chapter 37&38
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*
*AREWABOOK$✍️*
FACALA:: https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60
*UMMU MAHER COLLECTION👛👠*
***
EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️37 & 38
........... cike da mugun ruɗani ta buɗe bakinsa zai yi magana, me martaba ya wurga masa wani wahalallan kallo, sai kuwa yaja bakinsa yayi shiru ya yinda me shaida ɗaurin auren ya kamalla da ce wa" abisa asalin sadaki naira dubu ɗari biyar".
Tuni aka fara rabon goro da dabino, kowa kaga bakinsa a washe sai dai wasu ƴan tsirarun mutane ƴan hana ruwa gudu,ciki kuwa har da ƙannen me martaba waɗanda suke ciki ɗaya da kuma ƴan uba, waɗanda sukaso ace ƴaƴansu aka baiwa.
shi kansa shamaki kasa ko da matsawa yayi daga inda yake, tausayin yarima ya tsarga masa azuciya saboda me za suyi masa auren dole? don shi ya tabbatar yarima ba son yarinyar da aka haɗashi da ita yake ba, saboda haka da sun barshi ya zaɓo matarsa da kansa shi a ganinsa hakan ma wata fa'ida ce ta bada ƙofar sake saken da akeyi a aure, don auren dole yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara yawaitar zawarawa da kuma ɓata gari.
kasa magana ya yi har zuwa lokacin da kowa ya watse, masu tayasa murna na yi masu kuma baƙin ciki suka watse suna tafiya suna tunanin zuci.me martaba yana inda ya ke bai tashi ba tare da ƴan fadarsa da, ya kasa ko da motsawa har me martaba ya sallami kowa daga shi sai ɗansa sai kuma waziri dake gefe, yana taunar yatsa baƙin ciki fal zuciyarsa tamkar dai zai shaƙe su.
Me martaba ya kira sunansa cikin murya me ɗan amo ya ce"Aliyu inason baka haƙuri abisa wannan auren dana ɗaura maka yau kai da ƴar uwarka, sai dai ni nayi haka ne don in baka haƙƙinka wanda nake ganin kamar na danne maka ada, don a wannan shekarun naka yaci ace kai ma kana da iyalinka har da zuri'a ma, saboda haka ga ƙanwarka nan Amira yau dai an ɗaura muku aure, ka zauna da ita tsakani da Allah kada ka tauye mata haƙƙinta wanda ke kanka, idan kayi haka tamkar ka tozartani ne wanda ni ne nayi maƙasudin ɗauruwarsa,Allah ya yi maka albarka ya baku zaman lafiya me ɗorewa, sannan gidane dake cikim estate ɗinnan zaka zauna, me part biyu ne saboda haka ka faɗamin idan bai yi maka ba sai a canja maka"?.
bai saba musu da iyayensa ba, tun da can ma balle kuma yanzu daya mallaki hankalinsa, duk da kansa dake masa matsanancin ciwo amman duk da haka ya daure ya ce"me martaba ni duk abinda ka tsara arayuwata me kyau ne, ban isa ko inyi musu ko ja da ra'ayinku ba, sannan ra'ayinku ra'ayi na ne, saboda haka duk abinda Allah ya tsara zai faru arayuwata ban isa na hanasa ba".
Me martaba ya ce"kaje Allah yayi maka albarka, Allah yasa albarka a auren sannan ka dawo gida yau duk inda kake, part ɗinka yana nan a mazaunin naka ko da kayi aure zaka iya nishaɗi ka shiga".
ya tashi yayi gaisuwa sannan ya fita.
Waziri baiji daɗin duk abinda ya faru ba, saboda haka ya ce"Allah yajada ranka, sai naga kamar fa wannan dama ce da Yarima zai ga kamar baiyi komi ba, baya ga abubuwan daya aikata amman ka gafarceni idan nayi maka laifi".
