25
by @faddabanan
A cikin satin Yaya Mahmoud yayi mun waya yana tambayar tsari na game da makaranta, nayi ta inda-inda sai shi kuma ya kama faɗa akan yadda na ƙi mayar da hankali ko ƙila don na ga kitchen ɗina yana kawo mun kuɗi, zai yi magani na kwanan nan. Nan wurin da yayi faɗan shi anan na zubar da shi, in dai zancen makaranta ne kowa zai gaji ya bar ni, wa yace sai na yi makaranta zan samu ci gaba a rayuwa?
***************
Sattitika bayan haka, ranar Fa'iz ya baƙunce ni da yamma, ba ku daɗe ba sai ga kiran Humaira ta buƙaci ya haɗa mu ta waya jin yana wuri na. Ta roƙe ni alfarmar cake take so na yara 'yan shekara huɗu, na barka da zuwa, kuma nayi masu kwalliyar da zai ja hankalin yara, za ta kuma faɗawa Fa'iz ranar da take so, sannan muka yi barkwanci tare da sallama.
Fa'iz ya fara mitar 'yan gidansu sun fara takura mun, ba ita kaɗai ba ce mai son a yi mata abu irin wannan ba, birki yake ja masu don basa rabu da party na cikin gida.
Na nuna mashi ba damuwa ya dinga bari su suna kawowa aikinsa ne amma sam ya ƙi yarda. Da na dage sai yasa nayi alƙawarin zan dinga karɓar kuɗin aikin tukunna domin ya san halina.
Ranar Alhamis Humaira ta faɗa mun take so da yamma, don haka da safe na yi masu. Ni kaina abinda nayi ya burge ni don haka sai da na ɗauka a waya ta. Cake ɗin da nayi masu guda biyu ne, na farkon shape ɗin kan TOM shi kuma na biyun kan JERRY amma bai kai na farkon girma ba, an kuma rubuta 'welcome back home' akan kowanne.
Ranar da aka tafi kai kuɗin gaisuwar Yaya Naziru, don zumuɗi sai da ya baro Abuja ya zo kamar wanda aka ce auren shi yazo. Muna ta gulmar shi ni da Hassana muna dariya.
Jin cewar Hassana za ta je Sahad stores sai na bi ta kasancewar ina buƙatar siyan abubuwa da yawa, huɗu da rabi a ciki tayi mana. Tunda muka ja keken zuba kaya kowa ya kama gaban shi, domin abin da take buƙata ba irin wanda nake nema ba ne.
Idona ne ya kai kan wasu kyawawan yara, da gani wa ne da ƙanwar sa. Tana gudu yana bin ta tana ta ƙyalƙyala dariya, sau biyu suna wuce ni ina kuma jiyo muryar Mamansu daga nesa tana kwaɓar su amma sun ƙi sauraron ta.
Ƙaramar ce ta kama ƙafata tana dariya, ganin da mutane da yawa kuma ba daɗi yaro ya dinga gudu don za'a iya buge su, sai na ɗaga ta na sanya ta a cikin cart ɗina sannan na waiga baya na wurin da Mamansu take nesa kaɗan da ni, kafin na kai ga magana tace "amma kin taimaka mun, na kasa hana su daina gudun nan."
"Ayya, babu damuwa. Ya sunan su ne?"
"Ita Maama shi kuma Amir."
Ganin 'yar uwarsa a sama shi a ƙasa sai ya fara taɓa mun kafa yace "Ni ma anty za ki ɗora ni idan Maama ta sauka?"
Nace "Eh, idan ka daina gudu ba."
Kusan a tare muke tafiya da Mamansu, ina ɗan gaban ta kaɗan ita kuma tana biye a baya. Ta riga ni gamawa da alama sun riga mu zuwa, lokacin da ta je biyan kuɗin sai na sauke Maama na ɗora Amir na ɗan tura shi kaɗan har ta kammala ta zo suka tafi bayan sun yi sallama. Har suka fita suna ɗaga mun hannu tare da faɗin "Anty bye bye."
