ABBA NE

Part 7

by @saratalkasum88

_*🌻ABBA NE 🌻*_











Hakkin Mallakar


_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_





_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_





_*Littafin na kud'i ne only N500 ne domin karin bayani ku tuntubeni ta number na👉🏻 +966577675904 *_



بسم الله الرحمن الرحيم



0️⃣7️⃣





A hanzarce Rufaida ta shiga d'akin ta sameshi a kan gado yayi ruf da ciki, Zaunawa tayi tana kallon shi jin yadda yake sauke numfashi kamar wanda yasha gudu" Hannu ta kai ta tab'a kafad'arshi tana fad'in" Abie na! Waye ya tab'a min kai haka? Please ka tashi don Allah bana son ganin ka a cikin damuwa. Shuru yayi bai ce mata ko uffan ba, hakan yasa hankalin ta tashi ta hauro kan gadon ta shiga birkito shi daga ruf da cikin da yayi" Yana jinta kawai dai maganar ce ta gagareshi shiyasa yayi shuru, sai da ta juyo dashi ta tsareshi da idanu muryarta na rawa yace" Ab... Abie na baka da lafiya ne? Ta karashe tana tab'a wuyanshi, har lokacin bai bud'e idanun shi ba kawai ya kasa magana . Jijjiga shi ta shiga yi tana cewa Abie kayi magana don Allah, meye yasameka da ka kasa min magana? Ta fad'a tana sakin kuka mai sauti.. rintse idanu yayi sai kuma ya bud'e su akanta, ganin yadda take kuka ba ji ba gani sai yaji ta bashi tausayi" Hannu ya mik'a mata, da sauri ta kama hannun nashi ya jata zuwa gefenshi ta kwanta suna facing din juna. Cen kasan makoshi yace" Daughter kiyi shuru kinji" Tsayar da kukan tayi jin yayi magana, tashi tayi zaune ta d'ago kanshi ta daura a cinyarta ta shiga shafa sumar kanshi kamar wata Uwa.. lumshe idanu yayi yana jin K'aunarta na bin ko ina na jikin shi, hannu yasa ya zagaye bayan ta ya saki murmishi" cikin k'asa da murya yace" Daughter kiyi shuru mana babu abinda ya sameni, kai na ne kawai ke ciwo shima da anjima zai warke. K'arawa kukanta sauti tayi ta soma fad'in" Abie bazan iya sukoni ba matuk'ar baka cikin nutsuwarka, bana so ko na d'aya rana naga kana cikin damuwa, bazan juri hakan ba ina jinka a jinin jikina fiye da kowa Abie har Mommy na kanta bana mata son da nake maka, duk da ance ta mutu amma ni kaine komai nawa idan baka cikin walwala ni kuma sai na fika shiga ciki please Abie idan wani abu ke damun ka ka fad'a min, ni nan zan maka shi matuk'ar bai sabawa Addinin mu ba" Ta fad'a tana rik'e hannun shi gam.. Sake da baki Hisham ke kallon Y'ar tashi shi wani lokacin kalaman ta na sanyashi a Duniyar tunani, ajiyar zuciya ya sauke yace" Babu komai fa ciwon kai ne,shima da nayi allura zai warke" Ya fad'a yana tashi zaune, janyota yayi zuwa jikinshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta alamar rarrashi. A hankali ya shiga mata kalamai masu dad'i har tayi shuru, hira suka soma har bacci ya dauke ta" Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo, Baya yayi ya kwantar da ita ya sanya mata filo a kusan ta, mik'ewa yayi ya sanya k'ananun kaya ya koma cen gefen gadon shima ya kwanta bai jima ba bacci ya dauke shi....


