Chapter 16
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*16*
*GUSAU.*
Dakyar Innani ta bari Sultana ta yi sati daya a gidan mahaifinta tare da yan'uwanta.
Dafe ta yi ta kasa ta tsare yarinya taje domin ganawa da mahaifinta sannan ta samu zama da yan'uwanta, Ammh innani ba ta bari ba, ta na tare da Sultana kafa kafa kamar wacce za'a yi ma wani abun cutarwa.
Daga matan har shi kan shi Shitun ba su da mafita sun fi kowa sanin Halin Innani don ta fito ta tara su ta tsine musu to abu ba ne da zai zama mai wahala awajenta ba.
Hakanan suka rika Hakuri da ita ammh abu kad'an sai ta yi Allah ya isa akan Bakincikinsa da na matansa ya kashe mata Hauwa kulu akwai Hisabi Tsakaninsu Ranar gobe kiyama.
Sannan ta hana Shitu ya gana da yarsa da ya saka a ka kirata zai ga Innani tare da ita kafa kafa. Sai masifa ta ke yi ta na fad'in uban me zai kuma gayamata? Ba ta son iskanci da neman mgana da munafunci.
Dole Shitu ya kama kansa ya na ji ya na gani Sultana ta koma batare da mgana ta tsakanin Uba da yarsa ta shiga Tsakaninsu ba.
Sannan ranar da zasu koma Gusai Abba ya Turo Direba ya Dauke su Mallam Shitu iya karfinsa ya yi ma Innani da Sultana Hidima ammh sai Innani ta rika fad'in" Dama baka wahalar da kanka ba Shitu. komai da ka sani Sulaimanu na yi ma yarinyar nan babu abunda ta nema ta rasa, Sulaimanu da ka ke gani kudi garesa shiyasa ba mu rasa komai ba."
Ammh ta na jin kannen Sultana na fad'in zasu zo suyi mata Hutu wani Lokacin in suka samu Hutun makaranta karaf Innani ko tace"A'a ku yi zaman ku, wannan ai dora ma mai kokari wahala ne. wato kun ji nace Sulaimanu na da kudi shine za'a zo kwada'yi ko? To shima ba shi da komai Rufin asirin Allah ne ina ma laifi an Dauke muku wani Laluran? Wannan yarinyar Sulsana ko bante ubanku bai taba siya mata ba Sulaimanu ne da Salamatu. Allah dai ya biya su da Aljannah"
Shitu da Matansa da suka amsa da Ameen Innani dai ta rika masifan kada su so zl sulaimanu ba shi da komai sai Rufin asirin Allah.
Ammh tace su bari Bad'i in an tsaida lokacin bikin Magajin gida da Sulsana sai su zo.
Ba wanda yasan da labarin yanzu za'ayi auran Sadiq da Sultana ammh zuwan Innani Shinkafi labari ya bazu a kunnen kowa.
Har gidan su Baba Sammani da ta je duk haka ta rika ce musu bikin Magajin gida da Sulsana bad'i in sha Allahu. Shitu ma daki ta saka shi ta na fad'a mai cewa gwara ya fara Tanadi tun yanzu Sulaimanu dai ya yi masa na Allah ya yi masa na Annabi. In kuma ba na Shed'an ya ke jira ba sai ya nemi kudin aurar da yarsa Ina za su iya? Tunda shi Ubanta ya na raye? Daman ya mutu ne sai su Dauki na Musulunci su yi."
Shitu dai mamaki ya kamasa ya san da mganar auran Abubakar da Sultana ammh bai san da mganar nan kusa ba. Suna yawan mgana da Abubakar yaro ne mai hankali natsuwa da sanin yakamata wanda ko Alhaji Sulaiman ba su cika mgana da shi kamar yadda suke yawan mgana da Sadiq ba.
Ya na da tabbacin Innani ta zauna ta Tsara mganarta. Shiyasa a lokacin ya kalli Innani ya na fad'in"Ammah Innani Alhaji Ya fad'amin sai Sultana ta gama makaranta za'ayi bikin Lokacin shima Abubakar din ya gama karatunsa har ya kama aiki."
