GUGUWA BIYU

GUGUWA BIYU

by @109696625203084497219

*GUGUWA BIYU*



*Aysha D Fulani*



*5STARS EXPENSIVE COMPANY*



*BABI NA BIYU*


بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ






A daburce ta wai go zuciyarta na kakkarwa ganin Duna riƙe da bokiti ya sa tai baya da sauri don yanayin kallon da yake mata tsaf zai iya wanke mata fuska da ƴan yatsun shi, harara ya banka mata ya tara bakoti a bakin famfon ya ɗibi ruwa sai da ya cika bokiti tab sannan ya juyo ya kalleta yace "Matsamun daganan ƴar kwalta kawai haihuwar asara wacce aka rasa ina za'a zazzage kwanta sai akan kwalta.

Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata akan ƙuncinta, dafe saitin zuciyarta tai tanajin wani irin zugi a saitin zuciyar,matsawa tai gafe tana share kwallah kalamansa sai yawo suke a cikin kwakwalwata wani jiri-jiri taji yana ɗibarta tamkar zata zube a kasa.

Goge hawayene ta ke amma ji take kamar sake zubo da su ake yi, bakin famfom ta koma ta daura alwalah ta raƙuba gefen masallacin ta shimfiɗa dan kwalinta.

Sallah take amma hawaye ya ki ɗaina zubowa a idonta a sujadar karshe ta sunƙuya da kyau, tana fadin "Ya Ubangiji na san kai ne maji rokon bayaninsa hakika kaine ka so ka ganni cikin wannan halin, ban da inda zanje in guje ma ƙaddarata hakika kaine kaso ganina a cikin wannan halin, ya Ubangiji ka sani ban san wacece ni ban san daga ina tsatsona ya bullo, ban da uwa balle uba ban da wanda zan kallah ince shine ɗangin uwa ko uba, ya rahimu ka zama gatana ka haɗani da Uwata don in samu sauki daga abin da nake ji yana mun nauyi a cikin raina, Allah kar ka ɗauke idona ba tare da ka bayyana mun ahalina ba, Allah kana kallonsu yadda suke muzanta mu, suna tsine mana suna binmu da alƙaba'i iri-iri suna Allah wadai damu ɗan mun kasance akan titi Allah kai Allah

Allah kana sane da masu muzanta Ni masu kwashe mana albarka don sun ganmu kara zuɓe, Allah ina son inji ɗumin Uwata nima ina so nai mata kuka ta rarrashe ni, Allah ya Allah.........

Kuka ne ya ci karfinta don ɗole ta ɗago badan ta kamallah yiwa ubangi taliƙai magiya ba, sallame sallar tai ta goge hawayen wanda ta ke jin zuciyarta tai mata sanyi.

Addu'a tai sosai sannan ta tashi ta fito waje wurin mai gadin masallacin ta karasa ta gaidashi, cike da fara'a ya amsa yana tambayarta ina ta shiga yau sam bai ganta ba tun safe.

Nana Ali mai gadi shine dattijon tsonon da yake gadin babban masallacin juma'ar dake gefen kasuwa tsohone mai zuciyar musulunci, don Allah ya saka mai tausayi shi yasa duk yarinyar da yaga tana da natsuwa yake bata damar kwanciya cikin masallaci don ya tayata kare mutuncinta.

Dariya tai tace mai taje aikine yanzu ma abinci zata siyo.

A dawo lafiya yai mata ya cigaba da sabgogin gabanshi kudin dake maƙale a gefen zaninta ta ciro tana irgawa naira dubu goma ne, jujjuya kudin take zuciyarta na gargaɗinta akan kaddata taci ko biyar saboda tamkar sata tai musu, ɗayan barin na zuciyarta ne ya bata shawara ta dauki wani kaso a ciki kodan yunwar dake kwaƙular cikinta.

Miƙewa tai ta fara duba masu abinci amma shiru duk sun tashi wurin Mado mai ɗoya da kwai ta nufah ta na zuwa ta hango wata dankwaleliyar kaza a cikin gilashi miyonta ne ya soma guɗawa ji ka ke kut😂 tana haɗiyarsa, kallan Mado tai da sauri ta nuna kazar tana tambayar kudin.

Tsaki yaja ya furta "Dubu Uku kuma idan baki siya ba sai na naƙada miki dukan tsiya."

Zaƙulo kudin tai ta mika mai ya saki baki yana kallonta, girgiza kai ya yi ya saka mata a leda ya miƙa mata a zuciyarshi yana fadin anbi sahu Allah ya kyauta zaman bakin titi, wato kema kin fara bin maza har kina da kudin kaza.

Ruwa mai sanyi ta siyo ta koma bakin massalaci ta shifiɗa dankwalinta ta zauna ta buɗe kazar tai, tai mata cin Allah tsine uwar mai karya, sai da ta ci tai ket sannan ta kulle bakin ledar tai miƙa ta sake dauro alwalah ta ɗukufah gaban Ubangiji taliƙai tana mai magiya akan ya haska mata fitilar gabata wacce zata sadata da wani nata.

Tana idarwa ta kwanta zuciyarta cike da tunanin ta ya akai ƙatin samarin nan suna dauke ta a cikin anguwar nan amma babu wanda ya gansu, da mamakin abun ta kwana a ranta a garin Allah ya waye.

Koda ta tashi yau bata je Bara ba saboda tana da abin da zata siya abinci, wurin da Baba Halime ke sana'a kawia ta leƙa taga shiru yauma, abinci ta siya ta dawo gefen masallaci ta zauna yamma likis ta miƙe tana

Kalle-kalle take tana duban bakin masallacin, maza ta gani duk sun yayyaɓe bakin famfo karamin tsaki taja ta mike tana tafiya cikin natsuwa.

