KWAƊAYIN WASU IYAYEN

KWAƊAYIN WASU IYAYEN Chapter 4

by @ayshadansabo

KWAƊAYIN WASU IYAYEN...!

Arewabooks@ayshadansabo


 Short story...


      *Chapter 4*


Sati biyu Ahmad yayi a camp suka fito,ranar da zai dawo garin Kano sai ya kasance Ruky ta rasa inda za ta sanya kanta sabida farin ciki.Kasancewar ranar weekend ne babu skull sai ta fara shirya masa girki na musamman dasu snacks da za ta tarbesa da shi,tana jin yadda Umma ke faman zuba tsaki tana yada mata magana amma ta toshe kunnuwarta.Tana tsaka da yin aikin ne kuma aminan nata biyu Aysha Aminu da Zee Zubairu suka kawo mata ziyara,ta tarbesu cike da farin ciki suka nufi ɗakin su Rukyn suna faman jan juna da raha kamar yadda suka saba.Aysha da take ƙwararriya a fannin snacks ita ce ta kamawa Ruky aikin doughnut da spring roll,ita kuma Zee Zubairu ta tayata suka ƙarisa haɗa salad da Ruky ta koya a wani online class da ta shiga.Suka kammala komi akan time tare da zuba su a mazubi masu kyau,suna tsaka da gyaran kitchen ɗin ne Umma ta shigo tana aje ganinta akan yadda akai arranging kululinta sabbi bisa saman kitchen cab ɗin.Ta buɗe baki cike da takaici tana dubansu Zee ta ce, "Yanzu Zainab kuma izata kuke yi akan wannan ɗan talakan da sam bai dace ace shike neman ƙawartaku ba? Me yasa ba za ku tayamu gaya mata gaskiyar cewa ita ɗin bata dace da takala ba?" Daga Zee har Aysha jikinsu ne yayi mugun yin sanyi,mamakin kalaman da Umman ke furtawa akan Ahmad ya cika zukatansu domin sam su basu ga wani aibu ko rashin dacewarsa da ƙawar tasu ba.Murya a sanyaye Aysha da ta fi Zee baki ta furta, "Umma mu gani mukai Ahmad bashi da wani aibu,yana son Ruky sosai kuma yana da halaye masu kyau da kowace mace za ta yi fatan ta mallakesa,yana da sana'ar yinsa daidai gwargwado ga kuma iliminsa yayi a koda wani lokaci Allah zai iya ɗaukaka shi Umma." Umma baki sake ta dinga kallon Aysha har ta dasa aya,cike da ɓacin rai ta furta, "Okey! Sai yanzu na gano ashe kuke sake izata,to bari ku ji daga ku har ita kunyi kaɗan mu zuba muku ido ta auri wannan Yaron,da ɗaya daga cikinku yake so ina da tabbacin Iyayenku ba za su amince masa ba sabida kun fito daga gidan hutu ba za a taɓa bari ku raɓi tsiya ba,to itama ai Ubanta nada rufin asiri ba zai taɓa bari ta auri takalan da bai tara ba, kullum Uwarsa sai ta ɗaura tandan waina a wuta domin su samu abin rufin asiri." Tana kaiwa ƙarshen kalamanta ta fice daga kitchen ɗin ta bar su Aysha baki sake suna jinjina al'amarin a cikin zukatansu.Ruƙayyyah wasu ƙwallan baƙin ciki ne suka cika idanunta,cikin sanyin murya ta dubi su Zee tana sanar dasu irin yadda Abbah da Umma suka ɗauki dogon buri suka ɗaurawa kansu na cewa lallai sai masu kuɗi ko ƴaƴayensu za su aura musu.Ta ƙare maganar da faɗin, "Wallahi zuciyata ta fara shiga cikin muguwar damuwa,banga aibun Ahmad ba Zee,don Allah ku sanar dani yadda zan yi su Umma su fahimci cewa soyayyar gaskiya muke wa junanmu." Aysha ce ta dafa kafaɗun Ruky tana faɗin, "Calm down Ruky,kiyi haƙuri na tabbatar ai ba za su iya yi miki auren dole ba,idan har suka ga kin tsaya kai da fata shi ne zaɓinki dole su amince ki auri wanda zuciyarki ke so,koda Umma ke maganar Iyayenmu masu shi ne ba za su amince mu auri talaka kamar Ahmad ba,wallahi