KOWA DA ƘADDARARSA

46

by @faddabanan


Zuwa lokacin da nazo kan waya ta na iske missed calls ɗin Nu'uman bakwai, jiki na har rawa yake yi na kira shi a waya. Abu na farko da ya fara faɗa shine "Me ya faru ba ki ɗaga waya ta ba? Kin tsorata ni har na fara tunanin anya lafiya kike kuwa? Kin gan ni yanzun nan zan ƙaraso ƙofar gidan ku.......yauwa! Na ƙaraso ma. Za ki gan ni yanzu ko na juya?"

"Ina zuwa." Na faɗa masa.

A mota na same shi a can ƙofar gida yana jira na, zagayawa nayi ɗayan ɓangaren na zauna ina duban shi, sai ya miƙo hannu ya riƙe nawa yace "Na ɗauka ko wani abu ne ya same ki akan hanyar ki ta komawa gida, ganin ina ta kira kuma tsoro na ƙaruwa a raina, sai na yanke shawarar zuwa gidan da kaina don na gani ko lafiya."

"Babu komai fa, su Yaya Zainabu ne suka zo sai suka ɗauke mun hankali, shi yasa ka ji shiru don sai daga baya na ga calls ɗin naka." 

Bai daɗe ba sosai yace zai tafi, mun yi sallama har na juya zan shiga gida sai na ji muryar shi "Ummu?" Na dakata tare da juyowa na tsaya ina kallonsa. Ya ɗaga gira ɗaya yace "Me kika yi mun ne? I feel so attracted to you, gabaɗaya hankali na ya dawo gare ki. Do you have any explanation for this? Cause I can't explain why I like being around you all the time!" Ya dafe kan shi.

Cikin wani yanayi da ban san menene ba a tattare da ni nace "I have no idea, amma tunda ka iya kwatanta wa ba mamaki za ka iya sanin ma'anar hakan."

Ya fara kallo na irin kallon da babu wasa a ciki yace "Ummu kin tattare feelings ɗina gabaɗaya zuwa gare ki. Na ƙaryata kaina amma sam gaskiyar ta ƙi bari na, i think I'm in love and yes in love with you Ummu. Let's date!" Ya cigaba da kallon yanayin da na shiga ya sake faɗin "Yes! Ina son ki. Koma gida, so kawai nake ki san abin da ke faruwa da ni. Sai da safe."

Ina nan tsaye kamar an kafa ni har ya tada motar ya ja ya tafi, sam na kasa motsi bare magana. Zuciya ta tana ta zunguri na ma faɗa masa haka nake ji game da shi amma baki na ya ƙi ba da haɗin kai.

Na yi ta jiran wayar shi a daren amma bai kira ni ba sannan ko ta WhatsApp ma bai yi mun magana ba. Tunani kala-kala ya cika kaina har ya jawo mun ciwon kai kafin daga bisani na samu da ƙyar bacci ya ɗauke ni wurin ƙarfe biyu. Da yake Nu'uman ɗin a raina yake har mafarkin shi sai da nayi. Na ɗauka abinda ya faɗa mun jiya zai sani cikin farin ciki mara misaltuwa amma sai ya zama na ban san me nake ji ba, kamar tsoro na shiga ta da ya danne the supposed excitement.

Da safe ni ce na fara masa magana kuma ko kaɗan bai dawo da zancen jiya ba har na fara tunanin ko dai mafarki nayi. Sai da muka yi sallama yace 'love you', bai jira amsa ta ba ya katse wayar.

Wata irin shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu a satin da muka shiga, kwata-kwata ya daina zuwa agency ɗin mu, idan ma ya kama zai je yana zuwa lokacin da bana can ne, hakan ya sa su Rahina ba abin da suka sani a game da mu. Kawai dai rannan Rahinatu ta tsare ni a teburina tace "Kin canza sosai Ummu, ba ki da aiki sai bini-bini ki ɗauko waya kina karanta saƙo kina murmushi, ko kuma ki daina aikin gaban ki ki tsaya kina tunani kina murmushi, ni kuma nasan duka wannan alamar soyayya ne. Ba ni labari Hajiya ta, wa muka samo haka?"

Ina dariya nace "Kai Rahina! Wannan bayani dalla-dalla haka? Idan kuma hirar ce tayi mun daɗi fa kawai?"

