28
by @faddabanan
Satittika sun wuce amma cike suke da wayoyin Aliyu kuma ko sau ɗaya ban taɓa kuskuren ɗagawa ba, hakan ya jawo in dai ban san lamba ba bana ɗagawa a personal layi na sai dai idan a layin da nake bawa jama'a ne domin yin abinci ne, kuma sai aka ci sa'a bai taɓa kiran wancan layin ba.
Ban taɓa nadamar ɗaga auren mu da Fa'iz da nayi ba irin wannan lokacin, da lokacin da Aliyu zai gane ni ce, zai gane ne a ƙurarran lokaci. Da kuwa dolen sa ya sakar mun mara na yi fitsari.
Tun lokacin da ya danna ni a motarsa na kasance ko'ina zan je ina taka-tsan-tsan, a ankare nake da titi koyaushe idan na fita don kar ya sake samun damar yi mun hakan. Idan kuma makaranta zan je tun ina cikin gida nake ɗaura niƙabi na, na daina jira sai na hau tasi.
Mun fara shirye-shiryen bikin mu da Fa'iz amma ba mu tsayar da lokacin da zasu kawo kayan sa rana ba. Babansu yace su yanke shawara da Aliyu, tun da naji haka gaba na yake faɗuwa.
Ranar asabar da yamma Fa'iz ya zo gida, ba na gidan ma sai Hassana ce ta kira ni take faɗa mun, na kuma ce ta shaida masa ya jira ni don ina kan hanyar dawowa gidan ma. Sau uku ina kiran wayar shi ba'a ɗaga ba, a kira na ukun ma sai katse kiran aka yi kawai.
A gigice na iso gida, ƙwaƙwalwata kuwa ta sha aiki kan ƙoƙarin tuno irin laifin da zan yi wa Fa'iz da zai ƙi ɗaukar waya ta kuma har da su katse wa, na san bahaushe yace 'ta malam ba ta wuce amin' domin tabbas zancen ba zai wuce na Aliyu ba. Na shirya yanda zan faɗa mashi abinda ya hanani faɗa masa ya fi sau ashirin, jiki na sai rawa yake yi. Allah ya sa a iya fushi kaɗai zai tsaya ya haƙura, kar yace ya fasa aure na hakan zai sa Aliyu ya kasance mai nasara a tsakanin mu.
A harabar gidanmu na iske shi a zaune ya yi tagumi, har na ƙaraso bai lura da zuwa na ba. Ban da a harabar gidanmu ne da wallahi rungume shi zan yi, abin da ke yawo a raina kenan. Kallo ɗaya za ka mashi ka lura da irin ɗimbin damuwar da ta addabe shi kuma sai ka ji ya ba ka tausayi.
A sanyaye na ƙarasa kusa da shi tare da sauke hannayen shi da yayi tagumi da shi ban yi magana ba. Ajiyar zuciya ya yi tare da kallo na da idanun shi da suka kaɗa suka yi jawur.
Ba shiri na zauna a kujerar kusa nace "Fa'izuna me ya faru?"
Murmushin ƙarfin hali ya yi "Shiru kawai Ummu, na sa kin dawo gida babu shiri ko?"
"A'a, ni tsoro ma ka bani ganin ina ta kiran wayar ka ba ka ɗauka ba, sai kuma na ga ka katse kiran."
"Ayya, ban zo da wayar ba ne shi yasa na sa Hassana ta kira ki. Ƙila a wurin da na manta wayar ne aka yi maki hakan." Ya yi bayani.
Bai jira nayi magana ba ya ranƙwafo cikin sigar rarrashin yace "Ummu don Allah ki yi mun wani alƙawari mana."
Tsare ni ya yi da ido a yayinda gefe ɗaya zuciya ta ke dakan lugude, muryata na rawa na amsa "zan yi maka, faɗa mun damuwar ka don Allah."
"So nake ki yi mun alƙawarin za ki fuskance ni kuma ba za ki yanke shawara akan komai ba ba tare da kin tuntuɓe ni ba."