Ai sai Innani ta Zabga masa Dakuwa kafin tace"Allah ya tsine ma karatun albarka. Ka ji min ja'iran ci da lalacewa irin ta Shitu? A na mganar sunnar ma'aiki ka na mganar karatun Bokon tusa da tsiya? Maza ka yi istigifari domin ka yi sabo wajen Ubangiji."
Shitu dai ya ga abun mamaki ta wani bangaren kuma bai yi mamaki ba Tun kuluwa na raye sun sha zuwa Innani ta saka su a gaba ta yi masa wankan Tsarki. Wani lokacin tun Safe ta ke musu Dirar mikiya ka yi mgana ta tattara Tsinuwan bakinta a kanka shiyasa da yasan halinta sai yaci mganin zama da ita. Haka sauran matan masa ma tunda ba yau suka san Innani ba.
Haka suna mota da zasu koma Innani sai faman ciye ciye ta ke yi. ta na cewa su Hassu ba su da kirki sai ga shi ita ba ta kai musu komai ba ammh duk abunda suka bata sai da ta amsa. Aya ko ta yi tiya uku Wacce Innani ta zo da shi. Tsohuwar nan yar bala'i ce ba ta da hakora ammh sai Uban kwad'ayi da son abun duniya. Innani fa har goriba da rake ta ke sha, Wuka ta ke samu ta yi ta kankarewa ta na afawa a baki da hakoranta na Roba ta ke Taunawa.
Yanzu ma Aya ta ke ci sai faman mayau mayau ta ke da baki Direba ya fara Gudu Innani ta fara salati ta na Ihun ya rage gudu. Kuma ba fa gudu ya ke yi ba. Innani ta rika masifa har ta na kukan sai ta gayama Sulaimanu zai kashe masa uwa.
Sai Direba ya juyo ya na fad'in"Innani ba fa gudu na ke yi ba. a tamanin fa na ke tafiya."
Innani ta dake ta karfi tace"Allah ya Tsine ma maka kai da tamanin din. ni zaka raina ma wayau? In ni ba tsohuwar ka bace ka raina ni ai ka Daraja Furfuran tsohon ka ko?
Ya na jin haka bai kara mgana ba Sultana da ke ta kuka tun tahowarsa ta kallah cikin kufuluwa tace"Ke kuma kukan Uban me ki ke yi?
Sultana ta kalli Innani cikin Takaicinta kafin tace a hankali"Sati uku Fa Umma ta ce zan yi Innani.."
Innani sai ta saki baki ta na kallonta cikin mamaki kafin ta Dungure mata kai lokaci daya ta na fadin"Ta fi chan mara wayau ni gata na yi miki baki sani ba. Shitu da ki ke gani mugun bawa ne, da matan nan nasa ina barin ki cikin su sai kuma abunda Allah ya yi." Sai ta fara kuka ta na fad'in ke kad'ai kuluwa ta mutu ta barmin ta ina zan bari a nakasa min ke."
Bakinciki suka Hana Sultana mgana.
Ko da ta ke da kananun Shekaru ta san Ubanta ta kuma san yan'uwanta kuma ta na son su da kaunar su ba tun yau ba tasan Innani ba ta kaunar Abbanta ta sha zaginsa a gabanta tun bata damuwa har ta kai ga yanzu abun na yi mata ciwo.
Har suka iso Gusai Innani sai mugun Mgana ta ke fad'i akan Shitu har da tsohon Labarin aura auren da ya kara Saboda Kuluwa bata Haihu ba. Sultana kunnenta ta toshe ba ta son ji.
Saboda in dai Hadda ce ta rika gama haddace wad'anan Labaran.
Ko su kan su Umma sun sha mamakin ganin dawowarsu Sati d'aya kacal.
Da Umma ta yi mgana Innani ta harzuka tace"To uban me zamu tsaya yi!? Ina laifi ma an yi zumunci."
