KOWA DA ƘADDARARSA

51

by @faddabanan

Sai la'asar Mama ta ga ido na, tana ta mun dariyar ƙin biyo jirgi da nayi ga shi na wahala sosai ai. Sai a lokacin aka buɗe kayan bikin Hassana da na kawo, Mama sai yabawa take yi tun daga kan zaɓin kayan zuwa irin aikin da aka yi masu.

Washegari aka tashi da azumin arfa, ga aiki ga azumi. Idan na tuna gobe ne babbar sallah sai na ji gabaɗaya ina samun mixed feelings, jin daɗin sallah da kuma tunanin wahalar aikin nama. A ranar kuma Hassana ta dawo Kano, ita da komawa Yola sai an ɗaura auren ta sannan. Shi ma Nu'uman aiki yayi masa yawa, ba mu samu damar waya ba ma.

Ranar sallah da safe tare da Hassana da Hussein muka tafi sallar idi. Ko da wasa ban yi kwalliya a fuska ta ba in ban da farar hoɗa. Su Hassana kam an sha kwalliya sai ɗaukar hotuna take yi ana turawa Izuddeen. Wannan babbar sallar kam ko sha'awar yawo bana yi, ga ƙarin cewa Nu'uman ya takura mun. Duk wurin da zan nufa ta dole sai ya sani, idan kuma yace kar na fita, sannan na fitan zan sha masifa har ta ishe ni. Son da nake yi masa ne ya sanya nake ɗaukar dukkan waɗannan abubuwan da yake yi ba tare da damuwa ba. Oh! Wai duniya juyi-juyi, da wa ya isa ya juya Ummu haka? Hmm!

Kwana biyu da sallah Nu'uman ya iso Kano. Su Jamila don rigima har kaya kala uku suka aiko mun da su a ɗinke, wai sun ɗinka kayan sallah da ni, anko muka yi mu duka. Daɗi ya kama ni ganin suna so na, ni ma son nasu nake yi.

Sannan a karo na farko da Nu'uman ya fara bani kyautar wani abu. Turare masu matuƙar tsada guda uku ya kawo mun, farin cikin turaren ya fi na dukkanin abinda na samu a wannan sallar, kun san ai dole ma ya zama special ko don saboda hannun da kyautar ta fito. A ranar suka fara haɗuwa da Hassana amma sam ya kasa yi mata hira kamar yanda yake mun, don haka ba ta daɗe tare da mu ba ta koma cikin gida. 'Ya'yan Sauda da na Yaya Zainabu suna gidan mu tun washegarin sallah, don haka su ne suka samu barka da sallah daga wurin shi.

Bayan na dawo cikin gida daga wurin Nu'uman, Hassana ta hau mita wai ba shi da fara'a. Wai har ta baro wajen shi ko da wasa bai yi mata murmushi ba bare tayi zaton samun dariya. Har ma cewa take wannan wane irin mutum ne? Dariya kawai nayi ban amsa mata ba.

Satin da ya kama ne bikin Hassana. Ranar Laraba kuma Izuddeen ya iso da abokansa sai suka yi masauki a Tahir Guest Palace. Amma abinci daga gida ake kai masu, aiki ne ya chuɗe mun a satin nan gabaɗaya. Nu'uman ma tunda ya fuskanci hakan don haka ya ɗaga mun ƙafa akan waya, sai na samu sarari sannan zan kira shi. Shi ma ta ɓangaren shi aiki yayi mashi yawa ba zai samu damar zuwa bikin ba.

Ranar Alhamis aka fara bikin da kamu a Amneef Palace da ke kan lamiɗo crescent. Ƙawayen ta sun yi mata kara domin sun zo da yawa. Yau kam ajiye tunanin ɓatawa Nu'uman rai nayi a gefe, nayi kwalliyar da na daɗe ban yi ba sannan na sha jan baki na rangaɗaɗau. Alhamdulillahi ma da bai samu zuwa ba.

Washegari juma'a aka yi dinner a Afficent da ke Sultan Road har da kuɗin abincin aka biya domin na samu hutu kasancewar ni ce zan yi na gobe yini su kuma su Yaya Zainabu zasu yi na ɗaurin aure. Yinin a harabar gidan mu aka yi, aka sanya tampol da kujeru aka tsara wurin. Tunda safiyar ranar nake ta aikin girkin ranar, jama'a da yawa suna tare da ni a kitchen ɗina domin su taya ni, sai dai ba komai nake so a taya nin ba saboda kar a sauka daga yanda nake tsara abinci na.

Ranar Lahadi aka ɗaura auren goman safiya sannan sha ɗaya daidai muka ɗunguma domin tafiya Yola kai amarya. Dududu mu 'yan rakiyar ba mu fi mutum goma ba har da iyaye, Baba ne ya hana a tafi da yawa gudun ɗorawa su Izuddeen jigila wai.

