FACALA

chapter 29&30

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*


*Wattpad user name*

***


*Arewa book user name*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444


Whatsapp:***

 

*Ummu maher collection👛👠*

***

BmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️29 & 30


..............me martaba yaji daɗin shawarar da mahaifiyarsa ta bashi, ya tashi da ƙwarin gwiwarsa ya fito muƙarabbansa suka buɗe rigarsu shi kuma yana tsakiya har ɓangarensa, yana shigowa aka yiwa Fulani mazugal iso zuwa wajen me martaba, baya buƙatar kowa akusa dashi yafi buƙatar ɗansa yarima, saboda ya samu yayi shawara dashi don susan ta inda zasu ɓullowa lamarin.babu yadda ya iya dole ya cewa ɗan aikenta anyi mata iso kamar yadda taso.


da taƙamarta ta shigo, kamar yadda ta sabayi akoda yaushe wannan kuma shi ne banbancinta da fulani mahaifiyar yarima, ba tada girman ko kaɗan macece me haba haba da mutane, ita kuwa uwar gida sarautar mata ko amsa gaisuwa ma bata yi, sai dai ta ɗaga hannu idan taso hakan.tana shigowa ta samesa a bakin tafkeken gadonsa ya nutsa cikin tunani, ta ƙaraso cikin takun isa sai da tazo gab dashi sannan tayi sallama, ya ɗago yana kallonta don daman yasan ita ɗin ce me yi masa isa da kuma nuna rainin ta a fili, don sauran matansa ba haka suke masa ba musamman ma Fulani macece me mugun nutsuwa da kuma girmama na gaba da ita, musamman ma shi mijinta don ko sallama tayi sai ta tabbatar daya amsa ba wai da ta shigo ta nemi waje ta zauna ba, hakan kuma yana ƙara mata girma da martaba awajensa sai ya zamanto ita ya ke gani uwar gida a idonsa ba Fulani maxugal ba.


  ta ce"barkanka dai me martaba, dafatan na sameka lafiya".


 "lafiya".


 kawai haka ya ce mata ba tare daya ƙara magana ba, yaja bakinsa ya yi shiru ganin inda ya karkata sai ranta ya ɗan ɓaci, amman ganin tazo neman ingiza me kantu ruwa ne sai ta ce"yallaɓai wata magana naji, amman ban yarda da ita bane saboda nasan ɗanmu adali ne kuma kamili, ta yaya za ayi ace har haka ta kasance mu ba tare da mun sani ba? Wannan ma ai wani lamarine kamar na almara, to shi ne yasa nazo mu rufe mu binne ba tare da kowa ya sani ba".

  Kallon gefe yayi mata sannan ya juya da kansa don yasan inda ta dosa, wato har an kai mata gulma kenan? ya daɗe yana zargin uwar gidansa da aikowa ana masa laɓe, sai kuma yanzu ne ta tonawa kanta asiri don bai taɓa sa hakan azuciyarta har ya zargeta ba, sai gashi kuma ta kawo kanta da kanta. ya ce"to nime babban ɗaki kin sanyamu a duhu? baki faɗi ainin xahirin zancen dake cin zuciyarki ba"?.


  da sauri ta ce" akan maganar ciki da yarima ya yi wa wata yarinya ne? shin kasan da zancen ko kuwa sai yanzu ne ka sani a bakina"?.

Kallon tsaf yayi mata sannan ya ce" na sani menene kuma?".

 Ganin kamar ya harzuƙa ne sai abin ya bata mamaki, don bata zaci zai faɗi abinda ya faɗa ɗin ba sai kuwa ta ce" amman abin ya bani mamaki sosai, sai nake ganin kamar abin zai shafi wannan babbar masarautar da kuma ɓata mata suna, wacce aka ginata kusan shekaru dubu ɗaya da ɗoriya, kaga kuwa gwara tun abin bai fito kowa ya sani ba mu kirawo sa muji ta inda za a gyara ɓarakar, ko kuma ya bar maka masarautar amman zamansa zai iya cutar da wannan masarauta.........."


