BAQEER

Page 72

by @ayushermuhd

*BAQEER*

*NA*


*UMM ASGHAR*

DA

*AYUSHER MUHD*



*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BIYU*


{72}


(please jiya mune mukai mistake din numbering agun posting yanzu mun gyara asalin 71 mun mai dashi mun bar wannan page din free, sorry for the inconvenience 🙏)


Kallon juna suke yi kowa yana kokowa da abinda yake ji a cikin zuciyarshi, a wannan lokacin kowanensu ji yake yi kamar ya fallasa asirin dake cikin zukatansu ko sun samu suji sauƙi sai dai kowanne da tunanin da yake yi dake taka musu burki wajen amayar da abinda suke ɗauke dashi. Zainab ce ta fara kawar da kanta tana sakin ajiyar zuciya, murya ƙasa-ƙasa tace "Taya za'a yi mu nemeta Ya Baqeer bayan tunda ta tafi bata ƙara waiwayarmu ba tayi aure ta haifi wasu ƴaƴan da take so mu ta manta damu." Murmushi Baqeer yayi yace "Zainab kenan naga alama baki san wacece mahaifiya ba baki san girmanta ba shi yasa kike faɗar haka, idan ita bata nemeku ba kenan ku ba zaku taɓa nemeta ba? Bayan haka kuma kun ji ta bakinta ne kun ji dalilinta na ƙin nemanku da zaku yanke mata hukunci? Haka nan uwa ba zata saki ƴaƴanta ta watsar dasu ba sai da wani babban dalili don haka dolenku ne ku bata dama ta faɗa muku nata side of the story ba wai ku ɗauki fushi don tunda ta tafi bata ƙara waiwayarku ba. Komai na rayuwa ɗan uzuri ne, idan ta rabu daku ku sai ku nemeta kuje inda take tunda itama tana da hakki a kanku, bayan haka ma baku san a wane hali take ciki ba watakila akwai dalilinta na rashin waiwayarku da bata yi ba tun bayan barinta gidanku." 

Jikinta ne yayi sanyi da taji abinda yace, cikin ranta dai ta ƙudurce In Sha Allah zata yi amfani da shawarar shi tabbas lokaci yayi da zasu nemi mahaifiyarsu wacce rabonsu da ita tun suna ƙanana don ita bata jin zata ganeta ma saboda ta bar gidansu lokacin bata fi shekara huɗu zuwa biyar ba.

Har ta koma gida tana auna abinda Baqeer yace a cikin ranta, tana ajiye motarta ɗakin Kabir ta wuce. Murɗa handle ɗin ƙofar tayi ga mamakinta sai ta sameta a buɗe saɓanin kwanaki da sai tayi knocking kafin ya taso ya buɗe. Samunshi tayi yana kwance akan gadon shi yana danne-danne a waya. Zama tayi a bakin gadon tana kallonshi, ita sai taga kamar daga jiya zuwa yau ma har ya ɗan cicciko daga ramar da yayi ta tashin hankalin daya samu kanshi a ciki kwana biyu.

Tashi yayi ya zauna yace mata "Kwanan nan fa kin fara damuna bini-bini sai ki shigo mini ɗaki kamar wacce kika bani ajiya na cinye ban biyaki ba." Hararar shi tayi tace "Au haka ma zaka ce? Yanzu daka samu ka fita daga waccen matsalar shine har kake da bakin yi mini wulaƙanci ko, ai shikenan ni na nuna na damu da kai amma kayi da ƴa." Dariya yasa yace "Allah ke ɗin ce kin fiye damu."

Tashi tayi tace "Ai dai ka tsaya kaji abinda ya shigo dani kafin ka fara wulaƙancin ka daga yau kuma bazan ƙara zuwa inda kake ba."

