chapter 25&26
_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*
*_Wattpad:Rabiatu333_*
*_𝘼rewabooks:Rabiattu0444_*
*Ummu maher collection*
***
EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C
*Sirrinmu➡️*
manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da yiwa ƴaƴanmu zane kamar,kalangu,tattu da sauransu.domin canza halittar ubangiji ne.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️25 & 26
............wasu zafafan hawaye ne suka fara ƙwaranyo masa,ya sanya gefen hannunsa ya sharesu lokaci ɗaya yaji shaƙa daga me martaba gami da zabga masa wasu maruka har guda biyu,yana neman ƙara masa ne su waziri da wambai,da santali, suka riƙesa suna basa haƙuri da ƙer suka zaunar dashi suna basa baki.nuna sa yake bakinsa yana kakkarwa ya fara wasu faɗin munanan kalamai akan ɗan na sa.
"wallahi da nasan dawowarka xata haifarmin da masifa da ban shige gaba ka dawo ƙasar ban ba,ashe dawowarka zai famamin wani tsohon gyambu ne acikin zuciyata, alokacin da ban samu ɗa namiji ba gani nake tamkar duk duniya ni aka tsana, ashe abin ba haka ya ke ba shiyasa akeson idan zaka roƙi ɗa ka roƙi me albarka,amman ba kowani ɗa ba kai dai tunda na haifeka har yanzu ban samu ƙwanciyar hankalin dana ke muradin samu ba,inason kowa ya shaida daga yau na cire ka cikin ƴaƴana Galadima,kada ku ka ƙara tunani a matsayin mahaifinka..........."
maganar yaji tamkar saukar aradu daga sama,ya rintse idanuwansa ya kasa furta koda magana ɗaya, sai wasu zafafan hawaye ke fitowa daga idanuwansa masu masifar zafi tamkar tafasasshen ruwan zafi,yana a tsugunnan ya rarrafa zuwa wajen kyakkyawan kujerar zinaren da mahaifinsa ke kai,ya risinar da kansa gami da sanya lallausan hannunsa kan ƙafar mahaifinsa,ya ce"na tuba me martaba ka yafemin don Allah,rashin yafiyarka zai iya jefa ni acikin mummunar matsala,wannan ƙaddarar da ta sameni ni da kaina ban shirya mata ba,sannan banyi komi don na tozarta ku ba nayi ne sabida wannan itace ƙaddara ta,don Allah ka yafemin ko zan samu salama........"
Tsawar daya buga masa ne ya sanya shi yin shiru,hawaye suka zubo masa ya taune jajayen lips ɗinsa gamida taunesu har sai da suka fara zubar da jini, shin yaya zai yi da rayuwarsa? uwa fushi? uba fushi? shin wannan rayuwar tasa zata gyaru kuwa yadda yake tunani a baya? me yasa rayuwarsa ta lalace haka? me yasa ba za ayi masa uzuri ba? shin sunsan matsalar daya riska alokacin? Idanuwa sun rufe gajimare ya yi duhu, ya kamata yayi wani abu tun kafin lokaci ya ƙure masa.
Wambai ya riƙe hannunsa sannan ya ce"yarima ɗana,kayi haƙuri ni nasan komi yana da lokaci kuma yana da iyaka,saboda haka kayi haƙuri don Allah da abinda ya faru yanzu,sannan kafin komi ya lafa kaje gida na ka zauna da ɗan uwanka ma daki."
ɗaga kansa kawai yayi ba tare daya ce komi ba,ya fice daga babban falon sarki me babban masarauta.
rintse idanuwa me martaba yayi,yana jin wani irin suka a cikin zucoyarsa, ƙarfin addu'ah yasa ya rage jin abinda yake ji gani yake tamkar ya yiwa Allah wani babban laifi ne,daya jarabcesa akan ɗansa mafi soyuwa aransa.
ya riƙe saitin zuciyarsa yana karanto duk addu'ar da tazo bakinsa.
