FACALA

chapter 31&32

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*


*Wattpad user name*

***


*Arewa book user name*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444


Whatsapp:***

 

*Ummu maher collection👛👠*

***

NeSHdAl9EgqmlWo3Z3C


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️31 & 32

.........fashewa na yi da wani irin kuka me mugun cin rai, na tsugunna a ƙasa na dafa ƙafar Ammi na ce" Ammi don Allah ki daure ki yafemin, wallahi fushinki tamkar ƙara tafasar wutar da take tafarfasamin rayuwata ne, duk abinda nayi ba don komi na yi ba Ammi saboda ke da kuma Abiey, tunda nake arayuwata ban taɓa ganin kun samu saɓani me girma har haka ba, duk akaina ne komi ya faru bana son wata ɓaraka ta shigo tsakaninki dashi duk ta sabadiyya ta, don Allah ki yafemin sannan inason ki dage da yimin addu'ah saboda rayuwar aure na ta gyaru kamar kowacce mace da take zaman farin ciki da walwala agidanta". na faɗi hakan ina me fashewa da kukan tausayin kai na.


sosai na hango tausayina ƙarara akan fuskar Ammi na, ta riƙo hannuwana na tashi zaune ta ce"Adawiyya ba tsanarki nayi ba, Ahmad ne ahalin yanzu bana so ko jin sunansa, musamman ma a bakin ki sannan kuma ayau nr na yarda da son da kikewa Ahmad, saboda haka na baki goyon baya ɗari bisa ɗari ki koma gidansa, amman zan nemi alfarmar akan ya barki har sai zuwa jibi ma, don aƙwai abubuwan da na ke son kiyi kafin ki koma, sannan shima da kanshi aƙwai abubuwan da zan sanya Malam ya bashi, don na lura abin naku aƙwai lauje cikin naɗi".

Ɗan murmushi nayi wanda ya sanya wushiryata fitowa fara tas tas tamkar madarar ruwa, dimples ɗina suka samu damar lotsawa gwanin ban sha'awa, na ce"na gode Ammi Allah ya barki da Abiey". ta murmusa tana ranƙwashina na ƙwanata kan cinyarta, tana kallon kitson zara zaran kalba akaina, wanda ya ɗan jima kusan wata ɗaya akaina, ta ce"Amman yaushe kika zama ƙazama kuma?".


  Cike da shagwaɓa na ce"Ammi to wanda zanyi kitson ya gani be damu dani ba, ko nayi ma bai san nayu ba abinda ya sani yayi ta kallon mata awayarsa ba tare dani ya sanyani agaba ya kalla ba".

