08
by @faddabanan
Wasa-wasa sai da aka yi sati Uku Aliyu bai kirani ba tun bayan kiran da nayi masa a gidan su Darma, cikin ikon Allah Ni ma na iya daurewa ban sake kiran sa ba na tsaya na ga iya gudun ruwan sa.
Abun mamaki, ranar da Yaya Maijidda suka zo gida tare da Yaya Mahmoud (nan gidan mu suka sauka sai dare zasu tafi gidan su na nan Kano), ina cikin yi mata kitso na jiyo ƙarar waya ban kula ba, kawai ko ma waye me kiran idan na kammala mata kitso zan bi bayan kiran. Ina kammala wanda nake yi, na tsaga na gaba zan cigaba, nan ma aka sake kira kaman ana kallona ana jiran na gama, ita ta kora Ni kan dole sai na amsa wayar kafin mu cigaba da kitson. Na ƙarasa inda na jona wayar a chaji tana gab da tsinkewa. Ina jin zuciya ta ta kusa fitowa daga ƙirji na ganin sunan Aliyu, hannu na rawa na danna amsa kiran tare da fatan kar ta katse ban kai ga ɗauka ba karo na biyu.
Ban yi saurin magana ba don so nake bugun zuciya ta ya daidaita, hakan ya sa shine ya fara magana "Hello?! Are you there?" A hankali nace "Eh! Ya kake?"
"Lafiya lau. Me ya faru kika ƙi amsa wayar ki da sauri?" Ya tambaya.
A cikin raina Ni kuma mamaki yake ba Ni, lallai namiji mara kunya ne don haka a take na yanke shawarar nuna mashi rashin kira na a waya ko sabbin halayensa duka ba su dame Ni ba. Na amsa "Ba na kusa da wayar ne." Na kuma ja baki na na tsuke.
"Wani abu na damun ki ne Ummul?"
"Me ka gani?"
"Ga shi nan kina amsa Ni a gajarce"
"Aiki nake yi ne, akwai wani abu?"
"A'a, ba komai. Zan kira ki anjima." Muryar shi ba ta ɓoye mamakin shi ba. Ban amsa ba sai kawai na kashe wayar.
Cikin sauri na ƙarasawa Yaya Maijidda kitson na kuma koma bayan ɗakunanmu na kira Surayya don na san ita ce 'yar zafin kai. Wani ihun murna ta yi na jin daɗin halin ko'ina kula da na yi masa, ta ƙara mun ƙwarin gwiwa da roƙona da na jajirce na cije kar na tambayi komai, ko da rabuwa yake son yi da Ni gara mu rabu da dignity ɗina intact!
Na din ga jiran kiran bawan Allah amma shiru. Yaya Maijidda ma ta so na biyo su zuwa gidansu na zame amma na yi mata alƙawarin gobe a gidan zan yini.
Dare ya fara kenan na hango gilmawar Yaya Rufa'i cikin gida, amma har aka fi awa ban gan shi a falo ba sai na ɗauka ya gama abin da ya kawo shi har ya tafi, ba mamaki 'yan maganar yau ba sa kusa.
Wurin ƙarfe tara ina kitchen ina ƙarasa wanke kwanukan da aka ɓata,ta tagar da ke kallon bayan gidanmu na hange shi yana waya, fuskarsa a tamke kamar wanda aka aiko wa da mala'ikan mutuwa. Hannayena na cikin ruwan daurawa da na tara a sink, a yayin da idanuna ke nazarin shi. Ina kyautata zaton ji yayi a jikinsa ana kallon shi domin ɗago kan shi sosai yayi ya kalli kitchen muka haɗa ido, yatsa ya sa ya yafuto Ni, don haka da hanzari na gama ɗaurayar kwanukan na tafi wurin kiran na sa.
A ƙofar na iske shi yana jira na har ya baro bayan gidan ya zagayo, hannunsa duka suna aljihu ya jingina, idonsa kuma yana kan kafafunsa but fuskarsa ta zama kamar an sa mask ba abin da za'a iya karanta a ciki.
Bayan na gaishe shi muka koma kan fararen kujeru da ke zube nan harabar gidan muka zauna. Ko maganar farko ba mu kai ga yi ba, wayar shi ta hau ɓurari ya kuma share kaman ba shi ake kira ba har 3 missed calls. Ni kiran ne ma ya ishe Ni nace "ka yi haƙuri ka ɗaga kiran nan Yaya, ba kasan uzurin me kiran ba."
