KAZAMIN TAKU

4…Mayafin Sharri

by @hafnancy

"Kamar yadda na fad'a maka dazu magana ce nakeson muyi akan d'iyarmu _*RAHAMA*_ da kuma dan'uwanka k'aninka _*YUSUFA*_ , wato gabaki daya wannan kusancin nasu da juna ya soma bani tsoro, ina jiye mana ranar da zasu saka mu cikin tsaka mai wuya su manta da alak'ar dake tsakaninsu Sannan su furtawa juna kalmar SO....." Papa ya yanke mata magana ta hanyar sakin wani irin dariyar da ko kusa bai shirya yinsa ba, ita kuwa binsa take da idanu ranta na mugun suya, meye nufinsa ? Kenan shirme take fad'i ko menene ma'anar dariyar ?

   Dariya sosai fa hadda hawayensa, abun ya soma kai mata wuya tace cikin d'an fushi fushi"Haba Abdulmalik meye abun dariya kuma ? Ko kana nufin kace mun maganar da nayi sam bata kan hanya ne ?"Yace"Kema dai k'ya fad'a, dan ni dai ban tab'a kawo irin wannan tunanin araina ba, kece dai wallahi da ban san wani irin Zuciya Allah ya baki ba mai shegen zargi, hangen nesa da kuma kawo misalin abunda bazai tab'a iya yiwuwa ba..." da sauri ta tari numfashinsa"Bazai tab'a iya yiwuwa bafa kace ?" Cike da takaicinta yace"Yo! zancen banza dama so kike ya yiwu ? Ey Halima tambayarki nake ? Nace so kike Yusufa yace yana son Rahama ?" 

"Wai meyasa kake k'ok'ari juya maganata ne ? yanzu nayi laifi kenan dana gaya maka damuwata ? Nayi laifi dana bud'e maka zuciyata dan kaga abunda ke cin raina haka ne?" Sai kuma ta koma ta d'an sassauta"Haba Abdulmalik ka fahimceni mana, idan ka duba Yusuf matashi ne wanda da kadan yaba Rahama baya ashekaru, ka manta da batun wai yana matsayin k'anin mahaifi agareta, wallahi soyayya bai san wannan ba, yau da gobe idan shak'uwarsu ta wuce misali mai yiwuwa ta koma soyayya, abunda nakeso ka gane kenan amma ka kasa."

   Sosai takeson caza masa k'wak'walwa amma kuma ya fahimce ta, tabbas akwai kamshin gaskiya agame da zancen nata, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama harhad'a abun da zai gaya mata"Halimatu kibar wannan tunanin inshaa Allahu hakan ma bazai tab'a faruwa ba, bamu mafarkin hakan kuma bamu fatan hakan, karki manta anyi baikonsa da budurwarsa Ameerah, lokaci kalilan kawai ake jira arakashe asha biki da zarar ta kammalah karatunta, kin sani kuma nima na sani na cewa lallai yana masifar sonta dan haka ni bana irin tunanin dake kikeyi akansa shi da Rahama " 

    Dan siririn tsoki yaja na takaici yana mai dafe kai yace"Kai wallahi Halima wannan zance naki ma babu dadin ji ko kadan, abu sai kace daddawa a shayi ? Gaskiya in baki shawara kar ma ki sake yaran nan su ji wannan batu naki dan sosai zasu daina ganin girmanki "

   Uffan Addah bata sake cewa ba ta tashi ta fita daga dakin.


****


"Kina da maganin damuwata fa kikace ? ya kuma akai kika san Shuraim Dan'zaki dan'uwana ne ? Ko dan kinga yana amfani da inkiya irinna family d'inmu yasa kikai tunanin ni dashi muna da alak'a mai k'arfi ?"

