50
by @faddabanan
Asma'u ce take ta damun Anti sai ta tashi ta koya mata pancake, ita shi take so ta ci yanzu. Ita kuma Anti tace sai dai a jira sai bayan Papa ya dawo ta gama abinda take yi kafin ta koya mata. Ni dama dauriyya nake yi zaman wurin, don haka sai nace mu je kitchen bari na koya mata. Umma da Anti sun so hana ni, wai daga zuwa a matsayin baƙuwa kuma sai kitchen? Sai da na nuna masu nan ɗin ma ai gida ne sannan suka haƙura.
Mu uku watau ni, Jamila da Asmaa ne muka shiga kitchen ɗin. Su duka biyun gwanayen hira ne sai kawai muka saje muna ta surutun mu. Pancake 🥞 ba wani wahala ne da shi ba, amma sam sun ƙi bari nayi komai, daga na ɗaga abu sai wani a cikinsu ya karɓa yace na faɗi yanda za'a yi kawai. Ana la'asar muka kammala, Asmaa ta ɗauko plate da sauri ta ɗiba ta zuba mashi zuma a take ta fara cin abun ta, har da kai wa Anti wai ta ɗanɗana nawa ba irin na ta ba ne, ga shi yayi looking so fluffy maa shaa Allah. Ɗakin su muka shiga domin sallah, Ya ilahi! Ɗakin ya yi bala'in kyau, kamar na saka a jaka na tafi da shi. Wow!
Da muka idar da sallah nan muka baje abin mu ba wanda ya koma falo. Ina ta kallon hotunan Jamila, wai watan nan da ya ƙare ta kammala bautar ƙasa, su kuma sun tafi wanka a faɗar su yau me wankan la'asar ce, har ina tsokanar su da cewa wankan ƙazamai kenan ana dariya.
Ko da suka zauna suna shiryawa, kayan kwalliyar su kawai nake kallon yawan su. Abun har ya taɓa raina ganin ni bani da damar da zan yi kwalliya yanda nake so kamar ƙannen shi. Idona ya sauka kan foundation ɗin da Asmaa za ta yi amfani da shi, da sauri na tsayar da ita da cewa Asmaa wannan foundation ɗin ba irin na fatar ki ba ne duk da yana hawa, ya fi dacewa da Jamila.
Jamila tace "Ni gani nake kamar yayi mun duhu."
Nace a'a, mu ga irin wadda kike amfani da ita. Ta miƙo mun, ina kalla nayi murmushi nace wannan ne daidai, don wannan ke ma Jamila ta fi dacewa da fatan Asmaa. Ku yi canji kawai. Abinda na faɗa kuwa haka ne, don ta nuna a fatar su bayan sun shafa ɗin. Haba mana, ni rainon Rahinatu ce a wurin kwalliya, ai kuwa babu ta wurin da za'a kayar da ni a yanzu dai kam, ƙila sai gaba idan wasu sabbin kayan kwalliyar sun bayyana. Hakan ya daɗa sanyawa ta mu tazo ɗaya da su.
Sai biyar Nu'uman ya leƙo ɗakin, a zaune ya iske mu mun baje muna kallo ga lemona da biscuits kala-kala zube gaban mu. Ni ban ma san wurin da na zubar da ɗan kwali na da mayafin ba. Asmaa gabaɗaya ta fi mu gashi, ni kuma na fi Jamila. Ya kalle mu yace "Yanzu ɓata mun ita za ku yi da ciye-ciyen kayan zaƙi ko? Yanzu ma za mu tafi ai."
Su Jamila sai roƙon shi suke yi ya bar ni ko nan da ƙarfe shida ne. Shi kuma yace "Anti zan kai wurin Papa, yace yau zai bar gari, kuma kun san akwai holdup tunda yamma ta riga ta yi balle na bar maku ita, na je wurin Papa na sake dawowa ɗaukar ta."
Asmaa tace "NB don Allahhhhhhh, mu gaskiya in-law bata ishe mu ba."