Waziri ya fara hawaye yana ce wa"Allah sarki me martaba, kai dai har kayi auren ka baka janyowa iyayenka abin magana ba, amman gashi kai Allah ya jarabceka da wannan babbar jarabta, shiyasa aduk sa inda kake nunawa yaron nan soyayya nake hanaka wani abun, don dama duk yaron da aka nunawa soyayya sai kaga daga ƙarshe yafi ƙarfin iyayensa". ya faɗi hakan yana ɗan matsar hawayen munafurci nasan asan ya damu.
Wambai ya ce"Allah ya jada ranka, me martaba sarkin babbar masarauta ni aganina wannan hukuncin daka yankewa yarima kamar yayi masa tsauri,hannunka bai riɓewa ka yanke ka jefar ni aganina mu zaunar da yaron nan mu bigi cikinsa sosai, don musan yadda komi ya faru? Wacce yarinya ce? ƴar wani gari ce? To kaga da haka zamu samumu fiddashi daga cikin halin da yake ciki,amman barinsa ahaka idan ma yana wani abin a ɓoye sai kaga ya cigaba dayi saboda an nuna ba a damu dashi ba, amman ayafemin idan maganganuna sun baƙanta maka".
me martaba ya ɗan samu salama kaɗan, bisa shawarar da Wambai ya basa ya ce"madallah da Wamban babban masarauta,xan duba shawararka".
Murmushi ya ɗanyi, don bai san me yasa ba yana matuƙar son yarima da mahaifinsa, ko don abin alkhairin da sukewa ƴan uwansa da kuma iyalansa.Waziri sai hararsa yake,ji ya ke kamar ya shaƙosa don sam yaƙi jini yaga sarki yayi amfani da shawarar wani ko wata, yafi son kullum ayi ta amfani da shawarsa shi kaɗai.
kai tsaye shida fadawansa suka nemi iso zuwa wajen me babban ɗaki Gwaggwala.
tana yi musu iso suka shiga,ta kalli ɗan nata sosai ta ɗangutsiri goronta ta ce"Aliyu ko baka faɗamin ba nasan ce wa aƙwai matsala babba awannan shimfiɗaɗɗiyar fuskar taka,wanda karatun xuci ya fito fili saboda haka a shirye nake da jin abinda ya shigewa wannan buɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwar hanya"?.
rawaninsa ya cire ahankali,ya matsa wasu zafafan hawaye suka zubo masa ya sanya hannunsa yana gogewa ya ce"Gwaggo wata irin rayuwa ce wannan? wacce irin rayuwa Galadima keson saka kansa da kuma mutanen gari?". sai ya fashe da kuka me tsananin tsayawa arai.
sosai gabanta ya faɗi,wannan wacce irin rayuwa ce? kullum dai maganar ba ta wuce Yarima? tunda ya haifesabai huta ba har yanzu?.
cikin kalmar rarrashi ta fara ce wa"me kuma yariman yayi yanzu? faɗamin don musan ko wani sharrin aka kuma ƙulla masa, don wallahi wannan yaron ya shiga ukunsa da maƙiya? haba da Allah sai kace wanda ya hana kowa zama cikin masarauta? kowa ya tsani yaro ?".
muryarsa ta jiyo yana ce wa"babu wanda yayi masa sharri Gwaggo, shi da kansa ya tonawa kansa asiri ya ce wai ya yiwa wata yarinya ciki har ta haife mishi ɗan ya kai gidan marayu".........
tun kafin ya ƙarasa ta ce" ci me"?..............
*** *** ***
sosai na waro ido, ganin wasu manyan ƴan mata sun shaƙo ta sosai tamkar suna neman rabata da ranta,tana ihu tana neman taimako amman ihunka abanza don kowa neman gurin ɓuya ya ke, mamaki ya kamani na rasa me ma zance kawai sai na fashe da kuka na ƙarasa wajensu dagani sai shawul, na ce"haba bayin Allah me wannan baiwar Allahn tayi muku ne? daga zuwa na makaranta tazo wajena sai ku shaƙeta haka tamkar zaku kashe ta"?.