Murmushi mai kayatarwa Zalihat ta sakar, ayangance ta karaso inda Ubaida take tasa hannu ta dafata tace"Lallai kanki naja, wato last three month ne dana raka wata k'awata mai suna Keturah zubar da ciki acan Maryam Abacha hospital sai na had'u da k'awarki Rahama acan itama taje Zubar da cikin, duk noke nokenta sai danayi bincike har na gano abunda yakaita asibitin tunda mu ba sabon abu bane awajenmu, to anan dai shi Nurse Shuraim yayi ta fad'a akan su sun bar zubar da ciki awannan asibitin, kodayake dama can shi baya cikin masu taimakawa wajen zubarwan amma kar kiso kiga yadda ya fusata ainun ranar musamman ma Rahamar yafi jin haushinta kamar itace mace ta farko data fara yunk'urin zubar da ciki aduniya, to anan kawai naji ya burgeni, naji sonsa farat daya ya shigeni, banyi kasa agwiwa ba wajen tambayar ma'aikatan asibitin cikakken sunansa, basu kawo komai arai ba suka fad'a mun, nan take na aiyanawa kaina cewa duk yadda akai dan'uwanki ne ..."


  Wani irin mugun firgici da mamaki ne duk ya rufe Ubaida alokaci daya kuma wani irin zufa ya feffeso mata tamk'ar wacce tayi wanka da ruwan zafi.

Cikin k'aryewar murya tace"Wacc..ce...waccee Rahamar kike nufi wai ? Ban fa ganeta ba ?" Wani uban Harara Zalihat ta watsa mata aduhu, bata yi wata wata ba ta fuzgo hannunta sukayi hanyar waje gudun kar wani acikinsu Nuratu ya fito ya gansu tare dan kowa ya sani had'a alak'a da Zali ba alheri bane.

Saida suka fita acikin gidan gaba daya sannan Zali ta sakar mata hannu tana dubanta tace"Rahama dai k'awarki wacce lokaci zuwa lokaci kuke zuwa gidan nan tare " Dafe k'irji Ubaida tayi , idanunta suka firfito sosai tace"Abun al'ajabi dan wannan al'amarin ya wuce akirashi da abun mamaki, yaushe Rahama ta lalace ta zamo haka ? dama ita d'in fuska biyu gareta mutane basu sani ba ? To waya sani ko yawancin maza sun gano b'oyayyen halayyarta ne shiyasa suke guduwa babu mai son aurenta ? Yawancin maneman nata ma 'yan ayi rayuwa ne, sai kaga tana borin kunya wai su fita ahanyarta, ashe duk mu take ta sakawa akwana bamu sani ba.." ta furta tana mai tab'e baki, Murmushin jindadi Zali ta sakar dake nuni da alamun anci nasara akan abu kan ta cigaba"Wallahi kar kiyi wani mamak'i dan da'ace zaki ga ire iren abubuwan da mata irinta sukeyi abayan idon mutane, da tsoro da mamak'i sun kusa kasheki, wallahi wallahi da irinsu gwara irinmu sau dubu tunda mu namu abayyane yake, su kuwa fuska biyu garesu su ruk'a rud'a al'ummah, hhmm ai baki ma ga tashin hankali ba sai kinji wanda yayi mata cikin asannan ne zaki nemi kanki ki rasa" Wani irin faduwar gaba ne ya saukar wa Ubaida, daqyar ta iya cewa"Wa....wanene shi d'in ?"


Saida Zali ta kwashe da wani irin dariya kan ta dubeta tsaf dak'yau ta girgiza kai tana fad'in" A,a Ubaida ban tsammani kin shirya ji ba, kar in gaya miki ki taramun jama'a akofar gidan malam salele (haka ake kiran mahaifinsu).kije kawai in lokacin dana ga ya dace ki sani yayi zanzo har gidanki in fad'a miki." Ta juya da nufin komawa cikin gida, da sauri ta dakatar da ita"Dan girman Allah Zali karki mun haka, karki bar zuciyata cikin zullumi da rashin nutsuwa, ki taimaka ki gayamun don na tabbata abu ne wanda ya shafeni."

   Zali tace"To shikenan tunda kin nace, kuma tabbas kinyi gaskiya abu ne wanda ya shafeki dan in bai shafeki ba to meye dalilin da zai saka in nemi fesa miki ? Ko azatonki gulmarta na kawo gareki ? To bari kiji ni bani da lokacin gulmace gulmacen da bashi da amfani, tunda kuwa kiga na jaki gefe to ki sani lamari ne daya tab'oki shiyasa nakeso in gaya miki dan kisan makasud'in damuwarki, inace damuwar taki bai wuci akan wulak'anci da kuma cutarwan da Umar yake miki bane ?"