A gida muka baro su Yaya Mahmoud da iyalansa, su sai anyi azahar za su kama hanyar Minna. Surayya da ƙyar Yaya Naziru ya bar ta ta biyo mu, shi faɗa yake wai salon a wahalar Ummi ne kawai amma me ye amfanin tafiya da ƙaramin yaro? Tare da su Yaya Muntari muka taho, su sun koma gida kenan.

Sai dare muka isa gidan Hassana, gida kam maa shaa Allah! Gida yayi kyau sosai da sosai, anan muka kwana. Washegari aka yi buɗan kai sai muka koma gidan Yaya Muntari. Shi ma kashegari watau talata muka tarkato yanamu-yanamu sai Kano, Surayya ce kawai tafiyar ta ta fita daban don daga Yolan ta bi jirgin ƙarfe bakwai ta wuce Lagos.

*****************

Komai ya dawo daidai sai dai addu'ar samun miji na gari da na dage da yi koyaushe. Na koma makaranta da kuma wurin aiki na, zangon ƙarshe na mataki na uku da nake ciki ya rage saura sati uku da kwanaki mu kammala shi saboda yanzu haka bai fi saura kwana huɗu mu fara jarabawa ba. Karatu nake ba kama hannun yaro, so kawai nake na fita da ajin farko (first class) a lokacin da zan kammala makarantar gabaɗaya.

Tun bayan da muka shirya da Nu'uman ko da wasa ban kuma yi masa naganar aure tsakaninmu ba, haka shi ma ko da suɓutar baki bai gwada yin maganar ba. Abin mamaki ma duk bin ƙwaƙƙwafi irin na Surayya a wannan karon shiru gabaɗaya, ko irin ta tambaye ni ya ya muke ciki ni da Nu'uman, amma tsit kawai ake ji, kamar irin ba ta san shi ba ma. Idan na gwada ɗauko maganar sai ta kwaɓe ni da cewar na dinga neman zaɓin Allah kar na bi son zuciya ta. Don haka sai na jingine maganar gefe guda kawai.

A satin da na fara jarabawa ne na dawo gida kawai na iske Nu'uman a gidan mu, abun mamakin ma a falo na iske shi zaune da su Mama da Hussein suna ta hira. Ban tsaya a wurin su ba, ciki na wuce na yi wanka sabida sauke gajiyar da na ɗauko sannan na dawo falo na iske shi zaune shi kaɗai duk sun tashi. Yace mun ya zo duba agency ɗin mu ne, ga shi yayi missing ɗina sosai da sosai sannan ga jarrabawa ina yi yanzu. Idan ka shigo ka gan mu muna hira, kuma ka san Nu'uman ba ƙaramin mamaki za ka ji ba.

Ina gama exams ɗina ranar Litinin, washegari na koma aiki talata. Nu'uman kam har ya fara mitar wai bana son zama wuri ɗaya, kyan shi a ce na huta kafin na koma aiki ai, ban amsa ba saboda bana son maganar ta yi tsawo. A ranar ina komawa gida daga wurin aiki Mama tace daga gobe zuwa jibi tana buƙatar snacks masu yawa. Don haka ranar Laraba sai nayi marasa kayan lalacewa a ciki irin su cake kenan ba meat pie ba, sannan ranar Alhamis na ƙarasa mata ragowan da safe kafin na tafi aiki da yamma. Gabaɗaya ranar ban samu Nu'uman a waya ba, duk da na tashi da message ɗin sa cewa gobe zai shigo gari in shaa Allah.

A gajiye na dawo gidan bayan ƙarfe tara ta ɗan gota, abun mamaki Yaya Zainabu na tarar a gidan. Baki na buɗe nace kai! Yaya Zainabu ƙarfe tara fa, me kike yi a gidan mu? Ke fa kamata yayi ki daina fita ma kar ki haihu a titi.

Da fara'a tace "Ƙaniyar ki Ummu. Amma dai yanzu hidimar ki ce ta tsayar da ni, yanzu muke shirin tafiya."

Bangane me take nufi ba, don haka na wuce na shiga falo. Akwati na ne saiti guda biyu na gani a baje a falo, kusan kowanne a buɗe yake duk sun cika space ɗin falon, sannan ga maƙwabtan mu guda biyu suna ta kallon kaya. Cikin tsananin mamaki na kalli fuskar Mama da alamar tambayar mene ne wannan? Na san daga ni sai Hussein a gidan, kuma babu yanda za'a yi a kawo wa Hussein lefe, haka ni ma. Sai na gaishe da baƙin da na tarar na juya zuwa hanyar ɗaki na, ina jiyo su suna ce mun "Allah ya sanya alheri Ummu, Allah ya sa a yi da mu."

