BINTUN BATUUL

036

by @takwalam

036





Ko da Muka kammalla test din nayi tunanin kamar yadda aka Saba zai bimu ne one on one ya karba, Amma se yace Mana duk wanda ya Gama kawai ya kife sheet din ya fita, the class is over. Haka kuwan nayi na goge fuska ta sannan na sake dage hijab di na ya rufe kusan rabin fuskata kafin na fita, duk tunani na zaice na tsaya Amma shiru kake ji baice min ba, hakan ya sake tunzura ni naji kamar irin I'm worthless dinnan, na Fara tunanin ko dai shima he finds me boring kamar yadda kowa yake gani.


Ina fita napep na.sauke wata Dan Haka na tare Dan tafiya gida, sede kafin na Kai ga Shiga sajida ta fara Kira na. Se da na shiga sannan na dauki Kiran, Muka gaisa ta tambayi ko na gama lecture nace Mata na gama se tace tana son nazo gidan ta na zauna da yaran ita Kuma zata je biki da Batuul! Wato Ni na Zama Nanny kenan? Kowa idan ya dakko wahalar yaran shi se ya Kira Ni nayi babysitting ko? For the first time nace


" Na karba order cake yanzun zanje nayi suna jira na"


Na fada Ina sake tamke fuska ta, tace


" To kizo ki tafi dasu gida idan yaso idan na dawo se na biyo na dauke su!"


Nan ma nace


" Ai na kusa zuwa gida, sede ki biyo ki kawo su"


Nasan yau zatai mamaki saboda ko kadan ban taba Yi musu musu ba, duk wani abu da zasu saka ni Ina Yi dukda ba godiya ake yi min ba. Haka na kashe wayar Ina jiyo ta tana cewa Batuul ai nace na wuce ita Bata San yadda zatai da yaran ba. Ina zuwa gida na wuce daki kamar yadda na saba, kwamciya nayi zuciya ta ko kadan Babu dadi. Kawai hango dull fuskar shi nake da yadda ko kula ni baiyi ba, zuciya ta se ta Fara tuhuma ta da Wai me yasa na damu tun da kuwa nasan ni da shi Babu wani Abu da ya hada mu, he's just my lecturer, whereas I'm his only female student. To se menene Dan Bai kula ni ba, Naga Yan gidan mu karewa da muke related by blood ba kula ni suke ba shi ne Zan damu Kai na. Maimakon wannan tunanin yasa naji Dan Dadi ko na watsar da tunanin shi, a'a se ma wani bangare na zuciya ta ya Fara kokarin Kare muradin ta da nuna min, shi fa Akram mutum ne me muhimmanci cikin rayuwa ta shi din therapist di na ne, ta Yaya zaai naji Dadi idan therapist di na ya daina kula ni? Shi fa ya Dan Fara boosting confidence di na ya nuna min Nima mutum ce like all other person.


Ina nan kwance se sallah kawai ke tashi na har na Fara jiyo muryar hajja, kamar an tsikare ni Haka na mike, ita hajja mahaifiyar Mamaa ce, da gudu na fita na fada jikin ta Ina dariya, ta rungume ni tana fadin


" Ja'ira! Karya ni kike so kiyi?"


Nayi dariya Ina Zama kusa da ita nace


" Hajja Baki ce min Zaki zo ba Kuma? Sannu da zuwa! Me Zaki ci?"


I find comfort and love a wajen wannan tsohuwar, Mamaa da Adda se murmushi suke ganin yadda muke da ita, ita dinma sosae take sakin jiki da Ni ko jikokim ta albarka. Na tashi naje kitchen cikin zobon da nayi na kawo Mata, na dauki Jakar kayanta zuwa dakin mu. Cikin hour daya nayi Mata grilling kifi na kawo Mata hade da abincin da akai a gida. Se da Naga taci sosae kafin na bar ta ta tafi wajen Mamaa sannan na dawo daki Ina Jin dadin zuwan ta, ko ba komai zuwan nata ya saka hankali na ya dauke daga tunanin Akram. Bayan maghrib hajja ta dawo daki na Muna ta hira har na kasa karatu, Babu jimawa Kuma se ga Iyan KT, ban sani ba ko Kun tuna ta? Idan ba ku tuna ta ba to mahaifiyar Adda kenan. Ai murnar da nake se da ta bawa kowa mamaki, ita ko dakin su Adda da Mamaa Bata je ba, yadda na karbo kayan ta dakin mu na wuce da su, na hada Mata ruwa tayi wanka sannan na hada musu abinci ita da hajja suna ta yabon girkina, Wai ko iayye na albarka. Abin da nayi zai tabbatar maka how lonely my soul is, I'm yearning for love and attention.


