chapter 39&40
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*
*AREWABOOK$✍️*
FACALA:: https://arewabooks.com/book?id=6582a28d4ede3c5852b6cb60
*UMMU MAHER COLLECTION👛👠*
***
com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️39 & 40
...........ɗan murmushin nan na sa ya yi, irin na tsoffi sannan ya ce"Zulaiha abinda nake so ko gane shi ne kika ƙi ganewar ahalin yanzu, ki kasance me yarda da ƙaddara akoda yaushe, sannan babu yadda za'ayi kace wai kai kafi ƙarfin a jarabce ka, ki tuna fa iyayenki yau shekararsu nawa da rasuwa? suna da kusan shekara 20 yanzu kaf ahalinki suka mutu a jirgi, mahaifinki, mahaifiyarki, ƙannenki biyu, yayyinki uku, kinga kuwa ko a nan aka tsaya yaci ace kinsan ƙaddara me kyau da mara kyau, abinda ya faru kika ɗauke ƴarki ba fa shi ke nuna shikkenan an dena jarabtarku ba, shi bawa ana son ya zamana ko da yaushe cikin shirin ko ta ƙwana, sai dai addu'ah ya kamata ka dage da ita akoda yaushe, na farko ka tsaida sallah, na biyu ka bautawa ubangijo tuƙuru da kuma addu'ar samun rahama duniya da lahira, sannan kuma ka dage da addu'ar cinye ƙaddara me kyau ko mara kyau".
kukan Ammi tsananta sosai, har tana fyace majina nima sai na ƙarawa kukan nawa bolum don ganin majinginata tana kuka wato mahaifiyata, bata taɓa bani wannan tarihin na ta ba sai yau, abu ɗaya take faɗamim kullum shi ne iyayenta sun rasu, amman bata taɓa faɗamin maƙasudin mutuwar tasu ba.
Tsoho ya gyara zamansa sannan ya ce" ku kasance masu haƙuri da duk abinda xai faru, don kuwa indai baka mutu ba to fa tabbas ba a gama yi maka jarrabawa ba, saboda haka aƙwai rubutun da zan dinga mata dai ki dinga zuwa kina amsa, sannan duk halin da kika tsinci kanki kada kiyi ƙasa a gwiwa kizo ki amsar mata, saboda ita ayar Allah tsari ce sosai daga dukkanin abin ƙi".
Sosai muke ta masa godiya, ya ɗakko wani ɗan mitsitsin allo ya rubuta ayoyin Allah sannan ya wankesu ya bani a wani ɗan ƙoƙo.
Na amsa na shanye tas, duk da ina cike da tsoro amman haka na daure nasha, sai kuwa ya fara tsokanata da ce wa" sai haƙuri fa ƴar lelen babarta, don ko da yaushe zaki dinga sha ne ko da kuwa bana wajen, don naga ina wajen ma kina kallon gyatumarki kina ya mutsa fuska".
murmushi na ɗanyi, ba tare dana ce komi ba sai kuwa ya ce" ku shiga cikin gidan ku gaisa ko? daman wannan satin me bikin Isma'il".
a matuƙar firgice naga tana kallon tsoho, ina kallon yadda gabanta ke luguden faɗuwar gaba, shima ya fuskanci hakan amman da ya ke tsohon ya iya shariya bai ko kalle ta ba.
Muka shiga gidan duk jikinmu a matuƙar sanyaye daga ni har ita Ammin, a babban tsakar gidan muka haɗu da matan Tsoho da kuma matan ƴaƴansa wasu na daka wasu suna girki wasu kuma suna wanke wanke.
sosai suka ji daɗin zuwanmu musamman ma uwar gidan tsoho, wato Inna Sa'ada ta fara tsokanata da ce wa"oh yau sai ga jikata agidan nan, da aka rabani da ita don san ran gyatumarki".
Ni dai dariyar yaƙe kawai nake don har ga Allah kai na ya yi mugun kullewa akan wannan sarƙaƙiyar da suka jefa ni, wai an ɗaukeni a gidansu? to ni a yaushe ɗin na taɓa zama agidansu har ake iƙirarin anɗauke ni?.
