FACALA

chapter 33&34

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*


*Wattpad user name*

***


*Arewa book user name*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444


Whatsapp:***

 

*Ummu maher collection👛👠*

***

EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️33 & 34

..........Amrat mawashi, ƴa ce ga Alhaji mawashi shi ɗan asalin jahar katsinane, shararran me kuɗine wanda yasan menene kasuwanci kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suke faɗa aji acikin Nigeria bama iya katsina ba, yana matuƙar son yin mu'amala da masu kuɗi sannan ya tsana talaka ko sunan talaka ma bai son ji, shiyasa ko taimakonsu ma bayayi kuma babu wanda ya ke cin kuɗinsa sama da matansa da ƴaƴansa, sai kuma waɗanda suke musu aiki a ɓoye, wanda babu wanda yasan irin ta'asar da ya ke sai shi kaɗai, sai kuma wani mutum wanda yasan komi nasa, sai dai ya yi shiru ne ba don tsoro ba kowani abu yayi ne saboda talala da yake shirin yi masa.


 Amrat ita ce ƴa ɗaya tilo daya mallaka aduniya, itama sai da suka shafe wasu shekaru kamar shekara 15 sannan suka haifeta, shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗora mata duk abinda takeso shi take samu, shiyasa take taka duk wanda take so babu wanda ya isa ya taka mata burki, sannan babu ta inda ta baro mahaifinta awajen tsanar talaka, shiyasa ma kaf ƙawayenta babu talaka sai ƴaƴan masu kuɗi waɗanda iyayensu suka shahara aduniya ma ba iya nigeria ba.


Amrat ta fara sanin Aliyu ne a ƙasar America, inda taje party ɗin wani abokinta bature, alokacin shi kuma ya fito daga barrek ɗinsu na sojoji, yana training kan hanya ta tsaya har da ɗaukarsa hoto shi bai ma san tana yi ba, sai daga baya sannan yasan tana ɗaukarsa, ya ƙaraso inda take fuskarnan a matuƙar murtuke ya warce camerar ya nunata da ƴar manuniyarsa ya ce" na yi miki kama da mara aikin yi kamar ki? na yi miki kama da wanda yazo shan iska? wannan shi ne warning ɗin da zanyi miki kada ki ƙara zuwa wajen nan don ɗaukana hoto".


 har ya gama maganarsa bata tanka masa ba, kallomsa kawai take ko kyafta ido babu don har ga Allah ya tafi da ita sosai don tunda take bata taɓa ganin mijin da ya ƙwanta mata irin Aliyu ba, tayi yawo sosai cikin ƙasashen da taje babu irin mazan da bata gani ba, amman sai yau Allah yayi ta haɗu dana mijin daya zamar mata gamda katar.


  har ya wuce bata san ma ya wuce ba, sai da ta juyo taga babu shi babu alamarsa, sai ƙamshin turarensa perform me matuƙar tsayawa arai, tun daga ranar ta dinga bibiyarsa har Allah yasa ta gano komi nasa da ƙasarsa da asalinsa har ma da sunansa, ko da ta dawo nigeria sai hankalinta da tunaninta suka fara gushewa, saboda tunanin farin cikinta Abban sojoji malamin soyayyarta wato Aliyu, ko barci ta ƙwanta sai tayi mafarkinsa wai gata ga shi a wani babban falo tana maƙale a kusa dashi suna ta tsinkar fure, idan mahaifiyarta ta shigo tashinta sai kaga har kuka take saboda tsabar azabar da take ciki na son kasancewa da Aliyu.

