KOWA DA ƘADDARARSA

16

by @faddabanan

KOWA DA ƘADDARARSA


Mu yi amfani da wannan shafin wajen yi wa 'yan uwa, iyaye da abokan arziki da muka rasa addu'a, Ya Allah yayi masu gafara, ya jiƙansu ya sanya mutuwar hutu ce gare su. Ameeen


Sannan ina roƙon alfarmar duk wanda ya karanta shafin nan ya taimaka yayi wa ƙanwata SADIYA UMAR ALIYU addu'ar neman gafara, Allah ya sanyaya kabarin ta Ya kuma haɗa fuskokinmu a aljannatul firdaus. Ameen ya Hayyu Ya Qayyum. Babu rana guda ɗaya da bana tuna ta, ta tafi ta bar mana giɓi. Ya Allah!


Sannan 'yan Fadda_banan's group, I don't have words to show my gratitude but just know I APPRECIATE you all! Nagode da ku!


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Na dawo hayyacina na gan ni kwance ko'ina a jiki na laima ne. Da farko ƙamshin turaren Yaya Rufa'i ne yasa na rufe idona ina shaƙa a hankali kafin abubuwan da suka faru suka dawo mun. To ko dai mafarki ne? Sai na tashi zaune. Nesa kaɗan da ni na hangi turaren na miƙa hannu na ɗauko kawai na hau feshe jikina da shi.

Yaya Naziru ne ya buɗe ƙofa, ganin abinda nake yi yasa cikin hanzarin ya ƙaraso tare da karɓar turaren yana kallona cikin mamaki yace "Ummu lafiyar ki ƙalau kuwa? Yaya Rufa'i ne ya rasu fa, maimakon ki yi masa addu'a sai kuma ki fara wani abu daban?"

"Da gaske ne kenan." Duk wani ginin da nayi wa raina na cewa mugun mafarki nayi yanzu kam duk ya rushe tsaf, naji kamar an bar ki tsira a tsakiyar fili, a take wani abu ya tsira mun a zuciya na tsaya kuma ina kallon Yaya Naziru kaman zombie, daga haka kuma sai komai ya canza.

A firgice Yaya Naziru ya koma cikin gida ya tattaro su Mama yana faɗa masu su zo su ga halin da Ummu take ciki, tana cikin shock ne sosai har wani irin kallo take yi wa mutane kamar ba'a duniya ɗaya muke ba. Matuƙa sun kaɗu, ga shi ido na ko ɗigon hawaye babu a idona (kamar yanda Sauda ta ba ni labari daga baya).

An sanar da ni daga wannan lokacin ban ƙara magana ba balle kuka, sai dai na zauna ina kallon fili alamar ina tunani amma Yaya Naziru yace shi baya jin ma tunanin nake yi kamar i was just staring into space ne kawai."

Yaya Muntari ne ya dage sai an kai ni asibiti don wannan ba ƙaramin abu ba ne. Kowa ya san shock ne ya sani a halin da nake ciki, don haka gara a samu masana a ɓangaren da zasu taimaka da magunguna da shawarwari.

Sauda tace bana taɓa neman abinci, sune suke kintata ya kamata na ci abinci sannan a bani. Haka kuma tace idan za'a ajiye mun abinci ya kai cikin fanteka aka ce naci, ci zan dinga yi ba tare dana daina ba har sai an ce na bari ko an ɗauke kwanon, kenan ban san ƙoshi ko jin yunwa ba.

Idan kuma aka kira sunana sai dai na ɗaga ido na kalli mutum cikin mamaki kamar an dawo da ni wurin da na bana son dawowa. Idan kuma mutane suka yi yawa a wurin da nake sai na birkicewa kowa, don haka koyaushe ina ɗaki kawai.

Haka kuma lokaci zuwa lokaci za'a dinga jiyo ni ina magana ni kaɗai cikin sigar amsawa wani. An ce mun ranar da su Fatima, Zara'u Darma da Surayya suka zo duba ni sun sha kuka, amma ko ɗaga kai ban yi na kalle su bare ma magana ta haɗa mu da su.