Ya amsa "Kar ku damu, abinda taku ce? Ummu yi maza ki shirya nan da minti goma za mu tafi." Ya fita tare da rufe mana ƙofar. A take kuma na miƙe na kimtsa jiki na, muka dawo falo tare da su. Chocolates da biscuits suka tara mun a leda, duk da ina ta faɗin cewa su bar shi don a kunnen su yayansu ya gama ƙorafi, sai Asmaa tace "Ki ƙyale NB ki karɓi abun mu, idan ba ki karɓa ba kya son mu yanda muke son ki. Ko Jamila?" Ta juya wurin 'yar uwarta. Umma ma ban san me ta bani ba, domin shi ta miƙawa tace ya riƙe mun, har bakin mota su duka suka rako mu.
A mota ma ban ji nauyin Anti ba, domin sakewa sosai nayi da ita sosai. Ita ce ma ke mun bayanin wuraren da muke wucewa. Har muka ƙaraso wurin da za mu zo watau El Bashir Travel and Tours. Mamaki ne ya kama ni, ashe suna da wani a Legas. Babban wuri ne, ginin kan shi yayi fasali ba da wasa ba kuma bambancin sa da na Kano kamar Wudil da Abuja ne. Muna shiga ciki yace da Anti ta yi gaba ta fara samun Papa, bari ya zagaya da ni naga wuri. Kai anya ma Wudil da Abuja da na kwatanta ban yi son kai ba?
Muna zagayen ne na tambaye shi ko Papa baban su ne. Ya ɗan kalle ni kaɗan ya cigaba da tafiyar da muke yi yace "Papa ne ba ki sani ba? Au! Ashe da Yaya Bashir kike kiran shi ko?"
Cikin zumuɗi nace au wai Yaya Bashir ne dama? Kai ni mu gaisa, yaushe rabon da na gan shi?
Ya dakata da tafiyar ya juyo ya kalle ni bayan ya ɗan ɗaga girar shi ɗaya yace "Yanda kike yi yanzu haka sai a yi zaton ke ma ɗaya daga cikin 'yan matan nan ne masu bin shi." Ya yi murmushi kafin ya cigaba da faɗin "Na so a ce ni ma irin charm ɗin papa ne da ni, da na hautsina marasa aikin yi, shi kuma sai yayi ta sharewa kamar ba ya ganewa." Sai na harare shi jin abinda ya faɗa.
Sai ya fara dariya sannan yace "To me nayi kike harara ta?"
Na kalle shi nace shi yasa da Umma tace ba ta ɗauka miskilancin ka yana barin ka kula 'yan mata ba abun ya ba ni mamaki, don nasan kana mun magana sosai ba yanda suke tunani ba. Amma dai maganar gaskiya ka yi kama da players. Na ɗan matsa baya ina cigaba da kallon shi.
Dariya mai sauti yayi "Yanzu Ummu ni kike yi wa sharri irin wannan? But on a serious note, I'm always comfortable around you. Sai na dinga jin kamar da gangar jikina nake magana, so magana ba ta mun wahala in dai da ke ne." Ya juya domin ci gaba da tafiya yace "Mu je na kai ki wurin shi, nasan yana ta buɗe ido ya ga wace ce in-law ɗin ta shi don bakin Anti ba ya shiru."
Nu'uman ne ya fara shiga ofis ɗin, ni kuma na ɗan dakata ina gyara mayafi na. Ina jiyo muryar Yaya Bashir yana cewa "Ina in-law ɗin? Na ji ance tare kuke." Da murmushi a fuskata na shigo ofishin tare da sallama, yana gani na ya buɗe ido yace "Ummu? Dama ke ce surukar tawa? Ashe zan ci gashin kifi na more, gara da ka samo mun baiwa ai Nu'uman." Dukkannin mu muka fashe da dariya.
Anti ce ta tambaye shi a ina ya san ni? Shi kuma yace "Ita ce mai yi mun girki idan naje Kano. Kin tuna akwai wani dambun kifi da na kawo wa su Baby da na biyo Kaduna daga Kano? Wanda suka dinga damu na yaushe zan ƙara kawo masu? To ita ce" Mu ɗan ɓata lokaci anan, har sai da muka yi sallar magriba sannan Nu'uman yayi shirin mayar da ni gida. Anan muka bar Anti, idan sun ƙarasa abinda ya kai ta, direba zai mayar da ita gida.
Akan hanyar mu ta tafiya nake tambayar sa me yasa 'yan gidansu suke kiran shi da NB, haka ma waɗannan 'yan matan da na gan shi tare da su a Kano.