Tana murmushi tace "Ummu kenan. In dai tayi wari kowa zai ji ne ai." Ta koma wurin zaman ta ta bar ni ina yi mata dariya.

Abun mamaki sai na tsinci muryar Nu'uman yana gaisawa da wasu da ban gane su waye ba a ƙafar benen mu kafin ya shigo. Ai kuwa nayi tsamo-tsamo, don ofishin mu ba wanda ya san muna wata magana balle wani abu a tsakani na da shi, don haka ban san ta yaya zan fara kula shi ba bayan kowa ya san ko gaisuwa babu a tsakanin mu. Da sauri na jawo waya ta nayi masa text cewa "Don Allah kar ka kula ni, mu cigaba a yanda muke da can. Please?" Na tura. Da wayar a hannun shi ya shigo, ina kallon shi ya ɗan tsaya ya karanta, yayi murmushin gefe ya turo mun da cewa "Ba ni hujja mai ƙarfi, daga hujjar zan gani ko zan iya ko ba zan iya ba."

Ya tsaya suka gaggaisa da mutanen wurin sannan ya ƙura mun ido na sakwanni kafin ya nufi ofishin Manaja, yana kuma shiga ya sake turo wani saƙon "Ina jiran hujjar, ba zama zan yi ba."

Sai na rubuta "Ban san yanda zasu kalli abun ba ne, sun fa san ba ma magana sai kuma tashi ɗaya su ga wani abu daban? Ni kawai ka yi haƙuri mu dinga share juna anan, please? Ka ji?"

Sai ya turo 'hmmm' a matsayin amsar sa. Hankali na sai ya kwanta, da alama ya yarda don haka sai na cigaba da abinda nake yi. Gabaɗaya hankali na yana kan aikin da nake yi har ban lura da lokacin da ya zo gaban teburina ba sai muryar shi na tsinta yana faɗin "Ummu ina saƙo na?" Yana murmushin gefen nan sannan yana kallo na ta ƙasan ido. Wallahi a take na ji na ruɗe, na rasa me zan yi sai kawai na zuba masa ido ina kallon shi alamar ban ma san me yake faɗa ba. Ganin zan ɓata masa lokaci sai ya zagayo ya dawo gefe ya kuma sanya hannunsa ya jawo hannu na har sai da na miƙe na tsaya sannan ya jawo ni hanyar waje ba tare da sauraron komai ba. Hakan ya ja hankalin kowa da ke cikin ofis, tsabar gulmar su shirun da ofishin ya ɗauka mutum zai iya jin ƙarar faɗuwar allura, Rahina kam ta gefen ido da na hango ta bakin ta a hangame ya ke.

Saitin bayan shi ya maido ni lokacin da muke sauka daga matakalar benen kamar mai gudun kar na faɗi, irin ya yi amfani da jikin shi a matsayin shinge na. A matakalar ƙarshe ya tsaya sannan ya juyo ya fuskance ni yace "So kike ki sirrinta tsakani na da ke kamar ba mu da gaskiya? Whose validation are you seeking? Ko a cikin su akwai wanda kike dating da kya san ya san tsakani na da ke? Now that i announced it in my own style, go and deal with it." Ganin ba ni da niyyar magana sai ya juya zai tafi, a hanzarce na riƙe rigar shi don haka ya tsaya tare da juyowa yana me ɗaga gira alamar tambaya. Na yi shiru kawai, shi ma sai ya rungume hannayensa yana kallo na ba tare da ƙosawa ba sannan can jimawa yace "Wait.... Are you ashamed of being with me or what? Ko dai da gaske akwai wanda ba ki son ya san tsakaninmu ne?" Yana kallo na intensely yanzu kam.

Na girgiza kai, sai ya ɗan duƙa yanda tsayin mu zai zo ɗaya yace "Ba abun damuwa ba ne, kin ji? Ban zo don na yaudare ki ba, just be free with me and in shaa Allah ba zan taɓa ba ki kunya ba. Koma ki cigaba da aikin ki." Yana tsaye yana kallo na har na gama hawa benen, da na juyo don ganin ko ya tafi bayan na gama hawan sai ya kanne mun ido sannan yayi mouthing 'I love you' sai nayi murmushi na shige ofis ɗin mu.

