Part 4
_*🌻ABBA NE 🌻*_
Hakkin Mallakar
_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_
_JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION_
_*Littafin na kud'i ne only N 300 ne masu son labarin sai ku tuntubeni ta WhatsApp number na 👉🏻+966599791573*_
بسم الله الرحمن الرحيم
0️⃣4️⃣
D'ago da rinannun idanunshi yayi ya sauke su akan Abdul yace" Wai an tsinci Gawar Alhaji Buba a bayan Gidanshi tare da Matarshi da D'anshi Y'arshi ita kad'ai ce ta tsira , itama sun bata guba amma tana Asibiti. Cikin razana Abdul ya ringa fad'in" Innalillahi wa inna ilaihin raju'un To waye ya kashe su? Khalil shuru yayi yana kallon Abdul kamar yadda shima yake kallon shi" nisawa yayi yace" Gaskiya ina zargin Abokan shi. Da sauri Abdul ya kalleshi baki na rawa yace Kana ganin a yadda suke har zasu iya cin amanar shi? Guntun murmishi Khalil yayi sai kuma ya tsuke fuska kamar bai tab'a yin dariya ba, cikin kakkausar murya yace" Abdul kaima fa wani lokacin kamar mahaukaci kake, Waye ya gaya maka Aboki baya cin amanar Abokinshi? Girgiza kai Abdul yayi yace" A'a ai abun ne da rudewa Gaskiya indai har su suka kashe shi. Mik'ewa Khalil yayi yace kaje ka shirya yi sauri nima yanzu zan fito" Abdul ya nufi k'ofa yana fad'in Ok zan jiraka a mota, daga haka ya fita... Zama Khalil yayi ya dafe kanshi abubuwa da dama yake ta kissimawa a zuciyarshi, huci yayi ya mik'e ya kaiwa bangon dakin naushi har sai da Y'an yatsun shi sukayi k'ara, yace" No Idan kuka shigo hannuna zaku gwammace dama baku zo Duniya ba" Wallahi saina kashe ku da hannuna kamar yadda kukayi dalilin tarwatsa min farin cikin rayuwata" Wasu zafafan hawaye ne ke zarya kan kuncin Khalil da sauri ya janyo photon Su Abba wanda aka musu su uku" Rungume photon yayi yana kuka mai Zuma zuciyar mai karatu, sai cewa yake" Abbana Umma na zan rama abinda aka muku, nayi Alk'awari sai na kashe wanda sukayi dalilin tafiyarku lahira. Haka yake ta sunbatu yana kuka kamar karamin Yaro. Da sauri ya goge hawayen shi jin Ashma na fad'in" Abba! Abba! Mik'ewa yayi ya dauko ta daga kan gadon ya sauke ta k'asa.. tsura mishi idanu tayi ganin idanunshi sunyi ja tace" Abba ciwon ido kake? Murmishi ya mata yace" Eh zanje na dawo anjima zan kaiki wajan wasa kinji maza jeki wajan Mamy. Da sauri ta fita tana murna jin ance za'a kaita wajan wasa" Yana ganin fitar ta yayi saurin canja kaya ya sanya kakin shi ya dauki duk abinda zai dauka ya fito. Baba ya samu a parlo ya mishi Allah tsare tukun ya fita" Abdul ya watsa mishi harara" Murmishi yayi dan yasan kwanan zancen. Shiga sukayi ba b'ata lokaci suka nufi gidan Alhaji Buba.... Hisham na zaune a bakin gado wata Y'ar k'aramar Yarinyar da baza ta wuce shekara 16 ba ce kwance tana kuka abinta" Murmishi yayi ya kai hannu ya tab'a wiyanta" A razane ta d'ago sai tayi tozali da Hisham, juya mishi baya tayi cikin sautin kuka tace" Ni ba ruwana da kai ma. Dariya yayi ya d'ago ta yana fad'in" Am so sorry my Daughter aikin gaggawa ne ya sameni shiyasa. Dena kukan tayi ta d'ago tana kallon shi, cikin damuwa tace" Abie ko operation kayi ne? Jinjina mata kai yayi alamar eh. Rungume shi tayi tace" Abie kasan me? Dafe kai yayi yace A'a yanzu dai ki bar labarin ki muje kiyi wanka nima nayi sai muci abinci, daga nan sai ki bani labarin" Cike da murna ta sauka a jikinshi ta kama hannun shi suka fito.. Ammi dake zaune baki ta saki tana kallon su , sai kuma ta tab'e baki tace" Aikin banza futsararru ni dama inta nice sai dai ki kwana a haka, ni zaki nunawa Mahaifi nima ba daga sama na fado ba.. Rufaida ta iso gaban Ammi ta mata kiss san nan tace To ai Abie na yazo shikenan ni dama ba ruwana dake" tsaki Ammi taja tace Cen da tsiyar