"wannan dai duk ba hujja bace, ta yaya za'ace mace me aure ta zauna da kitso, kitson ma na kalba akanta har tsawon wata ɗaya? haba Adawiyya, bafa haka na koya miki ba ni ɗinnan da kike ganina sati bibbiyu nake kitso na, sannan kuma aduk sati biyun nan ina wankeshi kafin inyi sabo, adawiyya ƙazanta tana sanya namiji yaji ka fice aransa, duk kuwa da tsananin son da ya ke miki, balle yazo inda kike ya jiyo kina wari ko ƙarni ko hamami, kinga gobe ba zaki ƙara ganinsa kusa dake ba, sannan sai abu na biyu ki zama me yawan ɗauke kai aduk abinda mijinki zai miki, sai kiga kin zauna dashi lafiya duk da aƙwai abinda ba'a ɗauke kai akansa a aure shi ne idan namiji yayi dare, dole ne ka tambayeshi ko lafiya? shima ba ta hanyar rashim kunya ko fitsara ba, ta hanyar lallami da lumana idan da hali ma sai kin haɗa masa ruwan wanka ya yi bayan hakan ma kin bashi abinci yaci, aƙwai matan da babu ruwansu da yadda mijinsu ya dawo, abinda suka sani shi ne kawai a basu sai faɗa sai masifa, kuma waɗannan matan ba fa basa son mazajen na su bane, suna sonsu sosai amman kuma basu san yadda zasu zauna dasu bane, Adawiyya idan nace miki ke kika bawa mijinki ƙofar neman mata banyi ƙarya ba, don kuwa ke kike hanashi kanki, don har gidan nan ya kawo min ƙararki, wai akan facalar ki na cewa ke mayyar miji ce, to ke kuma kina tsoronta sai kika fara ƙaurace masa a shimfiɗarsa, haka nayi ta fama dake akan ki dena amman daga baya sai kika ɗauki hakan a banza, daga baya kuma yazo ya dame ki ko ayanzu abinda yasa na dake sai ya rabu dake saboda tsoron kada ya sanya miki wani ciwon, tunda ke kin kasa dena abinda kike masa na hana mishi kanki, nasihar da zan miki itace tunda har kinji kin gani zaki koma kina son mijinki, to ki dage ki kula da miji salo salo ki ƙara tabbatar da abinda ya keso da kuma wanda baya so, sannan duk yadda za kiyi ki hanashi yawon dare, don duk macen da mijinta ke dawowa gida da wuri to tabbas ba tada rabin matsalar aure, don a wannan yawon ne zai je ya ɗakko miki wacce zata sanya ki acikin mummunar matsalar da zaki kasa fita, ƙarshe mijin ya yanka miki red card ita kuma ta zauna agidan da kika kafa ɗan ƙaramin tarihinki aciki, don duk macen da ta bari ta fita gidan mijinta wata ta shigo to tabbas wannan kishiyar zata shafe babin tarihinki agidan sai na ta, duk irin tashen da kika yi saboda haka ki kula sosai sannan an jima zanyi magana da Mlm, aƙwai abinda za'ayi da kuma addu'o'i da kuma saukar alƙur'ani me girma".


sosai naji daɗin abinda Ammi ta faɗa, ko daman abinda ya hanata yin komi wai don ni ƴar fari ce, har mamaki Ammi nake da take kunyar ƴar fari dani don ni dai Allah ya sani bana jin kunyar ƴar fari da ita.


  tana tsefemin kai Malam da ya Ahmad suka shigo, na tashi da sauri ina gaida ya Ahmad ɗin amman fuskata ahaɗe take, sai kallona yake yana ƙara kalleni tsaf, sai naga yana wani mayen murmushi ya ce azuciyarsa, wai me yasa ma nake kula matan banza ne? alhali matata babu abinda bata haɗa ba, ƴar shekara 17 yarinya ɗanya sharaf ga komi na cikar halitta amman na tsaya a matan banza?. shi kaɗai yake saƙa komi aransa , amman ni ina fuskantar duk abinda ya ke ce wa, na tashi da sauri zuwa ƙuryar ɗaki.


 Ammi ta ce" Ahmad ina roƙo idan da hali ka barta zuwa jibi, don kuwa aƙwai abubu da yawan gaske dana ke so ayi, ciki kuwa harda addu'o'i da kuma saukar kur ani me girma."


  Malam ya gyaɗa kansa don ya aminta da hakan, ya ce"tabbas haka ne Zulaiha kinyi tunani me kyau,sannan kai ma Ahmad ka dage da azkhar na safe da maraice, yawancin mutane muna wasa da wannan babban azkhar ɗin, wanda shi ne Manxon Allah S.A.W ya keyi sannan kaima aƙwai tofin da zan maka na ƙwana uku, idan da hali kada ka faɗawa kowa wannan lamarin, don mugu ba shida fuska amman kayi haƙuri idan mun tirsasaka".


da sauri ya tari numfashin malam ya ce" ba komi Malam, nima ina toƙon gafara awajenku don Allah ku yafemin akan abinda ya faru tsakanina da Rabiatu".

Malam ya ce"ba komi Ahmad, tun ɗazu kake neman yafiyarmu Allah ya yafe mana baki ɗaya".


