ABBA NE

Part 13

by @saratalkasum88

_*🌻ABBA NE 🌻*_






_Hakkin Mallakar_


_*Sarat Alk'asum (Maman Nusaiba)*_





_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



_*Littafin na kud'i ne only N300 No +966577675904 *_


بسم الله الرحمن الرحيم



1️⃣3️⃣



A guje suka nufeta tana k'ok'arin bud'e get din sai buga kanta take tana son ya bud'e ta fita, Rik'e ta sukayi gam ta yadda baza ta iya kwacewa ba amma ga mamakin su sai sukaga ta girgiza su ta watsar ta nufi gefe tana magana wanda suka kasa gane me take cewa" Abdul ya iso wajanta ya kama hannun ta cikin lallami yace" My Princess meyasa kike haka? Dariya ta sanya tana kallon hannun shi kamar taga sabon abu, sai kuma ta sanya kuka kamar wadda aka zane.. Khalil kuwa kasa motsi yayi saboda tsananin tashin hankali, lafiya lau ya kai ta ya kwantar amma yanzu ta tashi tana abu irin na masu tabuwar kai" Ita kuwa Ashma ganin bazai sake ta ba ta warce hannunta ta koma gefe tana ci gaba da kuka, ta soma fad'in ABBA NE zasu kama shine nazo na kashe su, gasu cen suna cewa ni Y'ar Uwarsu ce naje mu tafi cen inda suke, nidai ku matsa na wuce" Papi kai baka ganin su? Zabura tayi ta shiga buga kanta da katanga tana cewa" Sai na kasheku indai kuka taba min Abbana zan zane ku.. Ganin zata illata kanta Khalil yayi karfin hali ya aro jarumta ya iso inda suke, a hankali ya kamo hannayen ta sai kuma ya shigar da ita jikin shi" Kiciniyar kwacewa ta soma yi tana surutai irin na wanda suka haukace, Cikin rudewa Khalil ya matse ta yana maida numfashi shi kanshi jikinshi rawa yake kamar ya fasa kuka yakeji ganin halin da Y'ar tashi take ciki. Saitin kunnen ta ya matso bakinshi ya shiga karanto Ayatul kursiyu. Tin tana motsi har tayi lakwas" Ganin yaki motsawa ne yasa Abdul amshe ta ya nufi ciki ta ita, Mamy kuwa tuni ta ringa kuka" A kan kujera ya shinfide ta yana kallon ta cikin tausayawa.. Baba yayi tagumi yace" Wannan wani irin abu ne Ashma tayi? Ko dama tana da Aljannu ne bamu sani ba? Girgiza kai Khalil yayi idanunshi sun canja launi saboda tsabar tashin hankali yace" Gaskiya Baba bana tunanin hakan da tana da aljannu ai da mun sani,kawai dai ciwon yau din nan ne kuma yanzu yanzu ya sameta... Mamy ta bud'e baki zatayi magana suka ji ta kwalla k'ara tana firge-fisge Sai wasu yaruka take wanda ba wanda yasan me take nufi.. Da sauri Khalil ya dauko ta ya rungume yana shafa kanshi yayinda ita kuma take zabura irin kamar ta tsorata sosai d'in nan.. karatu ya shiga yi a fili ya k'ara matse ta dan kar ta kwace Abdul ya rik'e kafafuwan ta cike da tausayawa.. Inna ce da Sanjina suka shigo gidan A kidime, suna shigowa a bakin get Direba ke basu labarin abinda ya faru shiyasa suka shigo ba ko sallama. Inna tayi zaman Yan bori tana kuka tace" Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un Ashmatu menene ya sameta haka? Baba yace Muma dai bamu sani ba Inna muna zaune kawai ta fita a guje" Sanjina ta kurawa Ashma idanu tuni ta gano abinda yake damun ta, hankali a tashe ta zauna tana kallon Baba tace" Baba wannan fa sihiri ne aka mata. Baba yace To taya kika gane Y'ata? Jinjina kai tayi tace" A k'asar mu Babana posto ne duk wanda aka yiwa asiri to kamar yadda Ashma takeyi shima haka yake, Dan haka mu kaita gun Babana ya mata magani" Ta fad'a tana zubar da hawaye dan ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba ganin abar k'aunar tata a wannan hali.. Khalil ne ya d'ago ganin Ashma tayi bacci yace" Mungode amma kiyi hak'uri mu Musulmai ne idan mukaje wajan Babanki yayi irin abun ku to mun sabawa Ubangijinmu , dan haka Malamai kawai zamu kira su mata rukiya.. A sanyaye tace To ba komai Amma ka kirasu yanzu mana" Inna ta face majina tace" Yusufa ku kira Malam Nafi'u yazo ya mata rukiya. Baba yace" To shikenan ina fita da mun had'u a Masallaci zanyi mishi bayanin komai sai muzo tare. To Inna tace tana shafa kan Ashma cike da tausayawa ganin yadda fuskarta ta jike da jini" Kallon Khalil tayi tace" Kai kuma ka kira Doctor Ma'aruf ya wanke mata raunikan dake jikinta.. Abdul ne ya kira Doctor Ma'aruf ya fad'a mishi yazo gida suna neman shi, gashi nan yace san nan sukayi Sallama..


