3…Ubaida are you ready for it?
by @hafnancy
....Saida Addah ta gama shan sambatunta kan ta mik'e tana jan jiki ta shiga bandak'i domin watsa ruwa.Kallon sha'awa yake binta dashi yana jin yadda wani irin sassanyar farin ciki ke ratsa zuciyarsa, bai san meyasa ba haka nan kawai yana son ganin Rahama cikin dawwamemmen farin ciki, tashin hankalinta yana nufin nashi tashin hankalin ne.
Yace"Rahama inaso ki cigaba da kasancewa cikin farin ciki akodayaushe, kiyi kokari ki dunga nesanta kanki ga duk abunda kika san zai jefaki cikin damuwa, idan kikai haka kin gama mun komai arayuwa "
Lumshe Fararen idanuna nayi, na saki lallausar murmushi mai birgewa nace"Wannan shine bukatarka kawai Uncle Yusufana ?"
"No, ban gama magana ba "
Matsar da kunnuwana daidai saitin bakinsa nayi nace"To ina sauraronka ida maganar taka babana "
"Daga rana irin ta yau nayi miki iyaka da gidan Umar, bani son ki sake taka kafarki da sunan kinje wurin matarsa, kin dai ga abunda duk suka miki, wallahi ko kadan banji dadi ba, da zaki iya bud'e zuciyata ne kiga yadda tayi duhu da abunda aka miki da kinyi mamaki, amma babu damuwa zan daga musu kafa, sai dai fa duk sanda suka sake maimaita irin Wannan gangancin to wallahi hukuma zata shiga maganar..."
Dasauri na tari numfashinsa"Insha Allahu ba zama takai mu ga haka ba, Ni Uncle kama manta da batunsu muyi maganar aikina "
Yace"To ai kece munyi dake akan cewar da zarar kin dawo gida zaki nemeni awaya ko meh nakeyi zan ture inzo gareki, sai kuma naji shiru, nayi ta k'iran layinki amma shiru ba'a daga ba, nan take hankalina ya tashi nabaro offis babu shiri, saida na k'ira Addarku take fad'a mun ai gashi gashi abunda ke faruwa, dan haka inyi maza in karaso in miki jan ido ki fito dan ita gaskiya ba iya shiga gidan zatayi ba, ko papanku ma nanan shima d'in ba shigar zaiyi ba, To nidai kinji gargadin dana miki ki nesanta kanki da wa'ennan mutanen, kibari suji da matsalolinsu karki sake ki bari ki shiga tsakiyar rigimarsu, ga misali nan ma kin fara gani, sannan abu mafi mahimmanci banaso ki kara cewa duk wanda yayi miki gori kan shi yazo ya aureki mana in har ya gaji da ganinki zaune ba auran ne, kul na haneki da furta hakan, dan zaiyi amfani da wannan damar ne ya juya maganar ta wani fuskar yace kina masa tallan kanki ne, daga nan kuma gari ya dauka kin fara bin maza kina masu tallan kanki, ke kin san mutane, *UMAR* ya zamo good example akan hakan, don haka karki kuskura ki bari ki sake maimaita wannan kuskuren am i cleared ?"
Ajiyar zuciya na sauke ina mai jin haushin kaina da irin wawancin dana tafka, Nace"Insha Allahu Uncle corrections taken "
Hannu ya kawomun muka tafa yana fad'in"That's my girl "
Daga haka muka shiga tattaunawa akan aikina da kuma department d'in da suka jefani, sai kusan Magrib Papa ya shigo gida, ya dawo agajiye likis, A Jamb offis Papa ke aiki, shi kuma Uncle Yusuf ma'aikaci ne awani gidan redio ta jihar tamu ta sokoto wato _*92.50 Vision FM Sokoto.*_
Babu wanda ya gayawa Papa abunda ya faru dan mu agidanmu muna da b'oye sirri, bamu da zubar magana, shima sosai yayi murna da wannan aikin dana samu a UDUTH wanda duk k'ok'ari ne na Uncle Yusuf harna samu aka ajjeni awuri mai tsoka.
