KOWA DA ƘADDARARSA

19

by @faddabanan

Yaya Zainabu kam mamakin gani na tayi da magriba ban kula ta ba sai da na idar da sallar magriba tukunna, kuma nayi sa'a Yaya Munnir ma ya shigo a lokacin, ba wani ɓata lokaci na zayyane masu komai da ya faru.

Yaya Zainabu tace "Kwanaki da ya faɗa maki ya je India ƙarya yake ko me?"

Na amsa "Exactly! Da muke hanyar tahowa sai da abun ya faɗo mun a rai, kin ga code ɗin India ai +91 ne, ashe tarkacen lambobin da idan ya kira ni nake ganinsu kamar international number masu lambar starcomms da ta fara da 064 suna yin wani trick sai ki ga numbers rakwacam, ɗazun nan Surayya ta nuna mun yanda ake yi, kuma babu +234 bare ki ɗauka daga Najeriya ne kuma babu +91 a kiran shi bare a ce ai daga Indiya ɗin ne, ashe shi yasa ko na kira shi bana kama shi a lokacin! Abun bai masu daɗi ba.

Su suka mayar da ni gida sannan Yaya Munnir ya zauna da Baba akan maganar kamar yanda Yaya Zainabu ita ma ya zauna da Mama tana yi mata bayani. Kafin su tafi sai da na ɗauko tsarabar kayan da ya kawo mun da ban taɓa amfani da shi ba, ni wallahi na manta da su. Su Yaya Zainabu da Sauda suka dinga ƙyalƙyala dariya don gwanjo ne, irin first grade ɗin nan, ni ban ma san yaya aka yi ba sai tsintar kaina nayi cin 'yan dariyar, amma Nuhu yayi matuƙar raina mun wayo. Kai!

Da safe Baba ya kira ni falon shi, fuskarshi ta gaza ɓoye irin tausayina da yake ji. Ya daɗe yana mun nasiha yana ƙara jaddada mun na kasance daga cikin masu ɗaukar ƙaddara, kar na bari sanadin jarabawar Ubangiji na jefa kaina ga halaka. Ya ƙara tuna mun da cewa duka yanzu shekaruna sha tara ne kawai amma har anyi mun baiko sau uku, ga shi nan kusa babu daɗewa aka koreni daga makaranta. 

Ni kam na ƙarfafa masa gwiwa da cewa Allah bana cikin damuwa, ya ji daɗi sosai ya yi ta sa mun albarka kafin ya sallame ni.

Nuhu kuma kamar yasan me ke faruwa har dare bai neme ni ta waya ba, ni ma kuma hakan take. Sai washegari da yamma ya zo gida, Baba ne ya gan shi domin ba ni da niyyar sake zama da shi ma, ya ba shi kuɗin da aka kawo na aure da kuma ba shi haƙurin cewa na fasa auren sa. Ya kasa magana ya rikice sosai sannan ya roƙi Baba alfarmar son gani na.

Har ƙasa ya tsugunna yana roƙo na na aure shi, bai taɓa son wata 'ya mace kamar ni.... Na kuwa katse maganar shi da cewa "Har matar ka ko?" Da sauri ya ɗago yana ƙare mun kallo.

Na cigaba "Sai yaushe ka yi niyyar sanar da ni cewa kana da mata Nuhu? Sai na tare a gidan ka? Ko sai yaushe? Ni da ka ganni nan bana son rufa-rufa don haka Allah ya ba ka wadda tafi ni. Saduwar alkhairi, sai an jima!" Na juya na doshi cikin gida duk ƙoƙarin maganar da yake yi, hakan bai sa na juya ba bare na tsaya.

Anty Maijidda matar Yaya Mahmoud ta dage ita da mijinta sai na je masu, wai Halifa (ɗan su) yana cigiya ta, tun da dai ba makaranta nake zuwa ba, ƙarin ba ta daɗe da haihuwa ta biyu ba kuma duk ba'a je ba. Duk da bana son zuwa ko'ina sai da nacin su yasa Mama ta takura mun na tafi Minna.

Duka waɗannan abubuwa da suka faru sai naji bana ƙaunar sake dating kowanne namiji, ɓangaren karatu da na dinga ci wa alwashi a baya da burin son na ga na wuce su Yaya Muntari a matakin ilimi yanzu kam duk ya kau, ko sha'awar karatu na daina, kuma ni dai gani nan ina rayuwa amma ba ni da wani buri yanzu. Idan kana neman ɓacin raina ka yi mun zancen makaranta.