A falo da muka dawo muka iske Yaya Naziru yayi reshe-reshe sai maganar auren yake yi wa Mama, ɗokin shi ya daina ba ni dariya yanzu, na fara jin haushin abin da yake don haka ban tsaya ba kwata-kwata a ɗakin, ɗaki na wuce domin yin wanka don tsananin sanyin da ake yi ya kusa haukata ni. Wankan ruwan zafi ne kaɗai zai rage mun shi. Tunanin Fa'iz kaɗai nake yi, nasan jikin shi baya son sanyi kullum yanzu da safar ƙafa, safar hannu, hula da muffler ta wuya yake yini duka wannan bayan rigar sanyi.
Kamar yana kallon me nake yi domin ina kammala komai kafin kwanciya sai ga wayar shi, don haka bargo na shige tare da amsa wayar "Hello?! Fa'izuna."
Murmushi mai sauti yayi yace "Ummu na! Ke ma kin zan 'yan gidanmu kenan?"
"Yauwa, me yasa suke kiran ka Fa'izunmu? Kuna da yawa masu irin sunan ne a family ɗin ku?"
"Ummu ho! Na yi kewar tambayoyin nan naki ' yar jarida ta. Aikin Humaira ne wallahi, ita ta fara yanzu kuma kowa Fa'izunmu yake kira na." Ya amsa.
"Ni Fa'izuna ya fi daɗi."
"Ummu na! Muryar ki har ta ɗumama ni, sanyin nan ne ya gigita ni sai kawai na kira ki ashe maganin sanyi na kira ma."
Ina ɗan dariya nace "Bari zolaya ta mana, muryar ka har yanzu ba ta daina rawa ba, ina jiyowa fa. Me kayi don rage sanyin yanzu to?"
"Na sa rigar sanyi, heater a kunne, ga safa hannu da ƙafa da hula kuma ina cikin bargo."
Dariya ce ta sarƙeni sannan nace "Kai! Sai kace kana ƙasar waje? Amma duk wannan shirin kuma sanyin bai barka ba? Gaskiya Fa'izuna daban kake. Wanka da shayi fa?"
"Na yi wanka, amma bari a bi shawarar ki a nemo shayin."
"Yauwa ko kai fa."
"Ni duk ba wannan ba, fata na bai wuce a ce ki yarda bikin mu ya zamo a kusa ba, ɗumin jikin mutum idan ya haɗu ya fi na heater fa."
"Sanyi ya zo konji ya fara aiki ba."
Yace "Bari nayi shiru kafin kice 'lust' ne ba 'love' ba. Ƙarfin kiran wayar ma yaya na ne ya dawo gari, ina so mu je ku gaisa da shi da matarsa, daga nan zuwa ƙarshen sati mai kamawa sai ki faɗa mun ranar da kike free sai mu je. Don Allah Ummu kar ki ce a'a, this is very important to me." Don haka sai na zaɓi juma'a kafin muka yi sallama.
Ranar talata na je wurin Yaya Zainabu, ita ta bani shawarar abin da zan kai masu. Ina hanyar komawa gida sai hankali na ya kai kan Downtown Take Away dake nan kan Maiduguri Road, dama tun jiya nake sha'awar burger da shawarma kuma ba na wanda zan yi da kaina ba, don gandar shiga kitchen nake ma kwana biyu kenan, don haka a wurin na sauka.
Ashe rabon ganin Aminu ne, domin ina shiga na ci karo da shi tare da wata yarinya baƙa siririya kuma doguwa. Da zan share kaman ban gane shi ba duk da mun haɗa ido, sai kuma don kar ya ɗauka kishi nake yi sai na ƙarasa wurin da suke da alama jiran a haɗa masu suke yi, ina fara'a muka gaisa.
Cikin ƙoƙarin ba ni haushi yace "Ummu ga mata ta Fatima fa, ƙanwar Muhammad ce."
Ɓoye mamakin jin cewar yayi aure a lokacin rabuwar mu nayi sannan nace "Maa shaa Allah, inye ango ka sha ƙamshi! Ba ni da labari da na halarta ai. Amma kai na yi maka uzuri, Muhammad ya kama ta na kama don shi ya kamata ya faɗa mana. Allah ya sanya alheri kuma ya bada zuriyya ɗayyiba."