Baba ne ya kalle Khalil daya fito yace" Maza aje a dauko Inna jirgin su ya sauke, Ashma dake kusan Baba tana shan yatsunta sai kallon su take jin ance Inna yasa ya mik'e tana cewa" Baba zanje nima dauko Innar. Khalil yace" Ba inda zaki je maza koma ki zauna salon kije ki b'ata ki samu uku a wajan Inna" Ashma ta barke baki ta shiga kurma kuka hade da ihu tana Shura kafafu a k'asa kamar wata mai bori,ta shiga fad'in" Nidai sai naje ai ba kai zanbi ba Papi zanbi nidai Alkur'an dani zaku tafi ko kuma naje da kaina. Mamy dake dariya tace" Da kyau rigimammiya yi abinki mai daure miki gaba da baya ta iso. Abdul ma dariyar yake yace Yi shuru to tashi sanyo hijabin ki sai mu tafi kinji, kuma ki sanya mai kyau wanda idan Inna ta ganki zata dauka Sarauniyar kyau ce. Da sauri ta tashi taje wajan Abdul ta bashi runguma tana dariya tace" Ina sonka Papi bari naje na dubo sabon hijabina wanda ka siyo min ranar. Murmishi yayi yana jan kuncinta yace OK to maza mana, da sauri ta fice daki.. Khalil ya cika yayi fam ganin Ashma ta rungume Abdul cikin b'acin rai yace" Kasan Allah tafiya ta zanyi baza ta bimu ba tayi zaman ta a gida, Abdul yace" Haba dai ka bari muje da ita mana meye a ciki? Girgiza kai yayi yace" No kai kanka kasan dalilin da yasa nake hana ta fita, muje kawai bana son muso. Ganin ba wasa Abdul yabi bayan Khalil suka fito harabar gidan, mota uku suka dauka tasu ce a tsakiya daya gabansu daya bayansu, abinda Khalil bayaso kenan ake wani binshi kamar Shugaban k'asa, dan ba yadda zaiyi ne tinda Umarnin Ogansu ne shiyasa yake tafiya da masu tsaronshi...


Jirgin su Inna na gama sauka Wata Mata dake gefen ta tace" Hajiya munzo fa muje waje" Inna ta rike baki tana cewa" Asha Y'ar nan ni kan ban tab'a zuwa Makkah ba ina fatan kafin na mutu naje. Murmishi Matar tayi tace ba damuwa muje kawai, kama hannun Inna tayi ganin yadda kafafun ta suke rawa suka nufi fita" Inna sai zare idanu take ganin ta a babban felin Airport d'in jama'a gasu nan bila'adadin kowa harkar gaban shi yake.. suna sauka Matar ta kalle ta tace" Mama ina wanda suka zo daukar ki? Tab'e baki tayi tace" Wallahi ki bari kawai wasu Narka-narkan jikokina ne zasu zo dauka na, amma da yake sun renani har yanzu basu iso ba dan ma k'asar ba kamar Nigeria bace da kana fita inba Allah ya dubeka da rahamar shi ba sai ayi caraf dakai kamar wani kayan abinci.. Yanzu ni daga cen nake D'ayan jikan nawa ne ke zagina da yaren nan ko uban me ma sunan shi? Matar na murmushi tace English" Inna tace eh shifa nifa ba Y'ar iska bace irin shi shiyasa nayi shuru da bakina ban fad'awa kowa ba na kira Yusufa nace azo a dawo dani nan" Gara nan da cen sai dai su nan matsalar duka jikon nawa Sojoji ne suna kallon ki zaki saki futsari dan ba Imani ba gare su ba, shiyasa banaso nazo na zauna a gidan kamar gidan mutuwa.. Amma tinda shi jikan nawa yana da D'iya sai muyi zaman mu da ita kawai. Ita dai murmishi take tana kallon Inna nata zuba har wani Kyakkyawan Mutum sanye da rawani ya iso inda suke cikin shigarshi da alfarma ya musu Sallama.. Amsa mishi sukayi Matar ta kalli Inna tace" To Mama ni anzo dauka na daga nan zamu wuce Ethiopia ne nida Mai Gidana. Inna data dauko goron ta a cikin jakarta zata kai baki sai kuma ta fasa ta kalli Mijin Matar tace"

Amma dai kai Dangin Dogayen mutanen cen ne ko? Dan murmushi yayi yace Eh Mama sauri muke sai kuma gani na biyu" Inna ta tab'e baki tace" Yo a ina zaku ganni nida za'a kaini gidan Sojoji masu ďamara a kugu, ganina ai zaiyi wahala, amma idan kukace ni kuka zo gani sai a barku " To Mama indai mun diro k'asar zamu nemeki. Murmishi tayi tace Allah ya muku albarka a sauka lafiya' Allah yasa sukace san nan suka shiga motarsu suka tafi...