Su Adda har Kawu anan Suka zo suka gaishe su. Wajen Tara na Gama musu shimfida anan nake Jin ai kudin Batuul zaa kawo shi ne dalilin zuwan nasu. Adda Dake zaune Bata tafi ba, hajja tace


" Asiya Ina Batula Kuma?"


Se Kuma Adda ta dube Ni tace


" Bintu Ina 'yar uwar ki? Me ya faru Bata dawo ba?"


Na dubi Adda da mamakin tambaya ta Inda shalelen ta take nace


" Tana gidan sajida!"


Se kuwa Iyan KT ta Fara fada


" Yanzun Asiya har Baki San inda budurwar Yar ki ta tafi ba, karfe nawa yanzun? Har yanzun Baki daina sakar ma yarannan suyi abin da suke ba. Ki wasu irin iyaye ne? Ke kawata.."


Ta fada Wanda nasan dani take, dama kokarin fita nake tace


" Wuce kije ki Kira min kawun ku da Maman ku"


Ita fa Haka Iya take, matsawar idan tazo gidannan to se kowa ya koma hankalin shi, bana mantawa akwai wani zuwa da tayi ta samu ana ta zabar kayan sallah Ina daki a zaune, ta Fara tambayar Mamaa ni Kuma fa? Se tace ai Ni bana zaba saboda Kaya na daban kawu yake kawowa tunda ni baka ce. Ta bude idanun ta, Ina Gaya muku katsinancin nata ya motsa. Ta Fara fada tana tambayar su ko sun bawa Allah wani Abu ne da yayi su farare, dama har wani dadi ne ko afuwa ne Akan zaman ka fari. Kusan ranar yini tayi tana fada har kayan da aka kawo min se da aka mayar kasuwa aka canjo min, danma dai shagon Kawu ne.


To daga hajja har Iyan KT dukka basu shiri da Batuul, dukda tafi zuwa inda suke Amma Basu shiri saboda wani dalili da ban sani ba. Haka naje na Kira Mamaa da Kawu, suna tare ma tayi Masa serving abinci. Tunda suka Shiga suka zauna take fada akan Batuul saboda dukkan su sunsan ta tafi makaranta Amma Basu ma San ta tafi gidan sajida ba. Karshe da lallami kawu ya Kira sajida wadda ta tabbatar Masa tun maghrib Suka rabu da Batuul ta taho gida


" Kun bani kunya, har yaushe yarinya daya ku kasa kula da ita, wannan ya tabbatar min cewar Haka take kullum, Kuma Baku ma sani ba. Yaushe lalacewar ku ta Kai haka Hamisu, Asiya da Rukayya! Batular nawa take da zata gagare ku?"


Dake hajja Bata da fada, shiyasa maganganun ta ko fada take to kamar nasiha take, Kawu da kowa dukka sukai shiru ga shi sun kasa samun ta a waya, Nima Kuma Ina parlor se Kiran dayar number ta da duk gidan Ni kadai nake da ita, Nima wani birthday party zaayi na friend dinta shi ne ta Kira Ni da shi da suna min kwatancen in da zaa Kai musu cake shi ne Dana gane contact din ta ne nayi saving.


"Wai menene kike damu na"


Shi ne abin da ta Fara fada da ta dauka, kawai Dan bani da saurin fushi, Kuma Ina da hakuri bacin Haka da tuni gaba ce tsakani na da wannan marar mutuncin. Nace


" Batuul kina kallon lokaci kuwa? Ina kike?"


Daga yadda take maganar nasan ranta a bace yake tace


" Ina gidan sajida Mana yanzun Zan taho"


Ban Karya ta ta ba saboda ni bansan an Kira sajida ba, nace Mata tayi sauri ta dawo saboda Kawu na neman ta, ai shi Bata Gama Raina shi ba. in no time zakuga ta dawo!


" Sannan me yasa auren Batula kawai zaayi Banda Bintu?"


Hajja ta tambaya, Adda tace


" Batuul ce kawai ta samu miji, ita kawar taku ko saurayi Bata da shi, sannan wannan yaron Suleiman muka so hada ta da shi Amma tayi ta Masa wulakanci..."


