36
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
36
A hankali ta goge hawayen da ke idonta ta je ta bud'e k'ofar d'akin, mamaki ya bayyana k'arara a fiskarta dan wanda ta gani a k'ofar d'akin ba ta yi tunanin shi za ta gani ba. Yassar, Azra ko Uncle Sajid ta yi tunanin gani sai kuma taga sa'banin haka. Ya kat'se mata tunani da cewa " May I come in?"
Wannan ne karo na farko da ya fara ma ta magana tunda suka had'u. Yadda suke tsantsar kama da d'an uwansa sai dai wajen magana da banbanci, muryarsu d'aya ce sai dai sa'banin Yassar da yake da saurin magana shi wannan maganarsa k'asa-k'asa take.
Bata iya amsa masa ba kawai ta matsa masa ya shigo d'akin. Abu biyu ta yi tunanin ya kawo shi, ko dai shima ya zo ya mata gori ne kamar yadda Zaytunah ta mata, ko kuma shima zai gindaya mata nasa sharud'd'an ne, koma minene yake tafe da shi ba za ta tanka masa ba tunda duk min rintsi yau zata bar musu gida.
Yamin ya jawo dressing stool da ke d'akin ya kawoshi kusa da gado ya zauna akai ya nuna ma ta bakin gado yace " seat" ba ta ma sa musu ba ta zauna tana binshi da kallon mamaki.
"I heard what Aunt Zaytunah said to you" ya tsaya da maganar yana danna wayarsa kusan minti d'aya kafin ya cigaba da magana. " Lokacin da Dad d'inmu ya d'auko mu daga Taraba ya kaimu Lagos, ba abinda ba mu ji ba, ba abinda ba mu gani ba a wajen Madam Bridget, gori ne, zagi ne, munafurci ne, etc. Akwai lokacin da Yassar yace mu gudu mu koma wajensu Alhaji tunda ba a sonmu a nan. Da farko na yarda, daga baya nayi tunanin idan muka gudu dama abinda Madam Bridget ke so kenan, kuma taci galaba akanmu, and our Dad will be depress. So, sai muka d'aura d'amaran k'watan kanmu a wajen Madam B, duk ta inda ta 'bullo sai mu toshe mata hanya,daga k'arshe mu da muke tsoronta da, sai ya zamana abin ya juya, ita take shakkarmu"
Ya nisa sannan yace " Naziha right?"
Ta gyada masa kai.
" Aunt Zayt tsananin kishi gareta, kuma ko da watace daban ta zo zama gidan nan indai akwai aure tsakaninta da Sajid toh bazata zauna lafiya da ita ba kuma sai ta nemi hanyar fitar da ita. But I also want you to know that barinki gidan nan zai kawo matsaloli mai yawa tsakanin Uncle Saj da Aunt Zayt. Idan ki ka tsaya ma haka, sai dai ki sani zamanki agidan nan zai saka wasu mutane farin ciki, take Azra for instance, ta riga ta saba da ke, idan ki ka tafi she'll always be sad. Inaso ki tambayi kanki, shin dan kud'in Uncle Saj kika biyo shi Abuja? Shin dan ki shiga tsakaninsa da matarsa kika zo?"
Ziha tayi saurin girgiza kai
Yace "then miyasa dan matarsa ta miki magana zaki ce zaki bar gidan?"
Ziha tayi shiru dan ba abinda zata faɗa
" Kin dai ji yadda Uncle Saj yace da ke da Azra duk d'aya kuke a wajensa, idan kuwa hakane, dan kun samu sa'bani da matarsa barin gidanshi ba shine mafita ba, idan kuma kika yi haka kin nuna cewa Uncle Saj bai isa dake ba kenan. Ni dai abinda zan gaya miki shine, Uncle Saj is stressed out, yaushe ya gama kujuba-kujubar fitar damu daga prison, ga nauyin kula da dukiyarmu dake hannunsa ga nashi asibiti da zai bud'e ga businesses d'insa plus kula da iyalenshi. He needs peace of mind ba wai tashin hankali ba. And I swear, zaman ki a gidan nan na d'aya daga cikin dalilan da zai bashi kwanciyar hankali"
Ya tashi tsaye yace " idan kuma kina son Uncle Saj ya shiga tashin hankali Bismillah, you can go back to Lagos" yana gama fad'in haka ya fita daga d'akin.