Kokarin tsallaka titi take taji an riƙo hannunta waiwayawa tai da sauri don ganin waye wannan, dariya ce ta subuce mata ganin Baba Halime ce, wace suke ma aikin wanke wanke a wurin sai da abinci ta.

"Ina wuni Baba Halime".

ta furta tana gyara tsayuwar ta.

Kallanta Baba Haleeme tai cike da tausayawa take fadin "Lafiya Qlau Alhmdulih ina zakije haka ki ke ƙoƙarin tsallaka titi".

"Wallahi Baba Sallah nakeson inyi kuma naga bakin masallaci maza sunyi yawa, shine zanje gidan Atine ko zan samu ruwa a chan".

"Ayya biyo ni muje gidana kin tuna kwanaki da nai miki magana nace miki zan samar miki aikatau na gida, ki ka ce ke ba sai an biya ki ba, idan zasu saka ki a makaranta zakiyi ko?".

"Eh! Baba Halime an samu ne?".

"An samu Aysha nai mata bayani kuma ta amince shine nace mata bari in nemo ki, yanzu idan da abin da ki ke dashi wanda zaki dauko maza je ki dauko kizo muje, tana chan gidana tana jiranmu".

Gyada kai Aysha tai tace "Muje babu abin da zan dauka,amma zan ma Baba Ali sallama gudun kadda ya dena ganina, gyada kai tai "Tace maza je kiyi mai inan ina jiranki".


Bata wani jima ta dawo suka kama hanya suna tafiya ta ke fadin "Baba Halime kafin mutafi zanyi sallah amma anan garin take saboda in dinga zuwa muna gaisawa bayan kwana biyu dake".

Tafiya suke suna cigaba da tattaunawa inda Baba Halime ke gaya mata cewa basu da wani nisa, idan taso ganinta ta sanar da Hajiyar zata kawo ta har wurin, basu wani jima suna tafiya ba suka iso wani madaidaicin gida wanda aka gina shi da kasa, shiga gidan sukai bakinsu dauke da sallama. Amsamu su matan gidan sukai wanƴan da ke kaiwa da komowa wurin karasa abinci dare, don mangariba ta fara shigewa, Baba Halime ce ta tsaya bakin kofah ta miƙo ma Aysha ruwa a buta tana fadin yi alwalar kishigo.

Bata wani bata lokaci ba tashiga cikin ɗakin bayan ta kamallah alwalar bakinta dauke da sallama ta shiga ta gaida matar data gani zaune akan dadduma da alama itama sallar ta kamallah. Matsawa matar tayi tace "Zo kiyi sallar anan".

Matsawa tai cikin sanyi jiki ta tada sallah cikin ƙanƙanin lokaci ta kamallah, ta sake gaidasu, Aysha Hajiyan ta kira sunanta. Sunkuyar dakai kasa tai ta amsa tana wasa da ƴan yatsunta, tsinkayo muryarta tai tana fadin "Kin kamallah mutafi ko?".

"Eh na kamallah".

Miƙewa Hajiyan tai ta dauki jakarta ta ciro kudi Naira dubu goma ta miƙawa Baba Halime tana fadin "Ga wannan ki riƙe in Sha Allah idan an kwana biyu zamu dinga zuwa tana dubaki kuma in sha Allah zan sakata makaranta kamar yadda nai miki alkawari da izinin Allah".

Hannu biyu Baba Halime ta sa ta amsa kudin tana godiya, har bakin mota ta rakasu bude gidan baya Aysha tai zata shiga Hajiya ta girgiza mata kai tace "Gaba zaki shiga ai Ni dake ne zamu shiga ko Hajiya".

Kunya ce ta kama Aysha ta sunkuyar da kai kasa a hankali takai hannunta ta buɗe tashiga ta zauna itama Hajiyar ta zauna tai ma motar key suka hau kan babban titi.

Inda take zaune sunkuye da kai Hajiya ta dube, Aysha! Takira sunanta tana dubanta, zuciyata cike da rauni take kallonta.

Lumshe ido tai tana fadin sunana Hajiya Fadila Lamido Ni bafulatana ce mazauniya garin Kaduna, Inan zaune a cikin anguwar Rimi , mu biyu ne a gurin mijinmu, ina da abokiyar zama sannan inada yara biyar sai dai duk sun rasu, kwaya ɗaya ne yake raye namiji mai suna Habibu Umar, amma baya garinan yana chan Abuja achan yake da zama kuma chan yake aiki, a yanzu haka baya kasar ya tafi wani karatu. Ni da abokiyar zamana kowace ɓangarenta da ban abin da zan roƙeki shine don Allah kiyi aikin ki, iya wanke-wanke da shara ne sai gyaran falona, sannan zan koya miki girki sannu a hankali har hannunki ya fada, abu nagaba zan saka ki a makarantar boko da islamiyya. Kiyimin alkawari zakiyi karatu sosai don ganin gobenki tai kyau. Sannan tambayar da zan miki itace wacece ke?, don Allah kadda ki boyemun komai domin Ni macece mai son gaskiya ban san in yadda da mutum daga baya inga ba hakaba bazan ji dadi ba ina sauraranki"

Wasu siraran hawayene suka samu nasarar saukowa a ƙuncin Aysha, jin duniyar tai ta mata zafi sakamakon tunowa da rayuwar ta tabaya, siraran hannun ta saka ta goge kwallar dake zubowa.



To jama'a mai yasa Aysha kuka?

Shin kuma kun zaƙu kamar Ni don san sanin wacece ita ɗin?


Ku biyoni a pejin gaba don jin meye labarin Aysha meye kuma ya fito da ita har ta kasa sanin su waye iyayenta.



Comment fisabillilahi