37
by @faddabanan
A daren ya zo, zuwan dare yanzu ba ya yi masa wahala. Ina ga kaman faɗan da suka yi da matar ne ya sanya shi yin jan wuya har ba ya shakkar zuwa waje na (mata ku kula, tashin hankali a lokuta irin wannan ya kan zama wata dama ga maza. Ki koyi dauriya da riƙe girman ki duk da ba abu ba ne mai sauƙi, sai shi kuma ya dinga yi maki kawaici).
Falon mu na kawo shi ranar saboda Surayya, don babu mutunci tana matar aure ta fito waje ta same shi don su gaisa. A hirar ranar kam gabaɗayanmu ne har da su Hassana da Hussein da ya shigo daga baya ya same mu. Komai nake yi hankalin shi yana kaina sannan kuma ruwa kawai ya kurɓa kaman yanda ya saba yi mun, ya ƙi cin komai.
Surayya tace masa "Kai kaɗai ne wanda na taɓa gani da yake iya tsallake tayin abincin Ummu. Gwanar girki ce, idan ba ta ja hakalin ka da tsarin abincin ta ba to kuwa dole za ta ja ta ƙamshin girkin ta."
Yayi murmushi idon shi a kaina yace "Ni kaina shaida ne Surayya, amma bana cin abinci da daddare sai fruits kawai, abin ki da mai jikin ƙiba sai an dinga kiyaye abubuwan da ake ci. UmmalKhairi ai nasan baki yi fushi ba ko?"
Hassana tace "Wai Alhaji sai ka yi ta lallaɓa Yaya Ummu kamar wata baby wallahi." Duk hararar ta da nake yi bai sa ta daina maganar ba.
Ya amsa da cewa "Haba Hassana, UmmalKhairi ai baby na ce, idan ban lallaɓa ta ba zan lallaɓa to? Ni a wurina ba ta girma ba ai."
Kusan duk rabin hirar da su aka yi, ni na kan tsomo baki ne kawai. Da ya tashi tafiya 'yan biyun Yaya Naziru yayi wa kyautar kuɗi, bana jin ya ƙirga don yana sa hannu a aljihu ya zaro ya miƙo mun domin na kai masu."
Da sauri na daɗa maƙale hannu na a jikina nace "Idan Baba ya ji zai ɓaɓallani ai."
Yace "To ai ba ke na ba wa ba, su yanzu zan daɗe ban kuma ganin su ba. Don Allah kar ki ɓata mun rai."
A sanyaye na juya na koma cikin gida, zuciya ta cike da tsoron faɗa. Dubu ashirin da uku ne ya bayar bayan su Surayya sun kirga kuɗin. Ta yi ajiyar zuciya tace "Alhajin nan naki baya jin garin nan, ga shi da bala'in sauƙin kai kamar ba mai kuɗi ba."
Sai da muka koma ɗaki sannan na tambaye ta "Ya ya kika gan mu? Akwai nauyin a tsakanin mu ko kuwa?"
"Ina fa wani nauyi anan? Kamar kina magana da sa'an ki, gaskiya idan kin aure shi za ki more abun ki, ga hutu ga rarrashi, ya tsaya maki ki yi shagwaɓar ki yanda kike so mutumniya ta."
Ranar lahadi suka tattara yanasu-yanasu suka tafi, sun bar mu da kewar 'yan biyun ta marasa baƙun ta masu shiga rai, gidan duk yayi mana faɗi.
Lokaci ɗaya kuma Alhaji Hamisu ya rikice mun da kyaututtuka, ganin a gidan ana faɗa idan ya bani zunzurutun kuɗi sai ya tsira yi mun kyautar abubuwa masu daraja, yanzu iphone 6s (lokacin ita ce a sama) gare ni da Ipad. Ipad ɗin ma kusan kala uku ne don har na ba wa Hassana kyautar ɗaya a ciki da za ta tafi adamawa service, sannan Sauda da ta dame ni da naci na ƙara ba ta ɗaya ya rage saura ɗaya nawa. Amma ko sati ba'a cika ba ya sake ba ni babbar su tare da MacBook.