ku karku ma kuskura ku shigo min parlo, inba haka ba nabar muku gidan na fita waje na zauna. Dariya sukayi a tare Hisham yace" Yi hak'uri Ammi na. Kallonta ta maida ga TV ganin photon da ake haskowa yasa tace" Kai Hisham zo kaga mai kama dakai. Hisham yace ki bari na dawo dama kince ai kinga mai kama dani idan mun fito sai ki nuna min.... Khalil har sun kusan zuwa Gidan Alhaji Buba Ogan su ya kira su yace su dawo kes d'in ya koma hannun Y'an Sanda" Rai ba dad'i suka nufi Office d'in.. A office suka samu Ogan nasu yana ta safa da marwar yana ganin su yace" Yauwa dama ku nake jira. Zama sukayi suna kallon Ogan nasu " Gyara zama yayi yace" Kun ga abinda ya faru duka saura minti nawa aje kamoshi amma sai aka samu wasu suka kashe shi.. cikin tafasar zuciya Khalil yace" Nifa Gaskiya ba wanda nake zargi sai Abokan sana'ar shi, ta yadda zaku yi duba ga yadda suke gudanar da kasuwancin su, shi Alhaji Buba shine Yaron su zai shigo da kaya k'asar nan san nan suzo su amsa ko yakai musu" Abinda nake tunani ko sun samu matsala ne da su ko kun manta binciken da mukayi wannan satin Alhaji Buba ya shigo da kaya" Amma abin mamaki bai siyarwa da su Abokan kasuwancin nashi ba, Tabbas akwai abinda ya faru tsakanin su jiya nayi bincike an Tabbatar min da wani abu ne ya shiga tsakanin.. Jin wayarshi sako ya shigo ne yasa yayi saurin dubawa" Wani k'ayataccen murmishi yayi yace To kunga abinda nake fad'a ko sab'ani suka samu shine yace zai tona musu asiri tinda baza su bashi kud'in shi ba idan sun amshi kaya" Shiyasa cikin dare suka sanya aka kashe shi" Ya karashe maganar yana nunawa Ogan nasu sakon da aka turo mishi... Abdul ya Jinjina kai shi wani lokacin ma Khalil tsoro yake bashi, idan yace abu kazane to hakan ne.. amsa duk sukayi suna karanta sakon" Ajiyar zuciya Ogan su ya sauke yace" To yanzu taya zamu kama su da lefin ne? Kun san dai mutanen nan sun iya takunsu" A fusace Khalil yace" Ko me suke wata rana da kaina zan kamasu, kuma in wuni sukayi suna tafi ni a tafe na kwana Insha Allah sai Alhaji Mati da Alhaji Kabeer da kuma babban dan iskan Shugaban nasu wato Alhaji Sammani duk nine nan zan kashe su da hannuna" Ya fad'a yana dakar k'irjin shi.. dukkansu idanu suka zuba mishi ganin yadda jijiyoyin kanshi suka tashi alamar yakai makura a b'acin rai.. tattaunawa sukayi sosai akan lamarin duk da yanzu kes din baya hannnun su yana hannun Y'an Sanda. Sai kusan la'asar kowa ya shiga Office d'in shi....
Zaune suke a wani tanfatsetsen parlo babba, gaban su an baje musu Abinci kala kala da kayan marmari" Wani daga cikin su ne ya kwashe da dariya yace Su Buba ana cen an bakunci lahira. Wanda yake gefen shi yace " kwarai kuwa sun dauka mu din wasa ne shi har ya isa ya fallasa sirrin mu ya rayu a Duniya. Dariya suka sanya Alhaji Sammani yace" Nifa baku san abinda yake damuna ba. Duk kallon shi sukayi a tare suka furta" ranka ya dad'e kai yanzu har akwai abinda zai dameka a Duniyar nan? Murmishi yayi yace Eh mana Wannan dan iskan Sojan shine yanzu damuwata, ko kun manta dan gidan Umar mai Nasara ne? Jinjina kai sukayi. Alhaji Mati yace" Ai kawai kabar komai a hannun mu zamu sa a kashe shi daga shi har sauran ahalin nashi da suka rage" Alhaji Kabeer yace Yaro yarone shima ya kusa tafiya inda ba'a dawowa, dariya suka sanya" Alhaji Sammani yace' Shine fa yasa aka kori Mansoor a wajan aiki wai dan ya zane wannan Y'ar tashi. Waro idanu Alhaji Kabeer yayi yace" Mansoor fa kace Ranka ya dade? Lalle bai san waye Mansoor ba" Hmmm ka rabu da dan iska mana shi fa gani yake ba wani wanda ya isa dashi a k'asar nan tinda ya kai matakin general, ai inya san wata bai san wata ba zamu biyo mishi ta baya gida.