To ko hana shi aure na aka yi? Amma kuwa da na nemi hanyar da zan kashewa Aliyu aure wallahi. Na zuba mashi ido cike da zumuɗin son sanin abin da ke faruwa.
Ya ƙara faɗin "Ba ki amsa ba."
"Zan iya bakin ƙoƙari na amma Fa'iz ba zan yi maka alƙawari kai tsaye ba. Kasan girman alƙawari sannan ban san me ke faruwa ba. Kar ka damu, har kullum ina tare da kai." Na amsa a sanyaye.
"Kin san me? Wallahi na rasa abin da yake damun Yaya Aliyu. Kin tuna Baba yace na same shi mu tsayar da ranar da za'a kawo kaya da fixing ranar biki gabaɗaya sai mu faɗa masa me muka tsara, kullum bin shi nake yi amma shunning ɗina out yake yi wai aiki yayi masa yawa. Saboda Allah maganar minti nawa ce? Ni ba taimakon shi nake buƙata ba ta wurin siyan kayan nan. Dukkannin abubuwan da suka yi ta faruwa ban ƙullace shi ba sai yau. Ganin yau asabar nasan ko yaya ne aikin zai yi masa sauƙi, amma tun goman safiya nake gidan sa amma ya ƙi sauraro na, in taƙaice maki ko falon ya ƙi fitowa har sai da aka yi la'asar. Maman su Amir ita kan ta abun mamaki ya dinga ba ta don ta kasa fahimtar ina yasa gaba. Kuma bayan ya fito da la'asar ɗin sai yace mun wai ba yanzu ya kamata a yi maganar kai kaya ba sai nan da ƙarshen shekara. Can you imagine?! Sai kace shi ne uba na! Ɓacin rai ya sa na faffaɗa masa magana shine na taho nan kai tsaye, a gidan su na baro wayoyin."
Zuciya ta tafasa kawai take yi domin Aliyu ya raina mun hankali, watau shi bai aure ni ba kuma ya hana wani aure na kenan. "Ba komai Fa'iz, yayanka ne ka dinga haƙuri, ina ga ba ka fahimce shi ba ne."
"Bari kawai Ummu, Baba so yake ya haɗa kan mu kaman shi ya haife mu gabaɗaya amma ya zo yana mun wani iko kaman shi ne ma Baban."
Ido na zazzaro cikin tsananin mamaki jin cewar ba babansu ɗaya ba, cikin saurin magana nace "What?! Ba babanku ɗaya ba?"
Murmushin takaici yayi yace "Ɓacin rai ne yasa nayi maganar, Baba ba ya son ma ana maganar ko da wasa, yanzu zai kama faɗa. Babana da Baba na Kano wa da ƙani ne, uwa ɗaya uba ɗaya. Kasancewar ni da Babansu Yaya Aliyu kamar mu ɗaya sai ya ɗauko ni tun ina yaro don a gidan shi nayi Firamare ma. Shaƙuwa ta da shi kuwa har ba'a kwatanta wa, don da na ɗauka babana mahaifi Kawu na ne kawai kamar kowa na gidan, sai daga baya na gane. Zama na a gidan su ne yasa Humaira ta sa mun Fa'izunmu, saboda ba ta son 'yan gidanmu su dinga cewa Fa'iz ɗin su ne, har kuka da bori take yi."
A nutse na kwantar masa da hankali, har kuma kafin ya bar gidan mu ya warware don har da su dariya da ƙyaƙyatawa. Da na raka shi motarsa domin tafiya, har na juya zan koma cikin gida bayan mun yi sallama ya sake kiran sunana. Na juya ina kallon shi amma ban koma jikin motar ba, yace "Ummu na! Zuwa na gare ki ya sanya mun farin ciki, godiya ta yau har babu adadi and I Love You!" Ya kuma juya kan motar shi ya tafi ya bar ni domin bai tsaya jiran amsa ba ko wani abu. I love You ɗin da ya faɗa sai amsa kuwwa take yi mun a kunne, murmushin fuska ta ya ƙi ɓacewa, Allah ma ya sani ina son Fa'izu!