Yanzu gidanmu daga ni sai Hussein, kuma na rage wasa da makaranta yanzu kasancewar naga a shekarar ƙarshe nake kuma ba na buƙatar spill-over. Sai da makarantar ta zo ƙarshe sannan naji ya kamata na dage ko zan samu damar amfani da result ɗin wurin shiga jami'a. Amma a rayuwa ta na soke BUK ba ni ba makarantar nan har abada.
Wurin aiki na ma yana nan yanda aka saba, Habiba har yanzu ba ta daina shan ƙamshi ba muddin Yaya Bashir ya iso Kano har sai ya bar gari tukunna. Rahina kuma an sa mata ranar biki, sai dai da sauran lokaci sosai.
Matsala ɗaya na fara fuskanta shine rama ba gaira babu dalili. Baba ne ya lura rannan ina tsaye a harabar gidan mu ni da Hussein, damu na yake yi akan sai na ba shi aron mota, ni kuma ina yi masa yanga da jan rai. Nace idan ya ji haushin ɓata masa lokacin da nake ya je ya ari ta Baba, amma ya ƙi fushi sai naci yake. Daga can gefe naji Baba ya ƙwalla mun kira.
Ina isa wurin shi ya fara cewa "Me ya same ki ne? Ba ki da lafiya ne?"
Cike da mamaki nace "Ni? Rashin lafiya kuma? A'a Baba, lafiya ta ƙalau fa."
"Tunanin me kike yi to? Kin ga yanda kika rame kuwa? Ko ke baki gani ba?"
Washegari ya umarci Mama ta sani a gaba mu je asibiti domin binciken lafiya ta, domin rama ba dalili abar tuhuma ce. Asibitin da muka saba zuwa muka je, Mama tace a yi mun medical checkup gabaɗaya na tun daga kai har ƙafa. Ina yi mata dariya nace "Ke mama sai ki dinga biyewa Baba, mara lafiya ce ni da har zan tuƙo ki a mota na kawo mu asibiti?" Ta yi shiru abun ta ta ƙyale ni.
Gwaji kam ba irin wanda ban sha ba ranar, kama daga na jini, fitsari, bahaya da sauran gwaje-gwaje. Yini sur muka yi a asibitin nan amma wasu sakamakon gwajin dole sai idan mun dawo gobe za'a karɓa. Tsoro na dinga ji da naga har da gwajin cutar ƙanjamau, tsoro na Allah tsoro na annabi a ce cutar ce da ni! Allah ya rufa mun asiri ya kiyaye! Don Allah na tuba bana jin zan iya rayuwa bayan haka kuma.
Jiki na a sanyaye har safiya, Hussein aka aika ya karɓo wani sakamakon gwajin da muka yi a wani lab nesa da asibitin gab da zan fita aiki, ƙarfin hali kawai nayi na fitan. Da muka taso ma dai ikon Allah ne ya maido ni gida, ban ma saurari gajiyar da na kwaso ba muka koma asibiti ni da Mama tare da sakamakon zuwa wurin likita, ya kuma tabbatar mana lafiya ta ƙalau a dukkanin sakamakon gwaje-gwajen. Cikin jin daɗi nace da Mama "Kin gani ko? Lafiyata ƙalau sai Baba ya kwantar da hankalinsa."
Cikin jin haushi Mama tace "Ke tafi can! Rama da rashin lafiya ita ce kwanciyar hankali ai tunda an san babu lafiya, idan kuma an samu lafiyar komai zai dawo yanda yake. Amma ke yanzu naki ba wanda ya san meye dalili."
Ban kuma bi ta kan maganar ba na wuce ɗakin mu bayan dawowar mu gida, ina cewa a raina ban da abun Mama me ye na damuwa ma? Yanzu da yayin siraran mata ake yi, ni gara ma da na rame abu na sai kace irin da ma can me ƙibar ce ni. Abun bai fara ba ni tsoro ba sai da na lura gabaɗaya kaya na sun yi mun yawa. In dai ina son na saka kaya dole sai nasa an rage faɗin riga da ƙugun siket.
