KWAƊAYIN WASU IYAYEN Chapter 1
KWAƊAYIN WASU IYAYEN....
Arewabooks@ayshadansabo
_Short story......
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI!_
*Ina miƙa dukkan yabo da kuma godiya zuwa ga Allahu Subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara rubuta wannan gajeran labari mai suna a sama,sannan ina jan hankali zuwa ga makaranta da su sani cewa,wannan labarin ƙirƙirarran labari ne dana rubuta domin jan hankali da kuma faɗakarwa.Don haka idan har yayi daidai da rayuwar wani ko wata to arashi aka samu,sannan ina sake kira da babbar murya ga waɗanda ke ɗaukar littafanmu suna karantawa a kafofin sadarwa ba tare da izininmu da su guji yin hakan.Domin zalinci ne da kuma shiga hakkin marubuta,don haka ni Aysha Ɗansabo ban amince a karanta mini labari a kowani kafar sadarwa ba tare da yarda ko amincewata ba.Don haka ku ji tsoron Allah ku guji yin hakan,ina fata makaranta za ku bibiyi wannan labarin daga farkonsa har zuwa ƙarshensa.*
*Chapter 1*
Malam Kabeer Muhammad Turaki asalinsa ɗan jihar Adamawa ne,bafulatani ne usul! Wanda ya fito daga jiharsa ya shiga yawon fatauci har Allah ya kawosa jihar Kano ta Dabo Tunbin Giwa.Tun kuma da yazo bai koma ba ya ce ya samu wajen zama,nan da nan ya faɗa wa harkar kasuwanci ka'in da na'in,domin dama yana da kuɗin da ya sayar da rabin dabbobinsa ya ƙullo kuɗin a mararsa ya fito nema.Cikin ikon Allah kuma sai Ubangiji ya tarfawa garinsa nono,kasuwancinsa na sai da atamfofi da kuma harkar noman shinkafa da ya fara suka bunƙasa.A haka har ya buɗe shagonsa na saida atamfofi yana haɗawa da yadikan maza har ma da leshi na mata,sanann yana da shagon sayar da hatsi da ya saka Yara na zama masa yana biyansu albashi duk wata.A nan Kano ya samu matar aure a wani unguwa da ake kira da ƙofar Na Isa,sun haɗu da Ameena ne a lokacin da ta zo yin sayayya a shagonsa.Tun daga nan soyayya ya shiga tsakaninsu mai ƙarfi har ya kaisu ga yin aure,Allah kuma ya azurtasu da haihuwar ƴaƴa maza guda biyu reras kyawawan gaske.Babban cikin sunansa Mahmud,sai mai bi masa kuma sunansa Muhammad wanda suke kira da Turaki tun yana ƙaraminsa.Sabida sunan mahaifin Malam Kabeeru ne ya ci da ake kira da Turaki,shi ne suma suka laƙawa Muhammad ɗin suna Turakin.Sun taso cikin gata da kulawar uwa da uba,domin daga Umma Ameena Mahaifiyarsu Turaki har Malam Kabeeru sun tsaya tsayin daka wajen ganin Yaransu sun sami ilimin zamani dana addini.Duk da kasancewar su basu samu ilimin boko mai yawa ba,amma hakan bai hana su jajircewa wajen ganin ƴaƴansu sun samu ba.
Muhammad Kabeer Turaki tun tasowarsu shi mutum ne mai yawan son kuɗi da son ya ga yafi kowa,yana da yawan son abin duniya tun yana ɗan ƙaraminsa Iyayensa suka laƙanci hakan.Hakan ya sanya Malam Kabiru yake yawan zaunar dashi yayi masa nasiha akan waɗannan halaye nasa,wanda yake nusar da shi cewa ba halaye ne nagari ba,don haka ya kula ya zare yawan KWAƊAYI da son abin duniya daga cikin zuciyarsa.
Muhmud da Turaki sun taso ne kansu guda sabida tseran shekara guda da wata shida shine a tsakaninsu da juna,tare aka sanya su makaranta ajinsu kuma guda tun daga nursery har ya zuwa sakandiri skull.