Daganan ta kama bakinta Mama ko tak bata ce ba Tunda taga yar gaban goshi Umma ta samu rabonta ta tabbata ta yi mgana sai Innani ta Taso mata.
Da Abba ya dawo bai ko yi mgana ba. Shi fa Ra'ayin Innani ne na sa Ra'ayin Magajin gida ne kawai cewarsa da Ra'ayinsa ke kan na Innani.
Innani bata yi mganar bikin Magajin gida da Sultana da ta gama bazawa a Shinkafi ba. Ta bari ne sai ta samu zama da Sulaimanu kawai ta gayamasa bad'i ta ke son ayi auran nan ta matsu ta ga ya'yan Magajin gida hakanan
Umma ta fara ji tunda Matar Baba Sammani Madiha ta kirata ta ke tambayan ya su Innani su ka koma gida? Daganan kuma sai ta ke tambayan Umma ashe biki kuma ya zo.
Cikin mamaki Umma tace bikin wa? Madiha tace na Magajin gida da Sultana mana, nan ta kwashe mganar Innani ta fad'aa mata Umma tace to bata san da mganar ba ammh za ta yi ma Abba mgana in ma da bikin za su fad'a musu.
To shima Abba Shitu ya kirasa ya masa zencen yace masa sai ya koma gida sun yi mgana da Innani Tukunna.
Sai a kayi sa'a Umma ke da Turaka ranar sai ta samu lokacin Tambayansa ko sun yi mgana da Innani? Abba yace a'a. Me ya faru? Sai da ta gayamasa ne shima yace sun yi mgana da Shitu.
Umma ta yi shuru kafin tace"Abban Siyama ka na ganin in muka ce Auran nan ya taso ba mu yi gaggawa ba? Sannan ba mu ji Ra'ayin Auta akan mganar ba."
Abba yace"Kada ki damu. Abunda Innani ta ke so shi za'ayi Salamatu. Innani ta tsufa a kwai rikicin Tsufa tare da ita gwara na samu na Rabu lafiya da ita."
Umma ta jinjina kai kafin tace"Duk na san da wannan. Ammh ta ya ya za su yi aure Sultana karamar yarinya ce. sannan Auta bautar kasa ya ke yanzu bai ko kama aikinsa a hannu ba. Sannan bamu san Wani Tsari ya ke da shi nan gaba ba. ni na dauka sai ta gama makaranta shima kafin lokaci ya san in da ya kama Abban Siyama."
Abba ya yi mirmishi kafin yace"Nima haka na so da farko. ammh ya zan yi da Innani salamatu?
Umma sai ta yi shuru ammh tasan in su ba su isa ba. Wanda ya isan zai ji kuma zai dakatar da ita, Shiyasa ta bar mganar.
Washegari da Safe gabadayansu a Shashen Innani suka karya daman Haka suke yi ranar aikin Umma. Salima ce kad'ai ke zuwa makaranta ita Direba ya dauka Sultana kuma da Siyama SS1 zasu shiga Tukunnah.
Bayan sun gama Sultana da Siyama suka kwashe komai suka fita suka bar iyayen na su su zanta.
Innani tun safiyar Allah sai Bare naman kaza take sala sala ta na ci Kai Tsohuwar nan akwai rikici a lamarinta.
Gabadaya a gabanta suka Durkushe Umma da Abba sai Mama achan gefe. Abba ne ya fara kora mata jawabin kiran Shitu Innani ta saki naman kazan hannunta ta na salati har da tafa Hannu ga gilashinta da ya kusa cika mata Fuska ta na fadin"Na shige su ni Dije? Ashe Shitu Annamimi ne ban sani ba? ni zai yi ma makirci da Tuggu?
Umma tace"Subhanallah Innani ba Makirci ba ne ya kira ne yaji tabbaci."
Innani tace"Tabbacin Uban me? Zan masa karya ne shi Sulaimanun ina ce ba ni ce uwarsa ba?
Umma tace"ke ce Innani har mu ma ke ce mahaifiyar mu ba mu da kamar ki."
