ABBA NE

Part 10

by @saratalkasum88

_*🌻ABBA NE 🌻*_






_Hakkin Mallakar_


_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_




_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_




_*Littafin na kud'i ne only N300, my WhatsApp number 👉🏻 +966577675904 *_



بسم الله الرحمن الرحيم



1️⃣0️⃣


A bakin k'ofar ta tsaya tana kallon shi kamar yau ta fara ganinshi, Juyowa yayi sai ya ganta a bakin k'ofa hararar ta yayi yace" To ki koma tinda baza ki shigo ba. Murmishi tayi ta taka zuwa inda yake,tana isowa ta kama hannayen shi duka biyun tana murmishi tace" Abbana! Murmishi ya subce mishi yace Na'am my Princess d'ina" hannun shi ta daura akan fuskarta tana kallon shi cikin idanu, Ganin hakan yasa ya gane mai take nufi" Jan hannun ta yayi suka zauna bakin gado ya janyo ta ya rungume yana shafa kanta. Lumshe idanu take tana k'ara lafewa a jikinshi dan ba k'aramin nutsuwa take ji ba in yana mata haka, shiyasa ko tayi kuka sai tazo wajan Abban nata ya mata haka. A hankali ta bud'e idanunta karaf suka sarke dana juna, Kallon kallo suke tsakanin su kusan ten minutes kamar baza su dena ba, ita ta fara janye idanun ta ta koma ta kwanta akan cinyarshi tana murmishi. Kuncinta yaja yace" My Princess ya ya akayi? Naga wannan bakin naki mai shegen surutu yana motsi da alama akwai abinda zaki fad'a min ne? Tashi tayi zaune kanta a k'asa tace" Abbana ka aureta Don Allah kaji" Ta fad'a tana zubar da hawaye. Girgiza mata kai yake yace Kin san abinda bana son gani a wajan ki zubar hawayen ki ko? Ki dena kukan muyi magana. Da sauri ta goge hawayen ta gyara zama tace Abbana ka auri Anty Sanjina kaji, ina sonta sosai tana da kirki kuma bata shigar banza duk da ita ba Musulma bace, amma Wallahi yadda take suturta jikinta wata Musulmar bazata yi hakan ba, ka aure ta kila ko nan gaba Allah yasa mu dace da babban rabo ta Musulinta, san nan ta haifa min K'ane ko K'anwa nima na samu D'an Uwa. Idanu ya zuba mata jin abinda take fad'a, dan murmishi yayi yace" Princess wani lokacin kamar babba kike in kina wata maganar ,wai wa yake koya miki irin wannan maganganun? Dariya tayi tana jan kuncin shi tace" Kawai daga ciki take fitowa Abba, kasan cikina yana da magana sosai daga nan take zuwa baki ni kuma sai na fad'a. Dariya yayi yana jijjiga ta yace" Eh lalle fa daga ciki take fitowa hakan yayi, zamuje gidansu a bamu auren ta daga yau anan za take zama . Yatsunta ta sanya a baki tana tsotsa tace" Abba za'ayi shagali ko? A'a babu abinda Za'ayi kedai kije waje gani nan fita zanyi wanka" Jinjina kài tayi ta mik'e ta nufi k'ofa,har taje bakin k'ofar ta juyo tace Abbana! murmishi kawai ya mata" sab'a baki tayi kamar zatayi kuka tace" Je t'aime" Murmishi yayi yace" I really love you so much my princess d'in Abban ta, Y'ar gatan Abba da Inna da kuma Papi din ta. Da sauri ta dawo ta rungume shi tana dariya tace" Abba inason koyon English kaji" Shafa kanta yayi yace ai da anyi conje de vacance shikenan in zaku koma za'a fara koya muku English. Tsalle tayi tace Kai naji dad'i to Allah ya kaimu da rai da lafiya,Ameen yace san nan ta wuce.. Yana ganin ta fita yaje ya kulle k'ofar zama yayi ba zato ba tsammani yaji hawaye na zuba daga idanun shi, gogewa yayi yana janyo wata loka dake kasan gadon ya bud'e, photon Iyayenshi ya rungume ya shiga yin kuka kamar wani karamin Yaro sai cewa yake" Abbana Umma na ina kewarku fiye da tunanin ku, ina fatan kuna cikin rahamar Ubangiji" Sai da yayi mai isarshi ya mik'e ya shiga toilet. Yana fitowa dama tuni su Baba na jiranshi shi da Abdul da Daddy Musa wanda bai jima da zuwa gidan ba, kai tsaye wucewa sukayi Masallaci...