Tambayar dana kasa amsawa kenan, don nima da kaina ban san me hakan ya ke nufi ba?.
bayan mun gama gaisawa ne ta ɗebo irinsu daddawa da kuka da sauran ƴan kayan miya ta bani, ina ta mata godiya sannan muka fito don tafiya gida, dai dai lokacin wani yazo wucewa ta kusa dani, ban san ya akayi jikinsa ya gogi nawa ba, sai kawai naga yana kallona nima na fara kallonsa Ammi tayi saurin jana nima na bita da sauri don wani irin abu naji ya tsargamin, tun daga ƙafafuwana ya zarce har zuwa ƙwaƙwalwata ya zarce zuwa abar tunƙahon ko wani ɗan adam wato zuciya.
***
Bayan ƙwana 2
komi ya kammala, don ayanzu haka ma ya Ahmad yazo ɗauka ta ne, ina jinsa Malam yana ce masa ya kula da shan maganinsa kada kuma ya yi wasa, ya ce" in sha Allah Malam ba zanyi wasa dashi ba Allah ubangiji ya ƙara girma da arziƙi". Mu duka muka amsa da amin.
Ban san ya akayi ba sai naga hawaye suna fitowa daga idanuwa na, alokacin da Ammi ta riƙoni tana ƙara jaddadamin duk hadisin da ta koyamin wanda tuni na iya ma har na haddace.
muka shiga ɗakin Umma, don yi mata sallama ta ce"Adawiyya duk wanda zai faɗi halinki baya gani ce, tunda ni ɗinnan ni na yaye ki a hannuna sannan rabi da ƙwatan zaman gidan nan da kika yi a ɗaki na ne, saboda haka nasanki nasan halinki ke yarinya ce me matuƙar biyayya da kuma sanin ya kamata, saboda haka ki kula sosai da zaman aure, saboda shi aure ibada ce wacce Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu yin ta, sannan babu abinda ya tsana irin sakin aure shiyasa abinda ya faru atsakaninki da mijinki abin ya tsaya azuciyata, sai nake ganin kamar kina da sakaci ta hanyar addu'ah, sannan kuma ki kasance mace jajirtacciya wacce ke iya ɗauke duk irin ɗawainiyar dake gidanta, shi aure ɗam haƙuri ne kada kice idan namiji yayi miki wani abu kema zaki rama,yin hakan zai iya janyo miki hanyar shiga wuta wanda ke kika ɗauka ba zai ja miki komi ba, alhali shi kuma Allah yana fushi dake.
sannan lamarin facalarki yana buƙatar taƙa tsantsan, don a kullum a shirye take don taga ta cutar dake saboda haka ki kasance me kaffa kaffa aduk sanda kuka haɗu, sannan ki kasance cikin addu'ah da kuma yiwa mijinki biyayya sau da ƙafa, sai kiga komi ya zama tarihi".
sosai na fashe da kuka, tamkar dai yau ne ranar da zan bar gidan amatsayin amarya, ina rungume ƙirjin Ammi muka shiga ɗakin mama uwar gida, Sakina da Badi'a suna a falon mama, kowannensu yana abinda yasa agabansa, don kuwa Sakina tsaye take da wayarta a hannu tana ɗaukar kanta a vedio, kuma daga ganin tiktock zata ɗora, don nima da kaina na taɓa ganinta a tiktock ɗin, sai dai ban wani samu nutsuwar dama zan faɗawa wani ba, ita kuwa Badi'a zaune take tana chart amman vedio call ne.
Umma ta ce"ku dukkanku baku iya gaisuwa bane?".
Cike da tsiwa Sakina ta ce" haba Umma vedio fa nake yi, yanzu gashi nan kin ɓata min".
Umma ta ce" ikon Allah, daman ke kullum rashin kunyarki ƙara fitowa take, sannan wannan wayar ban sanku da ita ba daga ke har Badia ɗin".
Badia dake vedio call sai yanzu ta juyo, ba tare da tayi magana ba sai kallon banza da take mana na ƙasan ido,sakinah ta ce" eh baki sanni da ita ba gaskiya, iphone 12 ce saurayina ne ya kawo min ita".
