48
by @faddabanan
Washegari kafin naje aiki, sai da na biya ta gidansu neman shi amma maigadin yace mun yallaɓai tun shida da rabi na safe yayi masu sallama, Sa'adu direba ya kai shi filin jirgi. Kafin kuwa na ƙarasa wurin aiki nayi dama-dama da hawaye, ga azumi da ƙunan zuciya sannan ga nadamar me yasa na faɗi abinda ba ya so. Ina ma laifin shi da ya neme ni? Ji nake kamar na dawo da hannun agogo baya domin na canza abinda na faɗa. Ya ƙi daga waya ta sannan ya sauke lambar shi daga WhatsApp ta koma irin lambar da ba'a yi wa register ba.
Har azumi ya kai ƙarshe ba Nu'uman babu kalar shi a Kano. Tun bayan neman da nayi masa farkon fushinsa ban ƙara ba, to nayi ta kira ya ƙi ɗauka watau ya bar ni na ƙarata kenan. Hakan ya sa na tattara sauran kima da daraja ta da tayi saura na daina neman sa duk kuwa da cewa wahala nake tayi akan tunanin sa, fata kawai nake yi na manta da shi. Ƙarfin addu'a ta a tahajjud kuwa shine "Allah ka kawar mun da Nu'uman daga zuciya ta idan har hakan ne ma fi alkhairi." Kuka iya kuka nayi, na ɗauka yanzu na zama jaruma, amma komai na Nu'uman ya zama sabo a wuri na.
Da sallah ta zo sai na tsiri yawo sosai domin neman distraction nake daga tunanin Nu'uman, har wurin da na fi shekara goma ban je ba sai na kai ziyara. Yawon yana mun tasiri ne kawai da rana lokacin ina cikin jama'a domin da zarar na kwantar da haƙarƙari na da daddare, sai tunanin Nu'uman ya sauko mun ya hana ni kataɓus. Yawan gajiyar da nayi ne kawai ya ke rage mun lokacin tunanin.
Jarabawa ta ma sai dai Allah ya kiyaye abun kunya kawai, domin ba wani mayar da hankali nayi akan ta ba komin hoɓɓasar da na yi. Don da aka kafe result ma maimakon first class da na saba samu, wannan karon da second class upper na tsira.
A lokacin da muka cika wata uku da rabuwa da Nu'uman annual leave ɗina daga wurin aiki ya samu. Duk da cewa makaranta ba mu daɗe da fara zango na biyu na mataki na uku ba, sai kawai na yanke shawarar tafiya gidan Yaya Naziru, har yau ba su samu damar zuwa Kano ba kuma ga alƙawarin da nayi wa Surayya kwanaki can. Kawai na sawa raina tafiyar a wannan lokacin ne saboda canjin wurin zama yana rage damuwa, kun ɗauka don an yi wata uku na manta da Nu'uman ko? Kawai dai na samu sauƙin zafin zuciya ne kaɗai amma ko sau ɗaya ban ƙara ɗaga ido na kalli wani namiji da har ya burge ni ba.
Ranar da na buga waya na faɗa wa Surayya zuwa na, murna kamar ta fito daga cikin wayar ta rungume ni, tace zan zo ma a daidai domin hutu take yi na aiki. Kasancewar ban taɓa hawa jirgi ba gudun kar na kwafsa, sai kawai nace ta mota zan tafi duk ina da bala'in tsoro amma haka na dake. Mama kuwa ta hau haɗa mun kayan tsarabar da zan kai masu kala-kala, duk wani abu da ta san Yaya Naziru na so sai da aka tattara mun sai kace shi kaɗai ne ɗan ta. Hussein, Mama har da Baba suka raka ni tashan mota da yamma. Sanadin tafiya ta Legas sai kawai aka haɗa ni da aikin yin jakunkunan da sauran wasu kayayyakin da za'a raba da bikin Hassana daga can. Biki kam ya ƙarato don ma an ɗaga sai zuwa bayan babbar sallah ne, don yanzu abinda yayi saura bai wuce wata ɗaya ba.
Baccin da ake yi a mota ni kam kasawa yi nayi don zan iya cewa ido na kusan biyu muka isa Legas, a tashar na iske Yaya Naziru ya zo ɗauka ta. Dukkan mu sai murnar ganin juna muke har ina tsokanar shi da cewa ya fara tumbi.
Girke-girke na tarar kala-kala Surayya tayi mun a matsayin na karin kumallo a faɗar ta, bacci da gajiya ne suka fi damu na don haka kaɗan na ci abincin, nayi wanka na kwanta sai bacci. Yaya Naziru ne ma ya matsa mun dole na tashi daga baccin wurin ƙarfe biyu da rabi, sai da nayi ƙasaru ta azahar sannan na zo tsakiyar su na zauna ina ta basu labarin 'yan gida bayan na fiddo masu tsarabar su.
Bebin su kamar ni ce na haifi yarinyar nan, muna matuƙar kama sosai da sosai. Tunda na iso Legas ba mu da aiki sai yawon zagaya gari, amma kafin nan sai da muka fara zaɓo jakunkunan biki sannan muka bayar da aikin buga masu sunaye, an haɗa da kofuna, plates, agogon hannu da na bango da wasu 'yan cute abubuwa dai haka.