Da sauri ya riƙo hannunta ganin kamar tayi fushi zata bar ɗakin yace "kefa daɗina dake baki san wasa ba sam, dawo ki zauna ni wasa nake yi miki." Komawa tayi ta zauna ta zuba ido tana kallonshi kamar mai tunanin ta yadda zata fara faɗa mishi shawarar data yanke, sai da taga kamar ya ƙosa da jiranta sannan tace "Ya Kabir nace baka ganin ya kamata ace mun nemi Ummi kuwa? Tunda ta bar gidan nan fa bamu ƙara sakata a idanunmu ba sai ƴan uwanta dake zuwa lokaci bayan lokaci suma ba'a taɓa katarin sun zo sun samemu a gida ba."

Wani irin kallo yayi mata yace "Wace Ummin kenan?"

Itama kallonshi tayi tace "Har Ummi nawa garemu, of course Ummi mahaifiyar mu nake magana akai."

A fusace ya tashi yace "Amma dai baki da hankali ko, matar da tunda ta watsar damu muna yara bata ƙara waiwayarmu ba tsawon wannan lokacin shine kike cewa muje wajenta, to muje wajenta muyi mata me bayan mun girma mun mallaki hankalin kanmu? Tunda ta nuna bata da buƙatar mu a rayuwarta ba shikenan ba muma bama buƙatarta a rayuwarmu sai kowa yayi rayuwarshi yadda yake so babu ruwan wani da wani."

"Ya Kabir mahaifiyarmu ce fa."

Katseta yayi yace "Mahaifiyar tamu, ki fada mini abu guda ɗaya da tayi mana da zai yi nuni da ita ce ta haifemu? Tunda ta bar gidan nan bata ƙara waiwayarmu taga a wane hali muke rayuwa ba, ko halin dana tsinci kaina a ciki ai laifinta ne idan da bata watsar damu tayi tafiyarta ba duk haka da bata faru ba."

Da mamaki Zainab ke kallonshi tace "Ya Kabir wane irin laifinta kuma? Ita tace Nabila ta ƙala maka sharri saboda Allah."

"Idan ma bata ce ba ai dai rashin zamanta damu ne ya janyo don haka ni babu inda zan je kema da zan baki shawara ki ɗauka da nace kada kije don bana jin ko ganinki tayi zata tuna dake don alamu sun nuna ta daɗe da mantawa da ta haifi wasu ƴaƴa data fita ta bari."

Tashi Zainab tayi tace "Ni dai gaskiya to zan je don ban san dalilinta na ƙin waiwayarmu ba tun bayan barinta gidan nan zan je naji ta bakinta kafin na yanke mata hukunci, bayan haka kuma ita ɗin mahaifiyarmu ce da bamu isa mu canjata ba duk kuwa da gatan da wata zata nuna mana ba zai sa ta amsa sunan mahaifiyarmu ba." Daga haka tai hanyar fita daga ɗakin har taje bakin ƙofa sai kuma ta tsaya tace "Kunyi magana da Mumy?"

 tana jin lallai zata je taga mahaifiyarta don sai a yanzu tasan tayi wauta da duk waɗannan shekarun bata taɓa tunanin ya kamata taje inda take taga a wane hali take ciki ba, ba zata iya tuna abinda yasa ta fita ta bar gidansu ba amma tana iya tuna wasu daga cikin moments ɗin su masu daɗi da tsayawa a rai. Takan tuna lokutan da take fita dasu yawon shaƙatawa a motarta ita da Kabir suyi ta faɗa akan wanda zai zauna a gaba, wasu lokutan sai ta hanasu zama gaba ɗaya tace duk su koma baya babu mai zana a kusa da ita tunda faɗa suke yi.

Tana shiga ɗakinta ta hau haɗa kaya a cikin akwati don ta riga ta sawa ranta zuwa Ɗambatta a gobe bata jin akwai wani abu da zai hanata zuwa. Sai da ta gama haɗa kayan tsaf sannan ta ɗauki waya ta kira Daddy don tunda ya fita ya bar gidan jiya bai ƙara waiwayarshi ba. Bata daɗe tana ringing ba ya ɗauka, a shagwaɓe tace"Daddy ina ka tafi tun jiya ban ganka ba?"