Su Turaki sun rasa Mahaifinsu Malam Kabeeru ne a lokacin da suke ajin ƙarshe na kammala karatun diploma ɗinsu,ya rasu ne a samakon haɗarin mota da ya ritsa dashi akan hanyarsa ta dawowa garin Kano daga Adamawa.Ya je ganin gida ne tare kuma da yin wani ta'aziyar maƙocinsu wanda ya kasance abokinsa ne da sukai wasan ƙasa tare,ashe nasa ajalin shi ma yana kusa.Suka tafka wannan mummunar haɗarin da babu wanda ya fito da rai a cikin motar,mutuwar ya taɓa su Mamuda matuƙa tare da jefa rayuwar Umma Ameena cikin wani hali.Tun kuma bayan rasuwar nasa bata sake lafiya ba,sakamakon ciwan hawan jini da ya sameta.Bayan an raba musu gado ne sai Mahmud ya sayi DE domin ɗaura deegree ɗinsa a jami'ar Bayero,ya kuma taki sa a course ɗin da ya zaɓa shi aka bashi zai karaci kimiyar siyasa.(Political Science)
Muhammad Turaki shi sai ya nuna cewa sam bashi da sha'awar cigaba da karatunsa sai dai kasuwanci,domin dama sun horu akan hakan tun Malam Kabeeru na da rai ya ɗaurasu akan neman kuɗi.Indai aka ce sun dawo skull to za su wuce kasuwa,sannan a ranakun mako ma su yake bari a shago shi ya yini a gida idan ba zai leƙa shagon siyar da hatsinsa ba.Umma taso ace Turaki ya ɗaura karatunsa kamar ɗan uwansa amma ya kafe cewa shi Abbansu zai gada wajen cigaba da yin kasuwancin da ya mutu akai,ganin ya dage sai tayi masa fatan alkhairy kawai.Shi kuwa Mahmud ya fara karatunsa cikin nasara,ya kuma tattara dukkanin burinsa da nutsuwarsa wajen ganin ya fito da sakamako mai kyau.A haka rayuwa ta cigaba gara musu suna kulawa da Ummansu da ta zama yau ciwo gobe lafiya,idan wani abu ya taso daga Adamawa suna zuwa su jajanta ko su taya farin ciki.Shekara guda da rasuwar Malam Kabeeru kasuwancin saida zanuwa da lesukan da Turaki ya fara ya bunƙasa,ya tara kuɗi sosai har ya sayi fili a unguwarsu ta Goran Dutse ya tada gininsa.Shi kuma Muhmud yayi nisa cikin karatunsa yana kuma taɓa business ɗin sai da shaddodi da harkar shinkafa,ya kan sara sanfararen shinkafar ne idan an noma,sai ya kai kura a gyara a ɗinke masa a buhuna ya siyar.Shi ma kuma Allah ya albarkaci neman nasa,domin ba ƙaramin samu yake yi ba.
A wata ranar juma'a da ba zasu taɓa mantawa da shi ba Allah ya ɗauki rayuwar Mahaifiyarsu Umma Ameena,ta rasu ne bayan tayi jinya na tsayin sati biyu a asibitin Aminu Kano.Mutuwar ya jefasu cikin mummunar yanayi sosai,domin an ɗauki tsayin lokaci kafin su dangana su barwa Allah komi.Suka dawo marayu gaba da baya waɗanda basu da uwa bare uba,kakarsu kaɗai wacce ta haifi Ummansu mai suna Hajiya Lami ita kaɗai tayi musu saura.Domin Kakanninsu na wajen uba sun jima da rasuwa,su kansu basu ma taso sun tadda su ba.Umman Ƙofar Na Isa kamar yadda suke kiranta,ita ce ta zame musu makwafin Uwa da Uba.Suka ɗakkota ta dawo gidansu dake nan Goran Dutse domin ta zauna tare da su,suka ɗauki nauyinta suna yi mata dukkan hidima da nuna mata gata da kulawar da ko ƴaƴan cikinta guda biyu da suka rage mata ma basa nuna mata irin gatar da su Turaki ke nuna mata.Musamman Mahmud da yafi Turaki zuciyar yin alkhairi,domin shi Turaki wannan halin nasa na shegen kwaɗayin son tara abin duniya baya barinsa yin alkhairi yadda ya kamata.Burinsa shine kullum ya nema ya ƙara akan abinda ya tara,amma