Idon kowa a kaina da na dawo ciki, sai nayi ƙarfi halin share kowa har da ɗan ɗaure fuska ta don na san duk cikin su babu mai iya tunkara ta balle ya tambaye ni, sannan na ƙi kallon wurin da Rahina take, ita ma na san ganin idon mutane yayi yawa ne ya sanya ta basar kamar ba ta lura ba amma nasan lokaci kawai take nema ta tarfa ni. Muna samun break ta jawo ni zuwa wani corridor ta ƙarshen ofishin Manaja tace "Munafuka! Ashe dai hasashe na akan gaɓa na yi. Ɗazun babu daɗewa kika gama yi mun musu, sai ga shi akan ido na da na wasu muka shaida. Dama ashe can baya fooling ɗin mu kuka yi kenan."

Na amsa "Wallahi ba haka ba ne, abun ya fara lokacin da aka yanke ni ne fa. Kuma kin san Allah abun ba wani ƙarfi yayi ba bare na faɗa maki, Nu'uman ne abubuwan shi sai shi ɗin." A halin yanzu kowa ya san tsakaninmu sannan cikin ikon Allah Habiba ko a ƙeyar ta don ba ta ƙara canza mun ba.

A satin da aka fara azumi Nu'uman yayi mun sallama ya koma Legas. Zuciya ta duk babu daɗi, kewar shi nake yi sosai sai kace irin a wuri ɗaya muka zaune ɗin nan. Hutun na shi bai ƙare ba tukunna, amma abu ne na ujila ya taso a can Legas ɗin. Mu kuma a nan aiki ya cuɗe mana saboda masu zuwa Umra, ni duk aikin ya fitar mun a kai yanzu, ga gajiyar azumi ga ta aiki ga kuma ta makaranta. Duk wanda yake aikin rana/yamma da suke shan ruwa a ofis, abinci na musamman ake kawowa amma ban san daga ina ba ne.

Yanzu idan aikin yamma gare ni motar kawai nake bar wa Hussein sai ya zo ya ɗauke ni saboda har kusan ƙarfe goma ake kai wa yanzu. Don haka kamar koyaushe wannan juma'ar sai ta faɗo mun a aikin yamma, break ɗin mu yanzu tun magriba har zuwa bayan isha kaɗan, daga nan kuma sai mu ɗora aiki. Tun biyar ɗin yamma ake tafka ruwa kamar da bakin ƙwarya don haka kafin magrib gari yayi sanyi sosai. Jiki na da ba ya raina jin sanyi ko min ƙanƙantar sanyi sai na ji shi, a take na fara rawar sanyi. Na warware ɗan kwali na na haɗa da mayafi na na lulluɓe jiki na amma ban daina ji ba.

Ana kiran sallar magriba muka miƙe domin gabatar da farali da kuma buɗa baki. Ina zuwa bakin ƙofar ɗakin da muke yin sallah na ji gaba na ya faɗi. Na ɗan dakata domin hanci na kamar yana ɗauko mun ƙamshin turaren Nu'uman ta iska da ke kaɗawa. Na kasa daurewa na juyo na kalli ofishin mu, ba kowa har wannan lokacin rawar sanyi nake yi. Zuciya ta na bani shawarar na wuce kawai naje nayi alwala amma jiki na ya ƙi biyayya, sai tahowa nayi na doshi ƙofar fita, ilai kuwa a bakin ƙofa muka ci karo.

Na zaro ido ina mamakin yanda jiki na ya sanar da ni zuwan shi. Murmushi cikakke yayi mun yau ba na gefe ba yace "Na ga ana jam'i, bari nayi sauri kar ya wuce ni." Sannan ya koma ƙasa ni kuma na nufi wurin da muke yin sallah. Na yi brush haɗi da cin dabino sannan nayi alwala. Kamar yana kallo na, domin ina idar da sallah sai ga wayar shi wai na sauko ƙasa. Sanyi ne ya fi damu na, ga wata irin yunwa, na kuma sani da wani ne da musu zan yi masa amma sai gani suka yi na miƙe ina faɗin su ci abincin ba sai sun jira ni ba. Ina duƙunƙune haka na dauka har zuwa harabar ofishin, a bakin ƙofar da za ta sada ka da harabar na iske shi tsaye yana jira na, ya ɗan tsaya yana kallo na yace "Sanyi kike ji ne haka?" Kai na ɗaga ma shi, a hanzarce ya bani wuri yana faɗin "Yi sauri mu ƙarasa mota to."

