KOWA DA ƘADDARARSA

21

by @faddabanan

Kwana na biyu ina baccin gajiya, daidai da waya ta a kashe na bar ta. Baccin har ya fara damun Mama, a rana ta uku baccin ta hana ni tare da sa ni yin girkin rana alhalin ga su Sauda a zaune suna kallo. Na gama zumɓure-zumɓuren jin haushin an hana ni baccin yau kafin daga baya na warware.

Da yamma sai ga kiran Yaya Zainabu domin jin ko ina gida, wai za ta yi mun aike, nace ina nan. Ko awa ɗaya ba'a kai ba ta sake kira wai na leƙa ƙofar gida ga saƙon nan an kawo.

Hijab ɗin Mama na sa na fice duk da ina jiyo ta tana cewa na dawo na cire mata abun ta, yaushe muka fara sharing kaya? Ina dariya na ƙara sauri ina cewa "Mama ba fa kaya ba ne, kuma saƙo zan karɓo a ƙofar gida kawai."

Kai! Amma Yaya Zainabu ta kwafsa mun. Fa'iz ne tsaye ya jingina da motar shi, hankalin shi kuma na kan ƙofar gidan. Na rasa ta yaya suka yi magana da su Yaya Zainabun. Ko cikin harabar gidan mu ban gayyace shi ba, ƙarasa fitowa wajen nayi kawai.

Kallon da nake yi masa ya sanya ya ke dariya tare da murza hannayen shi kamar mai jin sanyi yace "Wannan kallon fa 'yan mata?"

"Mamakin yanda ka biyo ta wurin su Yaya Zainabu nake, a ina ka samu lamba ɗin su?"

Ya amsa "Ni fa bamu yi waya da ita ba sam." Kuma bai ƙara komai akan wannan ba.

"Amma ai ita ta fiddo ni, tace mun akwai saƙo a waje."

"Yes, ni ne saƙon. But ni gidansu na je."

"Gidan su fa?!" Na zazzaro idanu alamar mamaki.

"Tubarkallah! Ga ki da ido, ga shi kin zaro shi. Kash! Dama na ɗauke ki hoto."

Na zumɓura baki tare da rungume hannayena na karkata gefe ɗaya nace "Ba amsa kenan ko? You are using style to avoid the question."

"Wannan shagwaɓar ta ki birgeni take wallah. Ammm.... Kin gane ko? Gidansu kusa da gidan wani abokina ne ashe. Na je chan sai kawai muka haɗu da Munnir, shine ma ya fara gani na ya tsaya mu gaisa. Shi ke nan fa."

"Shi kenan?" Na tambaya

"Au! 'Yar jarida ta! Na manta ke ce ai, ya dage sai mun ƙarasa gidan shi, shine na nemi ganin ki and the rest is history. Amma yayan nan naki yana son ki matuƙa domin na sha jan kunne kala-kala kafin ma ya bar ni na zo gare ki." Ya ƙarasa cikin murmushi.

"Ka cika murmushi." Baki na ya suɓuce ya faɗa ba tare da na yi niyya ba.

"Ni kaina na san murmushi na ya yawaita a kwanakin nan kuma ke ce sanadi. Murmushi nake yi duk lokacin da na tuno ki bare kuma yanzu da muke tare, shi kam bana sanin ma ina yi."

Ba mu daɗe tare ba nace ina da aiki cikin gida muka yi sallama ya tafi. Ba yanda bai yi da ni na ba shi lambar waya ta ba amma sam na ƙi, kuma ni kaina ban san dalilin hanawar ba.

Ina shiga falo Sauda ta wani ta so tana tambaya ina saƙon, uwar kwaɗayi ta ɗauka abun ci ne. Sai da na gama tsokanar ta sannan nace Fa'iz ne saƙon, kafin ma ta amsa har Hassana ta cafe zancen da cewa "Don Allah Yaya Ummu ki auri gayen nan, yana da kirki da iya zama da jama'a kuma ga shi tubarkallah mai kyau da shi, kin san namiji dogo baƙi ya fi farin namiji kyau." Sakin baki na yi ina kallon ta don mamakin zancen da ya fito daga bakin ta.