Kasancewar na baro littattafan da nake yawan karantawa a Kano, a Minna sai ya kasance ba ni da aiki daga raino sai kallo, kuma yaran da yake suna da mai rainon su sai ya kasance ina da free time da yawa a hannuna. Idan kallon ya ishe ni (ni na fi son karatu akan kallo, Sauda ce mayyar kallo sosai) sai na fara zaman social media sosai da sosai, ina ta exploring different platforms. Hakan ya sanya kusan dukkan kowanne platforms ina da account da su, irin su Facebook, Twitter, Badoo, WhatsApp, path, Instagram da Skype. Abokan hirar da nake samu anan ne yake ɗauke mun kewa, daɗin abun no strings attached, don bana taɓa yarda na yi hira akan abin da ya shafe ni komin rashin mahimmancin abun a rayuwa ta. Kawai sai da na zama social media addict, don sau dubu gara na zauna akan waya ta da nayi kallo.


A Badoo muka haɗu da wani gaye mai suna Aminu Ahmad, ɗan kundila ne. Mun shaƙu ne through our likes, saboda cikin novels ɗin da na lissafa a wall ɗina ba wanda bai karanta ba sai ɗaiɗaiku, sannan ga shi gwanin kallon finafinai ne irin na Hollywood, aka yi sa'a Yaya Mahmoud ma hakan take. Domin duk wani fim da Aminu yace naje na kalla yayi kyau, ina duba kayan Yaya Mahmoud zan samu, da zarar na kalla kuma sai na dawo mu yi discussing movie ɗin tare, hakan ne silar shaƙuwar mu.

Sannan halayyar mu kusan tana kamanceceniya. Yawancin abubuwan da ya ƙi jini za ka ga nima basu yi mun ba ko kuma basu dame ni ba, har da wannan fahimtar da ta daɗa kusanta mu. Duk da wannan abun ya tsaya iya chatting ta waya ne don ba mu taɓa magana ta waya ba, duk kuwa da ya karɓi number ɗina kwanaki.

Shi kaɗai a bare ne na taɓa tsayawa na bawa labarin komai dangane da ni, daidai da zancen Aliyu ya sani bare na sahibi na Yaya Rufa'i, yana kuma bakin ƙoƙarin shi wurin cheering ɗina up whenever I'm down, nasiha ce, misalai da zasu sa nasan ni cikin ni'ima nake, ko kuma ya ɗauke hankali na da hirar wani abu.

Abu ɗaya na lura da shi a tattare da shi, Aminu ya fi buƙatar yayi budurwa wadda suke kusan kai ɗaya. Abu na farko da ya fara ba ni mamaki kenan domin bahaushen arewa ba ya taɓa welcoming wannan idea ɗin bare kuma ya kamanta yi, saboda yarda wa kai da cewa za ta tsufa ta bar shi ko kuma raini zai shiga tsakanin ku.

Nayi zaman Minna na watanni ko tunanin Kano bana yi, bana son dawowa ma bare a yi mun zancen makaranta ashe addu'a ta bata ci ba domin a satin ne Mama ta kira ni wai na fara haɗa kayan dawowa domin shirin fara zuwa school of nursing ta Kano. An kusa zuwa interview, na sanya Yaya Mahmoud ya nemo mun text books ɗin sciences domin shirin aptitude test ɗin shiga.

A lalace nake karatun, kuma ina zaton Yaya Mahmoud ya lura da haka shi yasa ya zaunar da ni yayi mun nasihar cewa ya kamata na ɗau dangana har a aikace, domin rashin sa ka himma kamar ina ƙoƙarin nunawa Allah na yi fushi ne akan abin da aka ƙadarto Mani. Dole ƙanwar na ƙi na maida hankali tunda dai Allah ya bani ƙwaƙwalwa. Lokacin kuma na zuwa Yaya Mahmoud ya maido ni Kano.

Ranar kuwa da naje wurin aptitude test ɗin, ware kaina na yi gefe guda ina kallon sabbin yayayyun ɗaliban sakandare suna ta rawar kai za su fara school of nursing. Takaici duk ya isheni domin ba don HOD ɗin mu munafuki ba da tuni na kama hanyar gama degree. Wannan tunanin ne ya taɓa mun zuciya har ya jawo na fara hawaye ban lura ba.

"Baiwar Allah lafiya kike kuka?" A ka dafa kafaɗa ta.