Tsaki yayi a hankali sannan ya miƙa mun wayar wai na sallami me kiran. Ban kai ga amsawa ba kiran ya katse, sakan bai fi talatin ba tsakani aka sake wani kiran, na kalli fuskar wayar babu suna sai lamba kawai, na ɗaga tare da yin sallama. Shiru kaman ba za'a yi magana ba sai kuma aka buƙaci sanin ina me wayar yake (Muryar mace ce), na amsa da uzuri gare shi yanzu ba sai samu damar ɗaukar waya ba. Sai tace "wa ke magana?"
"Ummu Kulsum ce"
"God! Cousin ɗin sa ko?"
"Yep. Kin sanni kenan?" Ina mamaki na tambaya
"Probably. Ki faɗa masa na bugo, zan sake kira anjima don nasan shi ba biyo kiran zai yi ba. Bye!" Ta katse kiran.
Na miƙa masa wayar shi ina faɗa masa saƙon da ta bayar. Wayarsa kawai ya karɓa bai amsa ba sai ma wani tsakin da ya ƙara ja. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace ina saurayin ki? Me wahalar da ke ɗin nan? Sai kuma muka fara hira, anan Baba da Yaya Naziru suka iske mu, bai bar gidan mu sai goma da kusan rabi, Yaya Naziru ma yayi da shi ya kwana amma ya ƙi, a tare na bar su ma na wuce cikin gida.
Sai da nayi wankan daren da na saba kafin kwanciya sannan na tuno ashe Aliyu yace zai kira Ni an jima, missed calls ɗin shi bakwai na iske a mabanbantan lokutta. Cikin ikon Allah na ƙarar da katin wayar ɗazu da na kira Surayya, ina ta so na aiki Hussein ya siyo mun sai na manta, ga shi lokacin ma ƙarfe sha ɗaya har ta buga. Kamar na yi hauka nake ji, na rasa ta yanda zan samu kati a wannan lokacin bare na kira shi ga kuma tsoron kar ya ƙi sake kirana.
Gyangyaɗi na fara sai wayar Surayya ta tashe Ni wurin sha biyu, tana ta jira nazo na ba ta labarin abin da ya wanzu tsakanin mu ta ji shiru shine ta biyo baya. Nace ta taimaka ta yi mun transfer daga kuɗin wayar ta ko na samu na kira shi tunda mun yi saɓani ɗazu amma sai cewa tayi "Wallahi yanzu haka dubu huɗu da ɗari bakwai ne a waya ta amma sule ba zan iya ba ki domin kiran wani ƙaton banza Aliyu ba, dama daa ne lokacin yana da kirki..."
Shigowar kiran shi yasa na katse maganar ta ta da cewa "'yar baƙin ciki, to ga shi yana kira, idan kin ga dama ki kashe wayar ki Hajiya me kuɗi." Na kuma danna amsa kiran wayar shi na bar ta on hold.
Cikin Muryar da ake ƙoƙarin ɓoye fushi yace "Wai me ye haka ne Ummul? Sau nawa na kira ki yau? Ba ki ga damar ɗaukar wayar ba kenan? Saboda Allah calls ɗina nawa kika yi missing? Babu kira balle flashing? Ke ce kuwa?"
"Sorry don Allah, duka kiran da ka yi mun bana cikin gida ita kuma wayar na ɗaki sai sha ɗaya na gama shirin kwanciya na ga calls ɗin to kuma ashe na ƙarar da kuɗin wayar gabaɗaya ban lura ba."
"Ba kya cikin gida? As in fita kika yi? Yaushe aka fara barin ki fitar dare?"
"Ba fita chan wani waje nake nufi ba, muna tare da Yaya Rufa'i a compound ɗin gida."
"For all those hours? Tun wurin takwas nake kiran ki fa, yanzu da na kira ki da shi kuke waya kenan?" Ya tambaya cike da ɓacin rai.
"A'a. Wai me ya sa kake son koyon saurin fushi ne? Before kana da saurin gane abu ko ban faɗa ba, amma tun wayar ka ta rana kake ƙoƙarin yin mita akan ƙananan abubuwa." Na zumɓura baki kaman yana kallo na.
"Gani nayi kin canza gabaɗaya, ko nema na ba kya yi kamar wadda aka faɗawa wani aibu na."
Maganar sai ta ba Ni dariya sosai kafin nace "Ikon Allah! Da muka yi wayar ƙarshe da kai me kace mun? Kace za ka kira idan ka samu dama don ba ka da lokaci sai na karatu. To me kake so nayi? Na biyo ka Turkey ko me?"