Rannan da mitar Mama ta addabe ni sai na samu kaina da cewa "Mama ko wannan ramar ce da ake cewa 'yan mata nayi idan sun daɗe basu yi aure ba? Ba an ce idan mutum yayi ta farko zai sake cikowa ba? Sannan ya kuma yin ta biyu....."
Ta katse ni "Ke ni raba ni da wannan sakarcin naku da ba ya ƙarewa. Dududu nawa kike ne yanzu? Ashirin da biyar ko ba haka ba ne?" Ta yi kamar alamar tunani tace "Kina yin addu'a kuwa Ummu? Ko ƙila aljanu ne suka taɓa ki." Dariya na kama yi mata, Mama ta bi ta rikice akan abin da ni da ita bamu da ikon akan shi.
Kullum Baba ya dawo da maltina yake zuwar mun. A ƙarshe dai katan-katan na maltina ya siyo aka jibge mun a ɗakina tare da katan na madara peak milk. Kullum sai na haɗa su na sha, sai damuwar Baba da Mama a kaina ta sa na fara jin tausayin su.
Satin da su Yaya Maijidda suka iso Kano ita da Yaya Mahmoud, ba ƙaramin firgita suka yi da yanda na koma ba. Tambayar duniya ba wanda Yaya Mahmoud bai yi mun ba amma na tabbatar masa da cewa lafiya ta ƙalau, kuma ba ni da damuwa don ni na jima ban ji ni cikin sukuni irin wannan lokacin ba.
Da daddare tunda na ga kiran Yaya Muntari nasan Yaya Mahmoud ya fesa mashi kenan, shi ma haka na tabbatar masa. Ni ban taɓa relationship mara ciwon kai irin na Alhaji Hamisu ba, lau nake zaune da iyaye na, ba ni da matsala da makaranta ko wurin aiki na, to a ina zan samu damuwa?
Amma sai me? Washegari kafin sha biyu sai ga Yaya Zainabu, Yaya Muntari da Sauda a gidan. Har ina mamakin ya aka yi suka zo a wannan lokacin. A falo gabaɗayansu suka sa ni gaba har da Mama. Haka na dinga rantse masu ba ni da damuwa, na basu misalai ciki har da irin kulawar da nake samu daga Alhaji, don bawan Allahn nan kamar yayi mun numfashi yake ji. To me zai faru da ya wuce na baya da har zai sa na dinga ramewa saboda tunani? Ai na zama hardcore yanzu.
Yaya Muntari yace "Ko stress ne yayi ma ki yawa to? Ki bar aikin mana ko kuma ki dakatar da kitchen ɗin naki na wasu lokuta mana."
Mama tace "Yo ina ta ga ƙarfi yanzu? Cikakken bokitin ruwa ba ta iya ɗagawa yanzu ai. Kitchen ɗin kam ai an kwana biyu ba'a yi aiki a ciki ba sai dai kwastomomin da take jin kunya ba zata iya cewa a'a ba, shi ma sai dai ta zauna tana ba da directions wa masu aikin ta."
Yaya Muntari ya sake duba sakamakon gwajin asibiti, cikin jimami yace "Kuma ga shi dukkan gwajin da aka yi ya nuna ba ta ɗauke da wata cuta, ikon Allah sai kallo."
Haka suka ƙyale ni, ni kuma na taso domin komawa ɗakina. Ina gab da zan shiga na jiyo Yaya Zainabu na faɗin "Wallahi Ummu tausayi take ba ni, komai a kanta yake ƙare wa amma damuwa ba ta daɗewa a tare da ita take haƙura ta ci gaba da lamuranta." Ban tsaya sauraron su ba na wuce ɗaki na na bar su.
A ranar su Yaya Maijidda suka koma wurin da suka fito, haka ma Sauda da Yaya Zainabu, shi kuma yaya Muntari sai gobe Litinin zai koma ta jirgi da safe. Idon su fal tausayina.
