ABBA NE

Part 3

by @saratalkasum88

_*🌻ABBA NE 🌻*_








Hakkin Mallakar



_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_



_JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION_




_*Littafin na kud'i ne only N 300 kada ku bari a baku labari, my WhatsApp number 👉🏻 +966599791573*_



بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣3️⃣


A fusace ya iso bakin k'ofar classé d'in su Ashma yayi Sallama" Malamin su Ashma ne ya fito yana fad'in" Waye nan? Zaro idanu yayi gabanshi na dukan uku uku ganin Kakkarfan Namiji a gabanshi sanye da kakin Soja, fuskar nan a had'e nan da nan ya mishi kwarjini ya sunkuyar da kanshi k'asa yace" Bonjour Sir comment tu-çava? Saida ya watsa mishi wani kallo kafin ya amsa da" Bonjour çava très bien. Ashma ya kalla yace" Ashma na wannan ne ko? Ashma da take tsallen ta tana dariya jin abinda ya fad'a kawai sai ta fashe da kuka ta kalli Malamin nasu tace" ABBA ba wannan bane d'ayan ne ya shiga classé d'in Y'an C.M.2. tuni Khalil ya rikici ganin hawayen Y'ar tashi yana kuma jinjina kalar hukuncin da zaiyiwa wanda yayi sanadiyar zubar hawayen Y'ar tashi guda daya tilo da yake jin tamkar tsoka d'aya a miya" Rungume ta yayi yana shafa kanta yace" Yi hak'uri sai kuma ya d'ago ya kalli Malamin su Ashama yace ina ne classé d'in take? Cikin rawar jiki ya nuna mishi da hannu. Godiya ya mishi yayi nufi classé d'in da hanzari Ashma na jikinshi tana kukan shagwab'a. Shi ko Malamin su Ashma jinjina kai yayi yace" Allah ya soni bani bane na tab'a Y'ar gwal d'in nan, wai Alkur'an har na kusa sakin futsari... Khalil na zuwa yayi sallama Babban Malamin nasu ya fito da hanzari ganin wanda yake tsaye " Cikin rawar murya yace Yallabai barka da zuwa. Jinjina mishi kai kawai yayi ya d'ago Ashma yace" A cikin ku waye ya zane min Yarinya? Ai tuni cikin su ya duri ruwa, wani ne ya fito ganin Ashma a tsaye yace" Ke futsararriyar Yarinyar wannan mai yasa baki shiga classé kin zauna ba tinda shi Uban naki baizo ya dauke ki ba? Kamar wata aljana Yarinya sai shegen rashi.. Bai k'arasa ba yaji sauka wani gigitaccen mari a ko wani kuncinshi, tuni ya soma ganin taurari suna gilmawa.. Sauran Malaman duk suka cika da tsoro ganin marin da aka yiwa dan uwan su" Cikin tsananin fushi Khalil yace" Kai kasan wacece ita? Kasan kuwa wanene Ubanta a Garin nan? To ka tafka Baban kuskure a rayuwar ka, saina koya maka hankali haka ake koya karatun kenan? Kullum sai tace min ka zaketa kace mata Aljana Babanta mai halin Mugaye, amma da yake Yarinya ce nake shuru na rabu da ita ashe dai da gaske take" Damkar shi yayi ya sake daukeshi da wani marin ya shiga yin bol dashi yana cewa na k'are hakkin wani ma bare na Y'ata yau zaka gane baka da wayo. Da k'yar aka kwace shi a hannun Khalil ana ta bawa Khalil hak'uri. Babban cikinsu yaja Khalil gefe yace" Yallabai don girman Allah kayi hak'uri Wallahi bamu san hakan na faruwa ba, amma Insha Allah za'a gyara kai kanka kasan bama yiwa Daliban mu haka shima sabon Malami ne. A fusace Khalil yace" To dan sabon Malami ne sai yake dukar min Yarinya yake jifanta da bakaken kalamai? To yayi ta aikin shi sai naje naji waye ma ya dauke shi aikin" Hak'uri suka shiga bashi sai ga wata Kyakyawar Matashiyar Budurwa ta iso wajan da sauri ta nufi inda Ashma ke tsaye tana rera kukan sakalci. Da sauri ta dauke ta ta rungume tana fad'in" Ma chérie lafiya kike kuka? Ba'a zo daukan ki bane? Khalil ya kalli wadda ta dauki Ashma jin abinda take fad'i sai ya nufesu da sauri. A tsorace Budurwar take kallon shi taja baya bakin ta na rawa tace" Lafiya