bai damu da ya dinga yin taimako da alkhairi ba.Cikin hakan ya samu matar aure,sun haɗu da ita ne anan cikin kwari inda yake da shagonsa.Budurwar mai suna Habeebah ƴar ƙauyan garin kura ne,Mahaifinta ɗan can ne sarin kaya ke shigar da ita cikin garin Kano.Mahaifiyarta mai suna Hajara sana'ar sayar da ƙananun atamfofi take yi,hakan ya sanya take yawan tura Habeeba zuwa cikin garin Kanon domin saro mata zannuwan.Habeebah kyakykyawace fara jajir da ita,sakamakon Mahaifiyarta da ta fito daga tsatson fulanin garin Rogo dake cikin jerin ƙananan hukumomin jihar Kano.Wata iriyar soyayyar mai zafi ne ya shiga tsakaninsa da ita,wanda hakan ya sanya ba a ɗauki dogon lokaci ba Iyaye suka shiga cikin maganar har aka sanya musu rana.Turakin da kansa ya taka takanas zuwa Adamawa ya taho da Yayan Mahaifinsu mai suna Abubakar da suke kira da Jauro,shi kaɗai yayi saura cikin ƴan uwan Mahaifin nasu da suka fito ciki guda.Duk sauran sun rasu,wasu kuma sun nausa wani wajen ba a jin ɗuriyarsu.Watanni biyu duka aka saka ranar auren domin tuni ginin da ya tayar an kusa kammalawa,sabida ba wani gini mai faɗi can ya tattari yi ba.Three bedroom flat ne mai ɗauke da kitchen da bayika a cikin bedrooms ɗin,sai wani ɗaki a waje da kuma wani bayin extra.Sannan akwai wadataccen parking space daga cikin compound ɗin,sosai ginin yayi kyau yadda aka fitar da tsarin ko'ina a wadace.Shi kuwa Mamuda sam baya ma maganar aje Iyali domin so yake sai ya kammala karatunsa hankalinsa ya nutsu waje guda,shiyasa sam baya sakar ma ƴan matan da ke bibiyarsa fuska.
Habeebah wayayyiya ce mai shegen kwaɗayi da son abin duniya,halinsu ya zo ɗaya ne da Turaki ta wannan fannin.Sosai yake kashe mata kuɗi ita da Iyayenta,abinda ya janyo ta sake faɗawa cikin kogin sonsa har tayi nutso mai zurfi a ciki.Bata sake matowa a kansa ba ma sai da ta ji cewa bashi da Iyaye a raye,daga ita har uwarta Hajara sai hakan ya faranta ransu domin suna ganin sun tsinta dami ne a kala.Koda biki yazo sosai ya buɗe musu bakin aljihu suka yi yadda suka ga dama,aka kawo masa Amaryarsa sabon gidansa wanda kowa ke santin kyawunsa.
Watanni bakwai da yin auren Habeebah tayi ɓarin ƴaƴa biyu duka maza,ta sha matuƙar wahala kafin ta samu lafiya ya daidaita mata.Bayan yin ɓarin da watanni biyu ta sake samun wani cikin,murna wajen Turaki da Kakarsu Hajiya Lami ba a magana.Haka suka dinga rainon cikin har ya isa haihuwa,a wata ranar asabar ta haifo ƴarta mace ƙatuwa kuma kyakykyawar gaske.Duk da cewa kalar fatar Turaki mai duhu ta gado,amma hakan bai hana a ga zallar kyawun da Allah ya yi mata ba.Ranan sunan Yarinya ta ci suna Nadeey,kowa ya ɗauka cewa sunan Ummansa zai sa amma sai aka ji akasin hakan.Bayan suna ne Iyayen Habeebah suka tafi da ita wankan gida,a daidai kuma lokacin shi ma Mahmud ya samu matar aure.Duk yadda yaso sai burinsa ya cika na kammala deegree ɗinsa kafin yayi auren hakan bai samu ba,domin daga ranar da ya ɗaura idanunsa akan Mariya ta canza masa dukkanin lissafinsa.Sun haɗu da ita ne a cikin jami'ar Bayero ta rako wata cousine ɗinta za ta yi registration,a lokacin ita Mariyar ta kammala NCE ɗinta bata ɗaura degree ba.Soyayyarsu da juna bai ɗauki wani dogon lokaci ba aka sanya ranar aure