  wata gigitacciyar ƙara ya buga mata sannan ya ce" kiyi min shiru, daman kina cikin masu baƙin ciki da zamansa a masarautar ne? ke aganinki ni zan iya korar yarima daga wannan babbar masarautar? to in koreshi in zauna dawa? in zauna dake da ƴaƴanki waɗanda basu san mutuncin kansu bama ballantani mutuncina? to bari kiji idan har naji bayan ke wani yaji wannan maganar, wallahi sai ranki yayi masifar ɓaci don sai kin gwammace bakizo duniya bama, sannan inason ki bar min ɗakina nan da minti guda".


  yana huci ya ke maganar, tamkar xai dake ta abinda bai taɓa yi mata ba aduk kanin zamanta dashi, ta ɗauki wani alwashi da kuma wata mummunar aniya wacce take ganin ita kaɗai ce zata iya kawo ƙarshen wannan maras mutuncin yaron, wanda tunda yazo duniya har ila yau bata wuta ba.



cikin fushi ta fito daga ɓangarensa, daman ranar ƙwanan Fulanin sura ne saboda haka lokacin ta taho zuwa sashen me martaba ne, a hanya suka haɗu Fulani mazugal ta bangaje ta tawu ce, sosai abin ya yiwa fulanin sura ƙuna ta rasa me yasa ta zamo musu ƙarfen ƙafa, ita ce matarsa ta farko amman ko kaɗan bata son taga wani ya raɓe sa ko da kuwa ƴaƴansa ne indai ba nata yaran ba, da yake macece me haƙuri sai ta wuce gaba abinta don na abin mamaki bane daman don tasan halinta tun ma ba yau ba.


  tana zuwa ɓangarenta ta dinga kewaye tana neman matsaya guda ɗaya, can ta cafko wani abu ta zauna da sauri ta lalubo wayarta ta kira ƙanwarta wacce take auren waziri.


 tana ɗagawa ta ce"inason duk abinda kike kizo ki sameni, don kuwa mafitar da muka daɗe muna nema sai yanzu ne muka same ta, saboda haka kiyi maza kizo yanzu mu rufe ba tare da kowa ya san da hakan ba".

  kashe wayar tayi, ta koma ɗakinta gami da wani yin ƴan surutai, sai ga wata baƙar mata bokanye a gabanta, sanye da baƙaƙen kaya wulik.


  kuka ta fashe mata dashi sannan ta ce" binni, ki taimakeni na rasa yadda zanyi da rayuwata na rasa yadda zanyi da wannan ƙadangaran kan tulun wato me martaba da ɗansa, ta kai yau har tsawa me martaba ya bugamin saboda ɗansa? inason ayimin abinda zai wargaza rayuwarsa kamar yadda ta fara wargajewa, inason shaye shayen da aka sanya masa ya ƙaru anada, sannan ya afka neman mata kamar dai yadda aka fara ƙwaɗaita masa abin a baya, yanzu kuma sai ya faɗa wannan halin baki ɗaya, sannan asanya mugun saɓani tsakaninsa da mahaifinsa, ta yadda zasu tsanu juna su dinga kallon juna a matsayin abin ƙi ba abin so ba kamar yanzu".

 Binni ta kyalkyale da dariya sannan ta ce" haba ke kuwa sai yanzu ne kika tuno dani? Lokacin da kika haɗa kai da jakadiyarki kuka dinga makirci duk kin manta? Ke aganinki makirci zai yi wa waɗannan mutanen? to bari kiji idan zaki tashi tsaye ki tashi tsaye, don kuwa ina hango miki mummunan ƙurar da zata baɗe idaniyarki dana ƴaƴanki, ke bama ke kaɗai ba kaf danginki sun shiga uku, kuma ina yi miki albishir da cewa wannan ƙurar ta taho daf dake, har tana shirin binno miki duk sihirin da kika binne arayuwarki".