Sai Innani ta ji sanyi ta Sassauta Murya ta na fad'in"To shi ne shi ya ke Tunanin na yi masa karya ko? To ba karya ba ne da gaske ne Bad'i na ke son a yi auran magajin gida da Sultana."
Falon na Innani ya Dauki Shuru Umma ta kalli Abba ta na masa inkiyar ya yi mgana.
Sai ya muskuta ya na fad'in"Innani..Dama.."
Innani ta Dakatar da shi da Fad'in"Sulaimanu nace bad'i uwar haka naga Yarinyar nan Sulsana a dakin magajin gida ba na son wata mgana."
Da Sauri yace"Shikenan Innani yadda kika ce haka za'a yi."
Umma ta kallesa shi kuma sai ya kasa kallonta. Mama ta matsonta mata mgana a Hankali" Umman su ki yi mgana mana."
Karaf ko Innani ta gani ta balla mata Harara ta na fadin"wata gulmar kuma ki ke gayamata? Kin ga Suwaiba ki Fita idona kafin na ci miki Mutumci."
Da Sauri Mama tace"A'a Innani ina ce mata ne ta tambayeki wani wata ne za'a saka na bikin?
Innani ta kura mata ido kafin ta tabe baki tace"ke dai kika sani."
Daga haka ta cigaba da zare sala salan kazanta ta na tura a baki ta na ci.
Umma taga gwara ta yi mgana kafin komai ya zo ya kwabe.
Sai ta gyara zama ta na fadin"Innani.."
A Fusace tace"Mi ye wai ku ke ta kiran Sunana.?
Umma tace"Daman naga kin sauya ra'ayi ne. ni dai nasan a baya mun gama sai Sultana ta gama makaranta lokacin ta kai shekara sha takwas shima Auta ya gama bautar kasarsa har kila ma ya fara aiki kafin mganan auran na su ya taso."
Innani ta rika ballama Umma Harara ta na tabe baki kafin tace"Suwaiba ce ta kitsa miki ki ce min haka ko Salamatu?
Mama ta zaro ido ta na kallon Umma ita kuma da Sauri tace"Wlh a'a. innani."
Innani kamar bazatayi mgana ba Abba ta kallah kafin tace"Baka gayama matanka Umarnina na gaba da Umarnin kowa ba ne?
Da Sauri yace"Haba sun sani Innani. Su san Umarnin ki shine nawa Umarnin."
Kai ta gyad'a kafin tace"To ashe sun sani ke salamatu ban san me ya shiga kanki ba ki ke biyema Suwaiba da Munafuncinta ba, Ki yi ma murna magajin gida zai yi aure ko kema zaki ga jokokin ki."
Umma tace"Innani jikoki nawa garemu a gidan nan?
Kai Tsaye Innani tace"Ban gan su baa"
Mama ta yi karaf tace"Innani ba ki gan su ba? Kaf ya'yaan mu duk sun haiyyafa. Suma ai jokokin ki ne.".
Innani ta Daka mata tsawa ta na fadin"Ke ne zaki wani gayamin ya'yan ku sun haiyayyafa ce miki na yi ban san sun haihun ba ne? Ba na son tsirfa da Tsugudidi Suwaiba ba na so na gaya miki.
Sai Mama ta koma gefe ta na fad'in"Allah ya baki hakuri Innani."
A fusace tace"Ameen in da gaske kike yi."
Sai falon ya Dauki Shuru Umma na Tsoron sake mgana a taso mata Abba kuma na zaune kanzil bai kara cewa ba.
Ganin Umma ta yi shuru yasa Innani ta kalleta ta na saussauta Murya ta ce"Kwantar da Hankalin ki salamatu. Nasan sauran ya'yan ku sun haihu ammh su din ya'yan su ba jikokin sulaimamu ba ne halas malak . Duk tsiya suna da wani gidan kakanin na su magajin gida fa? Har abada ya'yan su shi da Sulsana ba su da kamar gidan nan. Duk duniya mu ne na su ba su kuma da kamar mu kuma jokokin ya'ya mata na gidan wasu ne jikan D'a Namiji shi ne Jika Salamatu."