watanni shida,kafin time ɗin ya yi shi ma yayi ƙoƙarin kammala gina filinsa da ya siya a Rijiyar Zaki.Filin ba wani babba sosai ne can ba,rabi da kwata ne aka yanka masa ya siya.Hakan ya sanya ya aka zana masa tsarin gina ɗanɗasheshen 3 bedroom flat kamar yadda Turaki yayi,sai dai wanda yayi zanen ginin na Mahmuda yafi wanda yayi na Turaki samun ƙwarewa.Anyi bikin a lokacin Nadeey har ta fara rarrafe,sosai Yarinyar ta shiga cikin zuciyar Abbah Mahmud ɗin.Yana da son Yara matuƙa da gaske,hakan ya sanya duk ranakun weekend yake leƙawa gidan Turaki don kawai ya gano Nadeeya ya kai mata siyayyar kayan wasa da baya rabo da siya mata su.Bayan bikin da watanni uku Kaka Mairo ta rasu a wata ranar alhamis da safe,ajalin ya sauka ne a sanadiyyar amai da guduwa da ya kamata cikin dare.Zuwa wayewar gari kuma ta amsa kiran Ubangijinta,sunyi kuka mai yawa tare da shiga cikin halin damuwa irin wanda ba zai misaltu ba.Ya zamana kawunnan su biyu kaɗai suka rage musu sai Iyalansu a cikin garin Kano,acan Adamawa kuwa Jauro kaɗai garesu wanda bai taɓa samum haihuwa ba su biyu kaɗai suke rayuwa shi da matarsa.Sannu a hankali rayuwa ta cigaba da gara musu cikin samu da wadata daidai bakin gwargwado,Turaki duk abinda ya samu kansa kaɗai ya sani bai damu da yiwa kowa komi ba.Daga shi sai matarsa da ƴarsa Nadeeya ke moran samunsa,amma baya ga su babu wanda yake cin abin hannunsa sai mai rabo.Kullum kwanar duniya sake fito da maitarsa na son tara abin duniya yake,ya haɗa sana'o'i da dama domin ganin kuɗi na shigo masa ta ko'ina.Amma da yake shi zafin nema bashi ke kawo samu ba,sai ya zamana Turaki kullum cikin raina abinda yake samu duk wata idan ya haɗa kan cinikin da aka samu yake.Hakan ya sababba masa yawan ƙorafi da butulcewa rufin asirin da yake samu,idanunsa kullum yana ga sauran abokanan kasuwancinsa da suka fi shi yana baƙin cikin yadda kasuwarsu a kullum tafi nasa buɗewa.
Mahmud koda yaushe ya ji yana ƙorafinsa akan rashin samun yadda yake so a kasuwancinsa,ya kan zaunar da shi yayi ta masa nasiha da nusar dashi cewa sai fa bawa na godewa ni'imar da Ubangiji yayi masa sannan Ubangiji ke ƙara masa buɗi da wadata.Sai dai kawai Turaki ya ji Yayan nasa da kunni,amma sam nasiharsa bata yin tasiri a cikin zuciyarsa.Ana cikin haka ne gobara ta kama a cikin kasuwar kwari,shaguna da yawa sunyi asarar dukiya ba kaɗan ba.Cikin shagunan da suka ƙone aka rasa dukiya mai yawa,har dana Abban Nadeey kamar yadda ake masa alkunya da ita tunda ya haihu.Ya gigita ya kuma fita a hayyancinsa,da ƙarfin addu'a ya dawo hayyacinsa.Kaɗan ya rage ciwon damuwa ya sameshi,sabida ya kasa yin tawakkali irin yadda ake son musulmin ƙwarai yayi.Tun daga silar wannan gobaran da ya rasa babban jari kasuwancinsa ya gurgunce,hakan ya sanya suka ɗaga gidansu na gado suka siyar suka raba kuɗin.Dama tun rasuwar Kakah Lami suka saka ƴan haya a ciki,tunda dukkaninsu sun yi gidan kansu bare wani ya dawo ciki ya zauna.Shiyasa da wannan jarrabawa ta faɗawa dukiyar Turaki sai Mahmud ɗin ya kawo shawarar a ɗaga gidan a siyar ya ja jari da kason sa,sannan ya sake dunƙula wasu manyan kuɗi ya basa.A haka Turaki ya samu ya farfaɗo da shagonsa,amma ko kaɗan bai kai na baya girma da cikar kaya ba.