Da kulawa yace "Raina ke ɓaci idan ina cikin gidan Zainab shi yasa na kauce har sai na huce don kada na yanke hukunci a cikin fushi daga baya nazo ina dana sani." Ɗaga kanta tayi kamar yana ganinta tace "haka ne kuma, Daddy dama zan faɗa maka ne gobe ina so zan je Ɗambatta na kwana biyu."

Shiru yayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin yace "Ɗambatta kuma? Lafiya dai ko?"

"Lafiya lau Daddy kawai dai ina so naje ne don Allah kada kace a'a," tayi maganar cike da shagwaɓa. Samun kanshi yayi da kasa musa mata duk da ba son zuwanta Ɗambattan yake yi ba bare da mutanen suka nuna mishi ba mutanen kirki bane su amma ba zai yiwu ya cigaba da hanasu zuwa wurin dangin mahaifiyarsu ko gunta ba don haka yace mata sai ta dawo amma kada ta daɗe. Da murnarta ta ajiye wayar har da ɗan tsallenta don bata taɓa tunanin Daddy zai amsa mata da wurwurii haka ba ta ɗauka hanawa zai yi kamar yadda ya sha yi a baya idan ta nuna tana son zuwa wurin mahaifiyarta.

Ƙara ɗaukar wayar tayi ta turawa Baqeer saƙo. "In Sha Allah gobe zan je Ɗambatta, nagode da tunatarwa."

Ajiye wayar tayi ta tashi tana ƙara duba ɗakin ko da akwai abinda take buƙatar ɗauka kada ta manta. Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, kallo ɗaya Zeey tayi mata ta juya ta cigaba da abinda take yi. Jikinta ne yayi sanyi ganin irin kallon da Zeey tayi mata. Ƙarasa shigowa tayi cikin ɗakin ta zauna a bakin gado tana bin yadda Zeey ta barbaza kaya a cikin ɗakin da kallo. "Wani wuri zaki je ne auta?" Ta tambayeta tana ƙara bin ɗakin da kallo.

Ɗan taɓe baki tayi tace "Um," kawai ta cigaba da abinda take yi. Kallon Zainab tayi tace "kema kina jin haushina kamar Daddy ko? Shi yasa kika daina kulani." Wani irin kallo Zainab tayi mata da itama bata san tayi ba har ta buɗe baki zata bata amsa sai kuma taji ba zata iya ba kawai tayi shiru, har yanzu ta kasa gane dalilin Mummy na ɓoye musu Nabila ƴarta ce bayan duk wannan tsawon lokacin da aka ɗauka, to da ace haka bata faru ba baza ta taɓa sanar musu ba kenan ko me?

"Ki bani dama nayi miki bayani," katseta Zeey tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tace "Bani zaki yiwa bayani ba Mummy don ba zamana kike yi ba a gidan nan mijinki ya dace ki yiwa bayani bani ba." Daga haka bata ƙara bi takan Mummy ba har ta gaji da zaman ɗakin ganin da tayi Zeey ba zata kulata ba yasa ta tashi jiki a sanyaye ta bar ɗakin.


*****

Kwanakin nan bata cikin nutsuwarta saboda ta daina samun Bello a waya ko zata kwana tana nemanshi wayarshi bata shiga, babbar damuwarta yadda kusan komai nata ya ƙare saboda dama ba wata sayayya suka yi mai yawa ba tunda dama a tsarinsu baza su daɗe a ƙasar ba shi yasa suka sayi kayan abinci na adadin kwanakin da suke saka ran zata yi anan kafin ta bishi to gashi kwanakin har sun haura ita bata bishi ba sannan kuma bai turo mata wasu kuɗaɗen da zata sayi wasu kayan buƙatun ba. Tana kwance a parlourn ta wurin yayi kaca-kaca don tun bayan barin Habi gidan bata ƙara saka tsintsiya da sunan shara ba, komai taci anan wurin take barin shi bata ɗaukewa don haka parlourn ya cika da ƙazanta. A gefe ga farantan da take cin abinci nan sun yi tsibi guda don ko su bata iya kawarwa sai dai idan tayi amfani da wani ta ɗora shi akan waɗanda ta tara, ga ledojin tarkacen kayan ciye-ciyenta nan da ribobin lemo da ruwan da take sha sun haɗa wata ƴar ƙaramar bola. Ita kanta idan aka kalleta ba za'a so sakewa ba don ga dukkanin alamu tayi kwanaki jikinta bai ga ruwa da sunan wanka ba, gaba ɗaya tayi biji-biji da ita duk ta fita daga hayyacinta.