Har ta gama maganata ba wanda ya yi ko tari Abba ne yace"Gaskiya ne Innani.."
Innani ta rausayar da kai kafin tace"Ku tashi ku je na gama mganata bad'i za'ayi auran magajin gida da Sulsana."
Abba ya mike ya na fadin"Allah ya kara girma Innani zan fita."
Kai tsaye tace"Allah ya tsare ka. Allah ya kiyaye min kai. Ya rabaka da Sharrin makiya da Mahassada ya Tsare maka dukiyarka"
Abba na ta amsawa da Ameen.
Ficewa ya yi ya na ce ma su Umma ya fita suka rakasa da Allah ya Tsare.
Su dai suna gaban INNANI sun kasa tashi.
Innani ta gama cin Namanta ta na so ta shiga ciki ta huta ta kalli su Umma ta na fadin"Wai lafiya ku ka sakani a gaba haka? ni ku tafi ku ba ni waje zan Huta ne"
Umma ta marairace kafin tace"Innani Auta bai gama bautar kasa ba. Sultana maka.."
Innani ta katse ta da fad"in"Allah ya tsine ma karatu da bautar kasar. nace Allah ya tsine musu tunda su zasu hana A cika sunar ma'aiki Salamatu."
Umma sai ta yi shuru Mama ko Dariya ta ke ta dannewa sai da Innani tace"Ba Magajin gida ba hatta jikokinsu Sulaimanu na da arzikin da zai yi musu komai a cikin gidan nan."
Dariyan da Mama ke dannewa ta Fito fili Innani ta tsaya ta na kallonta cikin mamaki da takaici.
Da Sauri Mama ta danne bakinta na zare ido.
Innani ta yi kafyci kafin tace"Ki yi dariya mana Tunda kin raina ni baki san Darajan Furfura ba. In wannan gajeran matar ne mai katon hanci zaki yi mata Dariya in ta na mgana? Nace zaki yi mata Dariya in ta na mgana Suwaiba?
Mama sai ta dawo cikin natsuwarta jin Innani ta yi kwantancen Uwarta.
Da sauri tace"Yi hakuri Innani ba da gangan ba ne."
Innani tace"Da hakurin ya mutu sadakan nawa kika ba ni?
Nace sadakan nawa kika bani? Iskancin banza da wofi nasan ai maganinki Allah yasa naga masu faska faskan kafafun dangin ki sun kara zuwa gida d'ana wato ana zuwa aci arziki gida babu ko? to wlh Karnukan nan na Sulaimanu ma su kama da Mutane zan saka mallam Saju ya sakar musu duk su farraka yan banza."
Innani ta fad'a ta na kumfar baki. Tasan karonta da karnukan ranar da likita ya zo duba su aka fito da su Innani ta gansu kamar wasu mutane Saboda girma sai da Suma.
Da ta farfad'o ko Har sulaimanu sai da ya sha Allah ya isa mallam saju da likita kuwa har da tsine musu sai da aka yi ranar.
Jawo sandarta ta yi lokaci d'aya tana mike ta ke fadin"Sai ku bar min falo. Tunda ba Sulaimanu ya gyaramin shi ba. nima mai kudi ce iyayena sun bar min gado Ehe."
Haka suka mike sumu sumu suka fice bayan Umma ta ce"a huta lafiya Innani."
Innani ta amsa a Dakile sai da suka Fice tace a fili"Salamatu ba wayau. Duk ba ta Fahimci bakincikin Suwaiba."
Daga haka ta tabe baki kafin tace"Sai dai ko bakinciki ya kasheta auren magajin gida da Sulsana ba fashi."
Da haka ta dogara sandarta ta shige ciki ta nemi gado ta kwanta da gilashinta a ido tunda tace in ta ijiye bacewa ya ke yi.
Wayarta ma ta gama Tsine tsine tace Allah ya tsine ma barawo da uwar barawo. Ahalin wayar gefen gado ta fad'a shikenan da ta nema bata gani ba tace an sace.