Nadeeya na da shekaru biyu aka sake haifo wata ɗiyar da ta ci suna Ruƙayyatu,kyakykyawar ɗiya fara jajir da ita wanke hannu ka taɓa.Tunda ta zo duniya ta shige cikin zuciyar Turaki yana jin alfaharin samunta a matsayin ɗiya,wani irin kulawa yake bata na musamman kai kace a kanta ya fara samun haihuwa.Shi kuwa Abbah Mahmud kar kawo wannan lokacin Mariya ko ɓatan wata bata taɓa yi ba,shekara guda har da watanni shida kenan da aurensu.Abbah Mahmud ɗin ne ya fara damuwa da rashin samun cikin matarsa,hakan ya sanya ya ɗauketa suka dangana ga wajen likita domin a duba lafiyarsu.Binciken farko aka gano shi ne keda matsala,sai dai ba a yanke masa tsammanin cewa ba zai taɓa samun haihuwa ba.An dai ɗaurashi akan magunguna,suka dawo gida jikinsa a mace zuciyarsa cike da tarin damuwa.Daga shi har Mariya babu wanda ya sanar da kowa nasa zancen likita,suka binne sirrinsu a cikin zukatansu Abbah Mahmud ɗin ya maida hankali wajen shan magunguna masu tsada da aka ɗaura shi a kansu.Sai dai har magungunan suka ƙare ya sake komawa ganin likita babu wani labarin ɗaukar ciki a wajen Mariya,sannu a hankali har Ruky ta girma tayi wayo basu samu biyan buƙata ba.Tun ana lissafin shekaru uku har aka fara lissafa shekaru goma amma shiru,zuwa lokacin ya jima da kama aikin gwamnati har ya fara taka matsayi.Gefe guda kuma harkokin kasuwancinsa na ƙara bunƙasa,domin har ya biya musu kujerar hajji shi da Mariya sun je dawo.Sunyi addu'a sunyi kuka sosai a ɗakin Allah suna roƙon ya basu haihuwa,amma har kawo wannan lokacin da su Nadeeya da ƙanwarta Ruky suka shiga primary 3 shiru ba zancen samun ciki.Tun suna saka rai suka fara fidda tsammani,dangi da ƴan uwa suka dinga surutun cewa ko suna tsarin Iyali basu son haihuwa ne? Daga Abbah Mahmud ɗin har Mariya toshe kunnuwarsu kawai suka yi,cikin zukatansu kuwa su kaɗai suka san irin ciwon da suke ji na rashin samun haihuwar.Zuwa wannan lokacin su Nadeey sun fara girma sosai,sun fara zama ƴan mata masu tsananin kyawun halitta.Kyawunsu da dirinsu kullum sake bayyana yake,musamman ma Ruky da take fara mai gashi duk an fi ganin kyawunta.Saɓanin Nadeey da take wankar tarwaɗa mai duhun fata,wacce tafi ɗakko kammannin Abban nasu sosai.Tunda daga kan Ruky Umma Habeebah bata sake samun haihuwa ba,sai yawan ɓari da ta dinga yi akai-akai.Daga ƙarshe likita ya basu shawarar a juya mahaifar baki ɗaya sabida gudun samun matsala,basu so hakan ba amma sabida gujewa shiga matsala sai suka aminta aka juya mahaifar.Abbah Mahmud yaso ɗan uwansa Turaki ya bashi riƙon Ruƙayyah,amma yana zuwa ma da Ummansu Nadeey da zancen ta nuna bata amince ba.Shi ma kuma dama maganar Yayan nasa ba wani kwanta masa yayi a zuci ba,sabida yafi buƙatar ƴaƴansa su rayu a gabansa ya basu kulawar da shi yake ganin ya dace dasu.Haka nan Abbah Mahmud ya maida kwaɗayinsa cikin cikinsa,suka duƙufa da addu'ar Allah ya basu nasu rabon suma.