 Dukkanmu muka amsa da amin, har ni dana ke cikin ƙuryar ɗaki ina jiyosa yana musu sallama, sai dai sallamar tashi cike take da manufofi don yana son yaga na fito, ni kuma na yi ƙulewa ta amman kewarsa cike take a ƙoƙon zuciyata, don inasom mijina shima yana sona na dai rasa dalilin canjawar komi, wanda ni na ɗaukesa ƙaddararmu ce haka.



***        ***       ***

shigarsa ɓangarensu sha maki yayi dai dai da shigowar dalleliyar motarsa cikin gidan, yana fitowa ya ƙaraso da sauri inda ya ke ya ce"Yarima yau kai ne a sashenmu? sannu da zuwa".


  ya ɗanyi murmushin gefen fuskar daya saba yi, sannan ya bashi hannu suka gaisa ya ce"muje ɓangaren mama mu gaisheta sai muje sashenmu ka huta ko?"…

saurin dakatar dashi yayi, ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce a taƙaice" muje sashenka kafin".

  

  Babu yadda shamaki ya iya dashi, dolensa ya yi biyayya don ko ba komi ya ɗan girmesa sannan kuma matsayinsa dana sa ba ɗaya bane, shi yana ɗan sarkin fada shi kuma ɗan sarki? ai matsayin ma ba ɗaya bane, kuma sannan yasan halin Yarima da rashin son magana, saboda haka ya yi abinda yace don azauna lafiya.


  suna shiga ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon shamaki, ya ce"miƙomin ruwa me ɗumi insha".

 da sauri ya tashi ya ɗebo masa ruwa a na'urar xafafa ruwa, sannan ya kawo masa a glass cup, da yake shamaki irin matasannanne masu tsaftar gaske, sannan komi nasu a tsaftace ya ke don har kitchen ne ƙato me matsaikacin kyau a ɗakinsa.


  tunda ya kafa kansa bai ajje ba har sai daya shanye, duk da yasan illar da take cikin hakan amman ajje ruwan tamkar ƙara tafarfasa zuciyarsa ne, shiyasa ya kwankwaɗesa tsaf sannan ya ajje yana ajiyar zuciya.

 Shamaki na lura dashi, duk da yana ɗan danna wayarsa don aikin banki yake yi kunsan aikin yadda yake da sanya mutum a busy.


  azuciyarsa kuws ce wa yake, Yarima ikon Allah wannan matarsa za tayi fama ba kaɗan ba, don mutunne shi mai masifar mskilanci, magana ma sai yayi niyyar yinta yake yi idan kuwa ya yita da yawa har haki za kaga yana yi, kyau tamkar shi yayi kansa musamman jan bakinsa dake matuƙar ɗaukar hankalin mutane da dama, ciki kuwa har da maza bama mata ba, gashi dogo ne samɓal irin mazan nanne masu tsayi sosai kuma yana da ɗan kauri amman ba can ja, idanuwansa sleeping eyes kullum alumshe suke tamkar me jin barci.


   Shamaki ya ce"Allah ya taimaki yarima, sai naga kamar kana cikin damuwa ko"?.


  da ƙer ya buɗe ƙasaitaccen bakin na sa ya ce" eh ina ciki,ba kuma za ka iya yimin maganinta ba, saboda haka you have to be carefull, bana son surutu nuna min bathroom zanyi wanka".

  shiru ya yi gamida tashi ya nuna masa sannan ya dawo ya zauna, yana mamakin abinda ke faruwa? sai dai ba shida ikon sanin meke faruwa ɗin, amman duk abinda zai sa kaga Yarima cikin damuwa ba abune ƙanƙani ba, don tun yana yaransa iyayensu ke yi mishi misali da yarima, yadda ko acikin yara ne babu me sanya sa kuka, sai dai ma kai ya sanya ka.