Me martaba ya murmusa duk da bai gane inda wazirin ya dosa ba, amman sai ya ce"waziri kenan ni kuma aganina wannan itace hanya mafi sauƙi da zan nunawa yarima kurensa akan abinda ya aikata ɗin, don kasan ance inda ba ƙasa nan ake gaddamar kokawa, kasan yarima ba zai taɓa gano matarda tayi masa ba, saboda ko kallon matan ma ba yi yake ba saboda haka kaga ni na sauƙaƙa masa hakan, sannan ko da wannan abinda ya faru ni aganina tamkar aƙwai lauje acikin naɗi, ba halin yarima bane neman mata balle kuma har ya kai ga yiwa yarinya fyaɗe ta haihu? gaskiya aƙwai dai abinda ya faru har hakan ta kasance".
tsabar haushi waziri kasa magana yayi, sai tura ƙeyarsa da yayi gefe yana kallon wani sashen.
Yana fitowa kai tsaye ɓangarensa ya nufa, shamaki ya biyosa har zuwa ɓangaren na sa, ya danna lifta nan da nan sai ga shi a ɓangarensa.
Shamaki ya zauna ɗaya daga cikin lumtsuma lumtsuman kujerun da suke falon, Galadima ya shige zuwa ɗakinsa bai san lokacin da wasu zafafan hawaye sauka akan kuncinsa ba, duk abinda zai sanya wannan tattaurar zuciyarsa tasa kuka to ba abune na wasa ba, bai san me yasa rayuwar ke canja masa zuwa haka ba, duk matar da zai aura cutar ta zaiyi don ba zai taɓa iya zaman aure da ita ba, sannan itama ba zata iya zaman aure dashi ba, saboda wani ginshiƙin daya lulluɓe gajimaren hadaran rayuwar da ta ƙawanye rayuwarsa ta hanasa sakat.
Shamaki ne ya dafa kafaɗarsa tare da ce masa"sai haƙuri Galadima, kasan komai muƙaddarine sannan duk zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi, saboda haka kayi haƙuri ka karɓi wannan auren a matsayin ƙaddararka, wacce duk inda kake sai ta bika".
kasa ce wa komai ya yi, don dama ba maganar yake sha'awar yi ba, haka shamaki ya zauna kusa dashi har ya tirsasa shi yin wanka, duk da yana ganinsa a matsayin ɗan sa ido da kuma ɗan takura, ammam duk da haka mutum alkhairi ne me girma sai yaji duk zuciyarsa ta ɗan ragu da harba masa ɗin da take yi.
Fulani ta kalli ƙanwarta ta ce"yanzu kina ganin ya kamata ace Yarima ya gujemin aduk waɗannan ranakun? Duk da shi ne yayi min laifi? mi zaisa yayi hakan? jin kansa ya girma kenan har yayi doron zabuwar daba zai iya zuwa neman gafara ta ba"? . Ta faɗi hakan tana kuka tare da nuna kanta.
Lanta ta dafata cike da tausayawa ta ce" kiyi haƙuri yaya komi yayi farko yana da ƙarshe, ke kika haifi yarima amman na fiki sanin waye shi ɗin, sam baya son zuwa wajenki ne saboda kina fushi dashi har sai kin sakko, amman baiyi hakan don tozarta ko wulaƙantaki don jin shi ya isa ba, kema tun farko kinyi kuskure yaya da baki zauna da ɗanki kinji matsalarsa ba, abin takaici abin haushi ya kasa ɗakko ɗansa don ya kawo miki domin me? yasan za ki iya tsine masa saboda haka, zamanin fa yaya kiwon mutum ake bana dabba ba, ki tsaya kiyi tunani akan wannan matsalar ni ina ganin yarima ba zai taɓa yiwa wata ɗiya ciki ba, har sai da hukunce hukuncen ɗaurin aure akanta, sannan duk hakan zai iya faruwa saboda haka a wannan gaɓar zan iya ce miki fushinki shi ne ya ƙara komi, sannan kuma ki dinga tunawa da maƙiyanku yaya,kada ki dinga tunawa da masoyanki don su zasuyi komi ne saboda suga sun lalata rayuwarki da ta ɗanki, sannan shi maƙiyi idan zai sare ka da adda ba lokaci ɗaya yake sara maka ba, sai yayi tunanin ta inda zai biyo maka kaji haush fiye da sanin me tunani, kamar dai yadda aka yi hakan don ganin an haɗaki da ɗanki, don kuwa ganin ke kinfi ƙarfinsu sai akabi ta hanyar ɗanki, wanda idan ke aka yiwa ba zai miki ciwo kamar ɗanki ba".