  Araunane tace"Hakane..." Tace"Toki sani wacce kika gama yarda da ita ne ke cin amanarki ab'oye...." Kallon rashin fahimta Ubaida tayi mata amma kafin ta kai ga magana Zali tayi saurin cewa"Abin nufi shine Rahama na mu'amala da mijinki Umar awaje, kuma shine yayi mata cikin da nake gaya....."Kan ta karasa maganar taji saukan wawan mari, da sauri takai hannu ta dafe wajen dan azaba, 'yar yatsa Ubaida ta shiga nuni da ita, yatsar na rawa sosai ga wasu zafafun hawaye na tsere bisa kumatunta tace"Wallahi k'arya kike, Nasan Umar kuma nasan irin rashin jituwar dake tsakaninsa da Rahama, da'ace sai da an kwan biyu ne kika zo mun da wannan zancen ina iya yadda dake Tunda ni shaida ce ayau sai da muka samu sab'ani da Rahamar akan tayin kanta da tayiwa shi Umar d'in." 

   Duk ta rud'e ta rasa nayi, ita kuwa Zali har zuwa wannan lokacin bata sauke hannunta akumatunta awajen data sha mari ba, kallon Ubaidar kawai take yadda take kai da komo tana cizar yatsa sai sambatu take tamk'ar mahaukaciya sabon kamu.

 "Kodayake zancen naki na iya tabbata gaskiya, tana iya yiwuwa sun dad'e suna mu'amalar nice kawai suka sa acikin duhu, ba shakka kuwa kila bayan ya gama moreta ya nemi jefar da k'wallon mangwaro dan yahuta da gud'a, ita kuma ta nuna masa bai isa ba don daga jin irin zafafen maganunganun da sukayi ta yayyab'a wa juna yau kadai ya isa ya gamsar dakai cewa lallai akwai wata akasa, Innalillahi wa'inna ilaihi raj'iun Ya Allah kana dai gani, kana ganin abunda ke gudana arayuwata, in fita daga wannan matsalar in shiga wata, kwata kwata bani da ranar jindadin rayuwata, Ya Allah kai kadai kasan karatun kurma da abunda yake nufi, Allah ka sakamun kabi mun hakk'ina ..." 

   Ta rushe da kuka kasa kasa, wani irin dariyar keta ne Zali ta kece dashi tana fad'in"Wayyooo Allah Uba inji hegiya, au! Wai dama ashe zaki dawo kan hanya da wuri haka ban sani ba ? Dan Allah ki cigaba da karyatani, Kar kiyi amfani da hannu wajen buguna ki samu lafiyayyen bulala ki had'a ina ganin zaifi, Ki sani albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan Zomo, ina nufin kinci albarkacin nina kwaso jiki na kawo miki wannan labarin shiyasa duk abunda zakimin bazan ji zafi ba tunda nina kawo kaina, amma da'ace kece kika zo gareni da kanki dan jin batu kuma kikamun irin wannan rashin mutuncin to da wallahi abin daya bugi hanci ido ruwa zaiyi."

   Ubaida tace"Kiyi hakuri amma ina kika samo wannan labarin ? Taya akai kika san da cewa suna mu'amala ab'oye ? Kuma menene tabbacinki na cewa cikin data Zubar na Umar ne ?"


 _*UMAR...#*_


Yana fita gida bayan ya gama cin zalin Ubaida kai tsaye bar house d'insa ya nufa mai take _*'Dan'baba's Bubbly moments'*_ wani d'an kayataccen wuri ne inda 'yan rayuwa ke haduwa ata iya shege da mashaya duka, kuma anfi bud'e wurin musamman da daddare ne kasancewar irin wannan rayuwar yafi nishad'i ne da dare, anan duk wani tattalin arzik'insa ke k'arewa, duk abubuwan da yasan ana yawan nemansa baya tab'a bari suyi kasa yake sake odansu, akwai mai yin suya na musamman agefe daya, akwai kuma kwararren DJ wanda idan ya soma sakin kid'a da rawa sai ya tabbatar daya jawo hankalin duk wanda yake cikin wannan bar d'in, zaka ga kawai ka tsinci kanka ne da motsa jiki.

