Part 2
_*🌻ABBA NE 🌻*_
Hakkin Mallakar
_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_
_JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION_
_Littafin na kud'i ne only N 300, my WhatsApp number 👉🏻+966577675904 _
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣2️⃣
Ta damki Hannun Khalil ta rike gam sai juya kanta take alamar haihuwa ce zatayi" Cikin Azama Abdul yace Khalil maza kayi lungu da ita haihuwa zatayi ka taimake ta. Khalil da duk ta gama bashi tausayi ya sunkuce ta ya ringa kutsawa cikin dajin dan ya samu inda zai b'oye ta" Gindin wata bishiya ya samu mai inuwa kuma inba lura kayi ba baza ka san akwai mutum a wajan ba, aje ta yayi yana huci ya kama hannayen ta yace Ki daure kinji baiwar Allah zan kaiki gidan ki .D'ago da rinannun idanunta tayi ta zuba su a kanshi tana girgiza mishi kai, cikin sarkewar murya tace" A'a kada ka mayar dani dan ba nan garin muke ba, Mijina sun bishi yayi cikin daji bansan a wani hali yake ba" Zata sake magana taji wani azababben ciwo wanda ya lumka na baya, Sake damkar hannun Khalil tayi tana salati Ganin haka yasa Khalil cire rawanin shi daya naďa a kanshi ya lulluba mata a jikin ta.. idanunshi ya rufe yana jin zuciyarshi na mugun bugawa da sauri sauri" Kamar daga sama yaji kukan Jariri ta sauri ya bud'e idanu yaga Jaririya a k'asa tana tsala kuka. Rasa yanda zaiyi da Babyn yayi shi bai san yadda ake yanke cibiya ba gashi ba wani a kusan shi. Matar ce ta sauke wani wahalallan numfashi ta bud'e idanu duk da ciwon da take ji ta kalli Khalil tace" Kana da reza ko wuka mai kaifi. Cikin rawar murya Khalil yace" Eh akwai reza yasa hannu a aljihunshi ya fito da rezar sabuwa dal ya mika mata... Amsa tayi ta mike daga durkushen da take ta dauki wannan mayafin na Khalil ta aje a gefe" Yankewa Jaririyar cibiya tayi hawaye na zirya kan kuncinta. Daukan Jaririyar tayi ta lullubeta da mayafin ta d'ago kai ta kalli Khalil wanda shima ita yake kallo. Cikin raunatacciyar murya tace Soja ga Y'ata na baka ita halak malak, ka rike min bisa amana idan ta girma kace mata Maman ta na matuk'ar k'aunarta. Na baka ita kyauta har abada ta zama Yarka daga yanzu ka amshe ta mana" Ta fad'a tana murmishi mai had'e da hawaye.. hannun Khalil na rawa ya amshi Jaririyar ya rungume ta tsam a jikin shi, nan da nan yaji k'aunar Jaririyar na ratsashi, cikin damuwa ya kalli Matar yace" Anty na miki Alk'awarin zan rik'e Yarinyar nan da amana, amma ya sunan ki? Kanta k'asa tace" Ni Sunana Zulaihat Don girman Allah ka tafi ni nasan kwanana ya k'are anan zan mutu, kuje kar su kashe min Jaririya ta.. Khalil yace No ki tashi muje duk da ina jin takun tafiyar su amma baza su ganmu ba. A'a kada kace haka Soja karka damu dani kai dai ka tseratar min da Yarinya ta hakan kad'ai zai sanyani farin ciki. Khalil zaiyi