A asibiti ma sun kwantar da ni na kwanaki saboda gwaje-gwaje kafin daga baya aka tura mun ɓangaren psychiatric domin tabbatar da lafiyar hankali na da neman hanyar dawo da shi.

Ire-iren waɗannan abubuwan ne suka yi ta gudana har can makaranta suka fara jarrabawar zangon karatu na biyu kuma na ƙarshe a aji biyun da nake.

Mafi yawan magungunan da ake bani bacci suke sa ni, hakan ya sanya kusan koyaushe a bacci nake. Yaya Mahmoud ne ma mara ƙarfin zuciya a mazan gidanmu don shi kam sa ni a gaba yayi ya yi ta kuka don shi ya dage cewar na haukace ne gabaɗaya.

Wata rana da bansan koyaushe ba ne, ina tashi daga bacci sai na fara making sense of abubuwan da ke zagaye da ni, abin da na mance rabon da naji haka. Sauda na hanga kan kujerar tana bubbuɗa abinda bangane ba. "Sauda" amma sai a kira na uku ne ta ji. Ta waigo ta kalle ni ta ga tabbas ita nake kallo, sai na ga ta wurgar da abun hannun ta ta fita falo a guje tana ihun da yasa na toshe kunnuwa na da tafukan hannayena. Kafin kace me ye haka, sun cika ɗakin da nake, domin kowa da yake gidan a daidai lokacin yana ɗakin har da Baba kuma basa hayaniyar saboda yana ɗaya daga cikin abinda ke birkita ni.

Cikin mamaki nake kallon su "Menene? Mama me yasa kowa yake kallona?" Ba ta amsa ba sai gani nayi tana hawaye tana dariya kuma sai maimaita "Alhamdulillah!" take yi.

Da kyar suka bar ni na miƙe nayi wanka na ci abinci kafin kuma na tambayi Sauda ina waya ta take? Tace nayi haƙuri zuwa da safe za ta ɗauko mun domin ta ɓoye mun ne.

A daren ne nasa ta a gaba har sai ta faɗa mun dukkan abin da ya faru da ni. Sai da gaba na ya faɗi da ta tuna mun da rasuwar bawan Allah Yaya Rufa'i. Daga labarin ta na gane cewa wata biyu nayi cikin wannan halin, abun ya tsorata ni ganin tsawon lokacin da na ɗauka ko addu'a ɗaya ban yi masa ba. Kukan da ke taso mun danne shi nayi saboda bana son na tayar da hankalin 'yan gidan mu, sun sha wahala matuƙa a kaina ya kamata na nema masu sauƙi.

Na ƙara jin rashin daɗi jin cewar ina cikin wannan halin ne har aka yi jarabawa a makaranta aka ƙare, hakan ba zai zama damuwa ba in shaa Allah domin kafin mu gama makaranta zan iya rama duka abinda na rasa yanzu, kenan zan raba courses ɗin tsakanin level 3 da 4. Dole kuma na koyi haƙuri ko na samu ladan haƙuri da sakamako mai kyau, jarabawar Allah ce. Kowa da ƙaddararsa, ni kuma tawa a hakan take.

Kashegari da na kira su Zara'u ba zan yi kwatanta farin cikin su da naji ba saboda samun lafiya ta. Na samu labarin su ma basu gajiya da kai mun ziyara walau asibiti ko gida duk kuwa da bana acknowledging presence ɗin kowa. Wurin ƙarfe uku kamar a tare sai ga su a gidanmu, don banbancin zuwan su ba wani yawa.

Su kuma suka lissafa mun waɗanda suka je dubo ni lokacin kwanciya ta a asibiti daga cikin 'yan ajinmu. Su mamakin su ta yaya babu abu ɗaya da na tuna duka tsawon lokacin nan, fuskar su zallar tausayi na. Hirar gajiyar da ni tayi, ƙila don na daɗe bana yi ne sai kawai na zuba masu ido ina sauraren su bana maidawa. Kuma ga shi jiki ba jiki ba, ga shi na ƙara faɗawa, ni bana son kallon madubi ma sai na dinga ganin kamar fuska ta ta koma irin ta Yaya Rufa'i a kwanakin shi na ƙarshe don sai ido da hanci kawai.