A satin da Hassana ta zo Kano, a satin na ƙara gano bala'in da nake ciki. Ina cikin bacci da daddare naji ana ta girgiza ni da ƙarfi, da ƙyar na buɗe ido na ina haki kamar na yi gudun famfalaƙi. A hankali tunani na ya fara aiki sannan na ga Hassana duk ta firgice tana ta maganar da bana ji. Abu ɗaya naji ta ambata "Me ye wannan a wuyan ki?" Ganin ina kallon ta kamar bangane zancen ba, sai ta fice a guje. A tare da Mama suka dawo, zuwa lokacin kuma na dawo cikin nutsuwa ta sosai da sosai.
Na amsawa Mama tambayar da tayi mun na cewar me ya same ni da cewa "Wata mata ce ta biyo ni da wuƙa, bana jin me take faɗa amma kamar ina riƙe da wani abu da yake na ta ne a hannu na. Shine ta kayar da ni a ƙasa tare da aza mun wuƙa bisa wuya na har ma ta fara yankawa." Na kai hannu na domin taɓa wajen, a yayinda da idon Mama ya bi motsin hannun nawa zuwa wuya na. Wurin yayi jawur kamar an yanka ɗin. Hankalin Mama ya tashi ƙwarai da gaske, har ta fara addu'a tana tofa mun. A haka muka ƙarasa daren nan tun wurin biyu da rabin dare. Da safe kuma ko alamar abun a wuya na babu, ya baje.
Kullum a haka muke, har dai su Mama suka gane abun na faruwa da ni kullum da zarar ƙarfe biyu da rabi ta yi, sannan a wannan lokacin ne kaɗai zan iya faɗin abin da na gani a mafarkin, haka ma wuraren da ake taɓa ni da wuƙar irin su ciki, wuya, kirji, damtsen hannuna alamar dai kashenin ake son yin, suna kuma nuna kalar ja jawur a daren. Kullum sai da rana suke rama baccin su, inda ni kuma idona yake ƙekashewa na kasa baccin. Daga safe har dare lau nake, haka ma idan safiya tayi ba zan iya tuna mafarkin da na yi domin jan nan na washewa shikenan komai ya ɓace mun.
A ranar da muka cika kwana biyar a haka ne Hassana take cewa da Mama "Allah na tuba Mama, amma ina ɗan wani tunani an ya babu sa hannun matar Alhaji Hamisu a cikin wannan abun kuwa?" Mama ta kwaɓi Hassana da cewar ta bar zato, a bar wa Allah abun shi kawai.
Hassana tace "Ashe fa Mama ba ki san abinda ya faru kwanaki ba tsakanin Yaya Ummu da matar ba ko? Ina zuwa." Ta tashi ta ɗauko waya ta a ɗaki ta kunnawa Mama maganar mu, har wannan lokacin ban goge ba. A take tunanin Mama ya canza, ita ma ta hau kan zargin.
Hassana ita ta kira Yaya Muntari wannan karon ta faɗa abinda ke faruwa da ni (mafarke-mafarken da nake yi), dariya yayi yace "Anya Hassana ba gizo abubuwan suke maku ba?" Ita kuma tace ya tambayi Mama ya ji. Jirgi ya biyo don ko ta kan motar shi bai bi ya taho Kano. A idon shi nayi mafarkin ranar, wannan karon tsintsiyar hannuna aka fara yankawa sannan da ƙyar na farka. Mutuwar tsaye yayi yana kallo na kafin na sake komawa bacci nan take.
Kafin ya koma washegari cewa yayi na dinga saita alarm ƙarfe biyu, na tashi nayi salloli a wannan lokacin don nema wa kaina kariya daga wurin Ubangiji.
Mama ce ma ta tashe ni a ranar wurin ƙarfe biyun tare da yi mun umarnin yin alwala. Zaunawa tayi tana kallona sannan tana kallon agogon ɗakin. Har lokacin ya wuce ina sallah amma a wahale, kaf ilahirin wuraren da aka taɓa ni da su da wuƙa ciwo suke yi sosai, haka dai na daure na cigaba da sallar har sai da uku ta ɗan gota na haƙura haka nan. Ashe tun daren kuma Yaya Muntari yake kiran wayar Mama, kasancewar tana ɗaki na ba ta ji ba. Sai da sassafe suka samu damar magana, Mama ta labarta masa yanda aka yi. Ya sa aka miƙo mun wayar, ya umarceni da na dinga daurewa kullum ina karanta Baƙara tun daga farko har ƙarshe tunda tana nisanta gida da shaiɗanu ga ta kuma kariya ce, sannan ko ta halin yaya kar nayi wasa da azkhar safe da marece haka na haɗa da addu'o'in kariya.