ni Ummata da Abbah ba haka suke ba,a koda yaushe sunfi fifita nagarta da halayyar mutum na gari sama da mai yake dashi ko mai ya tara,da ace ni Ahmad ke so har na kaisa gaban Abbahna,na tabbatar shi ne mutum na farko da zai tayani farin cikin samun nagartaccen saurayi mai ilimi da zuciyar neman na kansa kamar Ahmad,am sorry to say Ruky su Umma gaskiya suna da KWAƊAYIN abin duniya irin na WASU IYAYEN da ke ganin kamar idan sun haifi ƴaƴa mata to shikenan sun sama jari ne." Hawayen tsananin takaici suka zubo daga idanun Ruky tana mai jinjina kanta ta ce, "Wallahi Aysha maganarki haka take,su Umma KWAƊAYIN da son abin duniya ne kawai a cikin zukatansu,domin idan ba hakan bane mine ne aibun Ahmad da Khwamis ɗin Yaya Nadeey da aka hanashi zuwa zance wajenta? Please! Ku tayani da addu'a Zee wallahi idan aka rabani da Ahmad bansan wani irin hali zuciyata za ta shiga ba." Tausayin Ruky mai tsanani ya kama aminan nata,suka dinga rarrashinta da kalamai masu daɗi har ta saki zuciyarta.Suna tare da ita har zuwa shida na Yamma,sun fito za su tafi kenan domin drivern gidan su Aysha ya zo ɗaukarsu sai ga mashin ɗin Ahmad ya shigo cikin compound ɗin.A tsaye suka gaisa da su Aysha suna sake yaba iya ɗaukar wankansa,ya gama yin kyau cikin farar shaddar dake jikinsa.Sosai yayi kyau kwarjininsa na sake haskawa,idanunsa akan Ruky ya zubesu wacce ta gama yin kyau cikin straight gown ɗin dake jikinta.Ta yafo gyale da ya dace da shigar fuskarta na haskawa da walƙiyar makeup ɗin da tayi akan face ɗinta wanda ba mai yawa bane,ta raka su Aysha sukai mata sallama da juna kafin ta dawo garesa tana sake haskeshi da wannan kyakykyawar murmushin nata dake narkar da zuciyarsa. "Habeebi mu je daga falon Abbah please!" Ahmad ya waro idanunsa waje yana faɗin, "Habeebty falon Abbah kuma? Me yasa ba za mu zauna bisa kujerun can ba nan ɗin ma ya isa ai." Ruky sosai ta hango zallar fargaba a cikin idanunsa,hakan ya sanya ta shagwaɓe masa face tana faɗin, "Ba zai yiwu ka ci abinci a waje iska na hure maka shi ba,na shirya maka abubuwa masu daɗi da nake fata ka ci ka bani makin da ya dace,please! Ka amince mu je babu komi fa Umma ce ta ce na saukeka a nan ɗin." Jin hakan ya sanya shi bin bayanta har suka isa ƙofar shiga falon Abbah ta wajen,ita ta buɗe masa ƙofar wanda dama already a buɗe ta barsa tunda ta shiga shirya abincin da tayi masa a tsakiyar carfet ɗin falon.Ya shiga bakinsa ɗauke da sallama yana sake ƙarewa kyawun falon kallo,falo ne mai kyau da tsari irin na masu rufin asirin da suka fi ƙarfin komi bakin gwargwado.Hira sosai suke sha na luv yana sanar da ita irin missing ɗin ganin kyakykyawar face ɗinta da yayi,ita ma ta dinga sanar dashi tayi kewarsa sosai da sosai.Daga bisani ta tashi ta zubo masa dukkanin abinda ta shirya masa ta kawo gabansa ta aje,yadda duk ta narke masa ne ya sake susuta shi ya dinga ɗiban komi da ta aje ɗin yana ci domin faranta zuciyarta.Sosai ya yaba mata a fannin ɗaura sanwa,domin duka abinda ta tanadar masa babu wanda bai yi masa daɗi ba.Sai gabannin fara kiran sallar magrib yayi sallama da ita ya wuce bayan ya aje mata ƙatuwar leda mai ɗauke da tsaraban da ya ce yayo mata,ta rakosa har wajen mashinsa ɗinsa ya hau ya tafi suna ɗagawa juna hannu.