"Inye?! To duk ina kika san haka Malama?" Na tambaya. Sauda na gefe tana mana dariya kafin ta ceci Hassana da jefa na ta zancen na bin bayan maganar Hassana akan Fa'iz. Duk abin nan da muke Mama na zaune amma ko kula mu ba tayi ba.

Ban ɗauki lamarin Fa'iz da gaske ba, saboda bana son wani abu ya sake faruwa, gara na cigaba da lallaɓawa da Aminu da muke tare.

Sati biyu bayan nan sai ga Aminu ya zo gida gani na, rabo na da shi tun lokacin bikin Fatima amma muna waya da chatting da muka saba. Mun daɗe zaune a harabar gidan mu muna ta raha, kuma kasancewar Hussein mutumin Aminu ne duk tare da shi muke zaune ana hirar. Maganar wani fim muke, infact ma musu ne, shi da Hussein suna ɓangare ɗaya ni kuma na dage ba haka ba ne, hankali na gabaɗaya yana kan maganar har ban lura da mutumin da yake tahowa wurin mu ba sai sallama kawai na ji.

Matuƙar mamakin ganin Fa'iz nake da har magana ta ta maƙale na tsaya ina ma shi kallon tuhuma, shi kuma a ɓangaren shi ya miƙa hannu yana musabaha da Aminu da Hussein, ya kuma matsa can kusa da gate alamar jira na yake yi. Ni mamaki yanda ma ya shigo gidan kai tsaye nake yi, yanzu haka babu mamaki Yaro (mai aikin compound ɗin gidanmu) ne ya nuna masa wurin da nake (anan muke zance), saboda bai daɗe da fita ba ai ya shigo.

Na rasa wurin da zan sa kaina, idan na tashi ban kyauta wa Aminu ba, haka idan na zauna na yi wulaƙanci, don haka sai na cigaba da zama ina auna wanne ya kamata na yi. Muryar Aminu ta katse ni "Hussein wannan ba baƙon ku ba ne?"

"An ya? Ni ban taɓa ganin shi ba, na ɗauka baƙon Yaya Ummu ne ai." Ya faɗa yana kallo na.

Sai da nayi gyaran murya sannan muryar ta buɗe nace "Eh, Fa'iz ne, ina zuwa bari na sallame shi. Minti biyu don Allah." Na miƙe ba tare da na kalle su ba.

Ina ƙarasawa wurin da yake tsaye ban jira ya fara magana ba nace "Mu je na raka ka, haka kawai za ka kashe mun aure." Har na gota shi yana tsaye yana kallo na ba shi da alamar biyo ni, don haka na dawo da baya na jawo gefen rigar shi sai kawai ya biyo ni bai yi musu ba, nasan kuma don ya ga dama ne don ban isa na iya jan shi ba. Ban saki rigar ba har sai da muka fita gate, duk nayi wuri-wuri alamar mara gaskiya.

Da alamar mamaki ƙarara a fuskar shi ya ce "Wannan wane iri tsoro kike ji game da saurayin ki Ummu? Kin ga yanda kika rikice kuwa? Wannan tsoron ya wuce na halal ya zama na cutarwa ai."

Da ɗan sauri na na amsa "Ba haka ba ne. Ina daɗewa ban haɗu da shi ba ne, yau kuma ya zo bai kamata na yi wani abu da zai sosa masa rai ba. Me yasa baka faɗa mun zaka zo yau ba? Da kuma da ka zo bana nan fa?"

Sai ya fara murmushi wanda ya fi kama da dariya yake riƙewa yace "Ikon Allah! To ina zan faɗa maki bayan kin hana ni lambar ki Ummu?"