Mahaifiyarta bata taɓa bata damar wulaƙanci agabanta ba, macece mai matuƙar taka tsantsan da addini sannan tana matuƙar taimakon talakawa, don har sadaka ma take yi duk ranar jumma'ah sannan bata tsaya iya nan ba har gidan marayu tana zuwa ta basu taimako sosai, tun Amrah bata son zuwa har ta koya, domin Hajiya Rabi na tsaye akanta sosai saboda haka duk ƙarshen wata tana janta suje gdan marayu su kai musu goma ta arziƙi, da yawan mutane sun ɗauka Alhaji Kabir mawashi shi ne me wannan taimakon, shiyasa zakaga duk inda ya shiga ana matuƙar girmamasa da ɗaukar komi nasa amatsayar girma da kuma mutuntawa, mutane sun ɗaukesa tamkar wani waliyyi saboda yadda ake ganin matarsa na taimako sosai, don ayanzu haka ma tana da gifan marayu da kuma gajiyayyu na ta nakan ta, itace shugaban ƙungiyar OPHANAGE FOUNDATION GROUP, bama a iya nan ta tsaya ba tana ɗaya daga cikin mata masu matuƙar gyara fannin aure, don duk ranar laraba ana zuwa har gida wajenta don tana da ofishin da ta gina acikin gidanta, na taimakawa mata da kuma matasa zawarawa, da ƴammata har ma da gauraye, kuma tana haɗa aure sosai ƴammata da zawarawa duk tana haɗawa ta bawa miji jari ta bawa matar ma, Hajiya Rabi giwar mata hasken matan arewa, kinga jiya kinga yau zakin mata gagara badau, wannan itace waƙar da alan waƙa yayi mata, da sauran mawaƙan gargajiya da kuma na zamani.



Amrah mawashi irin yaran nanne marasa jin magana sosai, don duk irin ƙoƙarin da Hj Rabi take yi a banza, don duk abinda zata ɗorasa akai mahaifinta zai canja mata layi, idan ma bata yi wasa ba sai kiga abin ya dawo kanta don aƙwai lokacin da Amrah ta fita partyn dare bata dawo ba sai washe gari, ko da ta dawo a buge ta dawo tayi shaye shaye har ta gaji, ranar haɗiyar zuciya ne kawai bata yi ba don ji tayi awannan karon zata iya fito na fito da mawashi, don ko sakinta zai yi sai dai ya saketa amman ita baxa ta yarda rayuwar ƴarta ta salwance ba, aranar ta yiwa Amrah mugun dukan daya sanya ta farfaɗowa daga wannan mayen da take ciki, sannan ta kulle ta a ɗaki ta gargaɗi me aikinta akan kada ta sake ta buɗe mata zataje wajen aiki ne, da yake ƙwararriyar likitan mata ce wacce tasan abinda take, likita me lasisi a jihar katsina har ma da sauran jahohi a ƙasar tamu ta nigeria.


  tana fita Alhaji mawashi ya shigo, ko da ya shigo yaga ba kowa sai ya tambayi me aikinsa ina Lulu?, bakinta yana rawa ta shaida masa komi.


  idanuwansa sukayi jawur, ya dinga zazzaga ruwan masifa har yana iƙirarin zai iya sakinta akan ƴarsa, don shi bai ga amfanin a dinga takurawa ƴarsa agidansa ba, xai iya rabuwa da kowa indai akan Amrah wacce ya ke ce mata Lulu.

aranar sunyi tashin hankali sosai, har sai da ta kai ya saki HJ Rabi ta koma garinsu meduguri ananne fa ta zauna har na tsawon wata biyu, har sai da Lulu ta gaji ta dinga yiwa mawashi kuka akan ya dawo da mom ɗinta, sannan ya je har meduguri yayo biko ananne ta taho da mahaifiyarta saboda ba zata iya ɗaukar rashin mutuncin Lulu da mawashi ba, shiyasa ta ɗakko mahaifiyarta ta dawo da ita gidanta don ta ɗan rage zafi idan tana ganin danginta kusa da ita.


  wannan shi ne taƙaitaccen tarihin Lulu, kuma haryanxu wannan baƙin tarihin nata bai canja zani ba, don kuwa a rashin mutunci ba baya bace komi nata gaba yake yana ƙara tumbatsa saboda gudummawar da take samu wajen mahaifinta.


cigaban labari

Hj Rabi tana ɗaki tana waya da ƙawarta aminiyarta Hj Saudat, sannan matar sarki me babbar masarauta mahaifin Galadima.