Mun daɗe muna magana, don ko kafin mu yi sallama har zuciya ta ta wanke Aliyu, don kar nake kallonsa kamar an sabun ta mun shi a zuciyarsa. Lafiyayyen bacci na samu ranar ko mafarki ɗaya ban yi ba, haka kuma na tashi cikin walwalar da na daɗe rabona da ita. Mama kam sai bi na take da ido cikin alamun jin daɗi.
Gab da zamu koma makaranta ne su Yaya Zainabu suke kammala bautar ƙasa. Ni da Sauda kam so muke mu je Taraba POP ɗin su, sai mu dawo Kano tare amma Mama ta ƙi yarda. Wai da ace Yaya Naziru shi ma ba gamawa zai yi ba sai mu tafi tare amma mu kaɗai mu bi hanya? Ina! Gabaɗaya ranar yajin zaman farko na yi, na maƙale a ɗaki ina ta ƙunci.
Da la'asar sai ga kiran Yaya Rufa'i (Rabo na da shi tun ranar da ya sa na amsa wayar shi). Ina gaishe shi ya ɗau hasken wani abu na damu na, bai amsa gaisuwar ba sai cewa yayi "Kun sake faɗa da saurayin na ki ne?"
"A'a, me ka gani?"
"Ga Muryar ki nan kina sulking, abun ɓacin rai ba ya maki wahala. Me kuma ya faru this time around?"
A shagwaɓe na amsa ina fatan zai yi wa Mama magana ta ƙyale mu mu je "Ba Mama ba ce ta hana mu zuwa POP ɗin Yaya Zainabu ba?"
"Taraba wai?"
"Eh mana. Ita ma sai kiran Maman ta ke yi amma ta ƙi haƙura."
"To me zai kai ku kuma? Ba gida Zainabun za ta dawo gabaɗaya ba ne?"
"Kai Yaya Rufa'i, Ni son ganin gari nake yi har ita Sauda ɗin ma. Don Allah beg her on our behalf, Allah tun ɗazu nake kuka Ni ƙadai."
"Ni ma ban goyi bayan a bar ku kuna mata ku je gari mai nisa haka da kan ku ba, dama irin Zaria, Kaduna ko Katsina ne......" Sai kawai na fashe da kuka na wurgar da wayar ina bubbuga ƙafa bisa gadon da nake kai. Bai sake kira na ba. Na bawa kaina haƙuri sannan na fita kitchen neman abinci tun da ciki na bai gane fushi nake yi ba.
Ranar Laraba muna zaune bayan mun gama gyaran gida wurin ƙarfe tara Ni da Sauda sai ga Yaya Rufa'i, ashe wai Tarabar zai kai mu babu notice. Muna ihun murna muka wuce ɗaki don jefa kaya kala biyu a haka don ya ce idan muka kai minti talatin ya fasa zuwa. Muka biya ta gidansu muka ɗauko ƙanwar shi Samiha kafin muka ɗau hanya.
Tsabar murna da shirme irin namu ba wanda ya tuna ya kira Yaya Zainabu ya ce mata gamu bisa hanya sai da muka ji suna waya da Yaya Rufa'i tukunna. A gajiye liƙis muka isa, gidan da suka kama haya ita da wasu aka yi mana kwantance muka isa. Gidan kam yayi masu yawa don akwai spare rooms guda biyu don haka sai suka hana Yaya Rufa'i zuwa hotel, shi ma sai da aka sha roƙo da magoya ya yarda ya sauka anan.
Kayan ciye-ciyen da ya siya mana akan hanya muka yi amfani da su a matsayin abincin dare don a ƙoshe muka iso, Yaya Rufa'i ne kawai ya buƙaci Indomie mai zafi da shayi. Duk gajiyar da muka kwaso bai sa mun kwanta da wuri ba, hira kawai muka dasa.
Sai sha biyu da rabi na dare sannan muka fara shirin kwanciya. Yaya Rufa'i ya doshi hanyar ɗakin da aka sauke shi kenan sai ga kiran Aliyu a waya ta, ina ɗagawa zuwa kunne na shi kuma ya juyo ya dawo tare da miƙo hannun shi na hagu yayi alamar na ba shi wayar. Aliyu na yi mun magana ta cikin wayar amma hankali na gabaɗaya yana kan Yaya Rufa'i ina masa magiya da ido akan ya bar Ni na amsa wayar, da ya ga ina ɓata masa lokaci sai kawai ya sa hannu ya zare wayar daga kunnena, ban san lokacin da nace "don Allah Yaya Rufa'i ka bar Ni na amsa wayar, wallahi yau duka bai same Ni ba saboda rashin kyawun network."
