29
by @faddabanan
Cike da zafin nama na juya domin komawa cikin gidan, amma da yake shi namiji ne ya fi ni zafin nama ban yi taku uku ba na ji ya riƙo hannuna tare da jawo ni muka koma gefe. A gigice na dinga yi masa magiyar ya sake ni na tafi, tsoro na ɗaya kar matar shi ko Fa'iz wani a cikinsu ya gan mu.
"Kina so na sake ki ki koma?" Ya tambaya.
Cikin sauri na hau gyaɗa kaina ina faɗin "Eh!"
"Zan sake ki idan kin yarda za ki tsaya mu yi magana ko na minti goma ne."
Da sauri nace "Na yarda, Allah." Sannan ya sakar mun hannu
Na ja da baya tare da cewa "Ka yi maganar ka da sauri, so nake na koma kafin su ankara bana nan."
"Ƙara dawowa wurin da kika matsa daga ciki tukunna."
"Mun yi kusa gaskiya." Na zumɓura baki.
"Amma ɗazu ai ba ki lura da hakan ba, har wata rashin kunya kuke yi ke da Fa'izu."
"Fa'iz mijin da nake shirin aura ne ai, ga zato na ba rashin kunya muka yi ba. Besides, kai ma ba so kake yi jiki na yana kusantar naka ba, don haka ka faɗi maganar ka ina ji." Na karkata kaina gefe guda.
"Idan ki bana so ai ke kina da buƙata don na lura shine kaɗai abin da ya ja hankalin ki ga Fa'iz. Don ba sau ɗaya na ga kun haɗa jiki ba, Allah kaɗai ya san abin da kuke yi idan kun kaɗai ce." Fuskarsa na nuna wani ɓacin rai da ban san dalilin zuwan sa ba.
"Shi ne abin da ka kira ni ka faɗa mun?" Na tambaye shi.
"Ke a tunanin ki shafin mu ya rufe ba mu da buƙatar tattauna komai?"
Ban kai ga amsawa ba na hango Fa'iz ya shigo gidan, nasan yana ɗan juya kan shi zai ga mutane (watau ni da Aliyu kenan) ta gefe wurin parking, gaba na faɗuwa na baro wurin Aliyu na doshi Fa'iz da yanzu tahowa ta ta ja hankalin shi gare ni, nasan kuma ya hangi Aliyu ta baya na haka ma shirun da Aliyu ya yi na san shi ma ya hango shigowar Fa'iz ɗin. Ban tsaya na ba shi damar zargi ba nace "Kai na fito nema sai kuma na ga Yaya Aliyu a nan, shine na tsaya muka gaisa kasan ɗazun akwai taron jama'a ba mu gaisa ba."
Hakan kuwa yayi don babu alamun zargi ko wani abu face ma daɗin da ya ji ganin ban ƙullaci ɗan uwansa ba, don haka sai hankali na ya kwanta. Kuma tunda muka baro gidan sa ranar bai ƙara kira na ba, ni ma tuni na fara mancewa da sha'anin sa don na lura raina mun hankali yake son yi.
Kwatsam, sai muka sake haɗuwa a commissioner road, ranar na je gidan su ƙawata Saratu Aliyu. Kafin a ƙarasa gidan su aka sauke ni, don haka nake tattaki domin ƙarasawa gidan, shi kuma ya fito daga government house ya tare ni. Da yaga ba ni da alamar tsayawa sai kawai yasa hannu ya zare jaka ta da nake ta reto da ita kasancewar ba rataya ta nayi ba, saboda ya shammace ni shi yasa yayi nasara, ya kuma yi gaba da motar zuwa wurin wata bishiya yayi fakin.
Tsayawa nayi na bi motar da kallo har zuwa lokacin da ya samu waje ya tsaya, ban da akwai wayoyi na a jakar da wallahi tafiya zan yi na bar masa. A salon tafiyar hawainiya na ƙarasa wurin da yake, na riƙe ƙugu tare da juya masa ƙeya ina kallon wani wuri daban.
Dariyar shi naji "Ummul kin ɓaci da rigima wallahi, ashe abun da nayi missing kenan domin ni Ummun da na sani ba ta ƙetare abinda aka faɗa mata kuma yanda za ta faranta maka take nema."