Tana kwance tana danne-danne a waya ga alama ita wannan bolar data haɗa bata damunta don chatting take yi da sababbin ƙawayen data yi tana murmushi don sai fasa mata kai suke yi suna cewa ai sun ɗauka da suka jita shiru kwana biyu ko har ta tafi ne babu labari. Turo ƙofar yayi ya shigo parlourn bakin shi ɗauke da sallama yana rataye da jakar matafiya a kafaɗar shi sai akwatin trolley da yake ja a ɗaya hannunshi. Sallamar da yayi ce ta maƙale mishi a maƙohgaro ganin parlourn kamar ba nasu ba, fita yayi ya duba yaga tabbas gidan ne dai ya shigo don haka ya koma ciki yana ƙarewa parlourn da alamu suka nuna kamar babu mutum ɗin dake rayuwa a ciki. A kwance akan doguwar kujera ya ganota. A fusace yace "Asiya miye haka?" Yana nuna tsakar parlourn da hannu. Wai sai a sannan tasan da shigowarshi cikin gidan don hankalinta gaba ɗaya ya ɗauku ga wayar da take dannawa ko kusa bata ji motsin shigowarshi ba. Miƙewa tayi tsaye fuskarta ƙunshe da mamakin ganinshi a daidai wannan lokacin da bata yi zato ba tace "Bello! Saukar yaushe?"

Bin jikinta yayi da kallo sai yaji ranshi ya ƙara ɓaci, bsyan ƙazantar gidan har ma jikinta ba zata iya tsayawa ta gyara ba. Tsaki yayi kawai ya wuce ciki ya barta anan. Bin bayanshi tayi sai ta ganshi a tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo. "Tafiya babu sanarwa Bello, hala kazo ka tafi dani ne. Kamar kasan dama na gaji da zaman ƙasar nan wallahi duk na matsu na bika ashe ma kai da kanka zaka zo mu tafi shi yasa bana samunka a waya."

A fusace yace"Dallah Malama yi mini shiru, a hakan zan kwasheki na fita dake ƙasar waje kina zuba wannan uwar ƙazantar, kalli jikinka saboda Allah ki duba muhallinki kamar ba gidan amarya ba komai ya fita daga hayyacinshi tsabar ƙazanta." Kallon kanta tayi ta kalli ɗakin data manta yaushe rabon da a gyara a hakan ma wai shine mai ɗan dama don ba kasafai ta cika shigowa nan ɗin ba, cewa tayi "ya kake so nayi saboda Allah bayan nace maka zan nemo mai aiki saboda aikin yayi mini yawa bazan iya ba kaƙi amincewa."

Ajiye kayan hannunshi yayi zai fita daga ɗakin tace "To yaushe zamu tafi don na fara shiri?" 


Wani wulaƙantaccen kallo ya wata mata yace "Ina? Ai babu inda zamu don nima na dawo kenan," kawai ya fice ya barta a ɗakin.

Bin bayanshi Asiya tayi da kallo hankali a tashe tace "Iyyeee.......Bangane ba ba inda zamu je a ina? Ni kaga bari nazo na tattara kayanmu."

Tsaki yai kawai ya cigaba da tafiya, kallan mamaki ta bishi dashi ai ko za'a mutu sai ya fitar da ita daga kasar nan, tab ai bataga yban daya isa ya hanata ba....


Mukam mukace to ga fili ga doki🥴





*


*

*Ayusher Ce*

    *Da*

*Umm Asghar*