wani irin ihu ta sanya, idanuwanta sukayi jawur tuni ta fara aman jini awajen, don duk abinda binni ta faɗa mata sai ya faru, kuma duk sanda tayi sakaci sai wannan ƙurar ta taso ta baɗe ta, cutar aman jini ta fara sane tun lokacin da aka auro Fulani mahaifiyar yarima, irin fifitata da me martaba ya dinga yi da kuma nuna sonta agaban kowa, itace ta fara rura zuciyarta har ta fara aman jini ba tare dako wani mahaluƙi ya sanda hakan ba, tashin hankalinta ya ƙara ruru wuta, saboda lokacin da aka haifi yarima sai komai ya jagule mata, don kaf ƴaƴanta guda baƙwai mata ta haifa, tasha shan magani akan ta haifi namiji amman tamkar ana rura wutar a mahaifarta na samar da mace, don kuwa yanzu yaranta goma cif cif ne mata, sanadin son yara mata sai daya haifar mata matsala a mahaifarta, wanda shi ne sanadiyyar dena haihuwar arayuwarta baki ɗaya.




***       ***        ***

ba'afi minti goma sha biyar ba, sai ga inuwar ya Ahmad a ɗakin wanda ƙamshin turarensa ya tabbatar min daya iso, tun kafin kowa na ɗakin yasan da hakan.


  Gabana ya yi mugun bugamin, na sanya hannuna dai dai zuciyata ina kiran sunan Allah, har ya ƙarasa shigowa ɗakin ya zauna bansan ya zauna ɗin ba, sai dana jiyo amon muryarsa yana gaisawa da Malam, kana ya juyar da akalar gaisuwar ta shi wajen mahaifinsa, wanda ya ke ta cika yana batsewa.

kasa ɗagowa nayi, shi kuwa tunda ya shigo kallona ashe ya ke, bai san me yake damunsa ba? indai zai ga Rabiatu sai yaji tamkar yau aka dasa masa sonta, amman kuma daya zauna inuwa ɗaya da ita sai yaji babu wacce ya tsana sama da ita, kasa ɗauke kansa yayi akai na har sai dana ɗago kaina na kamashi da satar kallo.


  Maimakon naji haushi sai naji kamar an ƙaramim sonsa ne, na rasa wani irin so da kuma sabo mukayi wa juna, duk sanda zamuyi faɗa to kuma sai kaga mun shirya ba da jimawa ba, idan ma na ɗau zafi dashi da ya ke shiba mutun ne me ruƙu ba sai kaga mun shirya, abinda ke baƙanta min rai akansa bai wuce yadda ya ke zagina da kuma cimin mutunci ba, ko da agaban waye kuwa abu kaɗan zanyi masa ya zamar masa tafarfasashiyar wuta.


Baba ƙin amsa masa ya yi, Malam ne ya ce" Ahmad don Allah inason ka faɗamin a matsayina na mahaifinka me yasa ka canja halinka? me ye azuciyarka da har ka kasa mantawa dashi ya shafi matarka, wanda har muma ya keson ya shafemu a matsayinka na ɗana? kada ka manta ni nine waliyyinka, duk wani abu dake xagaye a auratayyarku yana da kyau in sanu, musamman ma idan na matsala ne, saboda haka ka faɗa mana komi don Allah".


  sosai yaji kunyar mutumin, don gaskiya iya bakin ƙoƙarinsa yana yi wajen ganin akoda yaushe ya bawa ƴarsa rashin gaskiya, aduk sanda sukayi faɗa to shi yanzu bai san ma abinda zai ce ba? don shi dai zuciyarsa ke tursasa akan ya wulaƙanta matarsa, amman bai san meye ke sanyasa hakan ba?.


  yin shirunsa ya ƙara tafarfasa zuciyar mahaifinsa, cikin zafi da ƙuna ya ce" wato bin matan da kake yi shi ne yasa ka raina mutane ko? har ta kai ni mahaifinka in kiraka ka bawa wata ƴar iska tayi min magana? saboda ni baka ganina da mutunci ko? to bari kaji inason wannan ya zamo na farko kuma na ƙarshe,wallahi ko da matarka ta yarda zata koma muddin ka saɓa mata wallahi babu ni babu kai, sai dai ka nemi wani uban tunda ka zama ɗan bariki".


sosai naga hankalinsa ya yi masifar tashi, ya ce"don Allah kuyi haƙuri wallahi ban san me ya ke damuna ba, amman don Allah ku dinga tayani da addu'ah sannan kuma zan ɗauki matata mu koma yanzu, amman ban san me yasa naƙi yarda da Rabiatu ba don nazan muku ƙarya ba, rabon dana neme ta yau tsawon wata baƙwai kenan".