Fatima ta bani shawarar naje makaranta idan jikina ya ƙara ƙwari sosai domin sanin me ya kamata nayi tunda an yi jarabawa babu ni kuma babu report. Mu duka ba wanda ya san abin da ya kamata a yi, kyau kawai na samu level coordinator zai bani guidance na yanda zan yi idan ma ba shi ya kamata na samu ba.

Duk lokacin da naji kewar Yaya Rufa'i rufe kaina nake yi a banɗaki nayi kukan rashin sa, nayi kukan nadamar abubuwan da nayi masa, na yi kukan me yasa na ɓata masa rai na wannan dogon lokacin? Me yasa ma na ƙi shi? Idan na gama na share hawaye na na fito.

Yanzu kam ba ni da aiki sai sauraron voice notes ɗin da ya dinga turo mun, har na haddace su. Waɗanda na iske ranar da ya rasu kowa kusan koyaushe hawaye suke sani, ba ma kamar wanda yace "Ummu na! Sai ƙiran wayar ki nake yi ba ki amsa ba. Wani urge ɗin jin muryar ki ke damu na a wannan lokacin fiye da komai da yayi mun saura a rayuwa ta. Ba ni da tabbacin me zai faru amma zuciya ta har zafi take yi mun saboda tsananin son ki da nake, bana jin akwai wanda zai so ki kusa da yanda nake son ki. I can't wait to see you anjima!" Yayi 'yar dariya a hankali yace "Na fa kasa tashi akan gadon nan bare na fara shirin zuwa wajen ki, ɗoki nake ji har ban san yawan shi ba. Take care! Sai na zo love!" Ashe zuwan da ba zai yi ba kenan.

Abubuwa da yawa sun faru a wannan lokacin da ya janye hankalina daga zuwa neman level coordinator ɗin mu na makaranta, ga kuma ƙarin ina ganin ai ba wani matsala ba tunda ba duka shekarar ce na rasa ba. Ga ƙarin Yaya Mahmoud da kan shi ya zo ya ɗaukeni zuwa gidan shi can Minna, wai ai sauyin wuri yana ragewa mutum damuwa. Daga shi har matar shi (duk da ita ma tsohon ciki gare ta) kulawa suke da ni kamar wata yarinya 'yar sha uku, ni kuma saboda na rage masu damuwa a kaina sai na dinga nuna ai bana cikin damuwa sam, ɓangare guda kuma na yawaita yi wa Yaya Rufa'i addu'a. Ikon Allah tawakkali na wannan karon ya wuce na lokacin lamarin Aliyu duk da lamuran biyu ba zasu haɗu ba.

Saura sati ɗaya a koma makaranta suka dawo da ni gida. Don haka washegarin dawowa ta na tafi makarantar kai report abin da ya hanani yin jarabawa, da Fatima muka je. Mun iske an ce level coordinator ɗin mu ya tafi ƙaro karatu sannan sabon da aka maida mana har satin ya ƙare bai zauna a makaranta ba, don kullum sai mun je ni da Fatima amma ofishin sa a rufe, jira kuma muke yi har yamma kafin mu taho gida.

Ganin muna ta wahala kuma ba mu same shi ba Darma ta ba ni shawarar zuwa wurin HOD, tunda dai maganar department ake yi, ga ƙarin cewa ya san su Mama. Duk rashin son hulɗa da bana yi da shi da gudun disgi da wulaƙancin sa duka na danne naje neman shi, domin yanzu a kaina ake magana.

Tare muka je dasu ofishin sa kuma cikin sa'a a buɗe, amma duk cikinsu ba wanda ya yarda ya bi ni ciki. Jiki na yana rawa na shiga tare da sallama ina addu'ar Allah ya sa kar ya wulaƙanta ni.

Sallamar da nayi ya amsa amma bai ɗago idon shi ba bare ya kalli wace ke tsaye yana typing ta laptop ɗin shi, don haka na dakata ina jiran shi. "Lafiya?" Da yake a ruɗe nake sai naji kalmar kamar tsawa don haka har sai da nayi wani ɗan tsalle na alamar razana, hakan ya sa ya ɗago ido yana kallona tun daga sama zuwa wurin da teburin shi ya ƙare ni sannan ya ce "Me ya faru?"