Ina shiga cikin gida kuwa tunani na gabaɗaya ya koma kan neman yanda zan yi da Aliyu. So nake na tare shi a ko ma ina ne na ci masa mutunci sannan na ja masa kunne. A take na hau laluben waya ta neman lambobin da nake zargin na shi na kama yi, guda uku ne. Kowacce lamba sai da nayi mata missed call guda biyar amma sam ba'a ɗauka ba, zuciya ta kuma ta hau tafasa kai ni har suya ma take yi. Haushin kaina ya rufe ni ganin ni da kaina na ɗaga hannu na kira shi a waya amma ya ƙi ɗauka, ba mamaki tunani yake ya kama ni a hannu, zai sha mamaki. Allah ya haɗa mu da shi.
Shi ma tun daga ranar bai ƙara kira na a waya ba, ni ma hakan take. Idan na fita unguwa ko makaranta kullum ido na yana kan titin ina laluben ganin shi, kuma abun haushin na manta wace iri ce ma motar ta shi, kawai nasan kalar makuba ce, kamar yana sane domin ko da kuskure ban gamu da shi ba.
Fa'iz kuma Maman Amir ya lallaɓa akan cewa ta lallaɓa mijinta ya sauka daga faɗin sai ƙarshen shekara kamar yanda ya faɗa a baya, kuma yayi hakan ne don ba ya son Baba ya ji ba daɗi akwai matsala a tsakaninsu. Amma fa lokaci ya ɗibarwa Aliyun, kuma idan lokacin ya cika bai canza ba, kai tsaye wurin Baban zai je ya faɗa mashi komai domin shi ya gaji.
*******************
Ranar da Sauda tazo gida tare da ɗanta me sunan Baba ana kiran shi Abbu, kasancewar kaya sun yi mata yawa da za ta koma sai muka raka ta har bakin titi inda za ta iya samun adaidaita sahu tare da Hassana. Muna tafe muna ta hirarrakin mu irin na 'yan uwa, muka kuma jira har sai ta hau ta tafi kafin mu baro titin.
Dan tsayawar da muka yi na ganin tafiyar ta ne na hango wani kaman Aliyu, Hassana kam har ta juya ta ɗauka ina tare da ita. Na ɗan dakata ina kallon shi kamar a shirin fim sai shi ma ya juyo muka haɗa ido. Ban san lokacin da wani takaicin sa da haushin sa suka kama ni ba, ganin fuskarshi a ɗaure sai na ɓata rai, na buga tsaki sannan na juya ina ƙara sauri domin taddo Hassana. Mamakin tsakin ma ta ji take tambayar me ya faru, nace wani abu ta can ɓangaren na gani da ya bani haushi, shikenan aka bar zancen.
Fa'iz ya sanya ni yi wa Amir birthday cake, sun shirya masa party na cika shekara biyar, bayan haka kuma yace maman su Amir na gayyatar Najwa don haka na tabbata na kawo ta ko don Maama ma.
Allah ya sani ba na son zuwa, nasan idan na kawo wani excuse zai ɗauka abin da ya faɗa mun tsakaninsa da Aliyu ne na ƙullaci Aliyun, sannan ba mamaki ba za mu iske Aliyu a gidan ba ko don saboda mutane da zasu je, tunda ai manya ne zasu kai yaran da aka gayyata, su kuma jira a gama su tafi da su.
Ƙarfe huɗu daidai muka isa gidan Aliyu, Fa'iz ya shiga rububi shi yasa nace ba sai ya je ya ɗauko mu ba, zan kuma tafi da cake ɗin. Abun mamaki ina zuwa sai na iske har an sa wani cake ɗin mai hawa uku kalar kayan Amir, raina ya yi mun ba daɗi amma yanayin tarbar da na samu daga Maman Amir da Humaira sai ya wanke mun zuciya, don haka raina a sake na miƙa masu kwalin cake ɗin. Mickey mouse ne cake ɗin, ihun murna kawai Amir yake yi sai kuma ya hau ture hannun aunties ɗin shi daga kan cake ɗin wai su daina taɓawa, a take kuma aka sa shi kusa da cake ɗin da na tarar.