Babbar cikinsu ce ta fara magana wacce ta tsareni da manyan idanuwanta tamkar zata cinye ni ta ce"idan muka kashe tama ai mun kashe banza, tunda babu ubanda ya isa ya ɗaga mana hannu ke kuma wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe, da zan miki don idan muna abinmu babu wanda ya isa ya kallemu balle kuma har yazo ya yi mana magana, saboda haka ki kiyaye kuma ma don kin minne shiyasa zan kyaleki muna fatan kema nan gaba ki shigo cikinmu a dama dake".
sai tayi min wani kallo,wanda ke nuna zallar wani abu dana hango acikin donta, gabana ya faɗi sosai idan banyi ƙarya ba sai naga kamar kashemin ido tayi yadda ya Ahmad ke yimin? anya kuwa waɗannan mutanen kirki ne kuwa? Don na ga wani abu a gefen hannayensu, kamar zanen kunama ta kai harbi,tsoro ya kamani sosai har naji bazan iya cigaba da tsayawa dasu ba, don wani irin mugun tsoronsu naji acikin zuciyata.
da sauri na juya baya na, amman sai nake ji kamar zasu janyoni saboda ƙarfin inuwarsu dana tsaya aciki, da sauri na fara addu'ah wacce manzon Allah (S.A.W) ya koya mana ita.
"A'UZU BIKALIMATILLAHITTAMATI, MIN SHARRI MA KALAƘA".
da sauri naga sun fita, hankulansu duk a tashe .
****
CIGABAN LABARI.
dai dai lokacin na farka daga dogon tunanin dana tafi, lokacin da Ammi ta ce" wai Adawiyya wani irin tunani kike yi ne? Tun ɗazu ina tayi miki magana amman kinyi shiru"?.
a hankali na share hawayena, tunowa da su MAYA ƴan makarantarmu waɗanda suka tsoratani aranar farkon dana fara zuwa makaranta, zan cigaba da baku labarin mummunan abinda ya faru dani, sanadiyyar ƴan ƙungiyarsu MAYA waɗanda na raɗa musu suna da KUNAMA ME HARBI.
Ammi ta juya cikin takaici, don tasan dai kukan da nake bai wuce akan ya Ahmad ba, na kalle ta don ganin irin kallon da take min ni kuma da zata shiga zuciyata tasan tunanin dana keyi da ta rabani dashi, don tunowa da wanman labarin tamkar famamin wani babban bango ne daya tarwatsa rayuwata.
Abbas ne ya shigo, idan baku manta ba shi ne ta bigeni har ya kawoni asibiti, na ɗan kalleshi kaɗan na sunkuyar da kai na suna gaisawa da Ammi tare da yimin sannu.
Ya ce"Ammi yau za a sallame ta ko"?.
Ammi ta ce"eh Abbas".
Ya ɗan shafa gashin kansa sannan ya ce" daman labar wayarki nake so Ammi don mu dinga gaisawa".
Ammi ta ce"ayya ai ba komi".
ta ɗakko wayarta tare da bashi numbar ya ɗauka, yana ta mata godiya bayan mun gama shiri shi da kansa ya ce zai kaimu gida, saboda yana son yasan gidanmu.
ni har mamaki ya ke bani, don gani nake tamkar ya fiya shisshigi don ban masan me yasa ba maza basa birgeni ko ɗaya.
a ƙofar gidan ya ajjemu, ya fito da kansa ya dinga fito mana da kayanmu Ammi na ta yi masa godiya, ni kuwa haushi ma ya sanyani wucewa gaba ko godiyar ban yi masa ba, haushin ya Ahmad ya sanya duk maza bana ganin ƙimarsu kaɗanne waɗanda suka taka gudummawa arayuwata ya sanya nake ganin girmarsu da darajarsu, ban san me yasa ya Ahmad ya juyamin baya ba don lokacin da mukayi aure bai taɓa nuna min wani hali mara kyau ba, amman da tafiya ta shuɗe ranaku da watanni suka wuce, sai rayuwar auratayyarmu ta zama tamkar zaman doya da manja.