magana yaji Harbin bindiga a matuk'ar razane ya juya yaga an same ta a gefen ciki" Dafe wajan tayi tace" Don k'aunar ka da Annabin rahama ka gudu karsu kashe ka, amshi wannan idan ka zauna ka duba" Ta fad'a tana mika mishi handbag d'in ta fara sol. Amsa Khalil yayi tace" Kaje nace komai na rayuwata na ciki kacewa Y'ata ina son... Bata k'arasa ba ta zube anan" A guje Khalil ya nufi wani cikin ciyayi yayi saurin warware mayafin ya saka Jaririyar ya k'ulla a jikinshi da kyau. Sosai yake tausayin Jaririyar da take baccin wahala ya k'ara kutsa kanshi wani waje.. Abdul na cen da sauran Abokan aikin su suna ta masayar wuta da Y'an Ta'adda" Ganin Khalil bai dawo ba hankalinshi yayi matuk'ar tashi, da baya ya soma tafiya sai kuma yajiya na nufi inda Khalil yayi. Waro idanu yayi ganin jini a k'asar bishiyar amma ba kowa a wajan. Sake kutsawa yayi yana wage-waige kwaran baya sukayi da Khalil" A hanzarce kowa ya juyo ya d'ana kunamar bindigarshi sai kuma sukaga sune dai.. sauke Ajiyar zuciya sukayi Abdul yace Ina Matar nan take? Khalil na huci yace" Ta mutu kaga abinda ta haifa zan maka bayanin komai muje kawai. Cikin tashin hankali Abdul yake kallon Jaririyar dake gaban k'irjin Khalil daya Goya ta ta gaba. Juyawa sukayi suka tunkari inda suke jin motsin su. Cikin azama Khalil ya hango wani ya juya musu baya da sanda Abdul ya damkeshi ya bud'e bakinshi ya sakar mishi alburisai.. sakinshi yayi nan Y'an Ta'addan suka ankare da su aka shiga musayar wuta baji ba gani" Sosai suke yaki inda Su Khalil sukaci sa'ar kashe su. Numfashi suke saukewa Khalil zaiyi magana yaji saukar harbi a kafad'arshi " Rintse idanu yayi cikin azama irin na Sojoji ya juyo ya harbe wanda ya harbeshi nan take ya mutu. Abdul ya tafi a guje cen ya hango Ogan nasu ya harbeshi a hannu da k'afa, nan da nan ya ringa kurma ihu mutanen dake gabanshi suka ringa kallon shi. Cikin tafasar zuciya Abdul ya wanka mishi mari lafiyayye ya damki wuyashi ya shiga dukanshi baji ba gani. Khalil a matuk'ar galabaice yake amma saboda karfi hali irin na Soja ya daure ya iso wajan su Abdul" bakinshi na rawa yace" Maza ku tashi muje kai kuma Abdul tafo mana da wannan dan iskan" Ya fad'a yana yin bol dashi.. da gudu suka ringa bin Khalil har bakin mota shima Abdul ya k'araso ya jefa shugaban Y'an Ta'addar nan a mota yasa mishi ankwa hannu da k'afa duk da a sume yake... Babu inda suka nufa sai Babbar Asibitin cikin Garin dama kafin suzo sun sanar zuwansu. Suna isowa aka ringa daukan wanda suka jikata da waďanda sukayi rauni aka shiga da su ciki dan basu taimakon gaggawa.. Khalil ya shigo ciki da k'yar yana rintse idanunshi shi ya sauke Jaririyar ya kwantar a wani gado zai yi magana yayi baya luuu ya zume anan sumamme. Abdul ya iso a guje ya ringa jijjiga shi yana fad'in" D'an Uwana