A cikin saurin magana na zayyana mashi cewar rashin lafiya nayi har na rasa wasu test da jarabawa gabaɗaya, kuma an ce ana zuwa a faɗa don kar abun ya zama matsala.

"Kin kwanta a asibiti ne? Ko kuma a gida kika yi ciwon har kika warke?"

"An ce an kwantar da ni amma a gida na ƙarasa jinyar har zuwa lokacin da na samu lafiya."

"An ce?"

"Eh sir! Bana cikin hayyaci na, ban san me ya gudana ba."

"Me yasa ba'a fara kawo ki clinic ɗin cikin makaranta ba? Da daga nan aka ba ki referral da abun ya zo maki da sauƙi."

"Ina ganin basu san ana yin haka ba ko kuma sun fi buƙatar babban asibiti ko ma fi kusa. Amma sir ɗaya daga likitan da na gani a can asibitin yana zuwa koyarwa a ɓangaren masu karatun likita na makarantar nan."

"Wane ne?"

"Dr. Salis"

Sai ya taɓe baƙi "Kin je wurin level coordinator ɗin ku?"

"Eh, na je sir, amma ya tafi karatu. Sabon kuma na kasa ganin shi ga lokaci na tafiya shi yasa nazo. Ka yi hakuri idan na dame ka."

"Ya sunan ki?"

"Ummu Kulsum Aminu"

A take naga idon shi sun faɗaɗa ya ƙara kallona sannan ya furta a hankali "The over roller! Is that even English?" Ya koma ya jingina da kujerar shi sosai sannan ya cigaba da cewa "Ki je ki kawo mun medical report da evidences ɗin ki nan da kwana biyu, zan yi ƙoƙari na karɓo maki Form ɗin da za ki cike."

Bai jira amsa ta ba ya koma ya cigaba da aikin da yake yi kafin shigowa ta alamu ya gama da ni. Don haka da sauri nayi godiya na juya tare da fita ina faɗar Alhamdulillah a hankali, hankali na yayi gaba ko godiya ban yi masa ba. A ranar da na koma gida na tattaro duka takardun asibitin daga wurin Mama har da kati tare da faɗa mata wurin wa naje akan matsalar.

Washegari na koma wurin shi ni kaɗai, su Surayya suna wurin registration tunda an fara a wannan satin da muka shigo, idan na gama da wurin shi zan same su mu cigaba tare. Da naje na iske Form ɗin amma sai dai yace abin da na kawo bai yi covering duka kwanakin ba, saboda wannan ma kafin a fara jarabawa ya tsaya, idan ma za'a yi amfani da shi sai dai ya zama excuse ɗin tests ɗin da na rasa. Don haka abu ɗaya zai yi mun, na koma wurin likitan ya rubuta mani tabbacin ya duba ni a lokacin rashin lafiyar sannan na haɗo da takardun hannuna na dawo. Jiki na take ya saki, ina tunanin abun mai sauƙi ne amma ashe ƙato ne.

Sai da na shafe kwanaki sannan na samu Dakta Salis ɗin a asibiti. Shi mamaki ne ya kama shi domin iya sanin shi abin da na kai ya isa a cike Form ɗin amma sai ya rubuta shi ya gan ni tsakanin lokaci kaza zuwa kaza, kuma ina wani state ne da bana iya comprehending komai, ba tare da ya faɗi ainihin ciwon ba saboda confidentiality na aiki. Ya ƙara da cewa evidence na jikin katin asibiti na.

Ranar da na koma ma shi da takardar da na karɓo daga wurin Dr. Salis kuma yana gama karantawa ya linke tare da maida ita cikin ambulan sannan yayi baya da kujerarsa ya jingina sosai yana kallona yace "Kin ga, wannan takarda can mean anything, ba mamaki Dr. Salis ɗin saurayin ki ne ko kuma ya san ki shi yasa ya haɗa maki wannan."