Wasa wasa karamar mgana ta zama Babba Domin washegari Innani Sashen Umma ta yini ta rika sata ta na kiran mata su Surayya da kanta ta ke musu mgana ta na fad'in su fara shiri auran Kaninsu da kanwarsu bad'i kowacce haka taji mganar Daga sama ba sanarwa.
Sai bayan Innani ta koma Shashenta suke ta kara kiranta suna Tambayan ba'asi ta na kora musu jawabi.
Surayya tace"Umma gaskiya abun bai yi ba me sultana ta sani na aure yanzu? Sadiq ma nasan ba shi da Ra'ayin aure yanzu."
Umma tace"To ya muka iya. Kun san dai Halin kakar ku."
Surayya tace"Umma kin gayama Sadiq?
Umma tace"A'a na kasa gayamasa ko yau mun yi waya da Safe. Tsoro na ke ji Innani ko Abban ku susan ni na Fad'a masa."
Surayya tace"Ummi ni zan kirasa na fad'a masa gwara ya dakatar da abun kafin ya yi nisa."
Umma tace"To Allah yasa kada sunan ki ya fito."
Surraya tace"ban damu ba Umma. Bikin Kaninmu so mu ke a yi shi one in Gusai in sha Allahu."
Surayya ita ta kira Sadiq ta gayamasa Halin da ake ciki.
Bai yi wani mamaki ba sai dai ya tausayama Innani da ta ke masa shisshigi a rayuwarsa.
Mgana ta waya bazai yuyu ba yasa ranar asabar ya ce ma Tahir zai je Gusai Tafiyan Ujila ya taso masa.
Tahir ya tambayesa kwana nawa zai yi? Yace daya gobe lahadi zai dawo.
Tahir ya yi masa fatan dawowa lafiya.
Domin kwanaki nan fad'a su ke yi akan mutanen da Sadiq yaga ya daukesu da Muhimmanci Fiye da Sauran mutanen da yasan ya na taimako.
In yau bai je gidan ba to gobe sai yaje bayan kullum ya na hanyar zuwa siyan Danwake da ya ke da tabbacin in ma wani tsafin ne ta nan aka saka masa.
Tunda har ka taimake su kuma matar nan ta samu lafiya ka rabu da su mana ammh ya lura Sadiq na so ya saka kanshi a abunda zai zo ya na danasani daga baya.
Shi fa tsoronsa kada Sadiq ya fara son zabiyar yarinyar nan. Tunda yaji Sadiaq din na fadin"kamar kanwarsa ya ke ganinta sannan suna ba shi Tausayi."
Tunda suna son su jaawosa a jiki ne komai ma zasu iya yi. Haka kurum ya ke jin baya son wannan alaqar ta Sadiq da Sabbin mutanen da garin Tausayinsa ya jajibo ma kansa.
Har Sadiq ya tafi shi kad'ai ya rika Tunanin hanyar da zai raba wannan Alaqar da ta fara kulluwa.
Ammh kuma ya kasa samun mafita in dai ta mgana ce har ya yi ya gaji Sadiq bai sauraresa ba.
******
Ba wanda yasan da zuwan magajin gida sai da aka ganshi kawai.
Kuma zuwan daman na Innani ne wanka kawai ya yi ya sauya kaya ko Shashen Umma bai shiga ba ya yi ma Falon Innani Tsinke da ta Rud'e da jin zuwansa
Yana shigowa ta fara
"Maraba maraba da Magajin gida."
Fuskar nan ba Fara'a Siyama da Sultana ne tare da Innani lokacin ma mganar auran ta ke karanta musu. sannan kuma wai ta na koyama Sultana Dubarun zama da miji Siyama na gefe ta na shan Dariya.
Fuskarsa ba Fara'a suna gaishe shi bai amsa ba yace"Ku ba ni waje zan yi mgana da Kakar ku."
Jin sunan da ya kira Innani yasa suka san ba lafiya da sauri suka fice.
Suna Fita Siyama ta kalli Sultana ta na Fadin"Sultana ko Ya Sadiq zai ce ba za'ayi auran ku yanzu ba ne?