dai Malam? Ta fad'a tana k'ara k'ank'ame Ashma dan ita bata san shine Baban Ashma ba. D'an sakin fuska yayi yace" Baban Ashma ne. Kallonshi tayi sai kuma ta d'ago Ashma tace" Ma chérie wai shine Baban ki? Ashma jan kuncinta tayi tace" ABBA NE fa Babana wanda nake baki labarin shi" Ta karashe maganar tana kai mata sunbata a kunci. Ajiyar zuciya ta sauke ta sauke Ashma tace" Ai na dauka ba da gaske kikeyi ba surutun ki ne da kika saba shiyasa ban kawo da gaske ne Abban naki Soja ne ba. Khalil yace" Dama kun san juna ne ke da Ashma? Wani k'ayataccen murmishi tayi tace" Sosai ma Ashma ai mun saba sosai da ita d'azu tana kuka ina kiranta naga ta fita da gudu sai nayi tunanin ko yunwa takeji anzo daukan ta.. Khalil jan numfashi yayi yace Ga dan iskan cen da yake dukanta saina koya maka hankali, kama hannun Ashma yayi yace To baiwar Allah nagode da kulawar ki akan Y'ata amma ya sunan ki? Murmishi tayi tana jin yau ta fito a sa'a tinda har General Khalil yake magana da ita, tace Sunana Sanjina. Waro idanu Khalil yayi yace" Sanjina kuma kamar Ba'indiya. Sunkuyar da kanta tayi k'asa tace Eh Yallabai haka Sunana yake" Tab'e baki yayi yace to sai anjima . Ashma tace Madam Sanjina sai an jima" Murmishi Sanjina tayi ta juya ranta fes yau dai taga General Khalil ido da ido....Suna isa gida ko parking bai gama yi ba Ashma ta ringa k'okarin bud'e marfin motar" Da hanzari ya paka ya kama hannun ta yace" Haba Ashma so kike kiji ciwo ne? Kuka tasa ya fito ya zagaya ya bud'e mata ta fito, ko kallonshi batayi ba ta kwasa a guje ta nufi kofar parlo tana fad'in" Mamy! Mamy! Da sauri Mamy ta fito daga kitchen hannun ta rike da albasa tana fad'in " Na'am Ashma Y'ar gatan Abban ta kin dawo? Ashma ta kurma ihu tana sanya kuka ta fad'a jikin Mamy tace" ABBA NE ya hanani na bude mota. Bubbuga bayanta Mamy take tace" To yi hak'uri zan mishi hukunci kinji muje ki canja kaya sai kiyi wanka kici abinci. Khalil ne ya shigo da sallama a bakin k'ofar ya tsaya ya harde hannayen shi a k'irji yana kallon Ashma da take kuka" Dafe kai yayi yace" Ke wai baza kiyi shuru ba? Zo muje na miki wanka kinji My princess d'in Abba. Ashma ta d'ago tana tsalle tayi dariya dan ita ko fushi take da Khalil da yace mata Princess to ta huce, da sauri ta isa gareshi tace" Abba har kwalliya nakeso. Murmishi yayi yana sauke ajiyar zuciya Saboda baya son b'acin ranta ko min kankantar shi. Mamy tace" Hmm yo dama duk wanda ya shiga lamarin ku shi zaiji kunya. Murmishi yayi ya nufi dakinshi da ita.. Malamin su Ashma mai suna Mansoor Kemis suka kaishi aka wanke mishi raunikan dayaji, sosai yake jin tsanar Ashma dama Uban nata, waya ya dauko ya kira Baban shi bayan sun gaisa yace" Daddy kasan wani Soja ko Khalil ko uban wa ma sunanshi? Daga cen b'angaren Daddy nashi ya mik'e tsaye yana dafe kirji yace" Wai General Khalil Umar mai Nasara kake nufi? Tsaki Mansoor yayi yace Eh shi nake nufi" Wallahi saina wulakanci shi saina sashi yayi kuka da idanunshi tinda har ya dakeni. Waro idanu Daddyn nashi yayi yace" Kuturu duka fa kace Mansoor? To ai kuwa ya dakin wa kanshi abinda yafi k'arfin shi. Wani sanyi Mansoor yaji yace" Ka rabu dashi ni nan zan rama abun da ya min yanzu haka an Koreni a aiki ta dalilin dukan daya min akayi bincike ,shine suka ga bani da Ilimi bana koyawa Yara komai shine suka bani takardar sallama" Kwafa Baban nashi yayi yace" Kayi duk abinda kaga ya dace dashi, ni kaina ina da kess dashi kaga sai anjima zanje wani taro a k'auye. Mansoor yayi dariya yace" Yo sai Daddy na zan wuce na dan hole san nan ya kashe kiran...