Motsi ta soma tana fad'in" ABBA!ABBA! take fad'a a hankali" Khalil ya shafa fuskarta yace" Na'am My Princess bud'e idanun ki gani a tare dake. Bud'ewa tayi ta ganta a jikinshi k'ara k'ank'ame shi tayi tana sakin kuka, tace" Abba na ganshi Wallahi.. Khalil yace waye kika gani? Wannan wanda nace ma mai kan jaki yana min dariya shine na gani yana bina zai kamani, kuma.. kasa K'arasa maganar tayi taci gaba da kuka. Bubbuga bayanta yake yana fad'in" Ba abinda zai sameki kinji. Ashma tace Nidai tsoro nakeji Abba karka tafi ka barni kaji" Ta fad'a jikinta na rawa.. duka Yan palon tausayi ta basu Inna kuwa ta rafka tagumi tana kallon su tama kasa magana...


*Nigeria*


Hisham ne yaje ya samu Daddy a d'aki, cikin girmamawa ya gaishe da Daddy" Amsawa yayi cikin sakin fuska sai kuma ya k'ura mishi idanu ganin yadda ya rame sosai, yace" My Son baka da lafiya dama? Kanshi a k'asa yace" Daddy zazzabin dare nakeyi amma jiya da yau banyi ba Alhamdulillah naji sauki. Ajiyar zuciya yayi yace To Allah ya k'ara lafiya" Ameen Hisham yace sai kuma yayi shuru.. kusan minti uku suna a haka kafin Hisham yayi karfin halin fad'in" Am Daddy dama nazo maka da wata magana ne, amma ban san me zaka fad'a akai ba. Gyara zama Daddy yayi yace" Okay ina jinka Son. Hisham yace" Daddy kuyi hakuri da hadani aure da Layla" A fusace Daddy yace" Saboda baka son auren ko? Wai kai anya ma kuwa kana da lafiya? In ma boye mana kake gara ka fada mana gaskiya asan abinyi" Kunya ce ta kama Hisham yace" A'a ni lafiya lau nake Daddy kuma bani bane bana son auren Layla ce.. Daddy yace ko kuwa ka zare mata idanu ba shiyasa taji tsoronka tace bata so mana. Dafe kai yayi yace" Don girman Allah Daddy ka bari na maka bayani yadda zaka fahimceni. Daddy yace tam inaji" Daddy yau da kwana uku Layla tazo gidan nan tana kuka kamar ranta zai fita, tacewa Ammi ta bani hakuri ita tana da wanda takeso kuma ta kawowa Kawu shi ,amma yace Sam bazai yiyuba dani zai hadata aure" Shine Ammi tace tazo tamin magana zan fahimce ta ni kuma ina jinsu lokacin da suke magana, Nan dai ya fad'a mishi duk abinda ya faru ya k'ara da cewa" Daddy ku taimaka kada kusa Aminina yake min kallon maci amana tinda nasan suna soyayya da Layla, ban san wani hali zai shiga ba idan aka rabashi da Layla don Allah ku barsu su auri junan su na tabbata Khalifa zai rike Layla tamkar yadda zan rike ta ko fiye da haka ma" Kai kanka ka yaba da halin Khalifa yana da hankali gashi da kirki yasan darajar manya, to a halayen D'an Adam me kukeso Khalifa yayi wanda kuke ganin shine abinda ya hana ku bashi Layla? Hisham ya fad'a yana dagowa ya tsare Daddy da idanu.. Daddy ya kalli Hisham sai kuma ya janye idanun saboda wani kwarjini Hisham ke mishi idan suna kallon juna, sai yaga ya cika mai idanu, ajiyar zuciya ya sauke yace" To duk naji abinda ka fad'a ai ni Muntari baice mini wani yazo neman auren Layla ba, kuma kayi tunani mai kyau hakan zai lalata Abotarku wanda tin kuna Yara kuke tare, tashi kaje zan kira shi Muntarin muyi magana. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kana ya mik'e ya fita. Rufaida dake bakin k'ofa jin ya fito ta rabe a bakin k'ofar" Yana zuwa ta sanya k'ara yaja da baya yana zare idanu.. Dariya tayi tana cewa" Abie yaji tsoro, kama hannayen ta yayi suka k'araso palo. Kallon shi tayi tace" Abie ba dan ba Layla Uncle Khalifa takeso Wallahi daka aureta tana da kirki. Jinjina kai yayi yace" Hakane Daughter tana da hankali shiyasa nakeso Abokina ya aureta. To Abie kai fa yaushe ne naka auren?" Ta fad'a tana jan hancinshi. Yar dariya yayi yace" Kinga bana son shirme d'agani in fita Khalifa na nema na" B'ata fuska tayi tace" Abie kaje dani. A'a baza ki bini ba wani guri ne zan rakashi kuma akwai nisa" A sanyaye tace To Abie a dawo lafiya" Allah yasa Daughter na" Ya fad'a yana wucewa daga palon..


