"Usman Mb na gaisheka."
Kai Tsaye Sadiq yace"Mun yi chart da shi dazu ina wajen aiki."
Tahir yace"Oh nima jiya muka yi mgana da shi."
Daga haka Sadiq bai kara mgana ba, ya cigaba da kallonsa Tahir kuma ya cigaba da latsa wayarsa.
Washegari asabar da gyaran Daki Sadiq ya tashi da kuma wankin kayansa. Tahir na kofar dakin kan jakar ruwan da suka siya ya na kallon Sadiq ya tube dagashi sai 3Quater wando da Karamar riga ya na wankin kayansa.
Cikin takaici yace"gaskiya ka na cutar da Magajin gidan nan da ake kiran ka. Wanki fa ka ke yi da kanka."
Sadiq kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Eh mana ai ban fi karfin wanki da kaina ba. Ko daman chan lalacewa ne ace mutum ya zauna yace komai sai an yi masa, kuma nagaya maka mai wankin nan baya min wanki mai kyau. Sannan ga batar da kaya wanduna na nawa ya ce bai gani ba? Har fa wannan wandon farar shaddar tawa ya bace kuma zencen kenan."
Tahir yace"To ba sai ka yi masa kashedi ba..?
Sadiq ya yi tsaki kafin yace"Sai dai in a cikin kunnensa zan zuba kashedin sannan sai ya ji."
Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Tsiyana da kai fushi. ni kam bazan iya ba. Ga ruguna na had'e da boxers dina na kawo ka wankemin?
Sadiq ya dago ya na nuna ma Tahir kwatan dake gabansu lokaci d'aya yana fadin"Kawo Tahir. Kwata ta kwashi nata rabon."
Tahir ya dage baki kafin yace"Mugunta phone store Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi."
Sadiq yace"ba ka ga mugunta ba sai kaga fararen rigunanka acikin kwata."
Dariya suka saka gabadaya. Tahir na zaune har Sadiq ya gama wankinsa ya shanya suna da Igiya nan bakin barandansu saura kuma kananun kaya a daki ya baza saman akwatinsu tunda igiyan bata da girma.
kuma ba shi kadai ya yi wanki ba Tahir dai bai yi ba son jiki shi dai ya fi gane ma ya kai wanki a kawomasa a goge acikin Leda shi kuma Sadiq yace ya gaji da Hannunsa ba mai kara saka shi ciwon baki.
*Janafty*