Sosai jikin ta yayi sanyi, ta tsaya cak da hankalinta waje ɗaya don tuno ilahirin abubuwan da suka faru a baya, da saurin gaske ta tashi tana ce wa"Lanta ya zama dole a binno asirin daya daɗe abinne, don kuwa cutar da yarima an daɗe anayi, tun wasu zamani da suka shuɗe a zuciyoyin shuɗaɗɗu masu sakaci irinmu, saboda haka zan tashi tsaye ganin komai ya zama tarihi a yanzu kuma ba sai an jima ba".
Tana faɗar hakan ta tashi zata fita.
Lanta ta riƙo hannunta cikin tausayawa ta ce"Amri zai nan".
tayi mata magana da fillancinsu.
Lanta ta murmusa duk da zuciyarta cike da takaici take fal sannan ta ce" haba ranki ya daɗe, me babban ɗaki amaryar sarki me babban masarauta, uwar yarima uwar mata, ina kuma zaki a irin wannan yanayin? Ai fita bata taso miki ba, zama waje ɗaya tare da kafe kunnuwanki kamar baki san komi ba shi ne abinda ya kamata, sannan ki ɗauki waya ki kira sahibin ruhinki yarima, wanda ko ban faɗa ba nasan daga me martaba sai shi, mu kuma muna gefe ba a tamu".
ta faɗa cike da zolaya.
Lanta kenan aƙwaita da son sanya mutum farim ciki ko da ita ɗin tana baƙin ciki, itace autarsu a ɗakinsu wanda suka kasance su huɗu mata namiji ɗaya.
da kanta ta kira wayar ɗan nata, cike da son jin muryar ɗan nata tuj tsahon ƙwana biyu da duka wuce.
cike da zumuɗi ya ɗaga bayan shamaki ya bashi wayar, da har ya ce ya barshi baya son hayaniya sai kuma ya ɗaga da fara'a ya"ranki ya daɗe, daman na bari ne ki sakko".
dungure masa kai tayi kamar dai yana gabanta, abin gwanin burgewa sannan ta ce"kazo ina nemanka yanzu". sai ta kashe wayar cike da son ganinsa.
*** *** ***
Hj. Rabi ta ce"Amrah kina cikin hayyacinki kuwa? kinsan waye yarima da kike son sai kin cusa kanki jikinsa? ba zai taɓa iya zama da kowacce mace ma ba ke ba, ke ɗin da kike banzartar da kanki a wajen yawon paty da asarar lokaci wajen yawon ƙasa ƙasa? ahalim yanzu ma mahaifinsa ya basa mata, wacce take a matsayin ƴar uwarsa wacce itama na tabbatar da ba iya zama da ita zai yi ba, saboda wani yanayi da ba kowa zai iya faɗarsa ba, amman ina me gargaɗinki da ki ciresa aranki, sannan kada ki sake inji wannan maganar a bakin Dadynki".
Amrah ta kasa magana tsabar takaicin abinda mahaifiyarta ta ce, to wannan dalili ne da za aƙi auren mutum? Don kawai anyi masa aure? Auren ma auren dole daba matar ya keso ba? saboda haka ita yanzu ma ta fara sonsa, duk kuma abinda zai faru sai dai ya faru amman sai ta auresa ko da tsiya ko da tsiya tsiya.ta kaɗa kanta ta fice ba tare da ta ƙara kallon mahaifiyarta ba, don dama ta daɗe da sanin ba sonta take ba, tafi fifita wasu da ita saboda haka zata fita a harkarta kawai, don indai akan yarima ne bata jin zata ragawa kowa, ciki kuwa har da HJ. Rabi mahaifiyarta.
*** *** ***
ganin ina nuna tsohon cike da firgici Ammi ta ce"lafiya adawiyya? nasan dai baki son tsoho ba? don sanda kike zuwa gidan nan kina ƙarama".
