FACALA

chapter 35&36

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*


*Wattpad user name*

***


*Arewa book user name*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444


Whatsapp:***

 

*Ummu maher collection👛👠*

***

EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️35 & 36


.........ina cikin wannan halin ne Ammi ta shigo ta same ni, hankalinta ya tashi sosai ta kama hannuwana muka shiga har ƙuryar ɗakinta, na fashe da kuka ina me lafewa luf tamkar mage a ƙirjinta, ita kuma tana ɗan shafa baya na har sai dana fara rage bolum ɗin kukan sannan ta ce" ya isa haka Adawiyya, menene ya sanya ki kuka har haka? ki faɗamin kada kiji tsorom komi, don naga kamar aƙwai abinda ya tsorata ki".


  matsawa na yi daga ƙirjinta na koma jikin filom dake manne a gadonta sannan na ce" Ammi wai mi yasa mutane da dama suke ɗaukata a bara gurbi? wai mi yasa tabo baysɗa gogewa ne daga allon ƙaddarar daya zamarwa ko wani ɗan adam tilas? sannan mi yasa wasu mutanen basu tunawa da mutuwa sai son duniya da kyalkyalinta suka sanya agabansu? abinda naji a kunnuwa biyu masu jiyowa kansu hatsari na rayuwa, ya girgiza ƴar ƙaramar ƙwanya ta Ammi, na rasa ma wacce irin addu'ah zanyi domin kuɓutar da kai na, Ammi don Allah ko bani shawarar abinda ya kamata inyi"?. sai na fashe da kuka me ratsa zuciyar me sauraro.


Ammi ta kalleni cikin ɗan jin haushina, sannan ta ce" wai mi yasa kike da zurfin ciki ne? kinsan kuwa hakan zai iya janyo miki ciwo? saboda haka ina umartarki daki nutsu ki haɗa zuciyarki waje ɗaya ki faɗamin abinda ya ke faruwa"?.


  Tayi ƙuri tana kallona babu alamar wasa akan fuskarta, na ɗanji shakkat ɓoye mata don nasan tunda na furta dole sai na ƙarasa wannan maudu'in dana ɗakko, don Ammi babu abinda ta tsana irin ka ha'ince ta a magana ko kuma ka ɓoye mata wani abu, musamman ma akan duk abinda ya shafeni ba ta wasa dashi. baki yana kakkarwa na fara maganar da ta kusa tarwatsa zuciyar Ammi, tuni hawayenta suka ƙame sai idanuwanta da sukayi jawur tamkar gauta.


  "Ammi mama uwar gida da kuma Hajiyarsu Ahmad naji suna hira, wai zasu sanya a haukatani inbi duniya, wai Balaraba Facala ta ita ce zata je wajen boka a basu magani su haukata nabi duniy.........."


  Kasa ƙarasa maganar nayi wacce ta tsaya a maƙogwaro na, saboda wani mugun wahalallan kukan daya ci ƙarfina, samnan Ammi ta dakamin wata gigitacciyar ƙara da ta kusa firgitani tun kafin asirin furgicin haukan ya kamani ta ce"me kike ce Adawiyya? su haukata ki kuma? mi yayi zafi haka? saboda kina auren ɗanta shi ne suke son su salwantar min dake, ke ɗaya tilo dana malakka arayuwata, tun bayan haɗarin jirgin daya mueƙushemin ahalina, mamana baba na, ƙanne na biyu, yayyi na biyu, wa nake dashi yanzu sai kakata da ƴan uwa kuma na dangi, shi ne ake son kema sai an rabani dake to wallahi ina musu albishir da sun taro mach ɗin da bazu su iya buga ƙwallo dasu ba, don kuwa sai na firgita rayuwarsu ta yadda ba zasu ƙara tunanin sanya wani ma ba wata ba a matsala".  tana faɗar hakan taja hannuna na muka fita da sauri ni da ita, ni kuwa sai kallonta nake don ganin inda zata kai ni, sai dai babu damat tambaya? Domin fuskarta a matuƙar haɗe take babu ko alamar giftawar wasa a kyakkyawan fuskarta me cike da sirrin kyau irin na su na shuwa arab.


bata tsaya dani a ko ina ba sai a tsakiyar falon mama uwar gida, tana ganin mun shigo tayi saurin kashe wayar da take, ta bimu da wani irin mugun kallo na tsantsar tsana ta ce"ke kuma meye zaki shigomin ɗaki ki tsayamin akai na tamkar wata sanda"?.