Ido na ya cika da hawaye da alama mutumin nan raina mun hankali yake son yi. "Wallahi sir ba ƙarya a ciki, ai yana shigowa lakca, za ka iya tambayar shi wallahi Allah." Murya ta na rawa.

"Ai ko na tambaye shi amsa ɗaya ce zan samu. Amma zaki iya sani na mance da komai akan maganar na kuma cike maki Form ɗin da kaina sannan na yi komai da ya kamata." Ya faɗa yana bubbuga 'yan yatsun sa guda biyu bisa tebur.

Cikin rashin fahimta na amsa "Sir bangane me zan yi ba ai" sai hawaye kawai ya biyo fuska ta.

Ya kalleni ya kwashe da dariya "Kuka kike yi? Wuƙa kika gani a hannuna ko me? Je ki kawai, duk lokacin da kika shirya sai ki zo ki ji me nake buƙatar ki yi mun."

Da sauri na fara share hawaye na zagaya ta ɓangaren da yake na tsuguna nesa da shi nace "Don Allah sir kayi haƙuri, gani nayi lokaci na tafiya so kawai nake na gama da wannan matsalar ne, sai kuma na ga abun ba sauƙi ne da shi kamar yanda na zata ba."

"Yayi kyau"

"Ka faɗa mun abin da zan yi ɗin don Allah."

"Kawai ki bani lokaci ko da awa ɗaya ce daga lokutan ki, ita kaɗai ta ishe ni."

Zafin kalmomin da ya furta ne ya jefa ni gefe ɗaya tare da zubo mashi idanuwana tubarkallah cike da firgici sannan nace "What?! Ba ka gane bi ba ne Malam?"

"Ummu Kulsum ce, ko ba ita ba ce? Ƙanwar Muntari" Ya faɗa cikin rashin damuwa.

Razanar da na kuma yi tafi ta farko, ashe yana sane da koma wacece yake ta ba ni wahala irin haka. Duhu kawai nake gani lokacin da na miƙe tsaye, sai kawai na rufta saman wasu tarin takardu dake zube gefe guda a ofishin. Mintina ƙalilan gani na ya washe sosai, na gan shi ranƙwafe a raina kamar yana nazarin ko lafiya ta ƙalau ko a'a, ganin kuma na kallesa sai ya juya ya koma kujerar sa bayan yace na fice masa daga ofis, kar ya sake ganin ƙafata unless na yarda da abin da yake nema ne.

Ba'a hayyacina na koma gida ba. Na rasa yanda zan yi, ga shi maganar tayi mun girma na kasa ko zuwa na faɗawa Mama bare kuma na kira Yaya Muntari. Gara Mama da Yaya Muntari ma, domin zai iya zuwa har ofishin HOD ɗin ya wanke shi, ƙarshe ya ɓallo mun ruwa. Da ƙyar na danne maganar a raina zuwa gobe idan na samu su Fatima sa taya ni tunani, gudun tsautsayi kar wani ya ji ni ina maganar a gida ya sa ko a wayar na kasa kiran su.

****Ƙarin bayani ga ɗalibai, duk lokacin da Abu irin haka ya faru tsakanin ki da wani malami kar ki bar abun a ranki ko tsakanin ki da ƙawayen ki. Ki nemi shawarar babba na kusa da ke sannan VERY IMPORTANT step shine ki yi gathering evidence, ki kai ƘARA! Kar ki sake ki kai ƙara baki da shaidar ya tunkare ki da hakan." Allah raba mu da bara gurbin malamai. Ameen.*****

Washegari da muka haɗu da su ba irin ashar da masifa da Surayya ba tayi ba, kai Darma ma da take shiru shiru a cikin mu ranar sai da naji zagi a bakin ta. Surayya ta ƙara da cewa "Dama wallahi anty Wasi ta faɗa mun ɗan iska ne na ƙarshe, duk wannan wulaƙancin da disgi cover ce kawai! Jiyan nan fa muka yi maganar da ita, tace nace maki ki haɗa shi da wani babba namiji daga gidan ku ki bar bibiyar shi akan maganar, ashe ɗan bunsuru har ya yarda hali! Amma mutumin nan ya cuce mu! Allah ya isa kawai!"