Sai godiya Papa yake ta mishi, yace"Haba Yaya ka tuna fa duk wani abunda ka mallaka na Yusufa ne, Rahama itama tawa ce dan haka bai kamata kana mun godiya dan na mata wannan taimakon ba, ka sani amfaninmu ne mu duka"
Jinjina kai akai ana yabawa kirkinsa, Nida Sakina muka shimfid'a katotuwar tabarma irin na shakatawar nan atsakar gida, anan muka ci abincin darenmu, Ni da Uncle Yusuf ah kwano daya muke ci tare, dan kullum kusan zan iya cewa ka'ida ne agidanmu yake cin abincin darensa.
Yana bani ina bashi haka muke cin abincin ayita mana dariya ana tsokanarmu, su Papa suce"Ni dai ban tab'a ganin irin wannan soyayya ta d'a da mahaifi ba sai akanku" amma ayau irin kallon da Addah take jifana dashi ban gane ba, kallon yayimun wuyar fassarawa.
Kwata kwata ma na lura tunda muka fara cin abincin ita ko loma bata kai bakinta ba, sai wasa da cokalin take akan kwano, duk da kasancewar papa na matukar kaunar suci abinci tare amma ita sam bata bari sbd kunyarmu, haka yake hakura yake ci tare da Adnan.
"Halimatuna lafiya kuwa naga bakya cin abincin sai wasa kike da cokalin, ko akwai abunda ke damunki ne ?"
". me kuwa ? Ni babu abunda ke damuna kawai abincin ne bani sha'awar cinsa " Cike da rashin gamsuwa da amsar data bashi yace"A,a Halimatu ban sanki da b'oye damuwa aranki bafa, ki gayamun menene ko kuwa so kike ne mu shiga daga ciki ?"
Kala bata ce dashi ba ta mik'e ta dauki abincinta tayi ciki, duk muka bita da ido, Cike da damuwa nace"Papa wai meyake damun Addah ne ? Tun dazu nake ankare da irin kallon da take ta jifana dashi mai wuyar fassaruwa "
Kallon Tuhuma ya shiga jifana dashi wanda ya tsinkar da gabana kan yace"Kenan ga dukkan alamu kece musabbabin shiga wannan yanayi nata, ma'ana babu tantama kece damuwarta, amma tambayar itace me kika mata ? Sai dai kuma ta wani tsiffar tatsuniyar gizo baya tab'a wuce na koli, watakila tsohuwar damuwarta akanki ne ya motso mata na rashin samun mijin aure....."
Wani irin kuka na rushe dashi ina fadi cikin tsananin fusata"Haba Papa dan girman Allah ku dunga dan sassautamun mana, wai wannan rashin auren laifina ne ? ina ce ai shi aure lokaci ne ? To papa ku had'ani da duk wanda ya kwanta muku arai ko ku badani sadaka ina ganin abunda zai fi kenan, amma meyasa wai ..." da hanzari na mik'e jiki na rawa zan bar wurin zuciyata na tukuk'i, ban yi aune ba naji saukar mari daga mutumin da ko jan ido bai tab'a mun ba sai ayau, muryata na rawa nace cike da mamaki ina kallonsa" Uncle Yusuf you just slapped me ? Me nayi uncle ? "
Da zafi zafi yake fadin"oh baki san me kika ma aikata ba ? abunda ya kamata ki gaya mishi kenan amatsayinsa na mahaifinki ? Maza duka ki bashi hak'uri, mahaifinki ne ba sa'an wasanki bane da har zaki maida masa da magana cikin raini, babu abunda Ni Yusufa nafi tsana arayuwata kamar d'a ya raina mahaifi, Rahama ba haka kike ba dan haka karki kuskura ki dorawa kanki halin daba naki ba in ba haka ba kina tare da tab'ewa arayuwa .."