Haka sukaci gaba da hira akan yadda zasu kashe General Khalil Umar mai Nasara da sauran dangin nashi wato su Baba....
Da sauri ta fito tana fad'in"
Abie! Abie!! Ina kake maza fito ka gani Wallahi na ganshi fito ka gani kar a wuce Abie" Ta fad'a tana sanyo kai cikin d'akin shi. Kwance ta sameshi yana bacci da hanzari ta hau kan gadon ta shiga jijjiga shi tana kiran sunan shi" Bud'e idanunshi yayi da suke cike da bacci ya sauke su akan Fuskarta yayinda itama shi take kallo tana dariya. Tashi yayi yana dafe kanshi dake mugun sara mishi yace" Ke wai yaushe zakiyi hankali? Turo baki tayi tana kallon shi, kwafa yayi ya lumshe idanun shi gashi ta katse mishi bacci shi kuma dabi'arshi ce indai ya fara bacci aka tashe shi to bazai sake komawa ba ko da kuwa da dare ne a zaune zai kwana, shiyasa idan ya kwanta Ammi take hana Rufaida zuwa wajanshi. Numfashi yaja yace" Menene ya kawo ki. Gyara zama tayi ta dauko wayarta ta shiga Instagram sai ga photo ya bayyana cikin zakuwa tace" Abie ka ganshi wanda nake fad'a maka kuna kama kuma ma Soja ne ka gani" Ta fad'a tana daura mishi wayar akan cinyarshi. Dauka yayi yana yatsina fuska" Da sauri ya zabura yana bin picture d'in da kallo, Cikin rawar murya yace" Wa... wanene shi wannan d'in? Rufaida tace" A Instagram na ganshi kuma ba dan nan k'asar bane ka ganshi ka shiga ka duba har da wata Y'ar K'aramar Yarinya Y'arshi ce nake tunani.. cikin kaduwa da Al'ajabi Hisham ya gyara zama hannu na rawa ya shiga account d'in shi sai yaga an goge komai a cikin account din sai picture din Yarinyar fuskarta dauke da murmishi, guda d'aya. D'agowa yayi yana kallon ta yace" Ai babu komai amma dan wata k'asa ne shi? Gaskiya Abie ban duba ba wani lokaci ne ina shiga na ga videon shi tare da Yarinyar yana daura mata dan kwali, wayar sai ta rufe to ban kuma gani ba sai yanzu shine nace bari na nuna ma kuna mugun kama ko? Ta fad'a tana daura kanta a kafad'arshi. Hisham dai kurawa pictures d'in ido yayi kamar dai shi yake gani a pictures din, sai kuma yayi screen shot d'in picture d'in ya tura zuwa wayarshi. Mik'a mata wayar yayi yace" Gashi kisa a caji yanzu dai kin hanani nayi bacci ko? Maza je ki shirya mu fita waje" Rungume shi tayi tana fad'in" Wow surprise Abie kamin ko? Murmishi kawai yayi ya cire ta a jikinshi ya shige toilet. Ita kuwa Rufaida sosai take mamakin yadda wannan Sojan yake kama da Abie din ta, mik'ewa tayi ta fita zuwa d'akin ta... Khalil na zaune shida Abdul a wani restaurant hira suke jefi jefi" Abdul yace" Uban Ashma Ikon Allah wai kai nan wata rana Suruki zaka dauka? Dukan wasa yakai mishi ya kauce yana dariya" Khalil yace" Kai yanzu kana ganin abu mai sauki ne rabani da princess? Ai banga ranar ba gaskiya idan har kuwa na ganta to bazan kwana ba a lokacin ina numfashi. Dariya Abdul yayi yace" Mu dai mun shiga uku da kai to idan kayi aure ai zaku dena kwana tare da ita, naga yanzu girma take sai ku raba wajan kwana" Wani kallo ya watsa mishi yana jan tsaki yace" Kai fa mugun dan sa'ido ne ko? To ai sai ka hana muke kwana tare. Abdul ya d'ago zaiyi magana sai yaga wata Mace na tinkaro su" Tana isowa tace Hello. Khalil bai d'ago ba kuma bai amsa ba sai Abdul ne yace Hey, zama tayi fuskarta dauke da murmishi tace" Abban Ashma dama ana ganin kyauta? Da sauri ya d'ago kanshi jin zazzakar muryarta, waro idanu yayi yace" A'a Madam kece sannu fa" Murmishi tayi tace" Yauwa ina Ma chérie take? Oh princess tana gida yau banzo da ita ba" Cewar Khalil yana kallon ta da kyau. Sunkuyar da kanta tayi ta mik'a mishi wata leda baka tace" To akai mata dama ita na siyawa idan taje Ècole na bata, tinda gaku sai akai mata kace ina gaishe ta" Ta fad'a tana murmishi.. Shima Khalil murmishin yayi sosai yaji nutsuwar Yarinyar ta burgeshi" Kallon ta yayi yace" Nace ba ya sunanki? na manta fa.