Na juyo ina goge idanuwa na da tafukan hannayena, don bansan ma wani ya zauna kusa da ni ba. Murmushi na yi mata nace "Halin rayuwa ne kawai, taƙaici na ma bai kamata a ce nayi kuka ba amma halitta ta ta ɗan adam ce ta sanya rauni na ya bayyana....mmmm ya sunan ki?"

"Badariyya. Ke fa?"

"Ummu Kulsum"

Kun san abin ku da mata, kafin a shiga mun sake da juna muna ta hira amma a iya abin da ya shafi zancen makaranta da kuma ta duniya, 'yar Kaduna ce.

Test ɗin ta kasance mai matuƙar sauƙi gare ni ko ba domin komai ba a jami'a sai da na kai mataki na uku sannan na bari ko banza dole yayi mun sauki sannan na ɗan taɓa karatu a Minna kafin na dawo, har Badariyya na taimakawa ta samu damar ƙarasa wanda ba ta gama ba.

Muka jira shi ma aka yi interview ɗin sannan muka yi sallama da ita na wuce gida, ita kuma ta wuce tasha domin komawa Kaduna a ranar. A yinin ranar kaɗai har mun saba, kuskure ɗaya muka tafka shine rashin karɓar lambobin juna, tace na bata lamba ta sai wani abun ya ɗauke mana hankali.

Tun dawowa ta Kano Aminu yake damu na yana son zuwa mu gaisa ni kuma bana so. Duk inda namiji yake yanzu na yafe shi, bana fatan wata alaƙa ta shiga tsakanin mu ma bare har kalmar so ta fito. Na fi ƙaunar kasancewa tare da shi a chatting ɗin kan a gaske. Don haka na dinga zame mashi har dai ya gane sannan yace zai ba ni mamaki.

Tunda na baro school of nursing ko ta kanta ban ƙara bi ba. Na bar wa su Mama tunda su suka siyo Form ɗin, da kuma bin hanyoyin neman admission ɗin.

Kullum da safe sai dai na ga Sauda na tafiya makaranta, karatun ma sauri na ga yake yi, domin yanzu a mataki na uku take su kuma 'yan biyu yanzu ajin su biyar a sakandare. Ina fara tunani irin wannan nake kautar da shi daga raina domin bana son zama mara tawakkali domin zai iya yin kuka. Haɗuwar mu da su Fatima duk ta ja baya, saboda yawan ganin su a halin yanzu fami yake mun.

A ƙarshen satin Yaya Naziru ya zo hutu daga Abuja, shi kuma ya bani shawarar na sake siyan Jamb Form domin komawa makaranta. Ban san lokacin da na kama kuka ba. Na dage ni da BUK sai a lahira idan ana yi. To tsautsayi ya sa na koma, HOD ya san na koma ya sake samun damar rama abin da nayi mashi?

"Ce maki aka yi dole can ne kaɗai makaranta? Ai ke kika bashi dama. Ba don Mama ta dage a haƙura da gaba ki kai shi, ko ance maki ba na gaba a makarantar? Rashin ƙwaƙƙwarar shaida ne da kuma dagewar da Mama tayi ya sanya na bar zancen kawai." Ya ƙarasa da tsaki ya miƙe ya bar ni.

A satin Yaya Zainabu ta haihu a yayinda na kwashe kaya na na koma gidan ta da zama baki ɗaya. Ranar suna waya ta na kashe na kulle ta a durowa, kar tsautsayi yasa naje na zubar ko a sace mun a zo ana wallahi tallahi. Su Surayya gabaɗayansu sun zo, sai a wannan lokacin na san nayi kewar su sosai. Sun kuma shaida mun an sanya bikin Zara'u Darma da Umar ɗin ta, haka ma tsakanin su da Fatima babu nisa, an kuma kusa yi, kenan ni da Surayya muka yi saura. Sai goman dare na samu damar kwanciya bayan nayi wanka sannan na zaro waya ta na kunna.

Saƙonnin Aminu na fara dubawa.... "Ga ni tsaye ƙofar wani gida mai fentin siminti da baƙin gate. Ina iya hango bishiyar mangwaro ta ɓangaren hagu na tana ɗan leƙowa waje ta katanga sannan ga wata farar mota mai lamba AZ 325 NSR....kuma gidan kaman a Hotoro yake🤔"

Sandarewa nayi da wayar a hannuna, tsaf gidanmu ya kwatanta mun sannan motar Yaya Naziru ce ya sake dawowa Kano, kuma ina zaton bayan ya bar gidan suna ne ya koma gida shine yayi parking a waje har Aminu ya ga motar.