Cike da nadama na rausayar dakai kasa nace cikin sanyi"Uncle kayi hakuri bada gayya nayi hakan ba, kawai banji dadin maganar daya mun bane"
"Ko kiji dadi ko karki ji babu yadda kika iya dashi dan mahaifinki ne wanda yake da iko akanki, kwata kwata bazai tab'a nufarki da sharri ba sai alheri, maza duk'a yanzu ki bashi hakuri"
Da sauri na duk'a ina shesshek'a na bashi hak'uri, ya nuna mun babu komai shi bai ma yi Fushi ba, yace in tashi abuna.
Ina tashiwa ko sake kallon inda Uncle Yusuf yake banyi ba dan sosai nake fushi dashi, da gaskiyarsa amma ni marin da yayimun ne banso ba, sai na koma ganinsa kamar Umar d'in Ubaida wanda ko kadan bai san darajar mace ba.
"Ki debomun ruwa abuta." Ina jinsa amma nayi banza dashi nayi shigewata kicin nayi zamana tare da rafka uban tagumi.
*B'ANGAREN ADDAH..#*
"Halimatu dan girman Allah ki gayamun damuwarki ni wallahi nasan wannan shirun naki ba'a banza bane.." Kamar baza tayi magana ba sai kuma tace"Akan Rahama ne da Yusufa..." da mamaki yace"Rahama da Yusufa kuma ?"
"Eh!"
"Ince dai lafiya dai ko ?"
Tace"In lafiya ne ai bazaka ganni cikin wannan yanayin ba, amma dai da sauki, kaje masallaci inka shigo kafin mu kwanta ma tattauna akai.."
Jiki asanyaye yace"Halima kina kara tadamun da hankali wallahi amma bari inje d'in in dawo."
Daga haka ya futo suka wuce masallaci shida Yusuf sallar Magrib.
Ina ganin ficewarsu Na tashi nayi daki abuna dan ban bari mukayi sallama da Uncle ba kasancewar daga masallaci sai gida, baya sake shigowa sai washegari, Kuma Nasan ya tafi ne da tsananin takaicina na rashin kai masa ruwan alwala, akarshe Adnan ne yakai masa.Ni da Uncle Yusuf bamu tab'a samun wani dan sab'ani ba kamar yau.
***
A b'angaren Ubaida kuma rikici sosai sukai da Umar akan Kudin data dibar masa wanda hakan yasake tunzurashi yayi mata d'an banzar duka, sai tsinewa Rahama bakin nata yake tayi kasancewar ita d'in ce ta bada shawarar su tab'a masa kudi, gashi abunda take gudun ma faruwarsa ya sauka kuma ya kare akanta ita daya.
Yana gama dukanta ya fice yabar gidan amotarsa, itama ta kokarta tabar gidan, ta samu d'an acab'a ta haye sai gidansu Umar d'in.
Da kuka wiwi ta shiga gidan alokacin ana kiraye kirayen sallar magrib, ta soma cin karo da Nuratu k'anwar Umar atsakar gidan tana niyyar fara alwala, da sauri Nuratun ta ture butar gabanta ta mik'e tsaye da nufin tarota tana fadin"Innalillahi Anty Ubaida meya faru..? Ko Ya Umar d'in ne ya mutu..?"
Bata tankata ba ta shige dakin Mahaifiyar Umar.
Mahaifiyar Umar wanda suke kira da Daada zub'e take saman gado, ita da matacce banbancinsu kawai numfashi.Shekarunta kusan bakwai kenan da kamuwa da lalurar shanyewar barin jiki wato stroke, daga faduwa abandaki fa shikenan bata sake mik'ewa ba, dake dama can tana da lalurar hawan jini, sai kuma abun yazo mata da yankewar magana, kuma duk damuwar Umar ya taimaka wajen jefata cikin wannan hali, bata uhmm bare a'a sai bin mutane da ido, tana da abokiyar zama Haj.Rabibiya kamar yadda megidansu ke k'iranta, Haj.Rabi itace uwargida kuma sosai suke zaman lafiya dan ba karamin kulawa take ba Daada da ya'yanta ba.