  Sosai naga mamaki akan fuskokinsu, amman mamakin yafi yawa akan fuskar Baba, ya ce"ikon Allah Ahmad kana nufin matan bariki sun fiye maka matarka? to ka sani wallahi tallahi sai Allah ya saka mata a duk tsawon wannan lokacin, sannan idan har baka nemi yafiyarta ba sai Allah ya taɓar dakai tun anan gidan duniya".


  Tuno da wani abinda ke faruwa aduk sanda yazo min, yasana fashe da kuka wato aduk sanda zai zomin komawa ya ke tamkar ba namiji ba, dashi da mace duk ɗaya suke komawa alhalin kuma da ba haka ya ke ba, na rasa me yasa komi ya canja lokaci ɗaya tamkar juyin lagwani.


Malam ya gyaɗa kai, don ya taɓa cin karo da irin wannan matsalar amman yana buƙatar zama daga shi sai Ahmad ɗin don yaji komi.


  Ahmad ya ƙaraso inda nake, ya ce"ki yafemin adawiyya sannan ki cigaba da yimin addu'ah".

  Sosai ya bani tausayi, don kuwa tsakanin mata da miji sai Allah.anan kuma na amince zan koma gidansa ba wai don inaso ba, ba kuma don wani ya tirsasamin ba abu ɗaya daya sanyani yarda bai wuce yadda akaina iyayena suka fara samun matsala ba, alaƙar da aka gina ta tun kafin inzo gidan duniya amman ta sila ta sai ta wargaje? tabbas bazan yafewa kaina ba matuƙar hakan ta faru kuwa.


Malam da Baba sai shimin albarka suke, na sunkuyar da kai na ƙasa Malam ya bani umarnin da in shiga gida idan sun gama Ahmad ɗin zai shigo sai mu tafi.


  Jikina asanyaye na shiga gidan, Ammi na tsakar gida tana haɗa wutar gawayi don ɗora dambun da zata yi, ta gallamin harara don ganin yadda ta ganni ɗin zai tabbatar mata da gaskiyar lamari, wucewa nayi zuwa ɗaki ta bini da do kawai don bata buƙatar maganar tawa dama, ina shiga na fashe da kukan tausayin kai na anya kuwa nadamar da Ahmad yayi ta gaske ce kuwa? anya zai canja dukkanin halayensa na banza? ina cikin tunanin Ammi ta shigo, gabana ya faɗi na tashi zaune ina kallonta.


"Ammi ki yafemin, banyi don in ɓata miki rai ba amman na tabbatarwa dasu Abiey zan koma gidan ya Ahma........."


  wani mugun bugu ta kaiwa bakina, sannan ta kalleni cike da takaici ta ce"amman kin bani mamaki, duk duniyar nan aƙwai wanda ya kamata ya soki sama dani ne? sannan aƙwai wanda ya kamata yaso aurenki sama dani? Amman duk da haka ni da kaina nace bana so saboda ba alkhairi bane auren Ahmad, ke yarinya ce haryanzu baki san rayuwaba ba fata ake miki ba wataran ya ɗakko wani ciwon ya sanya miki ki koma abin tausayi ya ɗakko ki ya dawo mana dake gida? to wallahi bari kiji daga yau sai yau kada ki ƙara kawomin ƙararsa ko da kuwa kashe ki zaiyi, tunda dai ke da kanki kika zaɓi hakan".........soon➡️

FACCALA NOVELS FANS

***

L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


*NABIHA DATA SERVICE*

kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.


MTN

500MB 150

1GB.  300

2GB.  600

3GB.  900

_____

GLO

500MB. 150

1GB.  300

2GB.  5,50

3GB.  850

_________

AIRTEL

500MB  150

1GB.  300

2GB.  600

5GB  1,200

__________

9MOBILE

500MB

500MB 150

1GB. 250

2GB. 450

3GB. 600


Via:-

5458227606

Nabiyyah Aminu

Moniepoint 


my no

***


*MRS GREEN CE*