 Cikin nutsuwa Lulu ta yi nocking a bakin ƙofar ɗakin, Hj Rabi ta bada damar shigowa ta shigo tamkar mutuniyar kirki, daga ita sai wani sikin tired wanda ya ɗame ta sosai sannan yasha uban crazy wanda har santala santala fararen cinyoyinta awaje suke suna tallam kansu, ta risina ta ce"mom morning".


 ta ɗago cikin nutsuwa ta kalle ta, don mamaki har buɗe bakinta tayi tamkar za tayi magana kuma sai ta kasa don mamaki,Lulu ta ce"Mom daman wata magana nake so muyi don Allah".


 kallon ƴarta takeyi cikin so da ƙaunarta, don tana masifar son Lulu fite ma da mahafinta Alhaji mawashi abinda ke haɗata da ita shi ne rashin mutunci, da kuma rashin girmama na gaba da ita sannan sam bata san komi a addini ba, ko da ta dage akanta wajen koya mata sai kiga mahaifinta ta hure mata kunne taƙi yi, har ta gaji ta koma taya ta da addu'ah.


  ta ce"ina jinki Amrah".


 da yake bata ce mata Lulu acewarta ai ba shi ne asalin sunanta na asali ba, shiyasa ma da tana da yadda za tayi da tuni ta cire sunan don bata sanshi ba tada yadda za tayi ne, don yanzu sai ubanta ya hau mata hauka duk akan Fitinanniyar ƴarsa.


ta ce"mom kin daɗe kina burin kiga na fito da mijin aure, to a wannan karon na yarda zan fito da mijin dana keso amman don Allah inason kuyimin ƙoƙari ya aure ni, wallahi ina sonsa kuma idan ban auresa ba komi zai iya faruwa da rayuwata, please and please mom".


  sosai taji daɗin wannan lamarin, don babu uwar da zata so ƴarta tana da shekaru irin na Amrah ta tsayar da miji har tayi aure, don ayanxu haka Amrah na da shekara 26 ne arayuwarta.


 ta ce"Alhamdh Amrah nayi farin ciki, sai dai inason insan waye mijin da kike son aura ɗin? sannan kuma ina son inasan ki faɗamin gaskiya agame dashi".


 cike da zumuɗi da rawar kai ko kunya babu ta ce"Mom sunansa, Canal A.A ɗan gidan sarkin babbar masarauta, ɗansa ɗaya tilo namiji wanda kuma shi ne magajin sarki ko ayau ya mutu, sannan mom yana da matuƙar son addininsa na musulunci, don a merica na fara ganinsa, sannan nasan mahaifiyarsa ƙawarki ce sosai don har gidansu ma kina zuwa, sai daga baya na tuno ma da hakan".


  da sauri HJ Rabi ta zaro ido cikin tsoro............



***       ***       ***


cikin nutsuwa ya shigo gidan sannan ya nufi ɓangaren kishiyar mahaifiyarsa, ya gaidata cikin mutunci ananne ma take shaida masa za a kawo kuɗin ƙanwarsa Maryam, yaji daɗi sosai don ayanzu dama su uku ne suka rage musu agidan ga kuma abinda yake aikatawa wanda ko kusa baya son yaga an aikatawa nasa ƙannen.

 Duk abinda yake tana kallonsa, yana shigowa ɓangaren Sakina tayi wuf ta je ta faɗa mata ga shinan yana hawowa sama.

yana shigowa ya gaidata cikin nutsuwa, kishi ya turniƙeta ta ce"Amman Ahmad ba kada hankali fa,yanzu sai ka rasa inda zakaje sai ɓangaren kishiyata? ka zauna har awa kusan ɗaya kana zaune kana zuba? sannan duk abinda ka aikata ina sane dashi a'i, kaje gidansu wannan mayyar yarinyar wai ka mayar da ita ɗakinta? saboda ni ban isa in faɗa maka ba kenan? anya kuwa kana neman albarka Ahmad? wato kai da yayanka Xubairu kun zama marasa mutunci ko? sai abinda kuka yi niyya shi kuke aikatawa ko? to wallahi bari kaji idan har ka sake ka dawo da wannan ƴar matsiyatan sai na tsine maka wallahi............"


  ba ma Ahmad ba hatta Sakina dake gefe sai da ta tsorata sosai, da jin furucin mahaifiyar tasu wanda ke nuni da zata iya aikata komi indai har ba a yi mata abinda take so ba.


  cikin rawar baki Sakina ta ce"Hajiya kinsan kuwa abinda kike faɗa?".


 da sauri ta ce" ban san me nake faɗa ba sai kin tunamin"?.


 ai kuwa daya ke bata san gatse ba sai kuwa ta ce" Hajiya ce wa fa kika yi zaki tsinewa ya Ahmad, akan mace zaki tsine masa Hajiya?".