  Ammi ta kalle ta kallon kin rainawa kanki wayo sannan ta harɗe hannunwanta a ƙirjinta sannan ta ƙara wurga mata wani kallo ta ce"ke kina tunanin wannan borin kunyar taki zai yi tasiri akai na? to bari kiji ni a halin yanzu daga ni har ahalina munfi ƙarfinki kuma Allah ya fiki, sannan ni bazan taɓa toma miki asiri ba, idan har halinki ne zaki ce zaki sake ko? to bari kiji ga fili ga mai doki saura sukuwa, sannan ni da ƴata ƙadangaren kan tulu ne, me taɓamu sai ya shirya ke har me kika taka aduniya? kuɗi ko matsayi? babu ɗaya acikin biyun nan sannan kuma maganar da kike na cewa zaku haukatamin ƴa gaki ga ta, idan har ke kin isa kina jin kanki ƙaramar ƴar iska to ki sani ni ɗin dai dai nake da ke, ga tanan gabanki ki cinye ta tsaf kada ki bar ko da romanta".

  ta faɗi hakan tana nuna ta da manuniyarta.


  kunya ta ishi Mama ta kasa ko da ɗago kai, sai dai tsabar jin haushin furucin Ammi sai girgiza ƙafarta take tana ɗan ciccije leɓenta alamar an kai ta bango, sanin idan tayi magana zata tonawa kanta asiri sai tayi shiru tamkar malam yaci shirwa.


hasina, maryam, badi'a, duk suna zaune komi ya faru sai harararmu suke ni da Ammi Hasina ita ce cikakkiyar mara kunya, wacce bata baro Mama a komi ba cikin rashin kunya ta ce" to ai mugun abu kema kina yi, tunda kim juyawa Abbiey hankalinsa baya ganin duk matansa da mutunci sai ke, Allah zai saka musu muguwa azzalu........."

  bata ƙarasa maganar ba Ammi ta sharara mata wani gigitaccen mari, sannan ta nuna ta da manuniyarta ta ce" duk ranar da kika ƙara yimin rashin kunya, sai kin gwammace baki zo duniya ba,banza jahila wacce bata san mutuncin manya ba".

Tuni dukkansu suka liƙe bakinsu, ɗan ƙunƙunin da suke sai suka rufe bakinsu tsaf, ba tare da ko kallon banza sun yi wa Ammi ba, Hasina kuwa kuka ta fashe dashi, da yake mai taurin zuciya ce ta ce"mama kina kallon duk abinda take yi? amman saboda kina jin tsoronta kin kasa magana"?.


  tuni Ammi ta ƙara janyo hannuwa na zuwa ɗakinta, ta jehomin mayafi na ta bani umarnin da in biyo ta,ni kuwa sakin bakina kawai nayi don nasan Ammi aƙwaita da masifar zuciya, matuƙar haƙurinta ya kai bango bata saurarar kowa, shi da kansa Abiey uxuri ya ke mata don yafi kowa sanin wacece Zulaiha.

kiran Abiey tayi awaya, kiran farko ya ɗaga tayi masa dabarun mu na mata, akan tana son taje dani kasuwa don siyo kauan kitchen saboda nawa wasu sun zama tsoffi, ya yarda ɗin kuwa muka tafi tunda muka hau mota babu wanda ya yi magana, har mukaje inda zamuje ɗin babban gida ne mai kusan kusurwa uku sannan yanayin gine ne na ƙasa, amman tsarin gidan ko a fuska yayi min sosai yasha daɓen farar ƙasa, wanda aka yisa a wanacan ƙarnin ko da ba a faɗamin ba nasan ba gine na yanzu ba.

Riƙo hannuwa na Ammi tayi muka shiga cikin gidan, kai tsaye ba tare da ɗar ko wani tsoro ba kamar dai ni yadda nake a tsorace, duk da nasan Ammin ba siyar dani za tayi ba, amman duk da haka a tsorace nake don kunsan mutum baya iya canja halittarsa, ni kuma aƙwai ni da tsoro da kuma rauni sosai.

muna shiga Ammi ta nufa babban sashen daya fi kowanne girma ta nufa tana riƙe da hannuwana har muka ƙaraso.

wani waje ne wanda aka ƙawatashi da lambu, sannan ga ciyawa awajen gwanin sha'awa, sallama Ammi tayi a ƙofar ɗakin, kusan sau biyu sannan aka amsa mata da ta shigo.

muna shiga naji gabana ya faɗi sosai da ganin mutumin dana gani ɗin.................