kada kamin haka ka tashi ga amanar da aka baka. Wani Likita ne ya iso yasa aka daura Khalil akan gadon dake kusan inda ya aje Jaririyar.. tuni suka shiga cire mishi bulat din da yake kafad'arshi , bayan sun gama suka sanya mishi magani suka naďa mishi bandeji a wajan" allura biyu suka mishi san nan suka sanya mishi ruwa... Abdul ya koma gefe ya zauna ranshi na tafasa duk da ya kashe wanda yayiwa Khalil wannan Harbin amma ranshi bai dena suya ba. Wayarshi ya ciro jin tana ringing, ganin daga Office d'in su ne yasa shi D'agawa ya k'ara a kunne amma baice komai ba. D'aga cen b'angaren Ogansu yace" Abdul Khalil baya kusa ne? ina kiran wayar shi bata shiga, gamu nan a Asibitin da kuke ku fito. Iska Abdul ya fuszar mai tsananin zafi ya kalli Khalil dake kwance yana fitar numfashi yace" Ai shima Khalil d'in gashi nan a sume an harbeshi ne.. Cikin tashin hankali yace Subhanallahi ina ne dakin da kuke? Kwatance ya mishi san nan ya kashe kiran. Yana zaune ya dafe kanshi sai kuma ya dauki wayar ya kira Baba ya fad'a mishi halin da ake ciki" Cikin Azama yace gasu nan zuwa. Ogan Sojoji na shigowa a sauri ya isa bakin gadon da Khalil ke kwance, hannu yasa ya shafa fuskarshi yace" Jarumi na sannu Allah ya kare ka. Banko k'ofar akayi da k'arfi hakan yasa Khalil soma bud'e idanunshi. Mamy ce da Baba ta sauri ta isa ga Khalil tana kuka tace" Ka gani ko Yarona dama sai da nace maka bana son aikin nan amma ka nace gashi yanzu ana son kashe ka a banza. Dafata Baba yayi yace" Haba ki nutsu mana don Allah" Bud'e idanunshi ya ringayi tin yana ganin dushi-dushi har ya bud'e idanun shi tar akan fuskar Ogan nasu. Hamdala sukayi kowa nata mishi sannu. Zabura yayi ya sauko daga kan gadon suka rike shi, Baba yace ina zaka je? Numfashi yaja yana jin kanshi na mugun Sara mishi kamar zai rabe gida biyu, yace" Amana ta zan dauka. Kallon shi Mamy tayi da mamaki tace Amanarka kuma Khalil ? Bai bata amsa ba ya isa d'ayan gadon ya dauki Jaririyar ya rungume ta yana lumshe idanu" Sake da baki suke kallonshi, Abdul ya isa ga Khalil yace Khalil ka bawa Mamy Jaririyar a gyara ta mana. Bud'e idanunshi yayi, sai kuma yace ni zan gyara ta da kaina wannan kyautata ce. Mamy da Baba da Shugaban Sojoji na kallon shi. Cen dai Mamy ta isa inda yake tsaye tace" Kawo ta mana Khalil a sanya mata tufafi. Ba dan yaso ba ya mika mata Jaririyar ta masa da sauri. Likitan daya shiga suka bawa Jaririyar Mamy tace A gyara ta" Khalil yace muje tare" Abdul yace kaga ka bari a gyara ta ba fa guduwa za'ayi da ita ba. Ko kala baice ba yabi bayan Nurse d'in data amshi Jaririyar. Koda aka mata wanka anan suka sanya mata wasu kaya masu kyau" Amsar ta yayi ya rungume ta ya mata kiran salla a kunne san nan ya raďa mata suna. Tashi yayi ya dawo wajan su Mamy basu tsaya ba suka wuce gida.....