Ya'yan Haj.Rabi sune manya kuma duka mata ne.Na Daada ma ya'ya matan gareta Nuratu da Zuhaira, Umar kuwa ba d'an maigidan bane , zuwa dashi gdn tayi, amma ta hanyar da aka sameshi ne dai har yanzu maganar arufe take, ko haihuwar saman titi ne ko d'an sunnah shine ba'a sani ba, sanin gaibu sai Allah sai kuma ita kanta mahaifiyar tasa.Itace gatansa da komai har zuwa lokacin da Allah ya had'ata da Alhaji Salisu sukayi aure, a inda ya rik'i Umar tamk'ar d'an cikinsa kasancewar ba karamin son d'a namiji yake ba, sai kuma Allah ya jarabceshi da rashin samunsa sai ya bashi agola, agolan da ko kusa baida godiyar Allah, duk da abubuwan akhairin da Alhaji Salisu yayiwa Umar arayuwa hakan bai sa ya dunga ganin girmansa ba, kwata kwata baya ganin idon kowa da gashi in bana uban gidansa *ALHAJI HALIDU DANZAKI..* ba, amma shima d'in ladabin kunama ne yake masa, da zarar kuma ya juya sai ya koma bin bayansa da zagi da kuma munafuntarsa...
Kusan zamu iya cewa rabin damuwar Daada adalilin Umar ne, tun daga haihuwarsa damuwar ta samo asali har kawo girmansa ayanzu da yayi mata mugun illa.
Bayan kusan shekara daya tana jinya Alh.Danzaki ya bawa Umar auren d'iyarsa Ubaida tare da k'ara masa matsayi akanfaninsa ta kayan filawa wato 'ALHAJI HALIDU DANZAKI FLOUR'.Ubaida bata tab'a ganawa da sirikar tata ba kasancewar ba magana take ba sai bin mutane da idanu tana zubar hawaye.
Duba da halin da Daada ke ciki yasa sam Ubaida bata kuskuren kwaso tata damuwar tazo ta k'ara musu akan wanda suke ciki, shiyasa akodayaushe take k'ok'arin shanye duk wani bak'in cikin da Umar yake kunsa mata, sai dai na yau d'in ne yaci mugun k'arfinta.
"DAADA! DAADA!! Kiyi hakuri amma ayau hak'urina ya k'are, bazan iya cigaba da b'oye miki halin da nake ciki agidan danki ba, ya zama dole in gaya miki kalar cutarwan da Umar yake mun, dan girman Allah ke mahaifiyarsa ce kiyi masa magana watakila yana iya canzawa ..."
Daga bayanta taji an furta ana shesshek'a" Da wani bakin kikeso tayi amfani dashi wajen yi masa maganar ? Ko kuwa mantawa kikai da cewa banbancinta da mataccen mutum numfashi ne kawai ? "
Da sauri ta waigo ta sauke kallonta kan Zuhaira data fito daga wani daki hannunta rik'e da ledar magungunan Daada wanda zata bata tasha.Kuka duk suka sake rushewa dashi wanda ya sake tsinkar da zuciyar Daada dake kwance cikin halin ha'ula'i.
Ahakan Nuratu ta fad'o dakin ta iskesu, rufesu da fad'a tayi akan dan me zasu zo su tasata gaba suna kuka salon su sake jefata cikin wani hali ?
Rufe idanu Nuratu tayi ta dubi Ubaida dake zub'e akasa tana rusar kuka tace"Kinga Aunty Ubaida wallahi ina masifar jin kunyarki dan haka idan har kina son in cigaba da ganin sauran guntun mutuncinki a idona to karki kuskura ki sake kwaso damuwarki kizo ki sauke gaban Mahaifiyarmu, dan girman Allah lallab'a wa muke da ita karki zo ki karasar mana da ita da taki damuwar, kibari taji da bakin fentin da mijin naki ya goga mata dan a iya sanina babu wani mahaluk'in da yayi sanadin shigarta wannan halin face Ya Umar..."
Ta ida magana gami da fashewa da kuka tana kallon Daada dake k'ok'arin girgiza mata kai alamun tabar fadin hakan, sai digar da ruwan hawaye take.