ina shigowa cikin gidanmu da Umma na fara cin karo, ta sakarmim murmushi tana ce wa"sannu Adawiyya, dama ɗazu malam ya ce yau za a sallameku, Allah dai ya baki lafiya.
ta riƙe hannuna, ni kuma na wuce zuwa ɗakinta don daman can ni ƴar ɗakinta ce, ko agidan aure na wata matsalar ita nake faɗawa ban fiya gayawa Ammi ba, don ba komi ake faɗawa iyaye ba agidan aure musamman ma uwa.
sam mama uwar gida bata ji shigowa ta ba,sai badi'a ƴarta ce taje ta faɗa mata wai na dawo, ai kuwa da sauri ta fito babu ko kunya ta leƙo ɗakin Umma, gami da riƙe labule ta tsaya tana ƙaremin kallo alokacin dana ƙwanta akan doguwar kujerar ɗakin.
abinda yasa bata samu damar magana ba ganin Umma dake zaune tana haɗamin tea a kofi.
na ɗago ahankali na ganta a kaina na ce"Mama ina ƙwana"?.
sai kuwa ta yi tsaki sannan ta ce" da ban ƙwana ba zaki ganni, ai dole dama ki dawo tunda an kasa zaman aure ana gidan auren amman ana yawo kinga kuwa dole miji ya yi saki.
Ammi tana bayanta duk tana jin abinda ke faruwa,Umma ta ce"haba wannan kuma wacce irin magana ce haka? yanzu zaki so ayiwa ƴarki ko ɗanki haka? Wannan ai muguwar ɗabi'a ce zagin yaran mutane".
harara ta gabza mata sannan ta ce" ba dake nake ba malama, uwar ƴam shisshigi tsabar rashin zuciya akan uwarta babu irin wulaƙancin da ba ayi miki, Amman saboda sadaka aka bada ke daman can shiyasa baki damu ba".
Umma ta yi murmushin takaici sannan ta ce"to sannu uwar gida, ke kuma naga ai tsabar bada sadaka sadaki ma sai wanine ya bayar tunda shi dai bai yaba ba".
sosai Mama ta harzuƙa, don tasan da gaskiyar Umma duk abinda ta faɗa gaskiya ne saboda haka sai ta hau kumfar baki, har da hawayen munafurci saboda iya kissa.ita kuwa Ammi kasa ce wa uffan tayi don ko wajen bata ƙarasa ba ta wuce abinta, don sam bata san hayaniya don daga ƙarshe abin ya dawo kanta, tana shigowa ɗaki kuwa taji muryar Malam ya shigo.
tana ganin ya shigo ta ƙarawa kukan bolin, Malam ya murmusa kawai don yasan halin uwar gidansa sarai, shiyasa kullum acikin takaici ya ke saboda duk wanda bai yi sa'ar matarsa ta farko ba sai kaga komi yana faruwa ba dai dai ba.
ko da ya isa ɗakin Ammi ya shiga, bai ma ko kulasu ba daman ranar a ɗakinta ya ke.
Umma kuwa banxa tayi mata har ta gama surutanta ta fita, daman ni tun tuni na tashi na koma ƙuryar ɗaki don sam nima bana buƙatar wata hayaniya, ina shiga ɗakin na fashe da kuka abin da ya ban mamaki bai wuce yadda Mama ta zauna tana ta faɗamin magana ba, wai ina aure ina yawo? shin daga ina wannan maganar ta fito na ina yawo? tuno da ya Ahmad na yi, domin da wannan maganar ya saba jifana gaskiyar magana indai har shi ne ya faɗa musu wannan maganar to dole ne ayimin tsakani dasu, don shi da kansa Ahmad ɗin bazan koma gidansa ba duk da kuwa ina sonsa har cikin ɓargon zuciyata da gangar jikina.......soon➡️
FACCALA NOVELS FANS
***
L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA
*MRS GREEN CE*