A motar ma heater ya kunna mun domin rage sanyin sannan ya jawo kwandon abinci a baya yana cewa "Tun la'asar na dawo Kano, abincin shan ruwa na tsaya dafa maki."

Ina dariya nace "Oh ni 'yar gatan Nu'uman. Amma a ƙasar hausa ba'a saba ganin namiji yana girki ba bare har ya yi wa matar shi. Kar ka ja a dinga cewa na mallake ka."

Ya amsa cikin rashin damuwa yace "Kyautatawa ce, sannan kuma yaba kyauta tukwuici. Na san ke ma za ki iya yi mun fin haka." Ya ajiye abincin da ya zuba a plate a tsakanin mu. Ban tsaya ɓata lokaci ba na fara ci har da su santi shi kuma yana dariya. Zufa na ga yana yi sai abun ya ba ni tausayi, shi baya jin sanyi ga heater har ta dame shi amma bai yi magana ba, sai na miƙa hannu na kashe heater ɗin motar don ko ni ma na daina jin sanyin. Sai da aka fara kiran Isha sannan yace na koma ciki zai je ya samu jam'i har da tarawee. Har na fara tafiya ya dakatar da ni, yana ƙarasowa kusa da ni ya lulluɓeni da coat ɗin shi. Ƙananun kaya ne a jikin shi, ba mamaki coat ɗin a mota take kawai. Da coat ɗin a jiki na nayi sallah, ƙamshin sa da na turaren shi ke fita daga cikin rigar yana ƙara mun nutsuwa.

Ragowan aiki na na ranar tare da shi muka ƙarasa. Kane-kane yayi mun akan kujera ta sai hakan ya sanya na zama kamar mataimakiyar shi. Abdul'aziz har tsokanar mu yake wai "Ɗankwali ya jawo hula." Duk abinda na miƙa hannu zan ɗauko sai ya dafe yace "Zauna kawai ki kalle ni, idan akwai gyara sai ki faɗa mun na gyara." Har aka tashi, shi ne ya sauke ni gida. Bayan mun yi sallama nace "Rigar ka ba yau zan mayar ba, ji nake kamar kai ne." Na juya domin shigewa gida na jiyo shi yana cewa "Ga ki ga mai rigar, da ni kika ɗauka ai, zan fi kowa farin cikin taimakawa." Kuma ban waigo ba na wuce ciki abu na.

A dunƙunƙune da rigar na kwana, kasancewar ranar ba ni da aiki bayan sahur da asuba sai na cigaba da bacci na har zuwa ƙarfe ɗaya. Da na farka ma rungume rigar nayi da ƙarfi har na jiyo alamun wani abu a aljihun rigar, hannu na na sanya na lalubo. International passport ɗin shi na gani, hoton shi a jiki kaɗai na kalla na ajiye akan durowar gefen gado na tare da fara shirin wanka. Ni ce nayi abincin shan ruwa ranar, waya ta na kusa da ni don kar ya kira bana kusa da ita. Ilai kuwa sai ga kiran na shi, don haka ina aiki na muna hirar mu.

Sai bayan isha na koma ɗaki na, idona ya sauka akan passport ɗin. Na miƙa hannu na jawo tare da buɗewa ina kalla. Abinda idona ya kai kan shi ne ya sanya ni faɗuwar gaba, a kuma take na san cewa duk wani mafarki da nake tayi akan Nu'uman ya rushe a take gabaɗaya! Na fi kowa sanin aure tsakanin mu ba abu mai yiyuwa ba ne. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na zauna daɓas a bakin gado na na dafe ƙirjina, hawaye kuma kamar an buɗe famfo. Waya ta daidai wannan lokacin ta ɗau ƙara, ina kallon ta ɗauke da sunan Nu'uman amma sam na gaza amsawa. Tana katsewa sai nayi masa magana ta WhatsApp, nace chaji na ya ƙare, Generator ɗin mu kuma ya lalace ga shi babu wuta yanzu. Sai kuma na kashe wayar gabaɗaya.