Fatima na gefe sai girgiza ƙafa take yi "Duk ku bar tada magana a nemi mafita, bamu da wurin da za mu kai ƙarar shi ko? Ko da ban sani ba nasan wannan laifi ne mai girma da zai iya ja wa malami kora a jami'a mai mahimmanci irin wannan. 'Yan uwana ina mafita?"

Darma tace "Ni a gani na mu ruɗa shi mana." Gabaɗayanmu muka zuba mata ido na neman ƙarin bayani.

Ta cigaba "To mu yi kwalliya mana tunda mun fi ta cika ido mu je mu same shi mu duka."

Fatima ta zato ido "Nufin ki ya zaɓi ɗaya daga cikinmu maimakon ita? Ai ba hikima a maganar nan, wani sabon aiki za mu ɓallowa kanmu."

Zara'u tace "Yes. Haka nake nufi amma so nake mu yi ta ja masa rai har sai ya gama yi mata abin da ya kamata sai mu zubar da shi gabaɗaya."

Surayya tace "Amma fa Zara'u ki tuna ba wayo muka fi shi ba bare ma yana ganin mu ƙanana."

Zara'u Darma da sauri tace "Yauwa! Shine plan ɗin ai! Ya san bamu fi shi wayo ba, so ba zai yi tunanin shiri ba ne. Mu je gobe mu same shi da yamma."

Hakan aka yi kuwa, washegari da yamma liƙis wurin shida muka doshi office ɗin shi tare da addu'ar kasancewarsa a ofishin nasa. Irin kwalliyar da ƙawayena suka yi ranar ni kaina mamaki suka ba ni, kallo ɗaya za kayi masu ka ɗauka wani bikin kyawawa zasu je domin ni ranar har tantama na fara na wai anya da gaske ne Surayya tafi kowa kyau a cikin mu? Ni kam idona zuru zuru ga zuciya ta cike da fargaba (shi yasa na ƙarfafa neman shawarar babba a lamari irin wannan, don zaku iya ɓigewa da ɓata goma biyar ba ta gyaru ba).

A bakin ƙofarsa sai da na dafe ƙirjina na sakwanni tukunna. Ina murɗa ƙofar ta buɗe alamun yana ciki, a tare mu duka huɗun muka shiga tare da sallama, ko minti ɗaya ba'a kai ba ƙamshi turaren su ya cika ofishin gabaɗaya ya bada wani ƙamshi me daɗi. Basu jira yayi masu izinin zama ba suka zauna, ita kuwa Surayya sai da tayi gaba da baya tare ɗan jujjuyawa kamar me neman wajen zama sannan ta zauna tana kuma taunar cingam, yadda kuka san ta saba harkar nan (ban da ina cikin tashin hankali babu abin da zai hanani dariya).

Ya kuwa bi mu da kallo ɗaya bayan ɗaya a yayinda fuskarshi ke bayyana murmushin nishaɗi bayan ya amsa gaisuwar mu sannan ya tsaida idon shi a kaina yace "Yaya aka yi? Saƙona ne ya iso?" Bai bani damar amsawa ba ya juya ɓangaren da suke zaune, a take ya ɗaure fuska yace su bar masa ofishin sa yanzun nan!

Suna fita ya maido hankalin sa gare ni tare da kafe ni da idanu, ni kuma na sauke nawa idon ina kallon hannayena. Cikin kakkausar murya yace "Ya muka yi da ke? Ban ce maki kar ki ƙara dawowa ba sai kin tabbatar da ranki ya amince ba?" Shiru ya ratsa tsakanin mu tunda ni ai ba ni da abun faɗa masa.

Ya ɗora "Abun haushi ma shine kika kwaso mun ƙawayen ki wai ke me wayo. Watau don sun fi ki ɗaukar ido sai kike tunanin za ki iya rikita mun lissafi bayan na fi kowa sanin abin da nake so da buƙata? Sai abu na ƙarshe, gobe ne kaɗai last chance ɗin ki, shi ma goben ƙarfe shida za ki iya zuwa ki same ni a guest house ɗin cikin makarantar nan. Kina iya tafiya."