Daga lokacin da su Nadeeya suka zama cikakkun ƴan mata suka fara gano irin burin da Iyayensu ke dashi a kansu,musamman Ruƙayyah da koda yaushe Umma ta buɗi baki take kiranta da matar manya.Time ɗin da suka kammala sakandiri sun gama zama cikakkun ƴan mata masu ji da kyawu da dirin halitta mai matuƙar ɗaukar hankali,qawayen Ruky su Aisha Aminu da Zee Zubairu kullum cikin zuzuta kyawun Ruky suke tana sake birgesu.Tana da farin jini da shiga rai sosai,ga shi Allah yayi mata sanyin hali da nutsuwa.Akwai ta da son karatun boko dana islamiya baki ɗaya,sosai kuma Allah ya bata kwanyar ɗaukar karatun da maida hankali.Tuni samari suka fara kawo musu hari da sunan soyayya,musamman Nadeeya da Allah yayi mata farin jinin samarin.Abbah da kansa ya zaunar dasu ya karanta musu cewa baya son koda wasa su riƙa kula ƙananun samarin nan da basu da komi,sannan kuma iyayensu ba wasu bane domin shi ba zai bai wa talaka aurensu ba.Nadeeya da ita ce ta fara sauraren samari masu cewa suna sonta ita yafi yiwa gargaɗin,domin ita Ruky burinsa a kanta na daban ne.Domin koda wasa baya jin zai taɓa bari jinin da bana arziƙi bane ya raɓeta,ya manta cewa wanna hurumin Ubangiji ne da ke arzurta bawa ko ya kaisa gidan hutu da arziƙin ba wai wayo ne ko dibaran mai dibara ba.Cikin iko da ƙudurar Ubangiji sai Allah ya haɗa zukatan Ruky dama wani matashi mai suna Ahmad,Ahmad kyakykyawar matashi ne black beauty da ya mallaki duk wani cikar halittar da ake nema a wajen ɗa namiji.Nutsatstsen guy ne da ya tsaida addini matuƙa da gaske,domin Mahaifinsa Malamin addini ne da suke zaune a can gaban layin su Ruky.Sun haɗu da shine a lokacin shi Ahmad suna zana final year exam ɗinsu a jami'ar Bayero,Allah ya haɗasu da Ruky a lokacin ita kuma suna shekarar farko a diploma ɗin da suka fara ita da Nadeey a nan jami'ar ta Bayero.Sosai suka faɗa a tarkon ƙaunar junansu domin daga shi har Ruky bada wasa zukatansu suka kamu da soyayyar juna ba,gashi kuma abinda ya sake birgesu da juna shine dukkaninsu ƴan unguwa guda ne.Kowa yana ganin ba zai sha wahalan gano asali da ɗabi'un ɗan uwansa ba,sun samu zai kai kimanin watanni biyar da fara soyayya kafin Ruky tayi ƙundunbalar amincewa Ahmad akan ya tura a nema masa izinin fara zuwa zance wajenta.Domin Ahmad ɗin ya matsa mata sosai akan ta amince ya turo a san da zamansa,domin yana tsoron kada wani yazo yayi masa shigar sauri.Lokacin da ya turo Yayun Ubansa Marigayi Mallam Sulaimanu domin su nema masa izini,sai a sannan Abbansu Nadeey ya san cewa ita ma Ruky ta fara soyayyah ba tare da ya ankara har ya bincike waye wanda take tare da shi ba.Zuciyarsa tayi mummunar ɓaci da jin cewa ba ɗan kowa bane ta turo masa face ɗan gidan Iya Larai mai waina,marayan da basu da komi sai rufin asirin sana'ar toya wainar da uwarsa take yi kaɗai.Domin dai Mallam Sulaimanu ya rasu bai barsu da komi ba sai tarin tulin littafan addinin da yake karantar da ɗalibansa,don haka Ahmad ɗin bai gaji komi ba sai tarin ilimin addini dana zamani haɗi da ingantacciyar tarbiyar da ya samu daga wajen nagartaccen Maihaifinsa Mallam Sulaiman.Mallam Sulaimanu Malamin addini ne masani a fannin fiqhu da sauran manyan litattafai,wanda yayi suna sosai a unguwarsu dama wasu wurare masu dama a cikin ƙwaryar Kano,sa'annan ya ƙarar da rayuwarsa baki ɗaya ne wajen karantarwa da hidimtawa addininsa.Tsananin nauyi da kunyar dattawan ƴan uwan Mallam Sulaiman da Ahmad ya turo masa,shi ya sanya Abban Ruky kasa bijirewa buƙatarsu na son a bai wa ɗansu dama ya fara zuwa zance domin su fahimci juna.Sai ya basu tabbacin cewa ya bai wa Ahmad ɗin dama ya fara zuwa zance wajen ƴarsa Ruky,suka koma gida da kyakykyawar albishir ɗin da zai faranta zukatan Ahmad da Iya mai waina......✍🏻