Ai kuwa Adda Bata San ta ballo ruwa ba, Iyan KT tace


" Ita din BINTUN ba Yar ku bace ba? Tsinto ta kukai? Dan me zata Yi soyayya da abin da Yar uwar ta ta Bari? Wai ku a gidannan kanku daya kuwa? Wanne irin rayuwa kuke? Kun bani kunya, ta Yaya zaku fifita wasu daga cikin yaran ku Akan wasu wannan ba daidai bane ba. Itama kawar tawa tana zaune mijin ta tsalale na idon duniya zai fito, Kuma ba Baki nayi muku ba Allah ya sakawa Bintu kada kuga Kun haife ta, akwai hisabi tsakanin iyaye da yaran su. Ku fita ku bamu waje!"


Dukka suka Mike suka fita jiki a sanyaye, har lokacin Ina parlor Ina jiran Batuul wadda ta sake Kira na Akan Ina Kawu, nace Yana daki tayi sauri ta shigo. Cikin rashin saa tana shigowa suna fitowa su kuma, sukai kicibis akace Wai kicibis mugun gamo! Ran shi dama a mugun bace yake, Ina fata Baku manta kawu da zuciya ba dukda ba sosae yake nuna hakan ba, Yana zuwa ya dauke ta da mari Yana fadin


" Daga gidan uban wa kike? Ina Kika je se goma kike dawowa?"


Marin ya girgiza ta ba kadan ba, Dan har Jakarta da Bata Gama rufewa ba Bayan ta karba kudi hannun honorable ta Fadi a kasa, a take kudin Suka fito, dukka Mamaa da Adda Suka bude bakin su suna fadin wannan wanne irin tozarci ne cikin dare. Kafin ta Kai hannu ta dauka har ya dauka, mint ne na 1k wrapper guda biyu, ai Ina Gaya muku wannan Daren kusan kashe Batuul yayi, duka dai seda hajja da iya da Kuma wani makwabcin mu suka so kafin aka kwaci Batuul hannun shi, kawu Bai hakura ba ya shigo dakin mu Dan ita se rusa kuka take ta gudu dakin Auwal, Ina tsaye Ina kuka saboda hankali na ya tashi na Kuma tsorota da dukan yace


" Ina ne wajen kayan ta!"


Hannu na rawa na nuna Masa, aikuwa ya bude ya dinga watso da kayan kasa, kudi Nadi Nadi Haka Suka din ga fadowa, kunsan se da aka hada kudin sun Kai 900k, ai Adda se ta Fara kuka, ana bude Jakar ta se ga mukulin wata Benz ya Fado, innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Munga tashin hankali wannan Daren Wai Saar mu saya sirikan kawu na nan, se da suka ji inama Basu ce Ina Batula ba da kilan hakan Bai faru ba. Tun da yaga key din motar ya ciri igiyar shanya ya nufi dakin Yaya Auwal ya fito da ita, tana ihu ga lokacin gari yayi shiru Bayan dare Kuma layout ce, kunga kowa na gidan shi, anan tsakar gida yace a gaban kowa ta Fadi motar waye? Da farko tace ta kawar tace, da ya zuba Mata wannan igiyar guys se tace


" Kawu wallahi tawa ce, tawa ce !"


Yace


" Uban waye ya siya Miki?"


Tana ihu Yana tafkar ta tace


" Honorable ne!"


Lokacin dukan yayi yawa har ya samu fuskar ta, nayi ta maza ganin kowa tsoron magana yake masa, na rike bulalar na tsugunna har kasa nace


" Kawu Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah!"


Kilan shima jira yake wani ya Hana shi, kunsan dai yadda kawu yake son Batuul, Dan da amincewar shi Batuul ta ruguza maganar Suleiman Dan abokin shi. Ya yarda bulalar sannan ya wuce dakin shi, Nima naja hannun kawaye na muka tafi, kowa jikin shi a sanyaye yake. Muna zuwa har sun kwanta se ga Batuul ta shigo har lokacin kuka take, tana shigowa Ina tattare Mata kayanta, warcewa tayi daga hannu na tace min


" Munafuka kawai!"


Sannan ta nufi gadon ta kafin ta hau ta hangi iya da Kuma hajja a gado na dake nawa na da girma tace


" Anan zasu kwana! Aikin banza uwar shishigi duk se kin da dakin mu yayi warin tsofi!"


Tana fadin Haka ta fice ta barni da Jin kunya, hajja tace


" Wannan yarinya iyayenta sun lalata ta da yawa!"






Ta_kwalam ce





Be reminded that BINTUN BATUUL is not free, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI! They're still ongoing with as low as N1300.