Bayan sati biyu da fitowar Ahmad daga camp Kawunsa ya sama masa inda zai yi Service ɗinsa a garin Abuja,zai yi Service ɗin nasa a airport ɗin Abuja ne wajen da shi Kawun nasa yake aiki ya kuma zama babba a wajen.Sosai Ahmad yake cikin farin ciki da fatan Allah yasa su riƙe shi bayan kammala Service ɗin,domin a ganinsa ko a airport ɗin ya sami aiki ya samu babban cigaba duba da yadda Kawun nasa ya kuɗance babu abinda tafi ƙarfin Iyalinsa.Ana gobe zai tafi Abujan ya zo sukai sallama da Ruky,ya damƙa mata sabuwar wayarsa da ya siya ya amshi tata wanda bata kai nasa tsada da girma ba.So yake shi yayi kakara da natan ya sai wata babbar da za ta basu damar fara yin vid call su riƙa ganin juna rangaɗaɗau,sabida zai dinga ɗaukar kamar sati uku zuwa ƙarshen wata bai shigo Kano ba duba da tsadar man fetur da ake a ƙasar.Sosai Ruky ta ji zuciyarta ta raunana da nesa da juna da za su yi sai dai ta waya,suka rabu Ahmad ɗin na rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.


Koda ta shida gida direct ɗakin Umma ta shiga ta nuna mata wayar da Ahmad ɗin ya bata,Umman ta kalli wayar tana taɓe baki ta ce, "To ina taki wacce Abbanku ya siya muku?" Ruky ta saki murmushi tana faɗin, "Ita ya amsa Umma zai yi amfani da ita kafin ya siya wata,kinga wannan ai tafi waccan tsada domin za ta kai dubu ɗari,watakila ma ta haura hakan." Ta ƙare maganar jikinta na mutuwa da irin kallon da Umman ke watsa mata.Cikin takaici Umma ta dubi Ruky tana faɗin, "Aikin ji halin tsiyar da ƙaranta irin na talaka,au yanzu bama zai iya baki sabuwa dal a kwali ba tare da ya amshi taki ba sabida bashi da arziƙin yin hakan ko? Allah wadaran kwanyarki da bata ja Ruƙayyatu,ni maza ki tashi ki bani waje tun takaicinki bai cika min ciki na rotsa wayarba shashasha kawai!" A guje Ruky ta ɗauke wayar ta nufi ɗakinsu tana jin zuciyarta na tafasa da matsanancin ɓacin rai.Nadeeya dake zaune tana packaging su tuwan madararta ta ɗago idanu ta zubawa Ruky,cike da kulawa take faɗin, "Mai kuma ya faru kike ta faman sakin tsaki da ɓata rai?" Ruky ta sanar da ita yadda sukai da Umma tana nuna mata sabuwar wayar Ahmad ɗin da suka yi exchanging.Nadeey ta amshi wayar ta juya a hannunta tana yaba kyawunta,cike da kwantarwa da Ruky hankali ta ce, "Ki daina sanya damuwa akan ire-iren kalaman Umma,tunda dai ke kina son abinki ai shikenan,ni banga aibu don ya amsa taki ya baki wacce ta fita kyau da tsada ba." Ruky ta jinjina kanta tana share hawayen idanunta ta ce, "Na daina Yaya Nadeey,abin ne ke ci mini zuciya idan na tuna cewa Umma fa Uwace a garemu, bai kamata ace wai ita ce ke son ɗauramu a turban da ba zai kaimu ga tudun mun tsira ba, sai ɗinbin nadama idan har za mu sanya KWAƊAYI a zukatanmu da cewa lallai sai mai kuɗi ne za mu aura." Nadeey cike da gamsuwa da jin tarin tsanar halayen su Umman na son abin duniya ta furta, "Nima abinda ke mini ciwo kenan Ruky,amma ya muka iya tunda bamu da tamkarsu,dole addu'a za muyi tayi musu har Allah yasa su fahimci cewa abinda suke mana kwaɗayin mu bashi ne a gabanmu ba." Ruky ta aje mayafinta tana ɗaukar wayar domin buɗe kafofin sadarwan da ta saba bibiya irin su Whatsapp,Instagram da kuma facebook.Sosai take shiga market place a manhajar facebook tana tallata stickers da lallenta,tana kuma samun customers daga sassa da yawa na jihohin ƙasan da take tura musu da shi garuruwansu idan sun sara mai yawa.