Ya san bayani nake nema akan 'yan matan da na gan shi tare da su rannan, don haka ya amsa ba tare da ya ambace su ba, yace "Suna na ne mana. Nu'uman Bashir."
Ni ko lokacin da na duba international passport ɗin shi hoton shi na kalla sai date of birth ɗin shi, ni ban wani tuna ainihin sunan shi na jiki ba. Na maimaita Nu'uman Bashir? Amma tsaya Yaya Bashir fa?
Yayi ƙaramar dariya yace "Bashir Bashir. Sunan baban mu gare shi, shi yasa kowa a gidan yake kiran shi Papa."
Baban ku fa? Shi yana ina? Ya ɗan yi shiru sannan yace "Ya rasu shekarun baya." Sai ban ji daɗin tambayar da nayi ba, don haka a sanyaye nace ayya! Allah ya jiƙan shi da Rahma. Allah ya haskaka ƙabarin shi ya kuma sanya shi a aljannatul firdaus. Sai amsawa da ameen yake tayi, da gani yana matuƙar jin daɗin addu'ar, da alama suna da kusanci na sosai da baban nasu.
Sai na haƙura da duk wata tambaya na juyar da kaina ina kallon titunan da muke wucewa. Hannuna da tun tahowar mu yake riƙe a nashi ya ɗan matsa a hankali domin maido hankali na gare shi yace "Ba su kaɗai ba ne tambayoyin ki, ƙarasa kawai."
Ina dariya nace ta yaya ka gane don Allah? Ya amsa "Zuwa yanzu nasan Ummu da yawa ai, cigaba ina jin ki." Ganin na samu dama sai na ɗora da cewa kenan sunayen travel and tours ɗin nan..... Ya katse ni "Sunan baban mu ne ba na Papa ba."
Na ɗan yi shiru kaɗan sannan nace kwanaki can baya da muka samu matsala, me yasa kayi tunanin space nake buƙata?
Ya ɗan matsa hannu na sannan ya amsa "Ranar da kika fara abun naki da daddare, watau ranar da kika ce ba ki da chaji, Generator ya lalace kuma babu wuta, duka ina tsaye a ƙofar gidan ku. Neman yanda zan samu Hussein nake tunda na kasa samun ki ta waya. Ina kallon wuta a gidan ku, don haka sai na tafi na zuɓa maki ido in ga iya gudun ruwan ki."
Na buɗe baki zan sake tambaya amma sai ya riga ni magana yace "Don Allah Ummu idan abinda ya danganci saɓanin mu za ki tambaya kar ki yi, ya riga ya wuce, nasan na sha wahala fiye da tunanin ki...."
Da sauri na katse shi da faɗin wahala fa? Ai ba ka kai ni ba! Na yi kuka kamar raina zai fita. Na kira ka a waya sam ka ƙi ɗauka. Washegari har gidan ku naje da rana, maigadi yace mun jirgin safiya ka bi ka koma Legas, duk ka sanya na rame... Na zumɓura baki.
"Ai ni kiran wayar da kika yi mun na ɗauka so kike yi ki ƙarasa faɗar abinda ba ki samu damar faɗa ba, sannan wahala kam ni nasan halin da na shiga, ni da kika sa na hauka ce da aiki saboda na manta da ke? Rama kuma kar ki damu, zan ciko da ke kwanan nan." Abun sai ya ba ni dariya nayi ta ƙyalƙyalawa. Har daina kallon titi yayi ya juyo ya kalle ni, wai dariyar kyau tayi masa sosai.
Gab da zai sauke ni gida na tambaye shi abinda nake ta son na tambaya tun kwanaki, me yasa ba ka faɗa mun matsayin Asmaa a wurin ka ba? Duk a zato na na ɗauka budurwar ka ce, ka ja nayi ta kishi a banza.
Murmushi mai sauti yayi yace "So nake yi ki gani da idon ki, sannan kuma...err.....err....."
Na amsa err me?
Yace "Ina jin daɗin ganin kina kishi na because you are not an easy person to read, mutum bai san matsayin shi a wurin ki ba, sai ki dinga ba ni mixed feelings, sai na ji kaman ana so na sai na ga kamar ban gane sosa....." Jaka ta na buga masa a kafaɗa, hakan ya sa ya yanke maganar da yake yi ya fara dariya. Ko da ya sauke ni a gida, bai tafi ba sai da ya ga Yaya Naziru sannan.