Kakaf Garin Sokoto duk wanda yace maka baida labarin _*Dan'baba's Bubbly momments*_ to bak'o ne agarin domin kuwa ko d'an yaro yasan da zaman wurin nan.Ba karamin kasuwa Umar ke samu shiyasa baya wasa da wannan waje, yadda kasan ibadarsa ya zame masa dole yayi to haka yake bautan wannan waje, gashi da Farin jinin mutane musamman Mata.Wani glass of Whiskey Smash drink ne ahannunsa yana kurba alokaci daya kuma yana latse latsen waya, Can sai ga wata matashiyar budurwa wacce da alamun ita kadai tazo bar d'in ba rakiyar Saurayi, tasha damammen Skinny dake nuni da zub'in halittarta, Zuwa inda yake tayi ta duk'a daidai fuskarsa tana murmushi, yana sane da zuwanta amma sai ya fuske tamk'ar bai san da zuwan mutum wurin ba, one finger tayi amfani dashi wanda yasha cortels ta d'an dago habarsa,sai alokacin ya watsa ocean bule eyes d'insa cikin nata cat eyes d'in, ai tuni ta ida rikicewa, cikin wani irin murya tace"Handsome yakake ? ina fatar dai baka manta da alk'awarinmu bako don yau nayi booking..." saurin taran numfashinta yayi bayan ya saukar da d'an yatsarta dake pinching hab'arsa yace"Wani alk'awari kenan ? dama ni akwai alk'awarin da zan daukar wa mutum sannan har ya daukeshi Serious ?" Ya furta yana dariya, Bata damu ba tace"Last month kamun alk'awarin rawa dani har kasa mana date kuma shine ya fad'a ayau, kusan kullum sai kayi rawa da budurwa acikin bar d'in nan ina kallo ina had'iyar maitana akanka, so please come rock me too Bcz i can't take off my eyes on you today." Ta furta tana d'an motsa jikinta, sosai take watching steps d'inta da kid'ar dake tashi, tana rawar ne hannunta na sakale cikin nashi tana k'ok'arin mik'ar dashi, da sauri ya fuzge hannunsa yace"Look Shama am not in the mood, nasan alk'awari kaya ne amma ki sani sai an nad'a gammo ake dauka.."


  *

  *


Hannu bibbiyu Zali ta dora saman kafadar Ubaida ta murtuk'e Fuska alamun babu wasa"Arayuwata banason in kawowa mutum labari wanda ya shafesa sannan ya kureni da tambayoyin inda na samosu ko kuma na jiyosu, Ki sani Ni Zalihat bana bibiyar labari da kafafuna sai dai yazo har inda nake ya shiga kunnuwana kana ya zauna daram acikin k'wak'walwata, ma'ana azo har inda nake afadamin, to idan kaci sa'a 'yan taimako na kusa ina iya nemanka in fesa maka in har naga in akayi wasa abun yana iya cutar dakai, kamar ke naga dacewar in gaya miki ne dan ki farga da Rahama, kibar bud'e mata cikinki tana gani sabida ita d'in maciya amanar ki ce"


 "Yanzu kina nufin kicemun haka zaki banni cikin duhu? ki tuna fa bani da k'wakk'warar hujjar da zanyi amfani dashi ayayin dana tunkaresu da batun, ki taimakamun Zali ke kadai ce kawai tsanina ayanzu .." Ta ida magana tare da kamo hannayen Zalin tana d'an murzasu abun dai gwanin ban tausayi.

   Murmushin jindadi Zali tayi kan tace"Naji Zan taimaka miki amma nima karki manta da nawa taimakon, shuraim nakeso.." duk da cewa tasan ba abune mai yuwuwa ba amma ita dai ayanzu babu abunda takeso sama da taga ta taimaketa, sai cewa tayi"Naji nima zan taimaka miki muddin kika taimaken..." Cike da farin ciki Zalin tace"Dak'yau tawajena, yanzu dai bazan bari kije ga Umar ba har sai na koya miki yadda ya kamata ki tunkarensu da batun bayan kin samu koshin lafiya kenan " cike da mamaki tace"Ya akai kika san bani da koshin lafiya ?" Murmushi Zali tayi tare da cizar kasan lips d'inta tace"Hhmmm Ubaida kenan kin maida Zali karamar 'yar duniya, Ki sani wallahi duk yadda kike tunanina na wuce nan, kin samu miscarriage yau kuma Umar ne da hannunsa yayi sanadin kashe ran, haka ne ko ba haka ba ?"