"Ameen" matar shi ta amsa, a yayinda shi kuma yayi kasaƙe yana kallo na.
A daidai kuma lokacin ne aka sallame su, suka yi mun sallama suka tafi. Ni duk burger ɗin ma ta fitar mun a kai, idan nace maku zancen aurensa bai buge ni ba wallahi ƙarya nake. Haka na karɓi kayan da na shigo siya zuciya ta na suya, sai su Hussein na bawa don kasa ci nayi kuma na ja baki na na kulle don zafin maganar ba za ta bar ni nayi zancen abun da kowa ba, har sai nayi hawaye na ji sauƙi-sauƙi a zuciya ta.
***************
Na san ba wata kyauta da ta kamaci na kai wa gidan yayan Fa'iz sama da abin da na iya, watau kayan gashi. Don haka su nayi da yawa na zuba a babban kwalin da nake zubawa kwastomomina. Da yamma wurin biyar ya zo muka tafi. Irin jan kunnen da Mama ta dinga yi mun har sai da nayi nadamar yarda da nayi zan je. Na san don Hassana na makaranta ne, da dole za'a ce mu tafi tare.
Gidan a unguwar Gandu yake ta wurin makarantar First Grade. Gidan shiru har muka isa falon gidan, sai a lokacin gaba na ya fara faɗuwa don tsoron kar dai abin da ake yi wa 'yan mata ne ya zo kaina yau, don ban ga alamar cewa da mutane a gidan ba.
Na ɗosana duwawu na a kujerar cikin shirin ko ta kwana, yanda gudu ba zai yi mun wahala ba. Wani sanyi na ji ya ziyarce ni saboda jiyo muryar yara, na saki ajiyar zuciya har ta fito a fili, hakan kuma ya sa ya juyo ya kalle ni tare da murmushi. Nasan ya gane tsoron me nake ji kenan.
Yaron da gudu ya shigo ya ɗane jikin Fa'iz bayan ya jiyo muryar shi. Yaron yace maman shi na kitchen sannan Fa'iz ya sauke shi yana umartar shi da ya gaishe ni. Ina kallon fuskar yaron sai na rasa a wurin da na san shi, kuma suna matuƙar yanayi da Fa'iz. Sai da naji yana ƙwalawa 'yar uwarsa kira na gane su "Maama! Maama! Ki zo ga anty." A take kuma nace "Amir?"
Fa'iz mamaki ya kama shi ta inda na san yaran. Ina dariya nayi mashi bayanin haɗuwar mu dasu a Sahad ƙarshen satin da ya wuce. Maama tunda ta ganni ta manne mun ta ƙi sauka daga jiki na.
Mamansu kamar haɗuwar mu ta farko sarkin fara'a ce sannan ga son hira, anan ɗin ma hakan take. A take ta buɗe kwalin abin da na kawo masu, sai da tayi wa Fa'iz burki domin ci yake bil haƙƙi ba daga ƙafa, tace "Uncle Fa'izunmu ai sai ka cinye mana kayan daɗin da ƙanwata ta kawo mana. Ya isa haka." Ni kam dariya nake ta yi masu.
Shi kuma ya amsa "Shikenan tunda kin hanani amma ba za ta ƙara yi maki cake ba. Ai kin tuna TOM & JERRY cake ɗin su Amir ko? Ita ce tayi."
Da sauri ta juyo ɓangarena "Don Allah da gaske yake? Da kyar Amir ya bari aka yanka. Kin san santin cake ɗin da aka yi a gidan nan? Kar ma babansu ya ji labari, ya fi kowa ci ma."
Fa'iz har da murnar shi yace "Ina ga muna aure restaurant za mu buɗe kawai. Kullum sai ƙara ƙwarewa kike yi."
A gidan muka yi magriba sannan ta dage dole sai mun ci abinci, ina jin nauyi amma haka na daure. Muna shirin tafiya maigidan ya dawo. Hakan ya sanya dole muka koma muna jiran shi ya zo mu gaisa kafin na wuce.