Ammi dai bata ce komi ba, saboda ita ahalin yanzu ko kallon inda suke ma bata yi don bata san rashin kunya, Umma kuwa da taga za ta iya dasu gata ga su nan wai ɗan koli a caca.
Mama na fitowa ta ce"lafiya ku kuma kuka cikamin falo? sai kace masu neman gafara?".
Ammi ta ce" lafiyar ce ta kawo haka, Adawiyya ce tazo don kuyi sallama yau zata koma ɗakinta".
Sai kuwa mama ta zaro idanuwanta duka waje, gami da sake kallona sosai ta ce" uhm jeka ka dawo ba".
Ta faɗi hakan tana harararmu.
Umma ta ce" ko dai jeka ka zauna ba, in sha Allah ta koma kenan sai dai idan mutuwa ce zata rabasu ko shi Ahmad ɗin ya birneta ko ita ta birneshi".
tana faɗar hakan muka fice, ina jin maman na ce wa"oho dai wannan gidan sai ta ƙara dawowa saboda mugun hali irin na uwarki".
Mu dau babu wanda ya kulata, muka wuce amman ni dai azuciyata takaicin halin mama ne ya cikamin zuciya, ita kullum tamkar yarinya ƴar yaye, kullum baka hankali sai dai rashin hankali da kuma hassada, bata kunyar faɗar duk abinda yazo bakinta matuƙar hassada ta rufe mata ido.
har bakin titi su Ammi suka rakamu sannan suka dawo.
Kallon ya Ahmad na yi cike da tambayoyi a bakina, shi kuwa kallon shauƙi yake mini tare da ƙara yimin kallon kina nan araina.
zaƙuwa nayi da tambayar dana ke son yi masa na ce" ya Ahmad ina motar taka yau kuma"?.
ɗan basar da maganar yayi ta hanyar ce wa" tana nan tana gida ban dai taho da ita bane, na yi sha'awar shiga adaidaita sahu ne".
Duk da ban yarda da amsar daya bani ba sai nima na basar da maganar, amman ƙasan zuciyata na tambayata akan anya kuwa da gaske yake min? tun da mukayi aure bai taɓa yarda ya hau motar haya ba, tunda yana da motocinsa har guda biyu shima ya zubair yana da tasa guda biyu, sannan guda ɗayan ta ya zubair ya ajje mana ni da Balaraba duk inda zamuje ake kaimu, nima da kaina bana shiga motar haya to amman yau sai gashi yazomin da maganar da ba zan yarda da ita ba.
sosai gabana ya faɗi, ganin ƙofar sashe na a kulle ga kuma wani sashe na ɓangare na a ƙone sosai na waro ido ma ce" ya Ahmad me kuma ya samu ɓangare na? me yasa baka gayamin ba"?.
Duk alokaci ɗaya na rattabo masa waɗannan tambayoyin?.
a ɗan kunya ce ya ce" ƙwarai ban gaya miki bane dama, lokacin da kika tafi gida washe gari ɓangarenki ya ƙone".
da sauri na kallesa na ce" ya ƙone fa kace? to me kuma ya ƙona sa ɗin?".
cike da basarwa ya ce"eh to ni dai bana ce ba, don sanda na fita na kashe komi na kayan wuta, sai da ya Zubair ya kirani awaya ya ke shaidamin abinda ya faru amman Balaraba tayi gaggawar kiran maƙota da ƙer aka kashe".
Sosai na waro ido, don nama manta da wata me suna Balaraba, sai yanzu ne dana tuno da ita hankalina ya yi matuƙar tashi saboda nasan halin Balaraba za ta iya komai don taga ta kassara rayuwata.
na jiyo idanuwana na zubar da hawaye na ce" ya Ahmad me yasa ka dage sai na dawo alhalin kasan ga yadda ɓangarena ya ke?".
ya ɗan ware hannuwansa alamar shima bai sani ba?.
