ABBA NE

Part 9

by @saratalkasum88

_*🌻ABBA NE 🌻*_











Hakkin Mallakar


_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_




_*Littafin na kud'i ne only N300 ku harzarta ku mallaki naku my WhatsApp number 👉🏻+966599791573*_




بسم الله الرحمن الرحيم


0️⃣9️⃣



Da hanzari Khalil ya mik'e ya shiga ciki daret ɗakinsa ya nufa hankalinshi a tare" zama yayi yana jin sautin kukan nata yace" Mama kika ce fa Sanjina? Ko wani abun ne ya faru da ita? Girgiza kai tayi kamar yana kallonta cikin zafin abinda Maman nata tayi mata tace" Ta koreni daga gida tace bani ba ita karna kuskura nace su suka haifeni" Zaro idanu Yayi yace" Ita Maman ta fadi haka? To me kika mata?".."Nidai kazo ka daukeni zan zauna dakai saboda kai ta koreni tace ni ba Y'arta bace" Khalil ya saki baki yana jin maganar Sanjina kamar daga sama, baki na rawa yace" Saboda ni kuma Sanjina? To me nayi ni kuma? Nidai kazo yanzu ma ina zaune a waje kila ma ta karya min hannu kazo don Allah zan iya mutuwa in baka zo ba" Ta fad'a tana sake sakin kuka. Mik'ewa Khalil yayi da sauri yace Gani nan amma ina ne Unguwar taku? Goge hawayen ta tayi tace *Tanko pomp* ina karshen layi fita daga Unguwar" To shikenan gani nan zuwa yanzu, kashe kiran yayi ya mik'e da sauri ya fito. Dakin Abdul ya nufa ko sallama babu ya shiga yace" Zo mu tafi" Abdul bai musa ba ya dauka ko wani ne zasu je kamowa dan haka ya sanya kakin shi riga baka wandon kuma na Sojoji har da daukan bindiga ya sanya a kugunshi saboda tsaro suka fito. Ashma data fito tana kuka ganin su yasa tayi saurin isa gareshi ta fad'a jikin Khalil tace" Abbana! Kakkarfar ajiyar ya sauke har sai da Abdul yaji ya kwashe da dariya, lumshe idanu yayi yace My princess lafiya kike kuka? k'ank'ame shi tayi tana ci gaba da kuka tace" To ba kai bane ka shareni, shine jiya ko kazo ka min Addu'a ma. Fesar da iska yayi ya banbareta daga jikinshi yace" Naji na dena fushin ki bari da na dawo sai nazo muyi magana zan kawo miki wani abu wanda kikeso sosai. Murmishi tayi tace To Abba Allah ya tsare hanya, Allah ya kare min kai Abbana" Cikin jin dad'i yace Ameen sai mun dawo" Abdul yace To lalle Princess wato ni baki ganni ba ma ko? Yar dariya tayi taje ta bashi runguma tana cewa" Papi ai bazan manta da kai ba sai kun dawo. Dariya yayi yace" Tam shikenan, fita sukayi Sojoji harabar gidan suka taso suna sara mishi" Hannu yake mik'a musu suna musabaha yana tambayar lafiyarsu, su kuma suna amsawa da lafiya" wani acikinsu yace" Yallabai ina zamu tafi? Unguwar Tanko pomp zamuje amma ba sai kun bimu ba wani abu ne zamu dauko mu dawo yanzu. Jinjina kai direban yayi yaja da baya ya mik'awa Captain Abdul key d'in motar su kuma suka shiga ciki, ba bata lokaci suka fita daga gidan..