 Hajiya ta buge mata baki tare da ce wa" eh haka na ce uwar iyayi, sai ke kuma? wallahi dukansu sukace ba zasu ji magana ta sai na tsine musu daga shi har yayan na sa".................


  furucinta bai kai ƙarshe ba taji an ce" ke kuma kibi hanyar da kika biyo tun da jajayen sawu ba".


  da sauri ta juya don jin Abinda mijinta Alhaji Badamasi ya ke faɗa, ya ƙaraso cikin falon ya harɗe hannayensa a bayansa ya tako gaf da ita sannan ya ce" bansan ba kida hankali ba sai yau, saboda tsabar rashin hankali kike buɗe bakinki kina ce wa zaki tsinewa yaranki? saboda suna kan gaskiya ke kuma kina kan ƙarya? to bari kiji ni bazan taɓa ɗaukar wannan rashin hankalin na ki ba, zan ki iya bin hanyar da kika fito muddin ba zaki zauna da yaranki lafiya ba, sannan in rabaki da yaran naki kaf ɗinsu".



da mugun sauri ta juyo idanuwanta na zubar da ruwan hawaye masu ɗumi da zafi ta ce" Alhaji akan wannan maganar zaka sake ni? saboda waɗannan mayun shuwa ɗin sun kama ka? shi ne kake ce wa zaka sake ni, to wallahi ko zanyi yawo tsirara Ahmad ba zai dawo da wannan matsiyaciyar yarinyar ba, wacce duk gidan da ta shiga sai masifa da bala'i sun afku agidan".

 tana faɗar hakan ta wuce fu tamkar kububuwa, Alhaji Badamasi ya bita da wani irin kallon banza har yana haɗawa sa tsaki, sannan ya fice shima ya bar Ahmad a durƙushe da kuma Sakina.


Ahmad ya rasa maganar wa zai kama? ta mahaifinsa ko ta mahaifiyarsa, sannan a gefe ɗaya yana jin ko me za'ayi ba zai taɓa iya rabuwa da Rabiatu ba, don shi kaɗai yasan wani irin qualities ne da ita.



***        ***       ***

Sosai Ammi ta gyarani a wannan karon, don har gyaran ƙafa sai da ta kaini akayi min, da kuma gyaran gashi na garari ga kuma gyaran jikin dana sha duk inda na zauna ƙamshi ya ke fita, nasha kitso irin masu mitsi mitsi ɗinnan, wanda ake tsagasu da allura na fito shar dani, sannan aka zanamin baƙin lalle da kuma ja me matuƙar kyau da kuma dacewa da kalar fatata.


 shar na fito a marya, sai dai ƙasan zuciyata na yimin wani irin zillo da kuma wasi wasi musamman akan maganar da Mama uwar gida dana ji suna yi ita da aminiyarta akan abinda suka shiryamin, tuni naji wata irin ƙwalla me masifar zafi ta fara silalomin, na kasa tsayar dasy har sai da suka fara ambaliya don maganganun na su ba suda daɗin ji balle kuma a faɗesu a harshe baki ya ambata su yadda aka zana.............➡️soon.


FACCALA NOVELS FANS

***

/L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


*NABIHA DATA SERVICE*

kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.


MTN

500MB 150

1GB.  300

2GB.  600

3GB.  900

_____

GLO

500MB. 150

1GB.  300

2GB.  5,50

3GB.  850

_________

AIRTEL

500MB  150

1GB.  300

2GB.  600

5GB  1,200

__________

9MOBILE

500MB

500MB 150

1GB. 250

2GB. 450

3GB. 600


Via:-

5458227606

Nabiyyah Aminu

Moniepoint 


my no

***


*MRS GREEN CE*