FACALA

chapter 23&24

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*


*_Wattpad profile✅_*

Rabiatu333

*_𝘼rewabooks profile✅_*

 Rabiattu0444


*Sirrinmu➡️*

yawaita azumin lafiya, yana karemu daga barin aikata ɓarna.


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️23& 24

…………………dariya Fulani take sosai,har sai da ta zauna daram akan lallausan kafet ɗin dake shimfiɗe ababban falon, sai taga wannan dariya da murnar ba zata yi ta ita kaɗai ba,har sai da ta danna ƙerarriyar wayarta ta dannawa faccalarsu kira,don duk wani tuggu da ita ake haɗawa.


kiran farko ta ɗaga tana mata kirari,katseta tayi da ce wa"ke nifa bana son wannan kirarin, don haryanzu bai yi dai dai da kirarin da nake so a dinga yimini ba,uwar gida awajen sarkin Babbar masarauta,uwar yarima me jiran gado to wannan kirarin shi nake so ki dinga yimin, ba wani uwar gida sarautar mata ba a ina na zama sarautar matan? bayan waɗanda basu kaini matsayi ko sarauta ba,har ana iƙirarin sune gida tunda sun haifi yarima?.dama albishir na bugo inyi miki wannan buɗaɗɗiyar wasiƙar dana daɗe inason ta warware kowa ya santa yay dai ta fashe,don kuwa ashe Yarima wata ya yiwa ciki ta haihu ƙarshe ya kai yaron gidan marayu,kai abin fa babu daɗi awajen fulani, amman ni awaje na tamkar hasken farin wata musamman tauraro me suna Zahra".

da sauri Fulanin soro ta miƙe tana kyakkyaɓa dariya,tamkar tsohuwar da ta daɗe batayi dariya ba ta ce"hhhhh wato daɗina da gobe saurin zuwa,yanzu kinga sai muyi abinda muka ga dama babu wani ɗan iskan da zai sanya mana baƙin kyalle,tunda shima abin kunyar a gabansa ya ƙare,kuma ina me tabbatar miki zuciyar Fulani yau bindiga xa tayi kowa ya huta,shegiyar da ta saka akayimin kishiya? saboda tsanar da take mini? ita ba uwa ta ba,ba komi na ba sunanta Faccala tauraruwa me wutsiya,ai dole ne innuna mata zaren ba kalar yadin bane".


  Dariya Fulani mazugal tayi sannan ta ce"uhm ai duk ba ma wannan ba,yadda mutanen gari zasu ɗauki al'amarin shine abinda ke ƙara sanya zuciyata cikin farin ciki da kuma walwala,yau kam sai nayi kyautar dawakai ɗari biyar,tare da haɗa kyakkyawar kilisa acikin babbar masarauta".HHHHH ta kyalkyale da dariya tana ajje awayar,ta ce"Fulani rayuwarki tana tafin hannuna".


***       ***        ***

yaya zubair ya yarda da shawarar Ammi ɗari bisa ɗari,bai sanar da hajiya komi ba ya tafi gidansu Balaraba,abin takaicin bai wuce ganinta da wani ƙaton alhaji ba yana ƙofar gidansu suna bakin mota,itan kuwa kamar zata shige jikinsa tsabar takan sanin barikanci, ita ko tunanin wani ya gansu ma bata yi,abinda ta sani kawai ita bata shayin kowa ya ganta dana miji,takaicinsa bai wuce auren wannan gantafalalliyar matar ba wacce ta gama bawa maza jikinta tayi ƙwantai tayi saura.sannan ne shi za a ɗauko masa ita ace ya aura? banda uwa uwa ce wa ya isa ya kawo masa wannan juyayyiyar shawarar,wacce da ita da babu duk ɗaya? shi kaɗai ya ke ta bayanansa har ya ƙaraso wajen da suke,bata gansa da farko ba har sai daya ƙaraso sosai.yana hango tsoro fal a fuskarta don shi bai ma ɗauka tana da wani abu tsoro ba,amman bai san me yasa take tsoronsa haka ba tuni jikinta ya yi sanyi,ta kalli alhajin ta ce"kaga nayi baƙo ka dawo gobe ko"?.