Sultana a sanyaye ta ce"Bansani ba. Ammh da hakan ta faru da zan so haka."
Siyama tace"Me yasa kika ce haka?
Kai Tsaye Sultana tace"Na fi so sai na gama makaranta Siyama. na kara wayau tukunna"
Siyama ta jinjina kai kafin tace"Eh kuma fa hakane gwara da wayan ka an fi sanin Darajan ka."
Suna tafe suna Hira har shashen Umma taga gansu ne ta ce suka bar Innani ita kadai Siyama tace suna mgaana da Ya Sadiq ne.
Umma ta yi mirmishi a ranta ta na jin Dadi tasan Dole kanwar naki Innani ta bar mganan auren nan.
Ilai kuwa Sadiq achan Falon Innani Wuta ya bud'e mata.
Kamar bai taba saninta ba sai ta fara kuka ta na fadin"Ni daman in ga ya'yan ku ne kafin na mutu."
Sadiq yace"Duk ya'yan su big sis da ki ke da shi baki godema Allah ba.! In kuma nazo Allah bai bani haihuwan ba fa ya zaki yi.?
Da Sauri Innani tace"Allah ba amin ba. Da ikon Allah sai ka tara zuru'a"
Tsaki ya yi kafin yace"To tunda kinsan Allah me yasa kike yi ma Allah Shisshigi? Aure da mutuwa da Haihuwa al'amarinsa ne na kuma sha miki gargadin cewa in kina so ki Mutu cikin salama ki kiyayi shiga Hurumin Allah."
Innani tace"Na bari alqur'an bazan kara shiga ba."
Kai Tsaye yace"Kin shiga mana. Ina ruwan ki da mganar aurena. Ke zaki zauna da matar in kika aura min ita yanzu? Ko ce miki akayi na gama karatun kenan? Ina gama bautar kasata zan dora masters dina. Mganar aure kuma na Soketa sai ranar da na Shirya Innani."
Innani ta yi shuru bata yi mgana ba.
Ganin haka yasa ya taso daga in da yake zuwa gabanta ya zauna ya rike Hannayenta ya na fadin"Innani ki kwantar da Hankali in sha Allahu ke zaki rakani Dakin Sultana ranar angwancina."
Jin haka yasa Innani ta washe baki ta na fadin"Allah ya nuna min wannan ranar. Allah yasa ina raye ban mutu ba."
Hawayenta ya ke share mata da Hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"In sha Allahu bazaki mutu yanzu ba Innani sai kin Dauki ya'ata ko d'a na ni da Sultana."
Sai Innani ta Rumgumesa ta na fad'in"Idon makiya a tsiyaye a kan jikana. Yadda kace haka za'ayin magajin gida"
Shima Rumgumeta ya yi ya na fadin"Yauwa Kakata mai kyau."
Shikenan mgana ta mutu murus. Kwana daya ya yi washegari lahadi ya Dawo zariya.
Innani haka ta tara su Abba akaro na Biyu tace mganar aure bata sai magajin gida ya yi masta dinsa.
Haka yaran ma duk ta kirasu ta na fad'a musu sai magajin gida ya samu masta za'ayi auransa da Sulsana.
Kowa yaji sai ya Dara, Duk wanda yace aikin waye haka da Innani ta Sauya mgana."
Umma na dariya ta kan ce"Aikin waye kuwa ban da na magajin gida magajin kowa."
To in ba magajin gida ba, Waye ya isa ya sauya wannan mganar ai sai shi kad'ai ne wanda mganarsa ke saman ta Innani da ta Abba shi kan shi.
*****
Ya dawo a gajiye dalilin da yasa bai leka gidan su Hasiya ba kenan.
Sai washegari litini bayan ya dawo daga in da ya ke hidimar kasar sa. Ya na jin Amma a ransa in ya ganta Umma ya ke gani Hasiya da Habiba kuwa tamkar Siyama da Salima ya ke kallonsu. Ya kuma san zasu damu da rashin ganinsa tunda bai fad'a musu zai yi tafiya ba.