*********


 *After 7 Month* 



Watanni bakwai kenan da fara yin Service ɗin Ahmad a garin Abuja,duka kuma sau huɗu ya kawo ziyara zuwa Kano tunda ya tafi.Duka zuwan da yayi sai ya kawowa Ruky tsaraban kayan ciya-ciye zuwa su turaruka masu kyau,a zuwan ƙarshe ma har da wasu haɗaɗɗun flat shoe masu tsada ya taho mata dasu.Ya sake yin kyau sosai fatarsa ta goge tamkar ba aiki yaje yi ba hutawa ya tafi yi,da alamu weather ɗin da ake cewa bai faye amsar kowa ba shi ya amshesa.Suna biyansu albashi sannan kuma ga kuɗin da gwamnati ke basu albashi duk ƙarshen wata,a ɓangaren kasuwancinsa ma komi na tafiya masa yadda yake so,jarinsa kuma na sake bunƙasa.Allah ya haɗashi da Yaron shago na gari dake da gaskiya da riƙon amana sosai,shiyasa sam bashi da wani haufi akan barin garin da yayi sabida komi na tafiya masa yadda yake so.Sosai ya fara taimakon Iya mai waina,har ya kai yanzu ba wainar kaɗai take yi ba, ta haɗa da sana'ar yin garin ɗanwake da yaji dakan hannu.Sosai kuma business ɗin nata ke shiga sabida tsaftarta da inganta haɗin da take yi,duk wanda ya siya sau ɗaya ya dawo tare da janyo mata wasu customers ɗin ma.Ko sau ɗaya dukkanin abinda ya kawowa Ruky bai taɓa birge Umma da Abbah ba idan Rukyn ta nuna musu,abinda ke matuƙar yi ɓata ciwo yana cin zuciyarta kenan.

A ɓangaren karatun su Ruky watanni uku kaɗai ya rage musu su kammala diploma ɗinsu,hakan ya sanya koda Yaushe Ruky ke lissafawa kanta yin aure nan kusa tare da masoyin nata Ahmad.A lissafinta sun kammala skull da wata guda shi kuma zai kammala service ɗinsa,a tunaninta tunda yana sana'ar yi bama sai an jira ya samu aiki ba za su yi aurensu cikin rufin asiri da ƙaunar juna.


Ranar wata asabar da misalin ƙarfe biyu na rana Aisha ta zo gidansu Ruky,bayan sun gaisa da Umma ne ta shaida mata cewa ta biyo ne ta ɗauki Ruky ta rakata SAHAD STORE yin sayayya.Umma ta amsa mata da to domin sosai take jin daɗin ƙawancen Ruky dasu Zee ɗin,sabida su ɗin Iyayensu masu kuɗi ne manyan Kasuwa da aka san da zamansu.Sannan suna kashewa Ruky kuɗi wajen yi mata siyayya duk idan zasu yiwa kawunansu shopping sai sun haɗa da Ruky,abin hannunsu sam baya rufe musu idanu da gaske suke ƙaunarta.Ruky cikin shigar Abaya baƙa da tayi mata mugun kyau suka fito,tayi rolling veil ɗin Abayar ta yadda ya sake ƙawata irin kyawun da shigar ke yi mata.Ba Aysha kaɗai ta tanka irin kyawun da Rukyn tayi ba,hatta Umma da Nadeey sai da suka tanka.Suka fice jere da juna da Aysha har zuwa wajen motar da Aysha ta zo da ita,ita da kanta ne za ta yi driving ɗinsu domin ta riga ta ƙware a tuƙi yanzu.Ruky na zaune a front seat Aysha na mazaunin driver ta tashi motar suka wuce,suna tafe suna hiransu abin sha'awa.Aysha ne ke bai wa Ruky labarin wani sabon saurayi da tayi mai suna Aliyu,ta sanar da ita cewa Babansa shine kwamishinan harkokin gona na jihar Kanon nasu.Ruky tayi musu fatan alkhairy tana yiwa Aysha tsiya akan cewa yanzu ne za ta san daɗin soyayya,domin ita Aysha a baya sam ba wai tana bai wa soyayya wata muhimmanci bane sama da karatunta.Cike da alhini da kuma tsantsar damuwa Ruky ke mata complain akan yadda kullum su Abbah ke sake nuna tsanarsu ga Ahmad,Aysha haƙuri kawai ta dinga bai wa Ruky domin ita kanta bata san ajin da za ta aje su Umma wajen KWAƊAYIN da son abin duniyan da suke fiddowa a fili game da ƴaƴayen nasu su Ruky.Sun isa SAHAD ɗin kenan kiran Ahmad ya shigo wayar Ruky,tayi receiving call ɗin suna fitowa daga motar suka nufi ciki.Gabaki ɗaya Ruky hankalinta na kan wayar da suke da sahibin nata,sam bata ma kallon komi a cikin mall ɗin tunda ta samu wani waje tayi tsaye abin ta.Sai da suka ƙare wayar ne ta shiga takawa a nutse tana kurɗawa side by side har ta samu ta lalibo inda Aysha ke tsaye tana zaɓan wasu desighner perfumes da take using ɗinsa,ta taya ta suka cigaba da ɗaukar abubuwan buƙatun Ayshan wacce ita kuma Aysha take haɗawa har da abinda ta san Ruky za ta so.......✍🏻