Khairat ta shiga damuwa na rashin kiran da Hisham baya dauka nata" Kwafa taja tana cewa saina sake komawa gidan K'awata.. Da dare bayan Sallar Isha'i ta dira gidan K'awarta sai dai kuma bata sameta ba sai Mijinta ta tarar a palo a zaune.. Da murna ya tare ta yana fad'in" A'a su Khairat manyan gari kece yau a gidan namu? To Bismillah zauna na kawo miki ruwa" Ya fad'a yana mata wani irin kallo ganin yadda ta sanya ringa da wando yan kanti, kayan sun kama ta sosai komai nata gashi nan a fili.. Cikin iya takun ta na makiran mata ta kalleshi itaba, a ranta tace Shegiya K'awata ta more Miji wannan hadaddan Namijin ai dole take kishi a kanshi.. Shi kam tuni ya wuce kitchen ba jimawa ya kawo mata ruwa da lemon mai sanyi" Zama yayi a kusan ta yace" Yauwa kisha ai K'awar taki tin jiya ta tafi bikin wata Y'ar Uwarsu a cen dangin Babanta, bata ce miki ta tafi ba? Ya fad'a yana kashe mata ido.. Murmushi tayi tace" Ina ai bamuyi waya ba nayi busy yau ma zuwan bazata naso na mata ashe bata nan, To bari na tashi na wuce tinda mai gidan ta fita" Ta fad'a tana k'ok'arin Mik'ewa.. Da sauri ya rik'o hannunta yace Haba ni ba Mutum bane ai sai ki zauna muyi Y'ar hira dama ni kad'ai ne a gidan duk na shiga tunani gashi ina j.. saurin yin shuru yayi dan kar ya fad'a kuma ta mai wani kallo.. komawa tayi ta zauna tace" Ayya gaskiya na tausaya maka kai d'aya a gida, to sai dai kasan ni bana aikin banza sai an biyani. Wani shu'umin Murmushi yayi yace" Baki da matsala Baby ko me kikeso zan baki" gyara zama tayi shi kuma ya bata runguma kamar wata Matar shi.. suna nan zaune suna shashancin nasu ganin Palon bai musu ba suka wuce d'aki, acen suka aikata alfashar su( wa'iyazubillah Allah ya shirya mana Al'umma) . A takaice sai k'arfe 11:00 pm dai-dai san nan Mijin K'awar Khairat ya maidata gida har sai da sukayi canjan number san nan suka rabu..