Sanin Tahir baya son ya ji zai je gidan nan sai ya fara maganganu yasa bai fad'a masa ga in da za shi ba, ce masa kawai ya yi zai je ya dawo
Takaici suka saka Tahir ya kasa mgana Sadiq ya fita ba Dadewa sai ga wani Mutum ya zo ya na masa sallama a kofar dakinsa.
Ya ma zata abokan zaman su ne Tunda in suna bukatar wani abu suna yi musu mgana. Tun ballatana sun san Halin Sadiq abun sa na mutane ne.
Ya na fitowa sai ya ga bakuwar Fuska da bai taba gani ba mutumin zai kai shekara arba'in dattijon matashi ne.
Hannu ya basa suka yi musabaha, cikin mamaki Tahir yace"Lafiya? Kamar ban gane ka ba?
Mirmishi ya yi masa kafin yace"Baka sanni ba shiyasa baka gane ni ba.?
Tahir yace"Oh to ko wani ka ke nema?
Da sauri yace"Ai naga wanda na ke nema dazu ya fita ko?
Tahir yace"Sadiq?
Cikin alamun tambaya kai ya gyad'a masa kafin yace"Abubakar Sadiq sunansa kenan shima."
Tahir duk bai gane ba yasa ya kankance idanuwana kafin yace"mallam wai lafiya?
Kai tsaye yace"Taimako ne yasa na zo gareka. na fahimci kai ne abokinsa da ku ke zama tare. To in dai har kana son abokin ka ya cigaba da Rayuwa ya kamata ka dakatar da shi da Rab'ar in da yarinyar nan ta ke."
Tahir ya saki hancinsa ya na shakan Iska kafin yace"Wata yarinya kenan.?
Kai Tsaye yace"Hasiya mai Danwake wata Fara farinta mai haske haka Siririya."
Tahir yace"Oh na ganeta lafiya? Da wani abu ne?
Mutumin yace"Sosai ko da matsala dan Samari ganin ko ba yan garin nan ba ne kada a cutar da ku ba ku sani ba. Kada ka bari abokin ka ya auri wannan yarinya ta na da bakin jini da bakin kashi mai kashe rai da asaran Dukiya."
Tahir ya ware ido kafin yace"Bawan Allah ban ga ne ba? Wa ya fad'a maka Sadiq auran wannan yarinyar zai yi? Taimakon su kawai ya yi shikenan ba wata mgana."
Shima kai tsayen yace"Duk da haka dai ya yi nesa da ita gudun matsala abu ne ya faru ba sau d'aya ba sau biyu ba kowa a anguwan nan yasan da labarinta gwara ka ba shi shawaran ya kiyaye domin tsira da Lafiyarsa."
Tahir ya gaji da jin mganar da ya kasa ganewa kai tsaye yace"Mallam ka tafi kai tsaye kan mganar ka. Ba na son wannan zagaye zagayen naka."
Jin haka yasa ya shiga warware ma Tahir komai da ya Dangancin Hasiya.
Har da mutuwar babanta ma itace cutar mahaifinta karayan arzikin su. Gujen su da Ahalin babansu suka yi. Auran ta da Abubakar da abunda ya faru da kuma na Salisu ya karishe da Fadin"yarinyar ba'a san mayya ba ce ko wani abu. Ammh tabbas duk wanda ya Rabe'ta akwai asaran rai ko Dukiya in ba'a Mutu ba za'a wahala sannan a rasa komai irin su zama da su bala'i ne da Masifa."
Har Mutumin nan ya tafi Tahir na Tsaye rike da kugu baki bude mamaki ya Rufe shi.
Lalle biri ya yi kama da Mutum yarinyar nan shiyasa farinta ya yi masa wani iri ashe ashe bakar daga ce Gobara daga kogi mganinta sai Allah.
Bari Sadiq ya dawo in yaji haka don Dolensa sai rabu da huld'ar da duk abunda ya shafi wannan yarinyar.
*Janafty*