Tsoro da mamaki sune duk suka cika zuciyar Ubaida akan Zali, sai girgiza mata kai take kamar wata tababb'iya tsabar rud'u"Eh...Eh..haka ne..." bata son ta dameta da tambayoyin da bata so in ba haka ba taso ne tace"Waya fad'a miki ?" Dan ita dai tasan bata samu damar yin hirar dasu Nuratu ba.Zali ne ta katse mata d'an guntun tunanin da take"Bari in kimtso ki jirani anan ina zuwa, dama jiya nashigo kuma na samu su Hajiya basa nan wai sun je biki, kin ga zama bai ganni ba tunda dama dansu nazo, kuma ko ba dan wannan ba tunda ga ki ai bazamu zauna agidan ba sabida Surukanki zasu farga da halin da muke ciki kuma ni bazanso hakan ba.."


   Tana gama magana ta juya ta shige gidan da sauri sauri dan bata son Abbansu ya dawo ya cimmata, tun jiya data shigo gari bai sai da zuwanta ba dan shi ya riga ya yafewa duniya ita ko, Shigar ta keda wuya ta cimma 10missed calls na Umar, babu b'ata lokaci ta nemoshi awaya, yana dagawa yace"Ke bariki ina kika shige ne wai ina ta k'ira?" Tsoki taja tace"dad'ina dakai Danbaba akwai gajen hak'uri, wannan irin k'iran sai kace duniya ce ta tashi aka manta dani aciki ?" Dariyar shak'iyanci ya sakar ya zuk'i tabar dake hannunsa yace"ya kike abu ne sai kace kin manta da wannan kalmar da hausawa ke yawan yi _*' wanda ya kwana cikin zafi yafi kowa k'osawar gari ya waye'?*_ Tace"Wannan kuma kaika sani, aikin banza wai faso a ido, da ina tare da waya yanzu shikenan daka b'ata mana aiki" gwalalo eyes waje yayi yana fad'i da d'an k'arfi"What ??? Kina nufin kiris ya rage da mun koma square one ?" Tace"Har ma abun dayafi Square one d'in" Shafa kwantacciyar sumarsa yayi yana fad'in"ai abunda yafi square one zero kenan...Shit! da wallahi na kopsa, yanzu ya ake ciki ina fatar kin kammala aikin naki ba tare da an samu wani matsala ba ?" 

 Mik'ewa tayi tana d'an rawa tace"ai wallahi ka bari kawai mutuniyar ta gamsu, na rud'ata sosai kuma ta yadda da duk abunda na fad'a mata akan Rahamar, yanzu haka ma ni take jira awaje Mu tafi can gidana dake Shagari." Wani irin sowa da fito ne ya saki yana fad'in"Wawoo Job weldon Uwar Bariki! ina yinki, yanzu abunda nakeso dake ki tabbata kin zugata, ki nuna mata dacewar taje har gidansu Rahama taci mutuncinta tare dana iyayenta, Kinga Rahama zatayi bak'in jini awajensu kuma zasu nemi ganina suji ta bakina ko dagaske nayi mata cikin har ta zubar ? Zata so taci musu amma kibar komai ahannuna zan yiwa tufkar hanci, zan tabbatar dana gamsar da iyayen cewa lallai nayi mata ciki, hahhahah Babe what next do you expect ? zasu nemi alfarman in rufa mata asiri in aureta, Ke dai kawai just watch how the legend wins, in har inaso in mallaki Rahama dole sai an bi KAZAMIN TAKU."


Zali tace"Shege _*Namiji Kumurci*_ , Namiji mai k'ayan baya, Namiji Hankaka, gabanka Fari, bayanka bak'i.." Dariyan farin ciki ya bushe dashi dan sosai yaji dadin wannan k'irarin yace"Wallahi wallahi saina auri _*Rahama Abdulmalik*_ tunda har ta diga mun kwadayinta araina, ki rubuta ki ajje wannan statement d'in yau uku ga watan Afrilu ashekarar dubu biyu da goma (03/04/2010)................✍🏻"


_*"And this was the beginning of my Sorrows! but mind you, my deepest sorrow among all was once the loudest happiness"________ *RAHAMA ABDULMALIK*_



Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.


Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.


Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 ***.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus




#OneLove

#KT

#HafnancyCe

#UltimateWriter

#IWrite4rmTheHeart❤️

#AnaTare

#Nagode🤝