Mansoor na zaune sun sakashi a tsakiya suna fad'a mishi abinda Boka ya fad'a musu, sai dariya suke. Alhaji Sammani yace" Dan iskan Sojan nan tinda baza mu iya mishi komai ba ta wannan hanyar sai kawai mu yiwa ita Y'ar tashi Ubanta ya Jaya mata shiga tarkon mu" Dariya suka kuma sanyawa har da tafawa a tsakanin su. K'uri Mansoor ya musu yana bud'e baki kamar wani sakarai, kauda mamakin yayi dan yasan kad'an daga cikin aikin mugayen Iyayen nashi ne ,sun kashe ma bare haukatawa ko maida mutum nakasashe, gyaran murya yayi yace" Am Daddy nace ba ita Ashma mai kukace ayi mata? Murmishi Alhaji Kabeer yayi yace" Munce Boka yake firgitata take fita a guje ana kamota, kaga daga nan zaka samu damar dauke ta ko. Tinda shi Uban nata ya gagare mu to mu koma kan makusancin shi da haka zamu ga bayanshi " Dam gaban Mansoor ya buga cikin rawar baki yace To yanzu yaushe ne maganin zai fara aiki?


To meye na gaggawa Mansoor? Yanzu Boka ya kirani yace Nan da wani lokaci zata soma shi kuma Ko ta halin Yaya sai mun san yadda zamu illata mishi rayuwa ba dai mu yake son kurewa ba.. dafe kai yayi yana binsu da kallo mik'ewa yayi a fusace kamar zai dake su yace" To Alkur'an idan kuka sanya Matata ta haukace nima nasan hanyar gidan Boka wanda ma ku baku sani ba, sai naje nasa a haukata ku kuma kusan zan iya aikatawa" Ya fad'a yana naushin bango san nan ya wuce fuu yana masifa har parlo ya iso Mommyn shi na zaune ta ganshi kamar an jefo shi" Mik'ewa tayi ta tareshi tana fad'in" Yarona lafiya wai ka shigo kamar an jefo ka? Kama hannùn ta yayi suka shiga daki ya zaunar da ita a bakin gado ya zuba mata idanu bai ce komai ba. Cikin sanyin murya tace" Wai baza kayi magana bane? Ajiyar zuciya ya sauke ya bata labarin komai da su Daddy ke son yi. Dafe kirji tayi tana salati tace" Eh lalle abun naku ya girmama wai don Allah mai General Khalil ya tsarewa su Daddyn ka ne? Saboda sun tsaneshi dan yana da gaskiya, dama sai da nace ki sato min Ashma mu gudu kika kiya yanzu gashi nan zan rasata" Ya fad'a yana goge hawaye.. dafashi tayi tace Karka damu indai Ashma Matar ka ce ko wani juyo za'a to saika aureta kaji,ka dena damuwa kuma ina rokon ka da ka dena shan giya kai shaye-shaye ma gaba d'aya ka dena indai har da gaske ne kana son Ashma.. murmushi Kawai yayi ya mik'e yana cewa" Okay Zan jarraba hakan sai na dawo" To Allah ya kara shirya ka, Ameen yace san nan ya fice da sauri ,sai cewa yake" Haba Mommy ai bazan deba shan giya ba har sai na auri Ashma, yau ni a club ma zan kwana nasha nayi tatul Wallahi. Dariya yayi yana fita waje ya shiga mota ya fita... Su Baba suna gama Salla bayan an fito suka nufi Unguwar Tanko pomp dan ganawa da Iyayen Sanjina" A k'ofar gidan suka tsaya Abdul ya buga, Mai gadin ne ya leko ganin Manyan mutane har wanda ko a mafarki bai tab'a tunanin zai gansu ba ya gansu a kusanshi" Baki na rawa yace" Sannun da zuwa Ranka ya dad'e.. Abdul yace yauwa Baba masu gidan suna nan kuwa? Eh suna nan, To kace sunyi baki" To yace ya nufi ciki da sauri jiki na rawa. Bayan kusan minti uku sai gashi ya fito yacè" Kuzo muje, binshi sukayi duk suna k'arewa gidan kallo" Khalil kuwa ran nan nashi a had'e yake dan sosai yaji zafin abinda aka yiwa Sanjina kuma duk saboda shi. Cikin dakin baki ya kaisu ya fita abinshi, suna nan zaune sai ga wata mata da Namiji da Yara uku biyu maza d'aya Mace. Dukkansu da tsananin mamaki Al'ajabi suka bin su Khalil da kallo, wai yau General Khalil ne a gidan su da Captain Abdul mutanen da suke gani a TV yau sune a gabansu , zama sukayi Baban Sanjina yace sannunku da zuwa Yallabai. Baba ne yace yauwa ina fatan dai kune Iyayen Sanjina ko? Cikin tsoro suka kalli juna sai kuma Baban nata yace Eh mune wani abu ne ya faru?