Takaici ya isheni har na kasa ɓoyewa cikin fushin na ce" to yanzu a ina kake son na zauna"?.
tambayar ma bata damesa ba ya ce"sashen Balaraba mana".
da saurin gaske na kallesa har ganina yana sarƙewa, matar daba a ɓangarenta nake ba taka yimin laɓe gamida shukamin muggun tuggu awajen mijina da sirikata, shi ne kuma yanzu zan koma sashenta? lallai an kaiwa kura nama kenan?.
Tuni hawaye suka jiƙa fuskata, ya riƙo hannuna sannan ya ce" yi haƙuri munyi magana da ya zubair, akan ɗakunansu biyu zasu bamu sannan nan bada jimawa ba za a ƙarasa gyara naki ɓangaren, don komi naki sun ƙone kayan ɗaki dana kicin, kinga to kenan yana ɗan buƙatar lokaci, sannan kuma kada ki damu dan zaki zauna da Balaraba, na daɗe da sanin kina jin tsoronta, alhali kuma ita kullum so take ta kyautata miki, motata kuma da kike tambaya dukansu sun ƙone da maƙudan kuɗaɗen mutane aciki, wanda ahalin yanzu nake kan ganin na biyasi kuɗinsu, amman bazan iya biyansu ni kaɗai ba, ya zubair da Baba sun bani miliyan ɗaya tunda kuɗin miliyan biyar ne".
da mugun kallo na bisa, gamida hawayen tausayinsa duk aɗan ƙanƙanin lokacin nan komi ya faru? ƙonewar motocinsa biyu da kuma maƙudan kuɗaɗen mutane? da kuma ƙonewar sashena?.
sai na fara girgiza kai ina ce wa" tabbas wannan abin da aƙwai lauje cikin naɗi ya Ahmad, ta yaya za'ace komi namu ne suka ƙone banda na su Balaraba"?.
ya Ahmad ya ce"Adawiyya bana son ki ƙara wannan maganar, idan har ban godewa Balaraba ba ai ba zan zage taba, tunda ita ce tayi sanadiyyar zuwa ta kira mutane aka kashe wutar, da ɓangaren namu ma toka zai koma".
yana faɗar hakan yaja hannuna zuwa ɓangaren dana kirasa da kura handame me kallonki.
tana zaune afalonta tana waya, tana ganinmu ta yi saurin ɓoye wayar ya yinda cikinta ya fito sosai haihuwa ko yau ko gobe, Nana tana ta wasanta a ƙasan tiles, babu ruwanta da yarinyar wacce akace a dinga kula da ita saboda ciwonta.
murmushin fuska take mana, gamida yi mana lale marhabin sannan ta shiga gaba wajen nuna mana ɗakin da suka bamu ɗin, wanda daman ɗakuna shida ne a ɓangarensu muma haka.
kasa tsaida hawayena nayi, saboda ganin wai ɗakin da aka bamu ɗin katifa ce a yashe a ƙasa, sai filo ɗaya sai banɗakin dake manne jikin ɗakin, sai kuma ɗayan ɗakin wanda ba komi acikinsa sai tvn bango ko risibar kallon babu.
kuka na fashe dashi gamida faɗawa kan katifar dake ɗakin.
Balaraba ta ƙunshe dariyarta gami da wuce wa cikin sanɗa sanɗa, har da turo mana ƙofa tsabar burinta ya cika akanmu.
ranar ƙwana nayi ina kuka, tun Ahmad yana rarrashina har ya dawo sanyamin ido saboda al'amarin ya fara basa haushi, in barsa yaji da abinda ya ke damunsa mana?.
Balaraba dake laɓe tana jin lallashin da Ahmad ke yimin ta tuntsire da dariya, gamida shigewa ɗakinta tana turo ƙofar ɗakin ta zauna abakin gadonta tana waro idonta waje ta ce"wo sai ni Balaraba duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, Adawiyya kike ko wa ma? uhm ai tunda kika ce zaki sanyani agaba idan na tashi ɗana miki tarko sai kinyi danasanin shigowa cikin rayuwata, sai na sanyaki kuka fiye da wanda kika yi yanzu, ba kince ke sai kin zauna da Ahmad ba? shima ya nace duk halin da ya ke ciki sai kin dawo masa? to zakuyi zamane ayanzu a ƙarƙashin ikona,wanda abinci ma sai ya gagareku duk sai nayi maganinku".