Kowa ya zo sai Humaira tace ga matar Fa'izunmu, roƙon ta na dinga yi da kyar ta yarda ta daina faɗawa mutane. Ƙarfe biyar kuma Fa'iz ya shigo gidan, ni kuma ya fara nema.
Gaba na ne ya faɗi jin Amir na cewa "Daddy zo kaga cake ɗina da anty Ummu ta kawo mun." Ko da wasa ban juya ba don nasan Aliyu ne ya ƙaraso wajen. Sai nayi kamar ban ji ba na cigaba da yi wa Fa'iz magana.
Tunda ya ƙarasa wurin cake ɗin na hango idon shi yana laluben jama'ar wurin, nasan cewar ni yake nema ba sai an faɗa ba ko wurin ban sake kalla ba kar tsautsayi ya sa mu haɗa ido, sai da aka ce mu taso za'a yi hotuna.
Duk hotunan da za'a ɗauka sai ka ji Amir yana faɗar a tabbata mickey mouse ɗin shi ya fito a hoton, ni wannan kaɗai ma ya isa ya sanya ni farin ciki don ina son yin abun da za'a a yaba.
Mun yi hoto da Amir shi kaɗai, sannan da shi da su najwa kafin daga bisani ni da shi da Fa'iz, har Humaira na tsokanar mu wai kamar mu ne ainihin iyayen Amir ɗin, don haka ya kamata su ba mu shi idan mun yi aure.
A hoton ƙarshe ne Fa'iz ya shammace ni, sai da ya bari mai Camera ɗin ya gama saita komai sai kawai ya rungume ni ta gefe haɗi da sumbatar kumatu na, don haka a hakan aka ɗauka. Cike da mamaki na ture shi kaɗan, su kuma na tsaye suka fara mana dariya. Idona kuwa ya faɗa kan Aliyu, fuskarshi a murtuke da wani irin fushi da ban taɓa gani ba.
Najwa ta shige cikin yara abun ta ba tare da damuwa ba, don haka Fa'iz ya tsare ni a gefe guda ya hana ni motsi kwata-kwata, ga shi gabaɗaya wurin 'yan uwansu ne da family friends. Mommyn su Amir har wurin ta zo tayi masa tsiyar ya hanani shiga cikinsu amma sai cewa yayi 'yaji ɗin', haka ita ma ta haƙura ta bar mu.
Da magriba tayi ciki muka shiga domin sallah, su kuma mazan suka nufi masallaci. Ban da Fa'iz ya dage shi zai maida mu gida da tuni mun tafi gudun dare, yanzu ma shi nake jira don sam na kasa sakin jikina. Sai ga text ɗin shi kan cewa na ƙara haƙuri sai an yi Isha za mu tafi, ba haka nake so ba amma ya zan yi?
Muna zazzaune a farko su suna ta hayaniya ni kuma ina ƙaryar kallon talabijin, mai aikin su ya kirani wai inji Fa'iz. Da yaga na fara ɗaukar haka tare da neman Najwa sai yace "yace wai ba tafiya zaku yi ba tukunna."
Tare muka fito daga falon, ya nuna mun wurin da Fa'iz ɗin yake sannan yayi na shi wuri. Ta wurin da suke parking motocin su ne, kaina tsaye na nufi wurin ina laluben shi kasancewar wurin akwai rangwamen haske.
Ko da na hango shi sai na fara magana a yayinda nake ƙarasowa "kace na bari sai anjima za mu tafi, what is it that cannot wait......" Ban ƙarasa maganar ba da na lura Aliyu ne. Cike da zafin nama na juya domin komawa cikin gidan, amma da yake shi namiji ne ya fi ni zafin nama ban yi taku uku ba na ji ya riƙo hannuna tare da jawo ni muka koma gefe. A gigice na dinga yi masa magiyar ya sake ni na tafi, tsoro na ɗaya kar matar shi ko Fa'iz wani a cikinsu ya gan mu.