_*Nigeria*_


Wani kyakyawa matashin Saurayi ne wanda ba zai wuce shekara 30 ba yake fitowa daga cikin wata katafariyar Asibiti, dogo ne mai cike da baifa da kamala. Hannun shi d'aya rike da rigarshi irin na likitoci d'ayan hannnun kuma yana mak'ale da waya sai murmushi yake ta zubawa. Bai ankara ba yaji yayi karo da wani abu" Da sauri ya d'ago idanun shi ya sauke su akan Wata budurwa tana sanye da riga da siket kayan sun matseta sosai, albarkatun jikinta duk sun bayyana kanta wani dan mayafi ne k'arami kana hango gashin dokin data saka" Tsuke fuska yayi yace" Ke baki gani ne kike kad'ar mutane ne? Wani Farr tayi da idanu tace" Nazo wajanka ne Doctor Hisham kuma sai gashi zaka tafi gida. Wani banzan kallo ya watsa mata yace" Bani da lokacin ki gida zanje ki bari gobe ki dawo. Marairaice fuska tayi tace" Haba Hicham bani da lafiya fa kuma kace sai gobe" Tsaki yaja ya wuce ta ya bud'e motarshi ya sanya jakar computer shi da rigarshi ya rufe k'ofar ya dawo mazaunin direba. Da sauri tasha gabanshi tace To yanzu goben yaushe zanzo? Ko ci kanki baice mata ba ya soma tada motar shi. Da hanzari tace" Zan dawo gobe ka duba ni sunana Khairat san nan ta matsa. Shi kam Hisham bai sake kulata ba yayiwa motarshi key yabar harabar Asibitin... gudu sosai yake burinshi kawai ya isa gida jin yadda yunwa ke neman dauke mishi nutsuwar shi" wani tanfatsetsen gida ya nufa hon yayi aka bud'e mishi k'ofa ya sanya kan motarshi ciki. Yana gama packing ya fito cikin nutsuwa ya soma takawa zuwa ciki yaji muryar mai gadi na fad'in" Barka da dawowa Likita. Duk da Khairat ta b'ata mishi rai hakan bai hanashi yin murmishi ba ya juyo yana fad'in" Yauwa barka dai Baba ya aikin? Baba mai gadi cikin fara'ar shi ya amsa da Alhamdulillah Likita" Dawowa yayi wajan Baba mai gadi yace" Baba bari naje na huta zanzo muyi hira. Baba mai gadi yace" Kai Masha Allah to a fito lafiya. Juyawa yayi yana fad'in Insha Allah san nan yayi ciki... Da Sallama ya shiga cikin parlon" Wata Matashiyar Mata ta amsa mishi tana murmishi, zama yayi a kusan ta yana fad'in" Wash Ammi na nagaji sosai. Shafa kanshi tayi tana cewa" Sannu My Son kasha aiki ka shiga ciki kayi wanka sai kazo kaci abinci. Lumshe idanunshi yayi yafi 5 minutes a haka kafin ya mik'e ya nufi wata k'ofa zai shiga sai kuma ya juyo yace" Ammi wai ina Rufaida ne? Ammi ta kad'a kai tace" Rabu da Y'ar banza tana cen tana kuka wai yau da zaka tafi baka bari ta ganka ba ka tafi. Murmishi yayi yana cewa" Kai Ammi kuma maimakon ki rarrashe ta ko kisa Direba ya kai inda nake sai kawai ki kyaleta" kwafa Ammi tayi tace" Kaga bana son damuwa kuje cen kai da ita ko breakfast yau batayi ba, ni bazan iya wannan abun ba kusawa mutum ciwon kai. Dariya yayi sai kuma yace bari naje na ganta, wucewa yayi zuwa dakin ta...