sai ta tuntsire da wata irin dariyar basawa sannan ta ce"saura plan B ɗina akanku, shi kuma daga gobe zai fara HHHHHHHHHHH".
ta dinga dariya ita kaɗai aɗakinta, sannan ta dannawa wata lamba kira, daga can ɓangaren aka ɗaga ta ce" yauwa kada dai ka bani matsala,idan kuma aka samu matsala komi zai iya faruwa da rayuwarka".
ta kashe wayar gamida wurgata kan gadonta, lokacin da taji shigowa motar Zubair gidan, sai ta ƙirƙiri tashi don ɗakko mana abinci wanda ada can bata yi ba, wai don duk ace mata tana kyautata mana.
ranar kasa rintsawa nayi, kukana yana ƙara tunzura zuciyar Ahmad, ya juyo ya ce" haba Rabiatu wannan wacce irin rayuwa ce, kinsan kuwa kukanki ya hanani barci, sannan kema kin hana kanki? don Allah ba don ni ba ki yi haƙuri kiyi shiru".
ganin naƙi yin shiru sai ya fita daga ɗakin, zuwa ɗakin kusa dani ya zauna kan shimfiɗaɗɗan kafet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin , yana jiyo kukana ya yinda yake jin babu daɗi abisa abinda yayi min, duk da ya yi iya yinsa.
wayarsa ce ta fara ruri, ya ɗaga duk da bai duba lambar ba gashi kuma cikin dare ne, muryar daya sani wacce ba zata taɓa ɓacewa ganinsa ba yaji, aka sheƙe da dariya sannan aka ce" haba Ahmad, ya zaka gujeni? duk irin nisan gudun da zaka yimin baka isa ka gujemin ba, tamkar taswirar inda kake ake zana min, saboda haka ka ƙwana da sanin asirinka ya kusa tonuwa wai an binno na binne".
sai aka kashe wayar, katse wayar sai yayi dai dai tsayawar ko wata jijiya ta jikinsa, yaji tamkar dama zai mutu ya huta da masifar dake tunkaro rayuwarsa, ranar yadda yaga dare haka yaga rana.
***
safiya na yi na tashi na ganni aƙasan tiles, ga uban sauran da suke kuka a ɗakin tamkar ba safiya ba, na kasa tsaida hawayena na fashe da kukan tausayin kai na, dana mijina shikkenan hankalin Balaraba ya ƙwanta ta cucemu.
banɗakin dake jikin ɗakin na shiga nayi wanka, da yake aƙwai sabulu sannan duk shayar gidanmu ta ruwan zafi ce, ina gama wanka na ɗauro alwala nazo na fara sallah ina kaiwa Allah kuka na.
ga kai na da yake masifar ciwo tamkar zai fashe, na ɗakko cikin sabbin kayan da Malam ya ɗunkomin, na sanya gamida saka babban hijabi.
na fito falom gabana yana faɗuwa, ya Ahmad da ya zubair suna falon suna hira.
ban san ya akayi ba sai naga sun koma min bibbiyu.
tun daga nan ban ƙara sanin me akeyi ba, sai lokacin dana farka likita na gani akai na, sai ya zubair da ya Ahmad suka dinga yimin sannu.
likitan ya ce"congratulations mrs Ahmad, kina da juna biyu har na tsawon wata uku".
A'i ban san lokacin dana hantsilo daga kan gadon ba, saboda tsabar gigicewa da rashin makama, to a ina na samo cikin? wanda rabona da mijin ma wata 8 kenan?.
tuni idanuwan Ahmad suka firfito gamida yin wani irin ja.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.
*SAI KU BIYONI A LITTAFI NA BIYU, DANA UKU WANDA ZA KUJI KOMI BA TARE DA ƊAGA HANKALI BA*
500 ne kacal ki karanta cikin ƙwanciyar hankali, zaki tura kuɗinki ta wannan banking.
2212328303
ZENITH BANK
RABIATU BASHIR.
Sannan kiyimin magana ta no ɗina.
***.
BYEEEEEEEEEE🥰
Alla ya jiƙan iyayenmu👏🏻🥹