Gyara zama Baba yayi yace" Gaskiya baku kyauta ba abinda kuka yiwa Yarku" Sunkuyar da kai sukayi Baban Sanjina ne ya d'ago yana kallon su cikin girmamawa yace" Ranka ya dad'e ni bana nan ai abin ya faru sai da nazo take fad'a min wai ta kore ta saboda tace General takeso ba wanda muka zaba mata ba.. Baba ya jinjina kai yace To amma shi wanda kuka zaba matan tace tana sonshi ne? Shuru yayi sai Maman cikin ruwan masifa tace" Malam kar fa ku rena mana hankali har sai tace tana sonshi zamu aura mata shi, mu fa muka haife ta ba wani ba, muna da ikon zaba mata wanda mukeso, ba dai ta nuna D'an ku takeso ba? To taje ta aureshi amma baza tayi Addinin ku ba..


Khalil kam ya shaka sosai jin abinda Maman Sanjina take fad'a yayi shuru dai, Baba yace Da alama dai ba sonshi take ba dan haka D'ana takeso Khalil ba wanda ku kukeso ku bata ba.. Maman Sanjina ta K'ank'ance idanu ta shiga surfa masifa tace, Ai indai tana son taci gaba da zama yar mu dole ne ta auri Krista irinmu, Musulmai basu da amana.. Daddy Musa ranshi ya gama b'aci yace" Ke karki rena mana hankali mana ita Y'ar taki ba kin koreta ba kuma kin cireta daga cikin D'iyan da kika haifa ba? , to mu zamu riketa D'a na kowa ne" Kai kuma da ka zama lusarin Uba baka da iko ne a gidan ka har Matarka itace zata yanke hukunci akan abinda kaine ya kamata kayi shi, to tinda baza ku yarda ba zamu kai k'arar ku gaban Sarki muce zaku yiwa Yarku auren dole, da ta kiya kuka koreta" Daddy Musa ya fad'a yana baza Babbar rigarshi cikin jin haushi, saboda shi d'in yafi Baba fad'a kamar Inna yake.. Baban Sanjina da Mamanta jin abinda ya fad'a suka tsure Maman Sanjina tace" Kayi min rai indai itace ni nabar muku ma har abada ku aurawa D'an naku" Baban nata yace Ni dama ba son wanda Maman ta ta zaba mata nake ba, kawai dai dan tafi karfina ne shiyasa nayi shuru.. Baba yace" Kai ne Namiji ya kamata ace ka iya sarrafa gidan ka yadda ya kamata ,ko a Addinin naku ku haka kukeyi? Girgiza kai yayi yace" A'a kawai dai mafadaciya ce shiyasa ni kuma bana son tashin hankali, Amma muje waje a daura auren kamar yadda kukeyi.. A fusace Daddy Musa yace" Anan za'a daura ba inda zamu je ga Uban Yaro ga ku Iyayen ta.. Kud'i ya fiddo a aljihun shi zai mika sai yaga tuni Abdul ya mik'a kud'in daga wajan shi,yace GA sadakin ta nan jika Hamsi.. Khalil kallon Abdul yayi wanda yake murmishi" Amsa Daddy Musa yayi ya mik'awa Baban Sanjina, sai Baba ya ciro jika dari yace Wannan kud'in na gani inaso ne tinda abun lokacin daya yazo" Amsa Baban Sanjina yayi yana murmishi wai yau shine ya amshi sadakin Y'arshi mafi soyuwa a zuciyarshi.. Maman Sanjina ma shuru tayi sai yanzu taji ba dad'i data kori Y'arta gashi kuma Daddy Musa yace bazaa kawo musu ita ba.. Daddy Musa yace Salati goma ga Annabi Sallallahu alaihi wasallam" Bayan An gama daura auren Khalil da Sanjina suka shiga gaisawa suna cewa Khalil barka, shi kuma yana murmishi.. mik'ewa sukayi zasu tafi Maman Sanjina tace Yanzu ba zan ga Sanjina ba kenan? Ta fad'a a tsorace tana kallon Daddy Musa ta gefen idanu.. Murmushi Khalil yayi yace Zan kawo miki ita idan ta samu lafiya" Dad'i taji tace to me ma ake cewa yasa muku albarka? Dariya sukayi , Baban Sanjina yace" Ubangijin ku yayi muku albarka na baku amanar Y'ata. Ameen sukace suķa rakasu har bakin mota sai da sukaga tafiyarsu san nan suka dawo gida..