Tsoho ya murmusa irin yadda tsoffi kan yi lokacin da wani abu ya shige musu duhu,bai yi magana ba ya nunamin wajen zama da hannunsa, na zauna ina me kallonsa cike da tsoro sannan kuma aɗan ɗarare na zauna, dom har ga Allah ban yarda da tsohon nan ba.
Ammi ta ƙara maimaitamin tambayarta? don taga yadda na zauna tamkar zan ruga da gudu, ina hawaye na ce"Ammi shi ne mutumin daya ke zuwarmin a mafarki, yana yawon jana zuwa wani haske, da mun kai zamu faɗa wannan hasken sai wasu suzo da baƙaƙen kaya su janye ni ina kuka ina kallonsa".
Ammi ta ce" daman da tsoho kike wannan mafarkin?".
Na ce"eh" a raunane.
Tsoho ya kalleni sosai ya ce"Adawiyya ni kakanki ne,bazan taɓa cutar dake ba don kuwa ke ɗin jikata ce,da kakanki wanda ya haifi mahaifiyarki dani uwa ɗaya uba ɗaya muke,sannan ba komi ne ya sanya mahaifiyarki rabaki da wannan gidan ba, sai wani shuɗaɗɗan al'amarin daya wuce wanda bama fatan sake ko da fatan rabinsa ya faru, sannan ni da kike ganina a mafarki fuskata ce dai kike ganin Allah ya nuna miki tunda dai an nisantaki dani".
Ammi tayi saurin buɗe baki za tayi magana yayi saurin dakatar da ita da ɗaha hannunsa guda, ba tare daya kalle ta ba ya ce"Zulaiha kenan, kin ɗauka saboda rabata da gidan nan dukkanin ƙaddarorinta sunzo ƙarshe kenan? Abu ɗaya yasa ɗan adam a wani yanayi ne, shi ne rashin yarda da ƙaddara sai ki ga Allah yana ta gwadamu da imaninmu, cinye jarrabawar rayuwa shi ne ya ke nuna lallai imaninka ya kai, duk da kin rabani da ita addu'ah nake binta da ita a koda yaushe, sannan ina roƙar Allah ya gwada mata fuskata ko da kuwa a mafarki ne, kin isa hana hakan? Ai da Allah ya tashi sai ya nuna miki baki isa ba ɗin, sannan sai yanzu da kika ga kin bar bashin gabar dani kika dawo"?.
Shiru Ammi tayi gami da sunkuyar da kai, hawayenta ya kasa ɓoyuwa har sai da suka sakko, ni kuwa na tsani ganin Ammi na kuka sai nima na fashe da kuka don aganina tamkar ci mata mutunci tsoho ke yi.
bai hanata ba, har sai da tayi mai isarta sannan ya ce" duk garin nan kina da wanda ya kai ni ne"??.
Ta ce"a a".
ya gyaɗa kai, sannan ya ce" to ya bayan rabuwa kuma? don nasan abubuwa da yawa sun faru har da abinda kike gudu acan baya ɗin".
da mugun sauri Ammo ta kallesa, don tasan tsoho tsaf duk abinda ya faɗa a baki to ko bai gani da idonsa ba ya riga daya gani ɗin, don mutum ne me mugun hangen nesa da kuma hango abinda ka birne a zuciyarka.
babu abinda Ammi ta ɓoye masa game da abinda ke faruwa, tun daga farko har zuwa ƙarshe.
Tsoho ya yi murmushi sannan ya ce"DA KUMA SAURAN RINA A KABA KUMA BA............"
sosai ni da ita muke kallonsa saboda firgici da ruɗani bisa fuskarsa me nuna tsofa..........soon➡️
FACCALA NOVELS FANS
***
L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA
*NABIHA DATA SERVICE*
kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.
MTN
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
3GB. 900
_____
GLO
500MB. 150
1GB. 300
2GB. 5,50
3GB. 850
_________
AIRTEL
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
5GB 1,200
__________
9MOBILE
500MB
500MB 150
1GB. 250
2GB. 450
3GB. 600
Via:-
5458227606
Nabiyyah Aminu
Moniepoint
my no
***
*MRS GREEN CE*