Hello Ranka ya dad'e ga Kakar tashi ta iso kuma basu zo ba kawai mu kwamushe ta" Shuru yayi yana sauraron abinda ake fad'a sai kuma yace" Okay Bari mu san yadda zamu mata wayo ta shiga akwai mutane a wajan baza mu iya sanya mata fauda ba, kashe kiran yayi ya kalli sauran yace" Muje. Inna na tsake tana so ta kira Baba amma bata iya fito da number ba, wani Ma'aikaci dake kusan ta ta mik'awa wayar tace" Kai ungu nan maza kira min Yusufa lambarshi tana kusan ta Musalle da Amadudu. Murmishi Ma'aikacin yayi ya amshi wayar yana dubawa, cen yaga an saka Yusufa a number danna kira yayi ,ana dauka ya bata" Cikin ruwan masifa Inna ta koma gefe ta fashe da kuka tace" Yusufa yaushe ka gantale ban sani ba? Nafi awa biyar anan ina tsaye kamar wata Soja, ka kama hanya kazo ka daukeni na fada maka ko a k'afa ne kazo ka daukeni, idan kuma kaina ka zama irin Amadudu sai na kira Musalle yazo ya daukeni. Haba niba Y'ar iska ba amma sai gantali nake a waje kazo nace ko kuma ni na dauki motar haya na tafi da kaina.. Ma'aikacin dake kusan Inna dariya yake Jin tana cewa wai tafi awa biyar a tsaye.. Inna na gama wayar zata juyo taga wasu Mutane guda biyu suna fad'in" Hajiya kece Kakar General Khalil ko? Had'e rai Inna tayi tace" Idan daukana kukazo yi to bazan shiga ba, shi shafaffe da mai ya zauna a gida ya turoku ku dauke ni ko? To bazan je ba ku b'ace min da gani" Cikin son mata wayo sukace ai yana cen baya a mota muje a kaiki" Maaikacin dake kusan su ya k'are musu kallo shi dai bai ga kayan Sojoji a jikin su ba, sai yace" Kuje mana kuce yazo tinda tace bata zuwa.. Inna tace" Rabu dasu sun dauka nima ďamarar dake yi kamar su, to bazan shiga motar Soja ba ato ake kallo na kamar lefi ne nayi aka je kamo ni.. Komawa sukayi inda suka fito suna tattauna yadda zasu ja hankalin ta" Wani yace daya ya zauna sai mu kai mata waya yayi magana da ita, dukkan su yarda sukayi fa shawarar shi sun mike zasu fito sunakaji jiniyar shigowar motocin General Khalil Airport d'in, ai a guje suka koma suna numfashi.