Duk jikinta sai yai sanyi da maganganun Yamin, ta sani idan ta tafi bata yiwa Uncle Sajid adalci ba, ga uwa uba Azra. Amma ya zata yi da Anty Zaytunah da bata son zamanta a gidan. Ta ja dogon numfashi sannan tace " Ziha you can do this, za ki shanye duk wani abinda Anty Zaytunah za ta miki" da wannan ta fara maida kayanta yadda suke, can cikin ranta tana mamakin Yamin, ashe bai da girman kai, koda yake dama Yassar ya gaya mata hayaniya ce Yamin baya so, kuma baida shiga cikin jama'a kai tsaye har sai ya karanci halin mutum amma ba shi da girman kai.
**
....Yamin na shiga d'aki Yassar ya tsareshi da tambaya " Man, na ga ka shiga d'akin Ziha miye labari?"
Yamin ya watsa masa harara sannan yace " magulmaci kawai"
Yassar ya biyo shi da gudu suka fara kokawa, daga k'arshe Yamin ya surrender yace zai gaya masa komai. Dama sun saba da haka indai suna tare abu kadan sai su hau bige bige na wasa.
Ya zayyanewa d'an uwansa duk abinda Zaytunah ta fad'a da kuma maganar da ya yiwa Ziha.
Yassar yace "ai dama na san dole a samu matsala da Aunt Zayt dan kishinta yai yawa" ya dafe kafad'ar Yamin yace "thanks for supporting Ziha"
Yamin ya naushe shi yace " ba dan kai nayi ba, Uncle Saj na yiwa dan ina bayan takararsa"
Yassar ya fusata " kuttmelesiiiiii" ya tashi zai sake kamashi da kokawa Yamin ya yi bathroom da gudu yana dariya......
.........BAUCHI......
Zaman Abba da Anty Zahra gwanin sha'awa, dukkansu hankalinsu kwance suna zaman soyayya da aminci. Abba har wani ki'ba ya yi ya murmure, da ka ganshi ka san yana cikin kwanciyar hankali. Sati uku cur Nazira ta yi a Kano kafin ta dawo. Taji dad'in da ta ga hankalin Abba ya kwanta, duk da ta san hukuncin da ta yankewa kanta zai d'aga hankalinsa amma ba ta da za'bi, ta riga ta yi alkawarin ganin k'arshen Alhaji Kadi koda zata rasa ranta wajen yin hakan.
Satinta d'aya a Bauchi kullum tana kitsa yadda zata gudanar da fansar ta, sannan ta wani hanya zata bar Abba ba tareda hankalinsa ya tashi sosai ba. K'arshe dai ta yankewa kanta matsaya.....
*
K'arfe takwas na safiyar Lahadi motarsu ta tashi zuwa Kaduna, sanye take da bak'in abaya, ta sa bak'in glass, kai hatta takalmi da jakar da ta sa bak'ak'e ne. Suna tafiya tana addu'ar Allah ya kawo mata saukin wannan al'amari ya kuma bawa Abba hak'urin tafiyarta.
....kasancewar Lahadi ce basu tashi da wuri ba, bayan sun koma baccin safe. K'arfe takwas da rabi Anty Zahra ta tashi ta fara gyara d'akin tana gamawa ta fito kitchen jin ba ta ji d'uriyar Nazira ba, ta d'auka ko itama ba ta tashi da wuri bane. Ta shiga had'a musu abin karyawa.
...sai da yai wanka ya fito ya sa kaya ya je wajen reading table ɗinsa, zai d'auki laptop d'inshi dan yayi wasu ayyuka ya ga wata takarda akai tareda wayan Nazira an ajiye Sims d'in ciki a gefe. Ya d'auko takardar ya sa eye glass ɗinsa ya fara karantawa.
*Assalamu Alaikum. Abbana ka yafemin bisa mummunan hukunci dana yankewa kaina. Ina sonka sosai, kuma Ina son farin cikin ka, Abba ba zan ta'ba yafewa kaina ba halinda Waheeda ta shiga zuwa irin mutuwar walak'anci da tayi. Abba ka yafeni domin na tafi d'aukan fansa, ko na mutu ko na rayu amma dole na yi abinda nayi niyya Abba......"*
Bai iya k'arasa karantawaba saboda takardar da ya su'buce daga hannunshi.......