Da sauri na mayar da amsar maganar ta shi da "Kai! Ta yaya ka gane gidanmu?"

Wannan ce ranar farko da muka fara waya, kuma dariya yayi ta yi mun amma ya ƙi faɗa mun ta yanda ya gano. Cewa yayi kawai na bari sai ya zo sai yayi mun bayani.

Kwana huɗu tsakani ya zo gidan Yaya Zainabu ya same ni, wannan ni ce nayi masa kwatancen, yana da kirki ƙwarai da gaske ga tsokana. Ba'a daɗe sosai ba muka daɗa wata shaƙuwar sannan na fara jin shi a raina ba mamaki saboda sauƙin kansa.

Ranar da Yaya Zainabu ta yi arba'in ne na fara tattara kayan domin komawa gida. Duk ƙoƙarin su ita da mijinta na son su riƙe ni abun ya ci tura. Da kyar suka lallaɓa ki na yarda zan ƙara sati ɗaya.

A ranar kuma da yamma ta sanya ni na takara jifatu domin siyayya. Ni ce riƙe da Najwa (sunan bebin na ta kenan). Muna ta zagaye tana ɗaukar abubuwan da take buƙata.

Ta madubin gaba na na hango shi, dogo ne wankan tarwaɗa yana da manyan idanu da suka ƙawata fuskar ta shi sannan hancin ma ya dace da fuskar. Gaba na ne ya faɗi, kallon sani nake yi masa amma na rasa wurin da na san shi.

Kamar ya san shi nake kallo sai naga ya waigo mun haɗa ido ta madubin. Yayi murmushi kaɗan ya juya ya cigaba da abin da yake yi. Murmushin ne ya ɗaure mun kai amma sai kawai na basar na juya neman ta wurin da Yaya Zainabu take.

Har muka gama siyayyar mu muka ƙarasa wajen biya ko kalar shi ban sake gani ba. Na rasa dalilin da yasa na kasa kautar da fuskarshi daga raina amman tabbas na san fuskar.

Muna daidai ƙofar fita ina ƙoƙarin ƙara rufe baby Najwa saboda iskar waje, wayata ta zame ta faɗo ƙasa, ita kuma Yaya Zainabu har ta kai wurin mota tana zuba kayan da muka siya ciki.

Na rasa ta yanda zan yi na duƙufa don na ɗauko wayar ga shi har baturin ya cire, sai kawai ganin shi nayi kamar walƙiya a gabana yana tattara mun wayar da ta tarwatse, ya kuma haɗa tare da miƙo mun yana mun murmushi.

Ban kai ga karɓa ba na tambaye shi "Do I know you? You look soooooo familiar."

"Tun a ciki nasan kallon sani kike mun. But ba ni kika sani ba, kuskuren ki ɗaya da sauran. Karɓi wayar ki." Ya faɗa yana murmushi.

Sai hakan ya daɗa ɗaure mun kai na miƙa hannu domin karɓar wayar a lokaci guda na cigaba da magana "Wane kuskure kenan? Ka daɗa ruɗar da ni."

Wannan karon dariya mai sauti yayi sannan yace "Kina kallon finafinan Hollywood ko?"

A zayyane a fuskata ruɗani ne kwance nace "Kana nufin kai actor ne ko kuma ya ya?"

Hannunsa ya sa a bakinsa don rage dariyar da yake yi yace "Kin sani dariya da yawa, nope! Amma ai kin san Idris Elba ko?"

A take ruɗanin fuska ta ya washe ni ma na fara dariyar sannan nace "Exactly! Wallahi kuna matuƙar kama da shi, banbancin ya fi ka cikar jiki da kuma ƙila tsawon."

Ya cigaba da murmushi "In ce ko 'yar jarida ce ke?"

"A'a, ko ɗaya....." Ham ɗin motar Yaya Zainabu ne ya katse mun magana ta, don wallahi na manta da ita gabaɗaya.

A gurguje na yi masa godiya tare da tafiya wurin motar, ko da na jiyo kafin na shiga motar ko alamar shi babu kwata-kwata.

Muna hawa titi tace "Uwar samari, wannan kuma waye?"

Ina dariya na ba ta labarin yanda muka yi da shi, ita ma dariyar tayi tana girgiza kai tace "Shine na cikin prom night da sometimes in April ko?"