Cikin hanzarin na karanto ma shi lambar ba tare da na jira ya ɗauko wayar shi ba, domin ba son ba shi nake ba, yanzu ma don kar mu ɓata lokaci ne wajen ja-in-ja, sai na juya na dawo gida abu na. Ban jiyo muryar shi ta amsa ba kuma ko sau ɗaya ban waiga don ganin ko ya doshi motar sa don tafiya ba ko a'a, buri na kawai na koma na iske Aminullahi.

Wannan karon shi kaɗai ne zaune da alama Hussein ya shiga cikin gida. Na zauna har na kusa mintina biyar Aminu bai tanka mun ba yana wasa da 'yan yatsun shi fuskar shi wasai ba wani alamar damuwa ko wani abu. Na tsare shi da ido ya ƙi kallona, don haka na tambaya "Akwai abin da ya ke damun ka ne?"

"Wani abu kamar me kenan?"

"Na ga ka yi shiru ne."

"Hmm! Babu komai, magana ta ce tayi bacci."

Sai maganar shi ta ba ni dariya "Dama magana tana bacci ne?"

Ya tsare ni da ido sannan yace "Ummu Kulsum wannan ba wanda na gani ranar dinner party ɗin Fatima ba ne?"

"Eh, shi ne"

"Idris Elba na Jifatu ko?"

Na ɗan zaro ido na amsa "Ta ya ka gane shi?"

"Haba Ummu, kana ganin shi za ka ga kamar ai, sannan idan na tuna da kyau ranar da kika ce mun kun haɗu ai ba ki bashi address ko phone number ɗin ki ba ko?"

"Eh, haka ne." Na zuba mashi ido ni ma saboda nasan ina tunanin shi ya dosa.

"Ya aka yi kika gayyace shi bikin Fatima to? Ko akwai abinda ban sani ba da ya kamata na sani?" Ya faɗa.

Abin da yake ba ni tsoro da maganar nan shine yadda Aminu yake magana a nutse da murya ƙasa-ƙasa sannan fuskar shi ba alamar ɓacin rai bare jin zafi, hakan kenan na nuna shi bayani yake son nayi mashi dalla-dalla ya fahimta ba wai yana neman na ba shi haƙuri ba ne.

Gaba na yana faɗuwa nace "Wallahi! Ka ji na rantse ba ni ce na gayyace shi ba, a wurin na gan shi."

"Na yarda, saboda iya sanin da nayi maki zan iya ƙirga sai nawa kika rantsuwa akan wani abu, but still me yasa na ga kuna ta zagaye a hall ɗin tare da shi? Kuma wai a ce duk ƙuiya irin ta Najwa tana ganin shi ta je wurin shi? Alamu ne na ta san shi kenan ai."

Ban ƙara barin shi yayi wata tuhumar ba, na hau warware mashi komai har zuwa ganin da nayi mashi na ƙarshe da kuma na yau, kuma nayi matuƙar sa'a ya gamsu. Daɗin Aminu kenan, in dai matsala za ta tashi kuma ka kwantar da hankali ka yi masa bayani zai saurara kuma zai fahimta.

Kafin ya tafi kuma sai da ya jaddada mun "Ummu ba na buƙatar sake haɗuwa da gayen nan a wurin ki. Ba wai don kar kice na so kai na ba, so nake kawai Ku rabu, kowa ya yi separate ways ɗin sa, kin ji, please?"

Kafin na kwanta ma haka ya sake jaddada mun bayan ya kira ni ta waya, har abun ya fara ba ni mamaki domin Aminu ba irin mazan nan ne masu zafin kishi ba, nasan ya iya ɓoye damuwarsa akan komai.

Abin da ya ƙara tsorata ni a lamarin ma shine sake tashi na da yayi wurin ƙarfe biyun dare ta waya tare da neman izini na na son ya turo magabatansa yanda hakan zai katange masa ni. Da kyar na samu ya ji rarrashi na har ya kwanta bayan na daɗa tabbatar masa ni tashi ce da izinin Allah.