Inna da tayi mucikur ta rike baki tana kallon motocin, cikin masifa tace" Kaga jarabar ko dama ai nace indai sune zasu zo kamar zasu kama wanda yayi lefi, shi Khalilu da yake ya renani nasan shi zaice azo da wannan maka-makan motocin nasu wanda ko ganinsu kayi sai sun tsorata ka.. Suna gama packing cikin takunsa na kasaita ya ziro kafarshi d'aya waje,sai da yayi kusan few minutes kafin ya fito da d'ayar k'afar. Inna dai na ta mita tana kallon Kafafuwan Khalil amma yaki fitowa" Kallon Maaikacin nan tayi tace" Kaga ai abinda nake fad'a ma kalli dan kan babbar butar sai wani zafin kai yake, kamar wani shugaban k'asa. Dariya yayi kawai, Abdul ne ya fito da hanzari ya nufi Inna ya kama hannun ta ko magana bai mata ba yaja hannun ta ya kaita cikin mota" Waige-waige ya somayi baiga kowa ba sai ya nufi wannan Maaikacin yace" Babu wanda yazo wajan Tsohuwar nan? Cike da girmamawa yace Yallabai wasu sukazo nan yanzu nan suka bar nan, suna ta fama akan Tsohuwar sai ta bisu tace babu Uban da zata bi. Da sauri ya katseshi yana cewa, Ina sukayi? Da hannu ya nuna mishi, Yaranshi yayiwa Umarni da su bi inda ya nuna mishi.. Su kuwa wanda suka so sace Inna hankali tashe suka nufi wani lungu suka b'oye jin ana binsu, da k'yar suka tsira" Dawowa sukayi suka ce basu ga kowa ba.. Khalil ne ya fito daga motar nan da nan mutanen wajan suka soma taruwa suna fad'in" La ga General Khalil tare da Captain Abdul ko me sukazo yi ne? Wata Budurwa da bata jima da sauka daga jirgin ba tace" Nifa ina mugun son General Khalil kamar raina, Wadda take gefenta ce tace" Tab lalle kin dauko ruwan dafa kanki Sojan ne zaki aura kuma babba wanda idan kika b'ata mishi rai mari d'aya sai kin kurmance. Khalil kuwa yasha mur ganin duk shi suke kallo abun na bashi haushi shi bashi da damar ya shiga cikin jama'a kamar kowa sai ayi ta kallon shi, kamar anga sabuwar halitta" Tsaki yaja ya koma ciki ya bada Umarnin su tayi ba b'ata lokaci suka bar Airport d'in.. Inna tinda aka sata a mota bata ce komai ba sai tagumi da tayi tana kallon Abdul wanda ya daure fuska, lokaci zuwa lokaci sai tace Hmm har suka iso gida.. da Sallama Inna ta sa kai cikin parlon, Ashma dake ta kukan tafiyar da sukayi suka barta ta mik'e da gudu ta rungume Inna tana dariya. Inna ma murnar ganin ta tayi ,tace" Ashmatu kece haka zabgegiya kamar wata Uwa? Dagota tayi tana binta da kallo kamar taga wata sabuwar halitta, ita kuwa Ashma sai murna take tana fad'in" Innata tare dake zan zauna kinji. Murmishi Inna tayi tace" Yo dama wani dan iska ya isa ya hana ki zauna a wajena ai daga yau kece Y'ata ni da kaina zan aurar dake. Kama hannun ta tayi suka zauna Mamy ta fito da murna tana fad'in" A'a maraba da mutanen Nigeria sannu da zuwa Inna. Tabe baki Inna tayi tace" Ko da yake ba dake zanyi ba sannu ya gida na sameku lafiya? Murmishi Mamy tayi kawai dan tasan halin Inna yanzu sai ta sauke mata gajiyar hanya.. Sai da tayi wanka taci abinci Baba ya dawo ya shiga mata barka da zuwa" dagowa tayi taga duk suna nan kawai sai ta rushe da matsanancin kuka kamar wadda aka yiwa wani abu" Baba yace" Inna lafiya kuma? Ka rabu dani Yusufa nayi kuka, dama suma wannan Samudawan mugaye ne ban sani ba? Wancen bakin mai kama da tukunya yafi kowa mugunta" Ta fada tana nuna Abdul. Sai ta sake sakin kuka har da face majina ta ce "Shi kuma wancen narkeken shafaffe da mai ko fitowa baiyi ba bare mu gaisa dan kan Ubanshi, Wallahi kai dai anyi k'aton banza, gara da ka zama Sojan dan inba haka ba Wallahi baza ka auro ba. Yawu ta tsartar tana cewa" Yanzu dan an maidani Yar iska wannan Basamudan ya ringa jana kiii a filin jirgi kamar yazo kama mai lefi, baka ga yadda mutane ke kallo na ba, yo ko ban haifi Ubanka Yusufa ba ai baza kamin cin mutumcin daka min ba" Cigaba da Kukanta tayi Ashma nata dariya ta kwanta akan cinyarta" Harara ta watsawa Khalil tace" Wai kai meye ma matsayinka a nan K'asar? Naga kowa sai kallon ka yake ana ga geniro ko wa ma oho ku kuka sani.. Dariya Abdul yayi yace" General ake cewa Inna ni kuma Captain wato mai biya mishi" Tsuke baki Inna tayi tace" To d'aga yau bance ku sake zuwa daukana ba, kum girma narka-narka daku amma ba aure, kai kuma na dawo kanka" Ta fad'a tana nuna Khalil, So nake ka samo wata Mata ka aura kana da wannan katuwar budurwar amma ace ka kasa aure" da Sauri Khalil yace zan samo Inna bari naje zamuyi magana da Abdul. Washe baki Inna tayi tace" Hakan yayi ke tashi mu tafi daki na baki abinda na kawo miki. Da murna Ashma tabi bayan Inna tana yiwa su Abdul gwalo. Kwafa Khalil yaja a ranshi yana fad'in wato ma da gaske fushin take kuma a dakin Innar zata kwana? Mik'ewa yayi suka fita shi da Abdul...

Koda suka fita Khalil ya jingina da jikin bango ya lumshe idanun shi" Cikin yanayin damuwa Abdul yace" Khalil wai meyake damun ka yau duk naga baka da kuzari? Ko har yanzu jikin ne? Girgiza kai yayi alamar A'a, To naji inba jikin bane menene? Cikin rawar murya yace My princess d'ina. Sake da baki Abdul yake kallon shi ya tako zuwa inda yake ya dafashi ya...





_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_