Na ɗan juyo kaɗan na kalle shi sannan nace "Idan ka tambayi Fa'iz, haka sak zai kwatanta ni domin kullum ƙoƙarin faranta masa nake." A take naji waya ta tana ringing, bai miƙo mun ba nima ban ce masa ƙala ba.
"Wai Ummu me yasa kike ba wa kan ki wahala ne? Kina so Fa'iz a madadi na ne kawai, sannan na san ba mamaki idan ma tun farko kin san cewar ƙani na ne shi yasa kike son shi. Ni ne nan original! Taimakon ki nake son yi don kar ki yi nadama daga baya."
Gabaɗaya na juyo na fuskance shi raina na tafasa don ji nayi gara ma Aliyu ya mare ni da wannan maganar da ya faɗa mun. Na nuna shi da ɗan yatsa nace "Aliyu ka kiyaye ni! Na yi maka kama da abokiyar wasan ka?! Ko an ce maka ni kwallon ce da za ka buga ta kowanne ɓangaren da ka ga dama?! Iye?! Idona har ƙanƙancewa suka yi saboda bala'in da ke ci na.
Ina jin daskarewa yayi a zaune domin ko ƙyafta ido baya yi, na kuma yi amfani da damar na fusgi jakata tare da tsugunawa na kwashe wasu abubuwan da suka zubo daga jakar na tsallaka titi na shige gidan su Saratu, na bar shi anan kamar mutum-mutumi.
Sai daddare bayan na dawo gida na lura wayar da nake ba wa kwastomomi na lambar ba ta cikin jakata. Kuma akwai waɗanda zan yi wa aiki a satin, don har sun turo mun wani kaso mai yawa na daga cikin kuɗin, yau ya kamata mu ƙarasa maganar zaɓin su cikin options ɗin da na basu sai su cika ragowan kuɗin. A take hankali na yayi masifar tashi, za su iya ɗauka yaudarar su zan yi kuma wannan ne karo na farko da muka fara hulɗa da su.
Ba na tantama a motar Aliyu ta zame ta faɗa lokacin da fusgo jaka ta. Matsala ta biyu ce, ba zan iya zuwa gidan shi tambayar waya ta ba, don dole hakan ya kawo wa matarsa zargi tun da a idon ta ba wani sosai ma muke gaisa ba bare a ce. Na biyu kuma ban san ina office ɗin shi yake ba, don can ne mafi cancanta na je. Ba yanda za'a yi na tambayi Fa'iz ko Humaira saboda nasan da wuya Aliyu ya ɗaga waya ta idan na kira shi, wannan rashin kunya da na tsula masa ɗazu kawai nake tunowa.
Ganin ba ni da mafita sai kawai nayi kasada na kira shi, ba damuwa ta ba ce ko yana gida kusa da matarsa ko wani waje, matsalar sa ce! Na kuma doka sa'a domin ya ɗaga wayar a kiran farko, magana ce kawai bai yi ba don haka ni sai na fara maganar.
"Hello Yaya Aliyu?" Don gudun kar matar shi ce ta ɗaga wayar ya sanya nayi hakan.
"Ci gaba ina jin ki."
"Waya ta ce nake tunani tana tare da kai kuma wallahi ina tsananin buƙatar ta, ban da dare yayi ma da nace yanzu." Na yi magana ta kai tsaye kamar yanda ya buƙata.
"Wane bawan kika ajiye da zai kai maki wayar?" Ya tambaya cikin halin ko'in'kula.
"Ba kawo mun za'a yi ba. Ni ce zan je na karɓa a office ɗin ka gobe idan za kayi mun kwatance."
"Sai ki kira ni gobe ki ji ina ne." Ya katse wayar.
Ni na isa naji haushi? Nema na yake ido rufe sai gani na kai kaina bayan na gama yi masa masifa kamar wani ƙanina ko ma ɗa na. Allah dai yasa ya ji haushi sosai kuma ya yanke shawarar fita daga sabga ta don gara ya sakar mun mara hakan nan na yi fitsari, yau ni Ummu na tsokalo tsuliyar dodo."
Fa'iz a daren nan bai gane kaina ba, tun kafin ya fara tunanin wani abu nace masa bacci nake ji kawai, don haka muka yi sallama na kashe wayar.