***       ***      ***

sosai yayi kyaunsa cikin farar shadda ƙal, kasancewar yau jumma'atu babbar rana ne, sai wani haske yake yana haɗawa da walwali tamkar wata acikin zarah.

Dai dai lokacin shamaki ya shigo ɗakin, ya kallesa cikin ɗan son shaƙiyanci sannan ya ce"bro irin wannan kyau haka? tamkar ango? ko da yake ai angon ne ma".

Yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa bai ko ɗago ya kallesa ba, don shi ayanzu mutum tsoro yake basa, ba kuma ya son ya shiga jikin ko wani mahaluƙi a cutar dashi kamar yadda aka yi masa acan baya.Shamaki bai wani damu ba ya cigaba da tsokanarsa har suka fito sallah masallacin dake cikin babbar masarauta, shamaki ya ɗaga wayarsa yana ce wa"to mama gani nan zuwa".

Yana katse wayar ya kallesa cikin girmamawa ya ce"ranka ya daɗe mama ce take son ganina, gashi kuma mun fito sallah ko in ce mata bari muyi sallah?".

Galadima kenan aƙwai sauƙim kai sai dai idan baka zauna dashi ba, zaka iya sanyasa a maza masu matuƙar girman kai da izza, haɗi da faɗa sai dai sam ba hakan yake ba kamar dai abinda ya faru yanzu, bai kalli shamaki ba ya ce"yanzun idan nace maka kace mata sai zamu tafi masallaci sai ka faɗi hakan? uwa tafi gaban komi shamaki, muna iya ajje komi don mu yi mata biyayya indai har ba zai saɓa da ƙa'idar musulunci ba, masallacin bamuyi latti ba don kuwa ƙarfe sha ɗaya ne yanzun, to kaga muna da damar maki wajen yiwa iyayenmu biyayya, saboda haka ka fifita iyayenka sama da son ranka, sai kaga rayuwarka na cigaba duk da awani halin kana haɗuwa ne da nau ikan ƙaddarori da jarabta ta rayuwa". ya ƙarasa faɗar maganar yana ɗan haki, don bai saba magana a jajjere haka ba.

 Sosai maganarsa ta tsaya masa, kuma sai yaji ya ƙara girmama Galadima sosai ashe haka halinsa ya ke? sai ka zauna dashi kake sanin hakan, amman da duk a wani matsayi suke kallonsa na me girman kai da izza da kuma son wulaƙanta mutum, ashe duk wanda kaga ya wulaƙanta wulaƙantacce ne kenan?.

Har suka isa ɓangarensu bai daina satar kallon Yarima ba, wanda ya ƙara masa wani ƙwarjini da kuma girma a zuciyar Shamaki, sai ya ke ganinsa tamkar shi ne sarkin Babbar masarauta.


falon ba kowa, saboda haka shamaki ya ce"ranka ya daɗe ina ganin kamar fa tana ciki, bari in shiga amman ka zauna kafin ta fito".

Galadima ya zauna ɗin kuwa, yana jan kyakkyawar tasbaharsa wacce ba komi yake faɗa ba sai HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL, ƙarfin wannan tasbihin ba kaɗan bane ƴan uwa mu kasance masu faɗar sa akowani yanayi akowacce rana, saboda ka bar kotun duniya ne ka kaiwa Allah kacokan buƙatar ka, sannan ko wanine ya cuce ka wallahi sai Allah ya saka maka, don ita ce fassarar Allah ya isa da waɗansu suke ganin don anyi musu Allah ya isa ai ba komi bane.


  Kusan sakin babban farantin da ta ciko da kaya tai, har sai da ta ɗan saita kanta mamaki take me ya kawo Galadima sashensu? wanda ita dai da wayonta bata taɓa ganin ko da me kama dashi ne ba, sai gashi yau Allah ya kawo sa har hawayen godiya sai da ta yi wa Allah, sannan a ganinta wannan ita ce dama guda ɗaya daya kamata ta isar da saƙonta na soyayya awajen Galadima.