gyaɗa kai ya yi sannan ya ce"ok an jima dai kinsan ina da time dake,saboda haka a guest house ɗina zaki sameni".

yana faɗar hakan yabar wajen.


  bai yi kishinta ko ɗaya ba,don daman yasan za tama aikata abinda yafi bin maxa,don yasan tarihinta sosai ba kaɗan ba shiyasa daya ganta da wannan baiji abin wani iri ba,don yasan awajenta ita ba komibane.

tana ɗan sosa ƙeya ta ce"am wannan wani ɗan uwa na ne,saboda haka kada kaji wani iri don ka ganni dashi".


 amsar daya bata shi ya ƙara tabbatar mata da ce wa shifa ba wai ya damu da ita ba ne.


 "au ai ni ba komi don na ganki da wani,saboda haka kada kiji wani iri kema".


 kasa ce wa ƙala tayi,zuciyarta na mata zafi tamkar tukubar gashin tsire,ta ce"lafiya kuwa kazo da ranar nan"?.

Ya murmusa ya ce"eh wani waje zaki rakani kaɗan".

jin hakan yasa ta ce"ok ai ba komi mu tafi kawai".

don daman ta jima tana son shima ya zama ɗan hannu kamar sauran mazan da ta rufta dasu da yaudararta,don Allah ya bata jiki don ba tada rama gaskiya,saboda haka take amfani da wannan don yaudararsu,gata fara kuma kunsan maza sa son mace fara ko da mayya ce.


  bai yi mamaki don bata tambayi mahaifiyarta ba,yasan za tayi abinda yafi haka ya biye mata kawai suka wuce,suka hau adaidaita suka wuce zuwa inda yayi niyyar kai ta ɗin.


  basu tsaya ko ina ba sai a asibiti,ta dubesa da sauri ta ce"Zubair asibiti fa ka kawoni"?.


 shima kallon ƙasan yayi mata sannan ya ce"to zan siyar dake ne"?.


 bata ƙara cewa komi ba,har suka ida shigowa asibitin ya haɗata da likitar da zata gwada ta,tuni gumi ya fara tsattsafo mata don wannan cikin batayi saurin zubar dashi ba,gashi har Zubair ya gano hakan? ta rasa amsar da zata bashi har sai da likitar ta shigo ɗauke da file ɗinta na binciken ta da akayi.


  ta rintse idonta tana juyawa gefe,likita kuwa ta hau faɗin abinda ke cikin file ɗin tuni Balaraba ta fara jiƙewa da gumi,shikkenan anyanka ta tashi don tasan Xubairu ba lallai ya aureta ba,gashi kuma tana masifar son shi sosai don yana da siffar irin mazajen da take so.



ko da ta gama jin komi,ya kalle ta ya ce"tashi mu tafi".


bata ƙara cewa komi ba suka fito,amman jikinta duk amatuƙar sanyaye ya ke a ƙofar gidansu aka ajjeta shi kuma yayi gaba abinsa zuwa gida.


 ya kalli mahaifiyarsa ya ce"Hajiya yanzu kinyi min adalci kenan? A rasa yarinyar da za a haɗani aure da ita sai karuwa? wacce ta gama yawon bin mazanta har ta kwaso ciki? wallahi Hajiya ko da na auri wannan gantalalliyar bazan iya zaman aure da ita ba".


  Hajiya ta ce"inji uban waye duk ya faɗa maka hakan? duk wanda ya faɗa maka so ya ke ya haɗaku,amman kada ka manta aurenka da Balaraba tamkar anyi an gama ne,zancan banza zancan wofi aure de babu fashi".




haka dai rayuwa ta cigaba da garawa,har sai da ya gaji ya faɗawa mahaifinsa duk halinda ake ciki,kai tsaye ya same ta yayi mata lilis sannan ya tabbatar mata shi fa ɗansa ba zai masa auren dole ba,ya auri duk wacce ya keso amman shi ba zai bari ɗansa ya auri me yawon bin maza ba,sosai akayi rikici don kuwa har sai da hajiya ta dena kula zubair saboda ya haɗata da Alhaji,sannan shi Alhajin ya shige masa gaba wajen kai kuɗi gidansu aminiyata Baby,ranar munyi murna sosai duk da itama anso a samu matsala daga gidansu,don gaskiya tayi ƙanƙanta sosai da aure duk da ta fini yawan shekaru ita tana fa 15 ni kuma 13,alokacin ne kuma ya Ahmad ya bada shawarar kai ni boarding,don dama mahaifinsa ya ce dole sai na kai 16, sannan za ayi auren sannan alokacin zan tafi s.s.1 ne saboda haka aka kammala komi na zuwa makatantar ƙwana.