A sanyaye tace" Sanjina sunana" Abdul ya saki baki yana kallon ta har zata juya sai yayi saurin fad'in baki ji ba. Dawowa tayi ta zauna tana fuskartar Abdul ta d'ago da fararen idanun ta ta sauke su akanshi. Abdul yace" Nace ba ki hak'uri zan miki wata tambaya idan ba damuwa" Girgiza kai tayi tace" ba komai ina jinka. Wai don Allah ke Musulma ce kuwa? Kiyi hak'uri fa naji sunan naki ne kamar bana Musulmai ba" Murmishi tayi tace" A'a ni ba Musulma bace ba. Da sauri Khalil ya kalle ta bakin shi na rawa yace" Ai kuwa ba wanda zai kalle ki yace ke ba Musulma bace yadda kike rufe jikin ki ko wata Musulmar bata yi. Kanta a kasa tace" Ni ba zan iya irin wannan shigar ba gaskiya duk bana jin dad'i shiyasa Nake rufe jikina. Khalil d'aya tsura mata idanu ya saki murmishi yace" Gaskiya hakan shine dai-dai, dan ke ba Musulma bace hakan bazai sa kike bud'e surar jikin ki ga kowa ba, kici gaba da kare mutumcin ki" Jin kai tayi tace" Hakane ranka ya dad'e na gode sosai bari naje gida yamma tayi. Khalil ya mik'e ya dawo kusan ta yace" Bani number ki idan naje gida sai na kira ki kuyi magana da Princess. Cike da matsanancin farin ciki Sanjina ta kalleshi hannun ta na rawa tasa mishi number ta,sai da ta kira taga ta shiga tukun ta musu sallama ta tafi... Abdul ya iso inda yake yace" Kai Oga ko dai ka kyasa? Tsaki Khalil yayi sai kuma yayi murmishi yana shafa kwantaccen sajen shi ya koma ya zauna.. mai kawo abinci ne ya kawo musu lemon guda biyu ya ake musu " Khalil ya dauki nashi ya shanye tass san nan ya kalli Abdul da yake danna waya yace" Ko baza kasha ba? Girgiza kai yayi yace no na koshi tashi muje gida. Mikewa sukayi a tare sai da Khalil ya biya kud'in abincin da sukayi san nan suka nufi motorsu" Tin kafin suyi nisa Khalil yake jin cikinshi na murdawa, daurewa yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera idanun shi a lumshe. Da k'yar Khalil yake gani cikin shi ya tsanan ta ciwo ,da sauri Abdul yayo packing Khalil ya bud'e ya fito da sauri ya nufi ciki numfashin na neman sarkewa, da haka ya shigo falon" Da sauri Mamy ta fito ganin Khalil ne tace" Sannu da zuwa. Jinjina mata kai kawai yayi ya nufi dakinshi, tin kafin ya isa a bakin k'ofar ya yanke jiki ya fad'i" A matuk'ar firgice Mamy tayo kanshi tana salati ta shiga jijjiga shi tana fad'in Kahlil! Khalil!! Ahma data fito da gudu jin ana kiran Abban nata dama shi take jira yazo" A guje ta k'araso inda yake kwance tace ABBA! ...
_*Taku har kullum Maman Nusaiba*_