Mamansu Amir tace na bata number ɗin da zata kira idan tana son kayan gashin fulawa. Kati na na ɗauko na juya bayan na rubuta personal number ɗina sannan na bata. Tana karɓa yana shigowa tare da sallama.
Kaina a ƙasa na gaishe shi, duk da ban kalle shi ba nasan ba wani babba ne domin tsakanin su da Fa'iz bana jin ya kai shekara biyar.
Mayafi na na ɗan daɗa jawowa domin kunya sannan nayi mashi barka da dawowa. Bayan ya amsa sai ya cewa Fa'iz "Fa'izunmu amaryar nan taka akwai kunya, ni na ɗauka an daina rufe fuska yanzu ai, bare kuma ni da nake a matsayin Yaya."
"Kai kaɗai take jin kunya gaskiya, don tun ɗazun suke hirar su da maman Amir." Fa'iz ya amsa shi.
"Idan kuma muka gamu a hanya ban gane ta ba ai shi ke nan."
Matar shi sai ta amsa "Haba Sweetheart, ku da zaku aure ta ma har sai kun gaji da ganin ta."
A haka muka yi sallama domin shirin tafiya gida. A yayinda na ɗan ɗaga idona domin ganin kamar yayan Fa'iz, so nake na gani ko suna kama... A take tunani na ya daskare domin fuskar ALIYU da take fuskantata. Rabon da na gan shi tun ranar da muka raka shi airport sai kaset ɗin bikin shi da na gan shi tare da matar shi. Duk da ba wani ƙiba yayi ba, sai ɗan cikowa da yayi.
Tunani na ne ya katse sa'ilin da nayi yi tuntuɓe da Centre table na tsakiyar falo tare da faɗin "Wash!" Hakan ya jawo hankalin su gabaɗaya zuwa gare ni. Fa'iz ne da hanzari ya tsugunna wurin ƙafa ta yana dubawa ko naji ciwo, shi kuma Aliyu da matarsa suna yi mun sannu domin shi har wannan lokacin bai samu sararin ganin fuskata ba.
Har bakin mota maman Amir da yaran suka rako mu, ƙafata har wannan lokacin raɗaɗi take yi mun amma gigitar ganin Aliyu ya danne zafin bana ji. A gaban motar na mayar da mayafina mazaunin shi tare da tsugunawa na rungume Amir da Maama domin sallama. Kafin na shiga motar kuma a kaikaice na ƙara waigawa domin ƙara kallon gidan a raina ina cewa yau gani a gidan Aliyu ni Ummu. Alamun shi da na hango ta jikin window ya sanya ni saurin shigewa mota tare da fatan Allah yasa bai gane ni ba.
Ko bayan da Fa'iz ya sauke ni a gida, tunanin abin da ya faru kawai nake yi. Sai da na gama shirin kwanciya sannan zuciya ta ta buga a yayinda ta halarto mun da cewar Fa'iz fa ƙanin Aliyu ne. Chab! Akwai dirama ashe!
Tunda na kwanta nake tufka da warwara. Ina son Fa'iz na sani, amma ganin Aliyu ya rikita ni. Na dai ja baki na na tsuke, ko Surayya ban dosa da maganar ba, alƙawari ɗaya na ɗaukarwa kaina ba zan taɓa nuna nasan Aliyu ba ko da zai nuna ya san ni. Soyayyar Fa'iz yanzu na fara, duk da ina da abubuwan da suka shige mun duhu, nasan a hankali zan gane komai.
A ɗan tsakanin nan ayyuka nake da su masu tarin yawa da ya sanya na mance da zancen Aliyu gabaɗaya don Fa'iz ne kawai a gaba na.
Sati Uku tsakani ina gidan Yaya Zainabu, Fa'iz ya kira ni akan cewar zai kawo su Amir, sun dame shi da son ya kawo su wurina. Don haka a gidan suka iske ni.