Ranar Lahadi Yaya Naziru ya kwashe mu zuwa bakin beach, abun ka da ba-sa-ban ba haka na dinga zagayawa, wani irin farin ciki da rabon da na ji shi har na manta ya dinga shiga ta. Su kuwa duka suna zaune suna yi mun dariya alamun sun saba zuwa kenan, Adil (ɗaya daga 'yan biyun Surayya) da ya biyo ni shi ma ya koma yayi zaman shi.
Ina zagaye na naji gaba na yana faɗuwa, har sai da na tsaya ina maimaita innalillahi tare da riƙe ƙirji na. Kawai na ji Nu'uman ya faɗo mun a rai, sai na hau dube-dube ko Allah zai sa na hango shi tunda su ma a Legas ɗin suke, amma hakan na gaji da dubawa na haƙura. Har muka dawo gida kallon titi kawai nake yi ko zan hango shi. In banda ni ma, ta yaya zan iya ganin Nu'uman a titin garin Legas? Ƙila ma baya garin a daidai wannan lokacin. Har da coat ɗin shi na taho a cikin kaya na, yanda zan samu dalilin da zan yi masa magana ko da Allah zai haɗa ni da shi.
Zama na a Legas, zama ne irin na wanda ya je hutu wani wuri, don in ban da girkin dare da nake yi masu ba ni da wani aiki sai zuwa yawo da wuraren shaƙatawa suna nuna mun gari, amfani tafiya kenan dama. Ji nake kamar kar na dawo Kano. Tare muke zuwa kasuwa siyayya, abun mamaki da dariya irin yadda naji Surayya tana yarabanci, ni mamaki abun ya ba ni ma.
Yanayin garin Legas na wannan lokacin ruwa ne, shi yasa ranar da za mu je cefane sai muka bar Ummi (sunan da ake kiran bebin Surayya da shi, da yake sunan Hajiyarsu ta ci) da 'yan biyu tare da Yaya Naziru a gida, muka hau motar haya muka tafi. Ni ta ba wa lema na riƙe mana amma wurin jiran ta ta fito mu tafi sai na manta ta a wurin da na zauna a falo. Sai da aka fara ruwan na tuna, haka kuma muka dinga yawo a ruwan duk da dama ba wai ya tsuge ba ne. Sai da kasancewar sanye nake da yadin material sai duka ya manne a jiki na don haka na samu wuri na zauna a shagon wata mata da suka saba da Surayyan, a yayinda ta je ta ƙarasa siyayyar sai ta dawo ta same ni domin komawa gida.
Muka zo bakin hanya jiran abun hawa, ga kaya. Mun daɗe muna ta jira kasancewar yamma tayi mafi yawan ma'aikata sun taso, holdup ya haɗe ko'ina. Jiki na ne ya bani ana kallo na daidai lokacin da Surayya ta samar mana abun hawa, na juya sai na ga wasu maza gefe na har muna haɗa ido da ɗayan, don haka sai nayi tsaki na shiga abinda zai kai mu gidan. Nasan mannewar da yadin yayi a jikina suke kalla, amma kuma sai na ji kaman na ga fuskar sani, na ƙara waigawa na kalle su amma tabbas su duka biyun ban san su ba.
Har na gama girkin dare, tunda Yaya Naziru ya tafi sallah ban ƙara jin duriyyar shi ba har ƙarfe tara ta gota. Surayya na tambaya ko lafiya, tace "Baƙo yayi fa, kin ga yanzun nan ma yayi mun waya a miƙa masu abinci, bari na miƙa masu na dawo ki bani labari." Ko da ta dawo, mu ma bamu jira komai ba muka ci namu abincin. 'Yan biyu nan kan kujera suka zuɓe suna bacci, sai na taya ta kwashe su zuwa ɗakin su.
Lokacin da ya dawo ciki, cewa yayi naje na kwaso kayan abincin da aka kai falon waje. Ni bansan me ke faruwa da ni ba yau don gabaɗaya jiki na babu laka, don sai da na zauna a falon ma ina shaƙar iskar wurin kafin na ƙarfafa jiki na na tattare kwanuka zuwa cikin gida. A kitchen ɗin ma duk da nauyin da jikina yake mun sai da nayi wanke-wanke. Kafin na kammala kuwa tunani ya ɗauke hankali na. Ni yanzu ba abinda nake so irin na gan ni tare da wanda zai kula da ni nima na kula da shi, amma tun bayan Nu'uman na kasa kallon maza a matsayin maza balle ma zuciya ta ta amshi wani. A watan ukun nan akwai mutum biyu da suka so shiga rayuwa ta, amma sam na kasa ko da basu damar a dinga gaisawa ne, ɗayan da yake ɗan rainin wayau ne ma har da sa mun suna 'Ice queen' saboda a cewar sa ba wani abinda yake moving ɗina har yana faɗin duk efforts ɗin mutum a kaina yana zuwa wurina zan yi freezing ɗin shi. To ni Ummu ina da rabon aure a duniya kuwa? Ko dai ƙadaddarar rayuwa ta shine na yi soyayya amma ba ni da rabon zama da wani? Wannan tunanin ne ya hana ni saurin kammala aikin da nake yi a kitchen, na sa hannu na goge hawayen fuska ta tare da wankewa fuskar sannan na fito na dawo falon. Ganin irin kallon da Yaya Naziru da Surayya suke yi mun ne ya sanya ni murmushi ba shiri, ban tsaya wata-wata ba na yi masu sai da safe. Daga gani wata hira suke yi da ta shafe su, ina jin sun mance cewar ina gidan. Soyayya manya!