 Kai guy ɗinnan kana da farin jin fa🥳ko zaka ɗan san min nima in yi wa Maher ɗina🧐😂😏, ko da yake ban san me gwaggwala ta jiƙa ta baka ba?🥹


 Karima ta ƙaraso da ɗan sassarfa ta tsugunna har ƙasa tana gaidashi,sai daya kai ƙarshen abinda ya ke ambata a bakinsa sannan ya amsa mata ciki ciki, ko a iya nan ya tsaya ita kam ya gama da ita ga wani irin mashahurin kyau da ta ga ya ƙara mata, tamkar mayen ƙarfe ya haɗa da idanuwansa da nata, haka ta dinga binsa da ido har ta shiga da abincin da ta ɗakko zuwa ɗakinsu.

  da mugun gudu ta ajje farantin, ta hau juyin a ƙaton ɗakin na su tana waƙa tana rawa, ƙawarta da tazo yanzu da ƙanwarta sai kuma Amina yayarta wacce take raye rayenta na ticktok, da sauri ta tsayar da vedion da take ta kalli ƙanwarta karima ta ce"wai ke wata irin mahaukaciya ne? ta yaya ina abina zaki dameni da ihu? sai kace wacce ta zare ko me aljanu"?.

karima ta ce"gaskiya yau ɗinnan haɗa ga garumin paty, don murnar ganin wannan ranar Galadima a falonmu? sannan ya amsamin gaisuwata? i'm happy to day"..

sai ta rungume ƙawarta karina wacce tuni ta kusan suman tsaye don jin sunan wanda aka ambata, bama iya ita kaɗai ba har da yayarta Amina, ita kuwa Karima bata ma san sunayi ba wai kishiya ta saci zanin kishiyarta.😏😂


  mamamsu Shamaki ta fito da fara'arta sosai ta ce" ah yau manyan mutane ne agidan na mu? ina ji idan banyi ƙarya ba rabonka da zama a wannan falon namu tun kana ƙaraminka".

ya ɗan sunkuyar da kansa alamar jin kunya, ta cigaba" Allah sarki yau kuwa daman nake ce wa zan shigo gidan na ku, sai kuma gaka ka shigo zanje wajen matar Turaki ƙanin babanka don mu tattauna kan bikin ƴarta da za'ayi".

Bai ce komi ba, itama tasan halinsa da miskilanci shiyasa bata damu ba, ta dinga sanya musu albarka har suka fito ta bawa shamaki saƙon da zata bashi.


suna fitowa ya ce" wai alkaki ne tayi shi ne ta ce inzo in karɓa da kai na, kasan yaran nan da ha'inci idan ta basu sunci na su kuma sai kaga duk a ɗan bubbuɗe an gitsira shiyasa ma zuwa da kai yafi samuwa.

"uhm" kawai ya ce, don shi abu me zaƙi bai fiya damunsa ba shiyasa Gwaggwala take masa nasa babu suga sai zuma kaɗan da take sanyawa.


  wayarsa ce ta fara ƙara, ya ɗauka kamar baya so ba tare daya ga wanda ke kiran ba, wani mugun daɗi ne ya lulluɓeshi don jin muryar me martaba, har hawayen farin ciki yayi lokacin daya ji yana ce wa" idan an idar da sallah kazo fada ina jiranka".

Sosai abin yayi masa daɗi har ya gaza ɓoyewa ya ce"to na gode ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya".

daga can ɓangaren me martaba yayi murmushi gami da jin daɗin jin muryar ɗan nasa, Allah dai ya sanya sa mugun ƙaunar ɗan nasa, ta yadda duk laifin da yayi masa daga baya sai yaji tamkar bai taɓa yi masa laifi ba.



bayan an idar da sallah ne akace mutane su ɗan tsaya aƙwai ɗaurin auren da za'ayi, haka kawai yaji gabansa ya faɗi ganin me martaba da ƙannensa da kuma mahaifinsu sha maki har ma da waziri suna ƙaddamar da ɗaurin auren daya kusa wucewa da numfashinsa daya fita a hankali hankali............➡️soon

Domin jin cigabansa sai a tsumaye ni ranar asabar. don gobe ba typing sai shiri dana ke gabatarwa a grp ɗina, don jin wannan shirin kao tsaye sai kayi joinin ta grp ɗina💃➡️.

FACCALA NOVELS FANS

***

L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA


*NABIHA DATA SERVICE*

kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.


MTN

500MB 150

1GB.  300

2GB.  600

3GB.  900

_____

GLO

500MB. 150

1GB.  300

2GB.  5,50

3GB.  850

_________

AIRTEL

500MB  150

1GB.  300

2GB.  600

5GB  1,200

__________

9MOBILE

500MB

500MB 150

1GB. 250

2GB. 450

3GB. 600


Via:-

5458227606

Nabiyyah Aminu

Moniepoint 


my no

***


*MRS GREEN CE*