Suna zuwa gida Mamy ta dauko ruwan zam-zam da dabino ta bata, har yanzu Jaririyar batayi kuka ba, su kansu abun ya basu mamaki. Mamy tace" Na tura Direba ya siyo mata madara da sauran abun anfani. Khalil ya sauke wata Nannauyar ajiyar zuciya yace" Nagode Mamy nawa ne kud'in? Harara ta mishi tace D'an Y'arka ce sai ka nuna sai kai zaka mata hudima" Murmishin gefen baki yayi yana shafa kwancacciyar sumar kanshi. Direba ne ya shiga da kaya a leda manya manya, gaishe da su yayi san nan ya aje kayan ya fita. Mik'awa Khalil Jaririyar tayi ta janyo kayan ta dauko kwankwanin madara babba da komai a ciki" D'akinta ta koma ta dawo da wani kofi dauke da ruwa mai ďumi da cikin. Madarar ta kad'a tace" Kawo ta a bata. Mik'a mata Jaririyar yayi ta masa ta shiga bata, kamar jira Jaririyar take ta shiga sha. Wani sanyi Khalil yaji ganin Jaririyar tashi na shan madarar. Gyara zama yayi ya basu labarin abinda ya faru" Kuka sosai Mamy keyi tana cewa" Allah sarki yanzu shikenan sun kashe mata Uwa? Shima Uban ba tabbas yana raye. Zuciyar Khalil na tafarfasa yace" Eh amma kuma Abdul yace bai ga gawarta a gindin bishiyar ba" Baba yace" Mugaye azzalumai Alhamdulillah tinda har an kamasu , kila ko dauke gawar sukayi su jefar waya sani. Khalil dai bai sake cewa komai ba" Mamy tace" Wani suna kasa mata? Khalil da ya jinginar da kanshi jikin kujera yace" Sunanta Zulaihat amma muke kiranta da Ashma. Murmishi Mamy tayi tace Sunan da nake so Ubangiji ya raya mana Ashma. Ameen suka ce Khalil ya d'ago idanunshi da sukayi jajur kamar an ďasa mishi jini yace" Ina neman wata alfarma a gareku. Baba yace muna jinka" Inason koda Ashma ta girma kada ku tab'a ce mata bani bane na haife ta, kunga Inna bata nan ta koma Nigeria da zama" Dama itace nake tunanin zata bani matsala ta fad'a mata cewa bani bane na haifeta. Dukkansu jinjina kai sukayi Mamy tace Insha Allah babu wanda zai fad'a mata cewa ba kai ka haifeta ba" Inna kuma dama tace wai ka samo mata kaga sai kayi aure ko saboda wannan Y'ar taka. Had'e rai yayi yace" Nifa ban tab'a yin budurwa ba amma saboda Ashma nan da wani lokaci zanyi. Dukkansu dad'i sukaji shi kuma ya amshe Ashma a hannun Mamy ya shige dakinshi da ita" Baba ya bishi da kallo hawaye na zubo mishi... Koda dare yayi Mamy tace Khalil ya kawo Ashma sai yace sam bazai iyaba
, ba yadda Mamy ta iya ta koma ta kawo mishi duk abinda zasu buk'ata ta koma .
Tin daga wannan rana Khalil ne ke kula da Ashma wanka wankie kayanta goyata a baya komai shi ke mata, wani lokacin ma dariya yake basu idan yana mata wasa yake ta magana shi kad'ai. Ashma tayi wayo sosai take gane Abban nata duk wanda ya dauketa indai ba Khalil ko Mamy bane to yanzu za tayi ta tsala kuka tana Abba! Abba, shi kuwa in yana gidan da sauri yake zuwa ya amshe ta su shige daki yayi tamata
Wasa suna ta dariya... samun Ashma a wannan lokacin ba k'aramin ragewa Khalil kewar Iyayenshi yayi ba, ita kad'ai yake sakewa yayi ta dariya da ita, amma inba ita ba babu wanda zaice yana ganin fara'ar shi Koda kuwa anyi abin dariya...
Da gudu ta nufo shi tana kuka, sanye take da kayan makaranta Y'ar k'aramar Jakarta na bayanta a goye" Fitowa yayi da sauri ya tareta suna had'ewa yayi sama ta ita tukun ya rungume ta yace" Ashma na waye ya tab'a min ke? Turo dan bakin ta tayi tace" Abba Malamin mu ne ya dakeni wai nayi rètar kuma har da ce min wai ni aljana ce" Kuma yace wai Abbana mai zuciyar mugaye kuma kasan me Abba wa... Bata k'arasa ba yayi saurin sauke ta ya kama hannun ta yace" Shi d'in ne duk ya fad'a miki haka? Itama tsuke baki tayi kamar yadda taga ya had'e rai, tace" Allah Abba haka yace. Ɗaukan ta yayi suka nufi ciki yana fad'in" ba dai ke ya zaga ba ya dauko ruwan dafa kanshi....
_*😂😂ni kuma ina ganin ran Soja ya b'aci na had'a kan takarduna na arce garin mu😂*_
Littafin na kud'i ne only N 300 ne duk mai son karantawa ga number na👉🏻 +966577675904
_*Taku har kullum Maman Nusaiba*_