Da safe na shirya irin shirin zuwa makaranta, riga ta da hijab kalar kore me duhu na sa yau, niƙab ne kawai ban sa ba. Wurin goma na kira shi, sai a kira na uku sannan ya ɗaga wayar, a ciki-ciki yace ki zo Audu Baƙo Way, ya sake katse kiran ko jiran amsawa ta bai yi ba.
Ko da na iso Audu Baƙo Way ɗin na daɗe ina kiran shi bai ɗauka ba, har sai da ɗan sahun da na hau ya gaji ya fara mun masifa, don haka na sauka kawai na nemi wuri na tsaya ina jira kiran shi. Sai bayan minti goma sannan ya kira ni tare kwatanta mun wurin da office ɗin yake, na baro wurin a baya sai da na sake hawa wani adaidaita sahu na koma. Bacin ina tunanin mutanen nan da tuni nayi zuciya na bar masa wayar.
Da na isa ofishin ma sai da aka shanya ni sannan aka yi mun izinin ganin sa, a taƙaice sai sha biyu da minti ashirin da bakwai na samu ganin shi.
Sallama ta kaɗai ya amsa a yayinda idanun shi suke zube bisa allon kwanfutar shi. Ban da na lura da motsin laɓɓansa da ba zan san ya amsa sallamar ba. Bai yi mun tayin wurin zama ba don haka ni na nemar wa kaina na zauna ina tsammanin manrabbuka.
Wayar da Surayya ta bugo mun ne ya katse shirun, ta bugo ne tana son na koya mata wani bread, na taɓa yi wa Yaya Naziru ya tafi da shi nasan kuma ya ji daɗin sa, wai yau ya tashi yana sha'awar sa shine yasa a kira ni su gwada yi da kan su. Daga koyarwar sai muka ɓuge da hirar ƙawaye don gabaɗaya hankali na sai ya koma kan ta, don wallahi na manta wurin da nake ma. Sai da muka fara sallama saboda Yaya Naziru ya dame ta ta tashi su fara sannan na tuna a ina nake. A hankali na ɗago kaina ina kuma tunano irin hirar da na gama yi yanzu ina fatan Allah ya sa ban saki baki ba, sai ƙaraf muka haɗa ido.
Da fuska ta kadaran-kadahan na gaida shi amma bai amsa ba, sannan kuma bai daina kallo na ba. Don haka sai na shiga magana kai tsaye tun da yanzu naci sa'a hankalinsa yana kaina "Ga ni nazo yallaɓai, a ba ni wayar don Allah, kasuwa ma zan je daga nan."
Ya amsa "Kin san kuwa yanda kalar koren nan tayi maki? Ƙara haskaka ki tayi, ga shi idon ki kamar an ƙara masa girma."
Na amsa da cewar "Don girman Allah Aliyu ka ba ni wayar, kar mutanen da zasu neme ni su ɗauka kuɗin su zan ci, please and please."
Ya cigaba da magana kamar bai ji me nace ba "Ummu wai meye abin so a wurin Fa'izu saboda lillahi?"
"Don Allah Aliyu ka daina zance kamar ba ka sauraro na. Rana tana ƙara yi fa."
"Fa'iz wani abun ya fi ni ne Ummu? Duk wata cikar halittar shi bai kama ta wa ba, ko na miƙe na jujjuya ki ƙare mun kallo yau don ki tantance?"
Wani takaici ya tsare mun wuya amma sai na yi ƙoƙarin dannewa domin yau sai nayi juriya tukunna zan samu abin da ya kawo ni. Ko nace bari naje na yi swapping layin sai bayan awa ashirin da huɗu (waccan lokacin, kafin ku ce Faddabanan ba haka ba ne) zai hau, kuma lokacin ya gama ƙure mun don ba amfanin da zai yi mun kuma.
"Aliyu!!!"
"Ummul!!!" Shi ma ya amsa a irin yanayin da na kira sunan shi.
"Don Allah waya ta."
"Don Allah matsala ta" ya sake amsa ni
Kaina ya fara ɗaukar zafi don ban san lokacin da hawaye suka cika mun ido ba, yau Alhamis kuma gobe juma'a suke son abincin su, bayan haka kusan wata guda kenan da suka yi booking. Wannan da na tuna sai hawaye ya fara bin fuska ta don na rasa abun yi.
