37
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
37
Jikinsa ya fara kakkarwa ta ke kuma ya dafe ƙirjinshi yana maimaita kalmar Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajioun. Kusan minti biyar kafin ya samu sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa, ya samu kujera ya zauna yana ambaton Allah ya kawo masa sauƙi cikin lamarinsa.
Anty Zahra ganin shiru ba ta ji ɗuriyar Nazira ba ya sa tace bari ta dubota a ɗaki. Ta shiga ɗaki wayam, bata nan, sannan an tattare ɗakin wasu abubuwan an rufesu tamkar dai ɗakin mutumin da zai yi dogon tafiya. Da mamaki ta fito daga ɗakin ta shiga ɗakin Abba tana faɗin " Yaya, Nazira ta ce maka za ta yi tafiya ne?...." ganin yanayin da yake ciki ya sa ta haɗiye sauran maganar ta ƙarasa wajenshi ta dafa kafaɗarsa tace "Yaya, miya faru ?" Bai iya cewa komai ba ya mata nuni da takardar da ke ƙasa. Ta ɗauki takardar jiki a sanyaye ta fara karantawa,tana karantawa hawaye na zubowa daga idanunta. Sun jima a zaune ba wanda ya iya cewa komai.
Anty Zahra ta yi ƙarfin hali tace " Yaya, ka tashi muyi alwala muyi sallah, mu roƙi Allah ya dawo mana da ita gida lafiya, ba abinda za mu iya yi da ya wuce haka" bai mata musu ba ya tashi suka shiga banɗaki suka ɗauro alwala. Nafila raka'a biyu suka yi sannan suka shiga jero addu'o'i. Yadda Abba ke addu'a yana hawaye ba ƙaramin tausayinsa ta ji ba, itama ɗin daurewa kawai take yi amma abin ya dameta sosai. Sai dai dole ta daure ko dan ta kwantar masa da hankali.
***
.....JOS.....
Addu'a takobin mumini. Addu'a da Hajiya Salma ta dage da yiwa Yaya Isa ya sa hankalinsa ya karkata zuwa wajen 'yanuwansa. Yanzu haka ya biya wa Nazima da Ummulkhairi computer school, saboda kar su yi zaman banza tunda Jamb kam sai wata shekarar, gara ma Khairy da ta cika Nursing school idan Allah ya sa ta samu shikenan.
Tunda Anty Zee ta dawo ta ga chanji a wajen mijinta, abubuwa sun fara kwaɓe mata, abubuwan da ta haɗo ma da ta je garinsu, ta yi amfani da su ta ji shiru ba wani chanji. Yanzu wani sabuwar shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsa da 'yanuwansa, farida ma duk weekend tana wajen Hajiya. Abinka da yarinya har ta fara sabawa da su, ta ma fi jin daɗin zaman gidan Hajiya da nasu gidan.
*
Hajiya Raudha kuma tun da Shabbir ya bailing ɗinta ta ke fishi da mijinta, har yau zamansu bai koma dai dai ba. Kwata-kwata ƙaurace masa ta yi, yau ma ɗin lallashinta yake yi amma ta ƙi sauraransa.
" ni fa Raudha na gaji da wannan iskancin, sai yaushe za ki haƙura ne, na baki haƙuri kin ƙi haƙura, shin wai zina ki ke so na je na yi ne?"
