Day 2
by @kwalisa
Take sadaukai suka xauki shewa da iface-iface na murna samun nasara, sannan ba tare da vata lokaci ba suka shirya domin kama hanyar komawa zuwa ga birninsu wanda kusan tsawon shekara biyu kenan da barowarsu, sun fito ne da burin yaqar duk wasu qasashen musulmai.
Ba su xauki tsawon lokaci suna shirin ba kowa ya kammala suka gabato gaban sarki Rum suka tsaya, suna jiran umarninsa. Bayan tsawon lokaci sarki Rum ya nisa gami da faxin “Bisa tsarin alqaluma za mu yi wannan tafiyar domin mu samu ikon qarasawa qasarmu akan lokaci, ina saka ran zuwa wayewar gari za mu qarasa domin jama’ar qasa su taryemu”Yana kammala maganar ya sake gyara zama akan kujerarsa ta tsafi.
Ko kusa wannan lamarin bai yiwa jarumi Hamri daxi ba domin ba shi da burin daya wuce ya kuma ganin Karsa domin yanda duk tunaninta ya mamaye masa zuciya, ga mamakinsa sai ya ji ya samu kansa a cikin baqin ciki da vacin rai. Take ya soma nazarin hanyar da zai bi domin guduwa daga cikin ayarin jaruman, amman yasan hakan abune mai matuqar wahala domin yadda duk motsinsa idanun mahaifinsa yana kansa.
Duk wani anuri dake kan fuskarsa ya gushe, ya samu kansa yana mai saqe-saqe na abubuwa da dama, abu xaya ya iya yanke wa shi ne ya zamar masa dole ya dawo, kuma idan ya dawo zai nemi soyayyarta, yana wannan tunane-tunanen suka kama hanyar komawa birninsu suna masu tafiya bisa sirrin alqaluman tsafi, lokaci zuwa lokaci sadaukai sukan yi iface-iface na mazaje dake nuna cewar suna cikin farin ciki.
Da sanyin safiya duk wasu mutanen dake cikin qasar Rumaniya suka fito wajen gari da zumar taryar sarkinsu da kuma dakarunsu waxanda suka yi shekara biyu da fitarsu fagen daga. Masu aure matansu da ‘ya ‘yansu da ‘yan uwansu suka sheqa kwaliya cikin suturu na alfarma suka fito domin taryarsu, kana kallon tsarin birnin Rumaniya zaka san cewar qasace da take da matuqar qarfi da tasiri a duniya. Tana da yawan tattalin arziqi hakan ya saka ta zama zakaran gwajin dafi a faxin duniya.
Gimbiya Laila itama ta fito domin ataryar mahaifinta sarki Rum, kana kallonta zaka shagala da kallonta domin tsananin kyawun da Allah ya yi mata, a wannan zamanin babu wata mace da take da zubin sura da cikar zatti kamarta, ita da kanta tana alfahari da kyawun da take da shi, wannan kyawun bai hana mata koyon dabarun yaqi ba, don haka idan suka shiga fagen fama da mazaje sai ka rantse cewar sadauki ne yake fafatawa domin yadda take da tsananin zafin nama na kai sara da kuma gociya idan aka kai mata sara.
Attajirai da manya sadaukai da sarakuna da ‘ya ‘yansu da yawansu sun mace akan qaunarta, ko wanne a cikinsu burinsa ya mallaketa hakan ya saka aketa faman gwagwarmaya na neman soyayyarta, amma a wajenta bata tsayar da kowa ba domin tace har yanzu bata ga gwarzon da zai yi daidai da ita ba, musamman idan ta tuna cewar ita jaruma ce mai ji da jarumtaka da qarfin sadaukantaka, hakan ya saka ta zama mafi girman kai da taqama, ko shaixan haka ya ganta ya qayale.
Gimbiya Laila bata girmama kowa kuma bata tausayin kowa, sai mutum uku, ita a ganinta duk faxin duniya babu wanda zata girmama sama da waxannan mutanen, daga mahaifinta sai mahaifiyarta cikon na uku kuma abin bautarsu, waxannan su ne suka tsalake siraxin makircinta, wannan halin nata yasa duk wani dake rayuwa a qasar Rumaniya yasan da shi, hakan yasa kowa yake kaffa-kaffa na ganin bai faxa cikin tarkonta ba.
Tana zaune cikin taqama da nuna izza tana sauraron zuwan mahaifinta can sai suka hango su tafe sadaukai sai hargowa suke yi. Nan da nan aka zabura domin taryosa lokaci qanqani suka qaraso gaf da gaf. Sarki Rum yana tsakiya a gefen dama Hamri ne a kuma gefe hagunsa babban sadaukine baban Hamri kowanensu suna cikin shiga ta yaqi da makamai kala-kala a jikinsu ganinsu kawai ya isa saka mai ciki haife abinda yake cikinta.
Fuskar Hamri a murtuke kamar an sassaqota daga ita ce, sai saqe-saqe yake a cikin zuciyarsa,bai saka kwalkwali a fuskarsa ba hakan shi ya baiwa gashin kansa ya watsu sashe zuwa sashe, yana tafiya akan ingarman dokinsa kallo xaya za kai masa kasan cewar cikaken jarumi ne, a shekaru biyu da suka gabata ya kasance mafi qanqanta amma a yanzu ya zama cikaken sadauki da kowa sai ya kalle shi, a yanzu da suka dawo sai idanun jama’ar qasar ya kasance shi kaxai ake kallo.
Gimbiya Laila ta matsa zuwa ga mahaifinta cikin tsananin farin cikin dawowarsa ta rungume shi,sannan ta sake shi tana mai kai dubanta zuwa ga vangaren da sadauki Kamsu yake ta kuma gane ko wane, duk da cewar a lokacin baya data san shi tana da qarancin shekaru, amma ta gane shi da jajayen idanunsa ma su kama da garwashin wuta, da kuma qaton kansa mai kama da masaki, sai kuma tavaven hancinsa mai kama da an yava amala a jikin siminti, duk waxannan kamanin nasa suna nan ba su sauya ba, da su ne kuma ko wanne mutum xan qasar Rumaniya zai gane babban sadauki Kamsu.
Ta kawar da kanta a hankali ta mayar da shi zuwa ga damansa suka yi musayar kallo da shi, taji gabanta ya yanke ya faxi, zuciyarta ta harba a tsakiyar qirjinta, ta shagala da kallonsa tana burin gano ko wane shi a cikin sadaukan qasarsu, amman iya tunaninta ta kasa gane ko waye, don haka cikin izza ta kawar da kai daga kallonsa ta matsa ta shiga tsakaninsu da mahaifinta kafin aka bada umarnin qarasawa cikin birnin.
Suna tafiya a hankali ta sunkuya tace da mahaifinta “Wannan sadaukin a ina ka samo shi?”