Ina kallon shi ya taso daga teburin shi tare da zaro tissue daga kwalinta dake ajiye bisa teburin, sannan ya zo gaba na ya tsugunna tare da goge mun fuska yana wani murmushi da kana kalla kasan na damuwa ne. Ya karkata tare da sanya hannun shi a aljihunsa ya zaro wayar, ya kuma haɗa ta da hannuna ya riƙe yana kallon fuska, a sanyaye yace "Hawaye kike akan kuɗin mutane Ummul?"
Cikin hawayen da har yanzu bai tsaya ba nace "A'a, zan iya mayar masu da kuɗin su, matsalar zuwa yanzu da ni suka dogara kuma za ta iya yiyuwa dukkanin kuɗinsu an kasafta zuwa wasu abubuwan, sannan harkar girki ba irin wanda za'a zo a ce yau ana so a yi ba ne balle na yi tunanin ai zasu samu me yi masu daga yau zuwa gobe. I'd hate to disappoint them."
Shiru ya ziyarci ofishin, inda shi kuma ya zura mun ido kafin daga bisani yace "Ummul wai fushin da kike yi da nine ne har yanzu ba ki huce ba?"
"Fushi? Wane irin fushi kuma? Nace maka ka yi mun laifin da ya sa ni fushi ne?" Na tambaya
"Don Allah kin ga mu bar wannan zagaye-zagayen, daga ni har ke ai mun san maganar."
"Ka dai sani, amma ni nan ba abun da na sani."
"To dakata mana, batun aure na da maman su Amir."
"Au ho! Wai wannan dama kake faɗa? Tsohon labari ne ai, abun da aka yi tun tale-tale lokacin ban gama sanin wacece ni ba bare kuma shi kan shi son." Na fara azamar zare hannuna daga nashi alamun tafiya zan yi tunda na samu abinda ya kawo ni. Har na miƙe tsaye ina ƙoƙarin janye ƙafafuwana zuwa gefe kasancewar gwiwoyin sa da ya jingina da kujerar da nake sun sa ƙafafuwana tsakiya. Ban ankara ba sai jin hannayensa nayi a cikinsa ya hankaɗa ni baya har nayi zaman 'yan bori akan kujerar tare da buge kafaɗa ta da bayan kujerar, Allah ma yasa ban yi allan-dungure ba zuwa can bayan kujerar. Cike da mamaki nake kallon shi, shi kuma ya miƙe cike da gadara.
Yace "Ƙarya ne, kin ji ko Ummul nace ƙarya ne! Ƙarya ne a ce wai ba ki so ni ba a can baya ba bare kuma yanzu. Kamar yanda na faɗa maki ne, darajata Fa'iz yake ci kike son shi. Ina kuma ba ki dama ta ƙarshe da ki dawo where you belong tun kafin ki yi nadama."
Faɗin na dawo gare shi ne ya daskarar da ni a zaune, amma Aliyu ya gama raina ni wallahi, watau ga ni banza wadda ba ta san ciwon kan ta ba, mai tsananin masifar son shi, wadda ba za ta iya rayuwa ba sai tare da shi.
Ya cigaba "Idan har kin tabbatar kina son Fa'iz ki rabu da shi tun lokaci bai ƙure maki ba...." Miƙewar da nayi a fusace ce ta katse maganar da yake yi, nace "Kul! Kul! Kul! Kar ka sake ka je can Aliyu....." Ni ma nawa zancen katse wa yayi da na hango kamar mutum ne tsaye a bakin ƙofa ta gefen ido. Fa'iz ne tsaye yana kallon mu, kuma kallo ɗaya za ka yi wa fuskarshi ka lura a cikin wani bala'in ruɗu yake.
Karanta ta yayi na sakwanni kafin ya juya ya fice. Aliyu taɓe baki yayi ya zauna ragwajab a kujerar ma fi kusa da shi. Ni kuma tunani na ne yayi bulaguro na wuccin gadi, sai da ya dawo ne nayi tunanin ya kamata na bi bayan Fa'iz. A hanzarce na doshi ƙofar fita, ina kuma jiyo muryar Aliyu yana magana amma sam ƙwaƙwalwata ta gaza fassara mun ma'anar ta, tsakin da ya biyo ni da shi kaɗai na gane.