Kulawa yabawa, bai kalleni ba sai ma kashe kiran da wayar yayi gabaɗaya sannan ya juya ya wuce masaukin sa ba tare da ya bani wayar ba, dukkanin mu muka bi shi da ido. Na koma na zauna jigib akan katifar da zamu kwanta ina ƙoƙarin share hawayen da suka fara cika mun ido, ta gefen ido na hango Yaya Zainabu da sister Samiha suna signal da ido suna dariya mara sauti, sai kawai na kwanta tare da juya masu baya.
Da safe har muka yi wanka muka shirya domin zuwa POP ɗin su Yaya Zainabu yau Alhamis, Yaya Rufa'i bai yi mun magana ba bare na ga fuskar da zan tambayi wayarta, sai na sa ma shi ido kawai. Babban abin takaicin shine ban riƙe lambar Aliyu a kaina ba bare naje neman yanda zan kira shi.
Tun tara muke harabar da za'a gabatar da POP ɗin, sun yi kyau sosai, mutane duk an fiddo wayoyi ana ta ɗaukar abun Ni kuwa takaici ya sa na zauna wuri ɗaya, don ma parade ɗin yayi mun kyau ƙwarai ne shi yasa kafin a tashi ma har ɓacin ran nawa ya ragu. Zuwa ƙarfe biyu an gama komai har ta karɓi certificate ɗin ta.
Mun baro wurin da niyyar zuwa siyan abinci amma Yaya Zainabu tace mu siya ɗanyen nama sai mu koma gida a yi girki kawai, tunda Yaya Rufa'i yace anjima chan za mu zagaya gari domin gobe da safe zamu koma Kano in shaa Allah. Hakan aka yi amma mun siya snacks da drinks don rage yunwa kafin mu gama abinci. Tunda Yaya Rufa'i ya shige ɗaki bayan mun dawo ba wanda ya ƙara jin duriyyar shi.
Da yamma liƙis da muka fito yawon zagaya gari kuwa, Ni suka sa a gaban mota su suna baya suna ta surutu a tsakaninsu Ni kuma na yi shiru ina kallon gari kawai ina kuma sauraron Yaya Zainabu tana bayanin guraren da muka je ko kuma directions ɗin in da zamu. Fitar tayi mun daɗi har na manta ma da batun wayarta, duk na jiyo ƙarar ta a aljihunsa alamun ya kunna wayar kenan, yanda ya share kamar ba daga jikin sa ƙarar ke fita ba haka nima na ɗauke kaina na fara sa masu baki a hirar su akasin ɗazun da nake banza da duk maganar da suka sa Ni ciki.
A waje magriba ta same mu kuma da zai shiga wani masallaci sallah sai ya miƙo mun waya ta ba tare da yayi magana ba. Sai dare muka koma gida, da alama kuma Aliyu yayi fushi mai tsanani domin bai sake kira ba, Ni kuma bana son kiran shi a gaban Yaya Rufa'i shi yasa na bari sai mun koma gida sai na kira.
Su Yaya Zainabu suna ƙarasa tattare kayan da ya kamata ta tafi dasu gida, na zame naje ƙofar gida domin kiran Aliyu a waya ta. Kiran na shiga shi ma yana ɗauka, sai kace dama ya sa wayar a gaba yana jiran na kira shi. Abun mamaki bai nuna fushinsa ba, tuhumar sa ta tsaya akan abu guda biyu ne kawai, rashin ɗaukar wayar shi da kuma tambayar me ya faru nake tare da Yaya Rufa'i har bayan sha biyun dare? Kuma duka na yi masa bayanin da ya gamsu, abun matuƙa ya ba Ni mamaki, Aliyu da shegen kishi? Shine har ya iya fuskantar bayani irin wannan? Lallai na taka sa'a yau.
Giftawar Yaya Rufa'i zuwa cikin gidan ne ya sanya Ni gaggawar yi wa Aliyu sallama. Ko da ya wuce ciki share Ni yayi kamar bai ga kowa ba a wurin. Da na shigo ma a tare na gansu a zaune suna ta hira amma idan na sa baki ba zai amsa maganar ba sai wani basarwa yake yi. Ganin haka ya sa na rufawa kaina asiri naje na kwanta abu na, kafin kace me ye wannan ma har bacci ya ɗaukeni don haka ban san lokacin da suka tashi suka kwanta ba.