Ta yaye bargon da ta rufu da shi ta ce "ko zinan ka yi ai ba abin mamaki bane, munafiki irinka ai ba abinda ba za ka aikata ba"
Tashi yai daga kan gadon a hasale yace "haka ma za ki ce ko, to wallahi kin yiwa kanki, barin fita na je wajen da za a tarairayeni a riritani kamar ƙwai" daga haka ya fice daga ɗakin. Ta na jin ƙarar ficewar motarsa daga gidan amma ko ajikinta. Punishment ɗin wata uku ta yanke masa kuma kwata-kwata ko sati uku bai cika ba. Shiru-shiru bacci ya ƙaurace mata sakamakon maganganunsa na ƙarshe da ya fara mata yawo a kwanya. Wuf ta tashi ta kunna wutar ɗakin ta duba agogon da ke bango, ƙarfe shabiyu da rabi na dare. Take jikinta ya fara ɓari, kar dai Muhammad wajen karuwa zai je. Abinda zuciyarta ke ayyana mata kenan, ta yi saurin ɗauko wayarta ta fara kiran numbarsa amma ta ji a kashe, duka layukansa da yake amfani da su a kashe suke. Hankalinta ya ƙara tashi, ta tashi ta fito falo tana safa da marwa, tana sake gwada layinsa duk bayan minti biyar amma shiru. Bacci kam babu shi ranar dan kwanan zaune ta yi. Washe gari ma all through layinsa a kashe ga shi bai zo gida ba har dare. Da dare ya ratsa still bai dawo ba kawai ta fashe da kuka a ɗaki, sai da ta yi mai isarta sannan ta ɗan kwanta ba a jima ba bacci ya saceta. Da Asuba zazzaɓi ya rufeta ko iya tashi Sallah ba ta yi ba. A haka yaranta suka shigo suka sameta. Babban ɗanta Ahmad ya ɗau wayarta ya kira numbar Babansu amma ba ta shiga. Gidan Maƙwabtansu ya je Maman Fadil, ya sanar musu Umminsu ba lafiya kuma Abbansu ba ya gida. Maman Fadil ta sa hijabi ta biyoshi. Ita ta taimakawa Hajiya Raudha ta tashi tayi sallah, sannan ta shirya yaran suka bi Abbansu Fadil ya kai su makaranta.
Tea kawai Raudha ta iya sha shima ɗin ba ta sha shi sosai ba. Abbansu Fadil ta kira ta sanar masa za ta raka Hajiya Raudha asibiti ya ce mata ba matsala. Da shike ta iya mota, a motar Raudhan suka tafi. Suna zuwa aka bata gado aka ɗaura ma ta ruwa.
Sai yamma suka samu numbar Muhammad bayan Abban Fadil ya sanar da shi matarsa na asibiti ya ce musu yana zuwa. Goshin maghrib ya shigo Asibitin, ya samu Raudha na bacci. Bayan sun gaisa da su Abban Fadil ya musu godiya sannan suka mishi sallama suka tafi.
Ƙarfe takwas ta farka ta ga mijinta Muhammad Kabir agefenta, wani sanyi ya ratsata tunowa da yadda suka rabu ya sa ta fashe mishi da kuka. Da ƙyar ya lallasheta ta yi shiru, bayan ya rantse mata ba wajen mace ya je ba. Sallama ya nema aka basu, suka koma gida, kasancewa dare yayi bai ma je ya karɓo yaransa daga maƙota ba. Ya kwana lallashin matarsa ta hanyar nuna ma ta kulawarsa gareta....
.....KADUNA.....
Gidan da Nuhu ya kama mata ta nufa bayan ta isa kaduna. Gidan haya ne wanda yawanci ɗalibai ne a ciki, ta buɗe ɗakin da yake na ta ta shiga, ba komai a ɗakin sai ƙaramar katifa, gas 6kg cylinder da bokiti ɗaya. Ta ƙarɓi tsintsiya a wajen wata neighbor ɗinta mai suna Alexa, ta share ɗakin. Da ta gama sai ta kwanta a katifar tana saƙe-saƙen abinda ya kamata ta yi....
*
yau kwana uku kenan ya na sintirin gidan Alhaji Kadi ya na surveying wajen. Ya riga ya gano Layla na cikin gidan ba wai ta bar ƙasar bane kamar yadda ake ta faɗa, sai dai har yanzu bai gano dalilin killace ta da aka yi ba.
Yau ma yana tareda wani mai sai da kayan marmari da ke layin gidan Alhaji Kadi ya ga wata keke ta tsaya ƙofar gidan. Wata budurwa ta fito daga cikin keken, shigar atampa tayi ta sa hijab baƙi, ta ƙwanƙwasa gate ɗin gidan. Ta jima tana bugawa kafin aka buɗe. Maganar minti uku suka yi maigadin ya kulle. Yanayin da ta yi ya nuna wa Shabbir maigadin koranta ya yi.
Ta jima tana tsaye kafin ta bar wajen, ta tsallaka titi ta ƙaraso wajen mai saida kayan marmarin tace ya bata Apple da Ayaba na ɗari biyar. Bayan ya haɗa mata kayan ta miƙa masa kuɗi ya karɓa. Za ta wuce ta ji ance " ba ki yi kama da mai bara ba, miya kawo ki gidan Alhaji Kadi?" Ta juyo ta kalli mutumin da ke magana, mutumin ya mata kwarjini, amma ta daure saboda ita yanzu tsoro ba nata ba ne ta ce masa" lafiyarka kuwa? Gidanka na zo da za ka tsareni da tambaya" ta yi tsaki ta wuce.