Bayan na koma baccin bayan sallar asuba sai ƙarfe tara na tashi, abin da ya faru jiya ne yake ta dawo mun na ƙasa barin gadon ma bare na tashi. Ƙarar waya ne ya katse mun tunani, na ɗauka Aminu ne again.

Lamba ce ba suna kuma abun mamaki Fa'iz ne! Lokacin da na faɗa mashi lamba ta fa wayar shi ba ta hannun shi, sau ɗaya jal na faɗa kuma cikin sauri. Don haka ban san lokacin da nace "Kai! Ta yaya ka riƙe lambar nan?" Sai ga ni a zaune kan gado na.

Ina jiyo sautin dariyar sa "Dama ba kiyi niyyar ba ni ba kenan? Allah ne yasa na haddace nan take sannan ba ki san yaya IQ ɗina yake ba ai."

Kafin dare Fa'iz ya kira ni a waya kusan sau takwas. Daren kuma Aminu ya sake sa ni gaba akan zancen neman izini. Sanin cewar ba zan zaɓi Fa'iz (da ko manufar shi a kaina ban sani ba) na bar Aminu ba, ya sanya nace masa yau ɗin nan tunda dare bai yi nisa ba zan sanar da Mama, abin da suka yanke zan kira shi na faɗa masa.

Ƙarfe takwas daidai na safiya Aminu ya sake tashi na domin jin yaya muka yi da Mama. Na shaida masa tace za ta yiwa Baba maganar sannan za ta sanar da ni da safe, zuwa yanzu kuma ban ma je wajen ta bare na ji me aka ce. Kar ya damu har kullum Baba zaɓi na zai bi, don haka ba shi da damuwa.

Abu kamar haɗin baki yana ajiye wayar kiran Fa'iz na shigowa. Ni dukkanin su neman dagula mun lissafi suke yi, ko dai shaiɗan na neman rikita mun lissafi ne yanda zan rasa su su duka? Haba wannan wane irin abu ne? A take ragowan baccin da yake idona ya tarwatse.

Zuwa wurin azahar na yi wa Aminu text cewa Mama tace su zo duk lokacin da suka shirya babu damuwa, amma su ba mu kwana uku tukunna (tun akan Nuhu Baba ba ya wasa da bincike, nasan abin da za'a yi kenan don ya yi mun tambayoyi ga me da Aminu sosai).

Minti uku kacal tsakani ya kira ni, murnar shi ta kasa ɓoyuwa. Kasancewar yana kan aiki ne ma yasa a gurguje muka yi magana, kafin mu yi sallama kuma ya mun alƙawarin ya na tashi zai kira ni. Kuma a ranar cikin kwana na huɗun suka kawo kuɗi.

Yawan waya tsakanin mu sai ya ƙaru, shi kuma ta ɓangaren Fa'iz ya san an kawo kuɗi na amma ya ƙi daina kira na, kaffa-kaffa nake ta yi bana son Aminu ya san har yanzu muna magana, amma sai yace mun "Daɗin hira nake ji da ke Ummu, ki haƙura mu zama friends zuwa kafin ranar ɗaurin auren ki tun da daga ranar shikenan ni da ke kuma."

Yawan wayar shi ta ɗarsa mana shaƙuwa (duk da nasan bai kamata mu ci gaba da magana ba both Islamically and culturally), amma duk nacin sa bana bari mu haɗu don kar tsautsayi ya sa su haɗu da Aminu. Nasan komai da ya dangance shi kama daga aikin shi zuwa rayuwar shi, haka komai na shi na ranar ina sane kamar irin wurin da zai je ko ya je komai dai, zai faɗa mun abu kafin yayi ko kuma da daddare ya bani labarin komai da yayi a yinin ranar. Yawan wayar da nake da Fa'iz ba na yi da Aminu (ai kun san shi mun fi magana ta chatting ko?).

Sannan a gida su Sauda da Hassana sun fi son Fa'iz, Hussein ne kawai ɗan gidan Aminu. Ni dai kawai addu'a nake Allah zaɓa mun ma fi alkhairi.