sosai ya saki ruwan ajikinsa, ruwa me xafi ya daɗe acikin wannan halin ya fara wanke ko ina na jikinsa tamkar mace, don sai yayi awa ɗaya zuwa biyu a banɗaki, har sai da Shamaki ya fara tunanin buga ban ɗakin ko lafiya? sai gashi ya motsa handle ɗim banɗakin ya fito, sanye da tawul a jikinsa yana tsane kansa da wani.


  yana fitowa ya hango kiran mardiyya, ƙanwarsa da kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga, shiru tayi ta kasa magana shima bai ce komi ba ya barta amman ya sanyata a handsfree, duk sanda ta tashi magana tayi idan kuma tayi shiru har kuɗinta ya ƙare a banza.

 Shamaki dai bai daina kallonsa ba, don ashe abin nasa har ƙannensa bai bari ba? sai kuwa ya ce"Yarima mardiyya ke kiranka fa? ni aganina ka ɗaga kaji ko menene"?.


  bai ce masa ƙala ba, sai ma lumshe idanuwansa da yayi, yana tuno wani mashahurin lamari, wanda aduk sanda ya rufe idonsa abinda yake gani kenan, indai ba ƙwayarsu ta soji yasha ba baya jin daɗin rayuwarsa.


  can Mardiyya tayi ta maza ta ce"bro Allah ya taimakeki ya ƙara maka lafiya, daman wata magana ce nake son muyi da kai, abinda Ammi ta faɗamin ɗazu gaskiya ne? wai ka yiwa wata yarinya ciki har ta haihu? i can do that, nasan hakan ba zai taɓa faruwa ba, ɗan uwana ba shida wannan halin don Allah ka faɗamin ko zuciyata zata samu salama".


  sosai gaban Shamaki ya buga, ya tsorata sosai daman abinda ya sanya yarima cikin damuwa kenan? gaskiya wannan ba ƙaramin mummunan lamari bane, kuma abin yana da ɗaure kai da kuma shiga ruɗu.


  kamar babu wani abinda ke damunsa ya ce" eh haka ne, meye matsalarki akan hakan? saboda haka kisan da wanda kike magana, ni ba sa an wasanki bane".

Yana faɗar hakan ya datse kiran wayar.


Shamaki ya kallesa da kuma ƙarfin halinsa, don shi koda ya aikata ba zai iya cewa shi bane, amman shi cikin dakiya har ya iya buɗe bakinsa yace shi ya aikata hakan, gaskiya ba kowa ne zai iya wannan sadaukarwar ba.




***       ***        ***

....... Amrat ta ce"Hamida kinsan kuwa yadda nake masifar son yarima? kinsan daɗewar danayi da sonsa a zuciyata? amman shi bai ma san na damu dashi ba? kullum burinsa bai wuce ya ƙuntatamin ba? idan har da ace zan iya cire soyayyarsa arai na to da tuni na cire shi araina, amman bazan iya hakan ba ya xama dole in auresa idan ba haka ba mutuwa zanyi".


  Hamida ta ce"come down besty, kiyi haƙuri mu zauna mu tattauna ta yadda ya kamata ace yarima ya kulaki har ya aure ki, ni aganina me zai hana muje wajen Dad muyi magana dashi, tunda Dad abokin me martaba ne wataƙila za a samu sauƙin lamarin, har ma ya aure ki ko yana so ko baya so".

Amrat ta juyo da sauri ta ce"yes yes shawara me kyau"..........soon➡️



FACCALA NOVELS FANS

***

lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


*NABIHA DATA SERVICE*

kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.


MTN

500MB 150

1GB.  300

2GB.  600

3GB.  900

_____

GLO

500MB. 150

1GB.  300

2GB.  5,50

3GB.  850

_________

AIRTEL

500MB  150

1GB.  300

2GB.  600

5GB  1,200

__________

9MOBILE

500MB

500MB 150

1GB. 250

2GB. 450

3GB. 600


Via:-

5458227606

Nabiyyah Aminu

Moniepoint 


my no

***


*MRS GREEN CE*