Maman Sanjina tace" Har naji ba dad'i kaga dukan dana mata kuwa? Had'e rai yayi yace ina zan gani badan su masu gaskiya bane kina tunanin har zasu iya yarda su tako kafarsu nan gidan ne? Idan kikayi sake Sojan nan ya fusata to ko ganin ta bazai bari kiyi ba saboda gidan su tsaro gareshi na gaban kwatance, burinki dai ta auri mai kud'i to gashi ma ta auro Babban Sojan da Duk K'asar Niger ake ji dashi.. murmushi tayi tana goge hawayen ta tace Pardon Maigida ba zan sake ba na san za ta samu kulawa fiye ma da tamu ma, amma ba ka ganin za ta iya komawa Addininsu? "To idan ta koma ma ai yanzu ta zama tasu tinda kin koreta" Cewar Baban Sanjina.. A'a bama zata koma ba indai har tana son ganina. Mik'ewa yayi ya wuce ciki ya barta a nan tana ci gaba da surutan ta...


Su Khalil na komawa gida suka samu Inna zaune a palo tana karkaďa k'afa sai hura hanci take ganin su Baba basu dawo ba. Da sallama suka shiga ciki Inna ta amsa musu sai kuma ta mik'e ganin suna murmishi. Mamy itama ta fito tana musu sannu da zuwa kamar da hadin baki sai ga Ashma sun fito tare da Sanjina wadda kanta yake naďe da bandeji har hannun ta daya.. Inna tace Da fatan dai kunyi abinda na Umarce ku dai ko? Zama Daddy Musa yayi yace" Sosai ma ai dan ma sun so su bamu matsala ne ma.. Inna ta kalli Daddy Musa tace Musalle su waye zasu baku matsalar? Iyayen ta mana Maman ce taso bamu matsalar" Inna ta sauko daga kan kujera ta zauna a k'asa ta rushe da kuka tana kallon Sanjina, tace" Amma ke dai bakiyi sa'ar Uwa ba mai sunan Jimina, Allah dai ya tsinewa halin Uwar nan taki yo in banda ma ta dauke mu Y'an iska taya za'a je neman auren Y'arta ta wani nuna gadara, ai ba sai tayi magana ba aka san ita ta haifeta. Mik'ewa Tayi ta koma kan kujera sai kuma tace" Musalle dan kan babbar rigar Uban Iyayen mai sunan Jimina gobe ka kaini gidan da kaina sai na musu wanki babban barko" Basu san nice Kakar Khalilu ba Uwar Umaruru, nifa na haifi Umaruru shi kuma ya haifi Khalilu, shine har akwai wanda zai nuna baya son had'a zuria da iyalina. Sake sakin kuka tayi har tana face majina,tace" Musalle yanzu an daura auren ne ko kuma ba'a daura ba na shigar da k'ara kotu? Daddy Musa cikin nuna kulawa ga Mahaifiyar tashi yace" An daura kuma Baban ta yace ya bamu amanar ta.. washe baki Inna tayi tace" Ke Mai sunan Jimina zo nan Matar jikana.. Sanjina dake dariya ita da Ashma ta iso wajan Inna tana jin kunyar su Daddy ta zauna a k'asa tace" Inna gani......





_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_