Sanin Fa'iz da son abinci ya sanya na shirya masa su kala-kala. A falon muka yi zaman mu, shi yana cin abinci yana mun santi ni kuma ina jin daɗi, domin ba abun da nake so irin na ji Fa'iz na yabo na a girki da alama hakan zai ƙarfafa mun gwiwar yi masa abinci kala-kala kodayaushe ba tare da gajiyawa. Su Amir da Maama tunda suka ga Najwa hankalin su ya koma wurin ta sai wasa suke yi da kayan wasan ta.
A ranar kuma Fa'iz ya bijiro mun da maganar aurenmu, ni kuma nace mu haƙura mun ɗan jinkirta namu zuwa bayan bikin Yaya Naziru. Ya kuma tambayi dalili, don ya fi ganin sauƙin abun idan an haɗa.
Nace "Kasan kusan duk wani buki da aka yi a gidanmu sai anyi tunanin a haɗa da nawa in ban da na Yaya Zainabu kaɗai. Ban san abubuwan da suke faruwa ba, ni kamar na camfa ne ma, gara kawai na yi nawa ni kaɗai."
"To Ummu ni kina ganin zan ƙi auren ki ne?" Ya tambaya da mamaki
Ganin na dage sai ya haƙura yace duk yanda nake so, haka za'a yi, amma dai yana fatan ba wani daɗewa za'a yi ba ko? Sannan ya ƙara da cewa "Amma ki sani soyayyar da nake maki har ta abada ce, ban taɓa son wata fiye da yanda nake jin ki a zuciya ta ba. Ki taimake ni kar ki bar ni, kin ji Ummu? Don Allah?"
Idanun shi cike da gaskiyar maganar shi, hakan kuma ya taɓa mun zuciya har wani guntun hawaye na tarar mun a ido.
Sai wurin biyar da rabi suka fara shirin tafiya gida. Fa'iz ya sanya na tattara mashi dukkanin ragowan abincin a food warmer domin tafiya da shi. Har Yaya Zainabu na tsokanar shi ko surukunta yake yi da ita ganin ba wani da yawa ya ci abincin ba.
Yaya Zainabu ce ta sallami su Maama da kayan ciye-ciye da gani na Najwa ne ta kwashe masu. Ita kam Najwa har da kuka za ta bi abokan wasan ta.
Wurin ƙarfe takwas na dare sai ga wayar Fa'iz, ina jiyo surutu da dararraki a wurin da yake.
"Kin san me?" Ya faɗa a shagwaɓe
"A'a, shagwaɓa kake yi mun fa." Na amsa ina dariya.
"Ai dole nayi maki, bayan Yaya Aliyu ne ya cinye mun abinci na gabaɗaya." Ya daɗa shagwaɓe mun.
Ni kuma shagwaɓar ce take ba ni dariya har da ƙyalƙyalawa, ina kuma jiyo muryar wani da nake kyautata zaton Aliyu ne yana cewa ba duka ba ne.
"Ta yaya aka yi ya cinye to?" Na tambaya
"Kawai fa naje sallar magriba ban dawo da wuri ba, shine yana shigowa ya ga warmers akan Centre table wai ya ɗauka nashi ne sai kawai ya fara ci, kuma na shi na saman dinning table."
Na cigaba da dariyar nace "Yi haƙuri Fa'izuna, Yaya Aliyu ai yayan mu ne, zan sake maka wanda ya fi wannan....."
"Hello?" Na ji an katse magana ta, sai da gabana ya faɗi domin muryar Aliyu ba zata taɓa ɓace mun ba.
Ya cigaba "Afuwa ƙanwata, girkin naki ne da ɗaukar ido. Yanzun baby (matarsa) take sanar da ni ashe ke ce kika yi cake ɗin su Amir."
Danne faɗuwar gabana nayi tare da ɗaga muryata cikin salon nuna ba ka san mutum ba na amsa "Ayya ba komai! Zan sake ma shi wasu ai."
Har da maman su Amir mun yi magana har da cewa dariyar da suka ba ta sai da cikinta ya kusa ciwo.
Ko bayan da muka gama wayar akwai sauran fargaba a tare da ni, amma zuciya ta tafi karkata ga Fa'iz. Aliyu is in the past!