Rabo na da farin ciki irin na ranar har na mance ma, tunda nayi wanka nayi sallar isha'i sai nayi zama na a ɗakin da na sauka na ƙi fitowa yi wa su Yaya Naziru hira. Wurin ƙarfe goma sai ga kiran Nu'uman, ya kuma shaida mun cewa aiki zai fara cuɗe masa daga gobe, ba mamaki ba zamu haɗu ba a ragowan kwanakin da suka rage mun a Legas ba. Amma tabbas zai zo Kano ko kwana ɗaya yayi mun idan ya dawo.
Ai kuwa hakan ce ta kasance, sai waya, ita ma ɗin ba kowanne lokaci ba don ko na kira bana samun shi sai dai idan shine ya kira ni, shi ɗin ma da wasu layuka daban ba wanda nasan shi da shi ba, sun fi kama da international number.
Ledar chocolates ɗin da su Asmaa suka ba ni na bar wa 'yan biyun Surayya. A cikin ledar Umma kuwa super exclusive ce guda uku, don haka na ba wa Surayya ɗaya, ragowan kuma na haɗe su a cikin kaya na. Yaya Naziru ya dage na hau jirgi wurin komawa, amma na dage kawai ni mota zan bi na koma, ga uban kaya na loda zan koma da su.
Bayan sun kai ni tasha, Yaya Naziru ne ya tsaya sai da ya tabbatar an gama sanya kayana a ciki, kuma suka jira sai da suka ga tashin mu ƙarfe biyar na yamma. Suna ɗaga mun hannu sai ga kiran Nu'uman ya shigo, wannan karon da lambar shi ya kira. Tambaya ta yake yi ƙarfe nawa za mu tashi, nace ai yanzun nan ma muka tashi. Da sauri yace "Kashe wayar ki, zan kira anjima idan kun isa."
Wuraren ƙarfe goman dare sai ga wayar shi ta sake shigowa. Abu na farko da ya fara tambaya shine "Ya kika je gida? Ya su Mama?
Na amsa da cewa gida a wannan lokacin? Sai asuba ai, muna hanya har yanzu. Bakin shi na saurin yin magana yace "Na'am?! A me kika tafin kanon ne?" Nace a mota. Habawa! Kamar na sanyawa auduga wuta, ya rufe ni da faɗan cewa don me yasa zan bi mota? Bayan na kwana da sanin cewar hanyar nan sai a hankali, ba kyau gare ta ba ko don 'yan fashin titi. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har faɗan ya karya mun zuciya na fara hawaye nace to ba kaya ne da ni da yawa ba? Ina jin alamun kuka ya jiyo a murya ta, sai ya sassauta faɗan yace "To jirgi ba ya ɗaukar kaya ne Ummu?"
Ban tsaya yi mashi musu ba nace Allah ya ba ka haƙuri, ba zan sake ba in shaa Allah. Ina jiyo saukar numfashin sa yace "Kar ki sake hawayen nan ya zubo, kin ji ni ko? Allah ya kai mun ke lafiya lau Ummu, Allah ya tsare."
Kasa bacci yayi a daren nan, bini-bini sai na ji kiran shi yana tambaya ta ko lafiyar mu ƙalau a titin. Ni ce mai kwantar masa da hankali akan babu abinda zai faru bi'izinillah, ba yanda ban yi da shi ya kwanta yayi bacci ba amma sam ya ƙi ji. Ga bacci nan ina ji a muryar shi. Sai da ya ji nace mun isa Kano lafiya, har ma Hussein ya zo ɗauka ta. Da farko ya ɗauka na faɗi haka ne kawai don na samu yayi bacci, don haka sai da yace na ba wa Hussein wayar su yi magana sannan ya haƙura.
Ina isa gida wanka da sallah kaɗai na iya yi, ko abinci ban saurara ba na kwanta baccin gajiya. Waya ta wurin ƙarfe biyu ta tashe ni daga bacci, muryar Nu'uman cike da bacci ta kwararo ta wayar "Me kike yi Ummu?" Na amsa, bacci ne kawai tunda na dawo. Ya ce "Ni ma tashi nayi zan yi sallah, tashi ki yi ke ma."