*Niger*


Sai da Ashma tayi kwana goma tana jinyar kanta san nan ta warware" Malam Nafi'u nayo mata rubutu kullum tana sha wani lokacin kuma yazo har gida ya mata Addu'a. Abin Mamaki daya soma janyo ayoyi Aljannun suke bari jikin Ashma hakan yasa Malam Nafi'u yace Gaskiya Aljannun jikin Ashma masu wayo ne guduwa sukeyi sai dai ake mata rubutu kawai tasha daga haka zasu barta. Jiki a sanyaye duk suka mata fatan samun lafiya, ita kuwa Ashma tuni ta rame sosai ta k'ara fari sai bacci kamar k'asa ko abinci sai taga dama take ci shima sai lokacin da Khalil ya dawo daga aiki yake lallab'a ta ya bata taci..


A hanzari ta fito sanyi da kayan Makarantar ta" Mamy tace" To sai Ècole su Ashma? Jinjina kai tayi tace" Eh ina son naje na had'u da Kawayena Yan wasu garin nayi kewarsu. Murmishi Mamy tayi tace"To shikenan ga abinci nan zauna maza kice in dai baki so Abban ki yayi fushi.. tana turo baki ta zauna sai wani yatsina fuska takeyi da haka dai taci kad'an ta mik'e" Mamy tace har kinyi me? Yo Mamy so kike cikina ya fashe ni sauri fa nake zanci abinci acen idan mun taso. Mamy tace To a sauka lafiya" Allah yasa tace san nan ta fita da saurin ta" Tana isowa suka bud'e mata mota tsayawa tayi jin suna gaishe ta, B'ata fuska tayi tace" Gaku nan manya daku kuke wani ce min ranki ya dad'e, to ni bana so ku bari nake gaishe ku tinda kun girmeni. Wani daga cikin su ne yace" To ai ba komai dan mun gaishe ki. Ashma ta turo baki tace" To Nidai karku sake gaisheni ni zanke gaisheku, To sukace ganin tana B'ata lokaci" Shiga tayi Direba yaja suka bar gidan...


Alhaji Kabeer ne da sauran Abokan nashi zaune wata Matashiyar Budurwa na zaune gaban su sai busa shisha take tana musu kallon uku saura kwata. Alhaji Mati yace" Mery da fatan dai kinji abinda mukeso ki mana? Aje kayan shishar tayi ta kallesu cikin murya maye tace" Na kuwa jiku Alhajin Allah, yanzu to yaushe kukeso na fara aikin akanshi? Gyara zama Alhaji Kabeer yayi yana murmishi yace" Nan da wata ko sati uku saboda zamuyi tafiya ta kwanaki zuwa k'asar Chadi duk lokacin da muka shigo zan kiraki sai ki fara aikin, inaso kiyi komai muna nan kin gane! Dariyar Y'an Duniya Mery tayi tace" Baka da problème Alajin Allah, zaku ga aiki da cikawa duk abinda kukeso nayi zan aiwatar.. cikin jin dad'i Alhaji Sammani ya fiddo kud'i masu yawa ya aje mata a gaban ta yace GA somin tabi nan asha giya asha kodin da shisha kafin mu dawo.. Mery taga kud'i masu yawa tuni ta susuce tana fad'in" Baka da Matsala da kun dawo ku taboni a waya kawai. Mik'ewa sukayi dukkansu suka bar gidan Mery sai dariyar mugunta suke....


Ashma sun taso daga École ta samu guri cen bayan class din nasu ta zauna ganin direban nasu bai zo ba" Kamar daga sama taji ance" Ashma Baby! A razane ta waigo ganin wanda ya yake tsaye a kanta kamar zai fad'o mata yasa taja da baya jikinta na rawa....






_*Taku har kullum Maman Nusaiba