Da gudu Nuratu ta karasa kusa da gado ta durkushe kasa tare da kamo shanyayyun yatsun Daada tana mai cigaba da magana"Daada kibari ana fadin gaskiya amma tunda bakya so toh nayi miki alkawarin bazan kuma ba.." Zuhaira itama karasowa tayi kusa suka had'e aka cigaba da kukan, Haj.Rabi bata nan balle ta tsawata musu kamar kodayaushe, tafiya ta kamata zuwa garinsu, biki taje tare da ya'yanta uku mata, duk sunyi aure babbar d'iyarta Zalihat ce kadai ta gagara samun miji kasancewar ita d'in rayuwa tasa gaba.
Ubaida ta mik'e tana jan jiki ta juya zata fita ganin babu wanda ke niyyar kulata balle ya lallashi zuciyarta, amaimakon taji an dakatar da ita, sai ji tayi Nuratu ta rakata da maganganu masu zafi"Bamu hanaki zuwa da kowacce irin damuwarki ba, in har abunda zamu iya tayaki magancewa ne to insha Allahu sai inda k'arfinmu ya k'are, amma in har matsalace wacce ta sako Umar aciki, to na had'aki da girman Allah karki kuskura ki kara kusanto inda muke da ita, mu babu ruwanmu da Umar da abunda ya shafesa, ke d'in ma muna d'an daga miki kafa ne sabida kina d'an k'ok'arin nuna kulawa akanmu, baya ga haka da wallahi baki isa mu kalleki ba dan kin kasance wata b'angare ne na mutumin da ko kadan baya da tausayin mahaifiyarsa, butulu wanda yake tare da tab'ewa arayuwarsa, wanda ga dukkan alamu bashi da rabo alahira..."
"This is too bad sister! Kar fa ki manta ko min lalacewar Umar babu abunda zai tab'a canzashi daga zama dan'uwanki.." Zuhaira ta furta with breaking voice, Cike da Zafi Nuratu tace"Ni ba dan'uwana bane, Uwa muka had'a dashi amma bamu had'a Uba daya dashi ba, in zan iya masa halacci zan iya k'iransa da dan'uwan ah inda babu Aunty Zali, Anty Khausar, Anty Fiddausi, da kuma Aunty Hidaya, kinga dai su 'yan uba muke dasu sab'anin shi da muka fito ciki daya ko? To narantse da wanda ya busamin rai sun fiye mun shi sau dubu, wallahi bani K'aunar Faruq dan shine ummul'aba'isin shigar mahaifiyarmu cikin wannan hali..." For the very first time taga Daada ta yangale baki ta rushe da kuka sakamakon Furucin k'arshe da Nuratun tayi, wannan ya jawo musu abu biyu, farin ciki da akasinsa.
Sunyi farin ciki ne da atleast anji sautin kukanta wanda tunda ta kwanta jinya ba'a sake jin maganarta ba inka cire tari, sa'annan suna masu bak'in ciki da sake cusa mata Wani damuwar akan nada da suka yi.
Ubaida bata sake bin takansu ba dan damuwarta kadai ta isheta, ficewa tayi tana shesshek'a, gabaki daya duniyan tayi mata zafi, ji take inama ace mutuwa tazo ta dauketa ta huta kawai, sannu ahankali take jan jiki har takai daidai tsakiyar gidan, ji tayi daga bayanta ance"Ina da maganin damuwarki, kuma ashirye nake da in taimaka miki, daidai da k'wandalarki bana so ki bani k'yauta amatsayin tukwicina, babbar tukwicin da nakeso ki mun shine inaso ki had'ani da dan'uwanki _*Shuraim Dan'Zaki........*_
Afirgice ta waigo dan ganin wannan d'in wani mai k'arfin halin ne yake k'ok'arin gindaya mata sharad'i muddin in har shi zai taimaketa ?
Idanunta ne suka sauka akan _*Zalihat Salees*_
Babbar d'iya ga Alhaji.Salisu da Kuma Hajiya Rabibiya kenan...................