Hisham yau jiki yayi sauki yana jin zai iya zuwa Asibiti da kuzarinshi ya shirya cikin k'ananan kaya ya feshe jikinshi da turare san nan ya fito zuwa parlo.. Rufaida ce ta tareshi tana murmishi tace" Good Morning Abie na" Shafa kanta yayi yace Morning daughter how are you? Yar dariya tayi tace Am fine Abie how are you feeling now? Alhamdulillahi am OK fa yanzu ma zan wuce Hospital ne kici abinci sosai kuma idan kinje Makaranta banda jan fad'a kinji ko" Ya fad'a yana zama.. Itama zaman tayi tace" To Abie bari na kawo maka abincin naka kayi breakfast,mik'ewa tayi taje ta hado mai abincin ta dawo kusa dashi a kan center table dake kusanshi ta aje itama ta zauna. Bismillah yayi ya dauko kamar zai kai bamin shi sai ya nufi nata" B'ata fuska tayi tace Abie kar fa kayi latti kaci abinci. Had'e rai yayi yace" Bana son muso kin sani ai" Bud'e bakin tayi ya shiga bata tana cin tana yamutsa fuska kamar tana cin sabulu. Sai da ya tabbatar ta koshi san nan shima ya soma ci ai kuwa tace ita zata bashi, gyara zama yayi ta shiga bashi sai da ya koshi ya janye kanshi yana fad'in" Alhamdulillah. Ammi ce ta fito cikin shigar ta ta alfarma tana ganin Hisham tace" To My Son jiki yayi sauki kenan har za'a fita aiki? Murmishi yayi ya tashi yazo ya bata runguma yace" Barka da fitowa Ammi na da fatan kin tashi lafiya? Murmishi tayi tace" Alhamdulillah ita kuma wannan sai yanzu takecin abinci? Ta fad'a tana nuna Rufaida. turo baki tayi tace" Dama Ammi ai baki so naci abunci yadda nakeso. Tab'e baki tayi tace" Ni da kici da karki ci matsalarki ce ba tawa ba ehhe, in banda ma shi Uban naki daya sangarta ki katuwa dake har sai ya zauna yana baki abinci a baki kamar wata babyn roba. Dariya sukayi Hisham yace na wuce, Allah ya tsare hanya suka mishi Rufaida ta bishi har bakin mota. Cikin sakalci ta soma dira kafa tana cewa" Abie to me zaka kawo min? Kallon yayi ,shi kam wani lokacin Yar nan tashi kamar mai aljanu lokaci d'aya sai ta rikice, wani lokacin kuma tayi abun masu hankali" Jinjina kai yayi yace zan dawo miki da ice cream shikenan? Tsalle tayi ta rungume shi tace" much love you Abie na saika dawo" Murmishi yayi kawai yaja motar ya fice...


Su Khalil na isa Unguwar ya kira ta tana d'agawa tasa kuka tace" Kazo ne kaga wasu ne suka tsareni yan giya ne sun hanani na wuce" Baki na rawa yace A dai-dai ina kike? Kwatance ta mishi san nan ta kashe kiran" Yan mayen dake kewaye da ita wani yace" Baby wai ina zaki je ne? Harara ta watsa mishi yace Ina ruwanka dani ku bani waje na wuce nace" Dariya suka sanya cikin maye suke cewa Ai baki isaba Yarinya tare zamu tafi. Wani da yayo kusan ta hankaďa shi tayi ta kwasa a guje, binta sukayi suma ita kuwa sosai take gudu tana kuka.. Khalil ya hango wata na gudu da sauri yace" Tsaya Abdul gata cen! Tsayawa sukayi ya fito da sauri kallon ta yake ganin yadda take gudu suna binta" Da sauri ya nufeta, kamar daga Sama Sanjina ta ganshi k'arawa gudunta wuta tayi har ta iso suka had'e da sauri ta fad'a jikinshi tana kuka. Rungume ta yayi yace" Okay yi shuru yanzu zamu tafi gida kinji Ashma na gida" Dena kukan tayi sai sauke ajiyar zuciya tayi.. Murmushi Abdul yayi sai kuma ya zaro bindigar shi ya harba yace" Duk wanda ya motsa zan tashi kanshi da alburusai. Cak suka tsaya suna zare idanu , agaba ya sanya su yace Muje Y'an iska lalatattu kawai, kuna shaye-shaye kuna bata D'iyan mutane, yau zaku gane baku da wayo" Wayarshi dake kan kafadar shi ya ciro ya danna wasu number ya soma fad'in" kuzo nan Unguwar Tanko pomp mota daya ta isa kuyo sauri" Yana gama fad'in haka ya maida wayar inda take.. Khalil da k'yar ya rabata da jikinshi yace" Muje mota. Kunya ce ta kama ta ganin abinda ta aikata tace Kayi hak'uri ban san na rungume ka ba. Murmishi yayi yace Ba komai ai nasan bakya hayyacinki muje" Motar suka shiga Abdul kuma na tsare da Y'an kwaya a gefen hanya.. suna nan sai ga Yaransu sun iso babu b'ata lokaci suka kwashesu suka wuce Office d'in Sojijo...