Khalil na zaune yana waya ranshi a matuk'ar b'ace sai yanzu yake nadamar kin saurarar Ashma da yayi idan tazo tace mai an dake ta, da yake ya jima bai mata wanka ba mai aikin gidan ke mata dan baya garin jiya ya dawo" Lokacin da yaje zai mata wanka ne yaga shatin bulala a bayanta sai hannun ta d'aya san kurje alama faduwa ma tayi. Hura hanci yayi yace" Abdul Wallahi duk da an kori Mansoor saina mishi hukuncin da ko mai irin sunan Ashma yaji an kira sai ya saki futsari. Murmishi Abdul yayi yace" Kayi hak'uri ai tinda kasa an koreshi shi kad'ai ma ya wadatar, kuma ni abinda yake bani mamaki yadda yake dan gidan masu kudi amma yake kuyarwa ,koyarwar ma ta Y'an C. P( wato aji biyu) abin fa ya bani mamaki. Khalil yace" Da abinda ya kawoshi ai ina da kes tsakanina da Ubanshi kila ko yaji labarin Ashma Y'ata ce shiyasa yake dukanta, amma ba komai zamu had'e daga shi har Uban nashi zasu gane basu da wayo.. Abdul ya mik'e ya fito daga daki dama yana gidan kowa yana dakin shi ne, Gyaran murya yayi yace Yanzu na gama cike takardun daka bani. Khalil bai jira sauran maganar ba ya kashe kiran" Kallon ta yake yadda take bacci hankali kwance ta k'ank'ame shi kamar wani zai rabasu" Murmishi yayi ya shafa fuskarta wani irin yanayi yakeji na farin ciki idan yana tare da ita.. Abdul na shigowa ya zauna gefen gadon ya sanya hannu ya dauki Ashma ya rungume ta" Cikin magayin bacci Tace

Abba! Abba na. Dariya Abdul yayi yace" Zanga ranar da Ashma zata kai mawar aure ko ya za'ayi da ita idan za'a yi mata aure? Had'e fuska Khalil yayi yace" Allah ya sauwake" Sake kwashewa da dariya Abdul yayi yace" Kan ubancen kana nufi a gaba zaka sakata kana kallo baza ka bari mu aurar da ita ba? Tsaki yaja dan ya tsani ayi maganar da za ake danganta rabuwar shi da Y'ar tashi. Amshe ta yayi ya kwantar ya gyara yace" To ya batun kama Alhaji Buba ne? Abdul yace" Na gama komai a kanshi abinda ya rage mana mukai takardun ga Oga ya bamu izinin kamoshi" Khalil ya nisa yace" Wannan Karon bazan taba kyaleshi ba kisa nawa akeyi amma da ka bincika sai kaga Alhaji Buba ne to anzo karshe, kasan Allah ko Oga bai bamu izinin kamoshi ba da kaina zan kashe banza ko Nabi ta kanshi da mota kowa ma ya huta da masifar irinsu.. Jinjina kai Abdul yayi yace" Da Abokan nashi ko ka manta ne? Murmishi yayi yace Ina zan manta dasu wannan kisa na musamman nakeso na musu. Abdul yaja numfashi yace" Amma ai kafin mu kamasu da lefi abu ne mai matuk'ar wahala.. mik'ewa Khalil yayi yace" Komin Daren dadewa ko zan rasa raina sai na kawar da wannan mutanen kai dai kasa ido kayi kallo, Insha Allah Nasara tamuce. Har Abdul ya mik'e sai wayar Khalil ta dauki ringing, dawowa yayi ya d'aga kiran" Tin kafin yayi magana aka soma mishi bayani" A matuk'ar razane yace" Me kace Oga? Bai san sanda ya saki wayar ba yayi baya ya zauna gwajam" Abdul dake tsaye yayi saurin dafashi yace" Meya faru? D'ago da rinannun idanunshi yayi ya sauke su akan Abdul ya....



_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_