Yaya Mahmoud da yayo waya cewa yayi wa Baba a mayar da ni asibiti, ba mamaki shigen ciwon da ya same ni lokacin rasuwar Yaya Rufa'i ne, watau a zaton shi abinda ya shafi ƙwaƙwalwa ne ya zo mun a sabon salo don jin labarin yake kamar almara. Baba bai yi mashi musu ba, a irin abun nan da ake cewa idan mutum yana neman ceto a ruwa ko wuƙa a ka miƙo, kamawa zai yi domin neman tsira.
Ranar Litinin kam da kan shi ya kai ni asibitin Malam Aminu Kano ɓangaren psychiatric. Ya samu likita yayi masa bayani, an yi tambayoyi, gwaje-gwaje da hotona kafin mu samu mu baro asibitin. A ƙarshe nan ma aka shaida masa lafiya ta ƙalau.
A gida ma ina jin sa shi da Mama, shi ya dage kan cewar ba mamaki shaiɗanun aljanu ne amma ita ta kafe matar Alhaji Hamisu ce, shi kuma sai kwaɓar ta yake yi ba kyau zargi (kamar ba haka tace wa Hassana ba) amma ta ƙi ganewa.
Wurin ruƙuya aka kai ni, ni duk abubuwan ma sun ishe ni. Haka aka ƙare yi mun karatu ina cikin hayyacina ina sauraren su, hakan ya tabbatar masu ba ni da aljanu. Don haka magungunan karya sammu aka haɗo mu da su tare da ayatul shifa. Sun cewa Baba a yi mun amfani da ganyen magarya na kwanaki marra watau uku, biyar ko bakwai, sun bada hanyoyi biyu da zan iya amfani da shi.
Na farko zan samu ganyen magarya arba'in da ɗaya, na dandaƙa sannan na zuba ruwa madaidaici sai a karanta ayoyin ruƙuya a ciki na dinga sha ina shafawa a jiki tun daga gashi har ƙafa.
Ko kuma ganyen magarya guda bakwai, na dandaƙa a ƙara ruwa sai a karanta Baƙara a cikin container ɗin, ya zama hucin karatun ne kawai ke taɓa ruwa ba tofawa za'a yi ba, sannan ba lalle sai a zama ɗaya za'a karance Baƙara ɗin ba.
Sannan aka haɗa mun garin habatus sauda cokali uku, garin yansun cokali biyar, garin hidal cokali biyar sai ganyen magarya rabin cokali aka gauraye su zuma. Shi wannan haɗin zan dinga shan cokali biyu da safe da kuma daddare. Sai kuma wasu abubuwan da suka bayar da ba zan iya cewa ga su ba.
Komai ina yi na dangane da abubuwan da suka bayar, haka abubuwan da Yaya Muntari yace na dinga yi. To kun san rashin lafiya tashi ɗaya yake samun mutum, amma magani sai an yi ta fama kuma an dace kafin a samu waraka. Yanzu kam na daina mafarkan gabaɗaya, na gane hakan lokacin da nake al'ada, kasancewar ba zan yi sallah ba a daren sai nayi kwanciya ta amma na kunna karatun Baƙara.
Alhaji Hamisu shi ma ramar tawa ta dame shi, don yayi maganar har babu adadi. Kullum cikin ƙara kyautata mun yake, ga shi masifar tausayina yake yi. Rashin ƙarfin da ba ni da shi yanzu shi ya fi damu na, amma haka nake manejin yi wa mutane aiki, amma fa ƙarfin aikin ya fi tattaruwa ga masu aiki na, ko babu ni ma yanzu tsaf zasu yi.