Tin kafin suje gida Khalil ya kira Baba ya fad'a mai zaizo da bakuwa" Ba komai Baba yace san nan ya kashe kiran.. suna isowa daret parlo suka shiga Sanjina na bayan Khalil duk jikin ta rawa yake bata san ko Iyayen Khalil d'in zasu amshe ta ba.. duk suna zaune a parlo Mamy ta mik'e ta kamo hannun Sanjina ganin duk shatin bulala ne yasa tace" Subhanallahi Yarinya meya sameki? Bata iya amsawa ba sai kallon Khalil take da shima ita yake kallo" Ashma data fito daga dakin Inna tana kunbura baki idanun ta suka sauka akan Sanjina, da sauri ta iso ta rungume ta tana cewa" Anty Sanjina dama Abbana kece zai kawo min? Murmishi tayi tace Eh nice ya kike ya karatu? Lafiya lau tace tana dariya...


Khalil yace" Am Sanjina ko zaki iya fad'a mana abinda ya faru har Mama ta miki dukan? Fashewa tayi ta kuka sosai,Mamy na rarrashin ta sai da tayi mai isarta san nan ta d'ago, ta soma cewa" Lokacin da mukayi canjan numéro dana dawo gida ina ta murna yau na ganka kuma har ka bani numéro d'in ka" Muna ta waya da kai har kace kana sona tinda ina son Ashma zaka aureni duk da ni ba Musulma bace" Ranar kasa bacci nayi saboda farin ciki ban fad'awa kowa ba mukaci gaba da magana, to jiya ne na samu na fad'a mata nifa kai nake so bana son wanda suke son aura min.. Mama ta min kallon banza tace" Amma Sanjina baki da hankali mutumin da ko hamshakin mai kudi zai ganshi sai da k'yar taya har kika ganshi kuma yace zai aureki? Ni ba wannan ba ma kin san dai ba abu daya muke bautawa ba, to ba ke bashi.. ina jin haka hankali na ya tashi na kwana ina kuka yau ina zaune kawai naga tashigo d'akina ta rufeni da duka, tace saina ce bana sonka ,ni kuma nace tayi hak'uri ta barni ina sonka shine ta ringa dukana har ta farfasa min jiki, daga karshe ma waje ta turoni da kayana kuma tace sai dai nazo gidan ku na zauna tinda kai nakeso, daga yau ko a hanya na ganta kar nace ita ta haifeni. Hakan ma bai mata ba ta sanya yara sukayi ta bina suna watso min k'asa" Ta karashe maganar tana sanya wani sabon kukan... Inna ta dauki salati tana fad'in" Muhammadu rasulullahi salallahu alaihi wasallam ni Indo, Kai amma Allah ya tsinewa halin wannan uwar taki yo ita haka ake rayuwa dan ba Addinin ku d'aya ba sai tace baza ki aureshi ba? To zan ga Uban da zai hana wannan auren ,kai Yusufa kuna fita masallaci da kun gama Sallah a daura auren Khalilu da wannan Yarinyar. Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace" To Inna amma zamu je mu bawa Iyayen ta hak'uri su bamu auren ta shikenan" Inna tayi mitsin-mitsin da idanu tace" Kaima dai Yusufa kamar wani Yaro wani lokacin, to bari na kira Musalle yazo sai ya daura musu auren" Khalil yace Inna bafa gaggawa akeyi ba Baba zaije ya nema min auren ta ba wai maidata za'ayi ba.. Mik'ewa Inna tayi ta kama hannun Sanjina tace" Dan Butar Uwaka yau nakeso a daura auren nan ko min dare, kuma ka kira Likita ya dubata wannan hannun nata kila ta karye ma, sai kawai Inna ta rushe da kuka tana fad'in" Wannan Uwar taki Allah ya tsine mata sau ďai-ďai har sau dubu, kamar bata san ciwon Haihuwa ba to ki rabu da ita wata rana zata zo ta nemeki a lokacin zan nuna mata nima tacacciyar marar mutumci ce" Tana gama fad'in haka ta damki hannun Sanjina ta jata suka yi dakin ta..


Jiki a sanyaye Khalil ya nufi d'akin shi, da sauri Ashma ta bi bayanshi tana goge kwalla....




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_