Jurewa kawai nayi har na iya yin wanka kafin na koma falo wurin Mama domin jin bayani. Abu ɗaya kawai tace "Lefen ki aka kawo Ummu." Sandarewa nayi ina kallon ta, bakin ta kaɗai nake ganin yana motsi amma bana jin me take faɗa sannan fuskar ta har wani hasken farin ciki da nishaɗi take nunawa. Da ƙyar na tattaro ragowan ƙarfin da yayi mun saura na koma ɗaki na, zuciya ta na tafasa. Na kira wayar Nu'uman kusan sau uku bai ɗaga ba, sai na kashe wayar ina mai cike da nadamar rashin takura shi da ban yi na fitowa neman aure na ba, ga shi nan an yi mun sakiyar da ba ruwa. Irin farin cikin da ke zayyane a fuskar Mama ko ma waye mijin ai ba zan iya cewa bana son shi ba. Ranar sai da bacci ya amsa sunan sa barawo sannan ya sace ni, da ƙyar na iya yin sallar asuba sannan na koma na kwanta ina ta tunane-tunane har wani bacci ya sake ɗauka ta don sai goma na farka.

Da sauri ba tashi na shiga wanka, na shirya cikin doguwar riga ranar ko 'yar farar hodar da nake shafawa ban samu sararin shafawa ba. Na kunna wayar da na kashe tun daren jiya, sai na iske saƙon shi kan cewa ya iso kuma zai zo wuri na da yamma. Ina! Ai ba zan iya jira ba, don haka makullin mota ta na ɗauka na fito, cikin sa'a Mama ba ta falon, kayan suna gefe ko wurin su ban kuma kalla ba na fice. A harabar gidan ma babu kowa, nasan Hussein yana wurin aiki shi kuma Baba yana gidan gonar sa. Cikin sa'a na hango Yaro yana fitowa daga can bayan gidanmu, shi ya buɗe mun gate na fice sai Nasarawa GRA.

Kafin na ƙarasa ƙofar gidan su Nu'uman na hango Asmaa tsaye da wasu 'yan mata biyu da ban shaida ko su waye ba. Don haka sai nayi parking nesa da gidan, sannan na fara tunanin ta yadda zan gan shi. Sau biyu ina kiran wayar shi ban samu ba, na cigaba da zaman jiran tsammani har Asmaa da 'yan matan suka rabu, ita ta shiga cikin gidan su.

Sha biyu saura minti sha uku sai ga Sa'adu zai wuce, da sauri na fito daga motar na ɗaga masa hannu, sai aka yi sa'a ya gan ni har ya tsaya. A gurguje nake magana, nace don Allah Malam Sa'adu ko za ka ɗan dubo mun Nu'uman? Ya ɗan yi jim sannan yace "Hajiya naji tana faɗar cewa bacci yake yi, amma saboda ke ce bari na koma na gani ko zan samo maki shi." Yayi parking motar, ya taka zuwa gidan. Minti kusan goma tsakani sai ga su tare sun fito.

Fuskar Nu'uman kaɗai za ka kalla kasan baccin da yake yi bai ishe shi ba. Ko bari bai yi Malam Sa'adu yayi mun sallama ba ya sallame shi sannan ya shigo motar da nake zaune. Kuma tunda ya fito daga gidan su nake kallon shi. Ina jin yanayin kallon ne ya tsorata shi, don da alamar tsoro da kuma tashin hankali yace "Ummu kuka kika yi? Ya salam!" Ya riƙo hannuna.

Yana faɗar haka sai duk wata dagiya da na taho da ita a take ta narke, sai hawaye shar-shar ya fara bin fuska ta kamar an buɗe famfo. Hankalin shi ya kai ƙololuwar tashi, kawai cewa yake yi "Ummu yi mun magana, talk to me please! Menene? Kin ga! Kin ga! Damn it!"

Kawai sai na kwantar da kaina akan ƙafar shi na cigaba da kukan domin na kasa magana gabaɗaya. Don haka yace "Taho mu je cikin gida to." Na girgiza masa kaina nace su Asmaa, sai kukan ya daɗa saukowa. Bai ƙara magana ba sai kawai ya jingina da kujerar da yake zaune yanda zan ji daɗin kwanciyar sannan yayi amfani da hannun shi yana ɗan bubbuga baya na da kafaɗa ta har ma zuwa kaina alamar rarrashi. Na kai minti goma zuwa sha biyar ina kukan kafin ƙirjina ya saki, sai na fara kiciniyar tashi zaune, ya tallafa mun na zauna sosai sannan ya sake tambayar abinda yake damu na.

A sanyaye nace lefe na aka kawo jiya fa. Sai wani hawaye, ido na har sun fara raɗaɗin zafi saboda kuka.

Ya zaro ido yace "Bangane bayanin ki ba fa." Daga wurin da nake zaune ina jiyo bugun zuciyar sa, ganin ban yi magana ba sai ya ɗan girgiza ni tare da faɗin "Yi mun magana mana."

Na cigaba da magana alhalin ina kuka nace, jiya bayan na koma gida ne na iske an kai lefe na, aure za'a yi mun da wani fa. Kuma ko waye na san bana so sannan ba zan iya cewa masu a'a ba. Nu'uman ina zan sa kaina idan ban rayu da kai......." Matse kafaɗa ta da yayi da hannun sa na dama ne ya katse maganar da nake yi.