munyi kuka sosai ni da Ammina,da kuma aminai na biyu Baby da kuma Amira daga bisani kuma muka haƙura,Abbana da Ammi sai babansu ya Ahmad,da kuma ya zubair da ya Ahmad sune suka rakani makaranta.


 sosai nake kallon makarantar,duk sai naji jikina yayi sanyi sosai yanzu anan zan rayu tsawon shekara uku? ba tare da Ammi da Abiey ba?ba tare da ya Ahmad ba? tuni na faɗa jikin Ammi na dinga kuka tamkar zan amayar da abincin dana ci,ai kuwa Ammi ta shiga cikin damuwa sosai nan da nan itama idanuwanta suka kawo ruwa,ta rungumeni da ƙer aka rabamu suka tafi muna banƙwana bayan sun sadani dame makarantar,aka kai no hostel na ƴammata jikina yayi sanyi lokacin da muka shiga sai kallona suke,har mukaje dai dai gadon da ya zama nawa ne ayanzu.bayan na zauna na jera kayana a wadrof ɗin dana gani,na ƙara fashewa da kuka acikin ƴammatan wata tazo ta dafani ta baya ta ce"sau haƙuri makaranta ki dena kuka,zaki saba damu yanzu idan kin gama sai kije kiyi wanka".



na ce"to".


ashe wannan makarantar dana shiga,itace tushe da kuma ƙaddarar da ta janyoni har zuwa uwa duniya zuwa wannan makarantar,me cike da firgici da kuma tsoratarwa acikin wannan ƴar gajariyar rayuwar ta wa.


  ina fitowa daga wanka na tarar da ita agefen gadona,ta ɗakkomi har da kayan da zansa nayi murmushi gami da ganin kirkinta na ce"na gode sosai".ta ce"haba ai ba godiya a tsakaninmu ke de kawai ki zama me kula da kuma taka tsantsan acikin wannan makarantar ta mu,idan kuma ba haka ba zaki shiga irin rayuwar dana faɗa a baya,wacce taso ruguza rayuwata ahalin yanzu ban dama Allah ya taimaka da rayuwata ma na rasa ta baki ɗaya".


  da sauri na kalle ta,sannan na ce"ban gane me kike nufi ba ƴar uwa?".


  tayu murmushi sannan ta ce"kiyi haƙuri bazan faɗa miki yanzu ba,amman nan gaba za kisan komi".


  jikina asanyaye na amsa tare da shiga banɗaki na sanya kayan sannan na fito,abinda na gani ne bayan fitowa ta ya sanya ni kusan sandarewa awajen gamida fasa ihu........



***       ***        ***

tsugunnawa yayi hawaye na ƙwaronyowa a idonsa,sannan ya fara magana cikin dakushewar murya da kuma rauni,duk da yana aro jarumtar amman ba zai taɓa iya yiwa mahaifinsa ƙarya ba,don abaya yasha yi musu ƙarya ya yinda kuma su suka yarda dashi ɗari bisa ɗari.


  da sauri me martaba ya kallesa sannan ya ce"yarima lafiya na ganka haka"?.

ƙasa ya yi da kansa sannan ya ce"na sani ni me laifi ne awajenka dama mutanen gari,don Allah kuya femin abinda zan faɗa muku ba lallai ne yayi muku daɗi ba,amman faɗar alkhairi ce,saboda haka na taɓa yi wa wata yarinya ciki har ta haihu,yanzu haka yaron yana gidan marayu".


  ya faɗi hakan jajayen leɓensa na haɗewa waje ɗaya.


  wani irin razananniyar tsawa me martaba ya yi,gamida miƙewa tsaye tamkar zai yi amon wuta............soon➡️


FACCALA GRP


***

L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


MRS GREEN CE