Yana gani ta sake tsare
Keke ta wuce, ya girgiza kai yana murmushi, idan ya ga mace na falli abin na sa shi nishaɗi.........
Bai yi tunanin ganin yarinyar jiya a wannan waje ba, tabbas akwai abinda ta ke nema, ya ƙarisa wajen da take tsaye tana jiran Hajiya ta iso, ya ce " yau ma baran kika zo yi?" Nazira ta juyo ta kalleshi sama da ƙasa, mutumin jiya ne, ta gane shi sarai. Ta ja ƙaramar tsaki tareda kau da kai daga kallonshi.
sosai SY ya ji haushin tsaki da ta masa amma ya danne saboda yanayin aikinsa, ya sake jefa ma ta wata tambayar " kina neman shiga rayuwar Alhaji Kadi ko?" Ba ta amsa masa ba, ta cigaba da kallon gefe.
" fiskarki ta nuna min ɗaukan fansa ki ka zo yi, amma ki sani kin yi kuskure " ya fidda ƙaramar joter ya yaga takarda a jiki ya rubuta numbarsa da sunan Yunus a jiki ya miƙa mata, kamar ba za ta ƙarba ba, sai kuma ta daure ta ƙarɓa ba tareda ta ce komai ba. Shima ɗin tana ƙarɓar takardar ya shige cikin gidan marayun wanda tuni ya samu dama a wajen yana aikin volunteer .
Tsawon lokaci Nazira na juya takardar da Shabbir ya bata, daga baya kuma ta jawo wayarta ta sa numbar ta kira, ringing ta yi ba a ɗauka ba, ta ja tsaki ta ce " kila ma mutumin nan ɗan damfara ne"
Kusan minti biyar da kiran da ta yi aka kira wayarta, ta duba numbar da ta kira ne, a hasale ta ɗauki wayar tareda sallama, ya amsa sallamar tareda cewa "ashe dai da wuri kike son ganin bayan Alhaji Kadi"
" mi yasa kake bibiyata?"
" ba ni labarinki, ina ga hakan zai fi muhimmanci fiye da tambayar da ki ka yi" cikin zuciyarta ta ce lallai ma wannan ɗan rainin wayo ne. Ta ƙatse ƙiran tareda ajiye wayar gefe ta cigaba da rubuta plans ɗinta. Zuciyarta ne ya tuno ma ta numbar mutumin da Alyasa'a ya taɓa haɗata da shi. Sai dai shima ta san ba rabuwar kirki suka yi da mutumin ba, dan haka sai ta yak'ice zancensa.
Ta fi kwana uku tana sintirin gidan Alhaji Kadi, kamfaninshi da ma gidan marayu amma ko gizau ɗinsa ba ta gani ba, matarsa ma haka, ganin ta ɓata lokaci ba wata hanya da za ta sada ta da Alhaji Kadi ta yanke shawaran kiran Agent SY kamar yadda Alyasa'a ya faɗa ma ta sunansa.
Ƙarfe tara na dare yana zaune akan gado yana duba wasu saƙonni a system ɗin AY, ya ji wayarsa na ringing, mutane ƙalilan suka san wannan numbar tashi dan haka sai yayi mamakin ganin numbar yarinyar can tana kiran wannan layinsa. Ya ɗauki wayar tareda cewa " who are you?" Ƙirjinta ya buga jin muryan mutumin nan. Da ƙyar ta iya cewa " da ma kai ne Agent SY?"
Sai lokacin hankalinshi ya bashi yarinyar da AY ya haɗata da shi ne, ya ɗan haɗa rai ya ce " and so"
" ka yi haƙuri ban san kai bane, ina buƙatan mu haɗu gobe dan Allah"
Yai shiru kafin ya ce " zan mi ki text ɗin lokaci da wajen da zamu haɗu" daga haka ya ƙatse kiran.
Ta yi ajiyar zuciya tareda addu'an Allah ya sa ta cimma burinta.
***
........ABUJA........
Kowa ya hallara a wajen dining ɗin banda Ziha, Yassar ya kalli Azra ya ce ta je ta kira Nazzy a ɗaki.
" idan ba duniyanci ba ai ta san, yanzu ne lokacin breakfast ta wani laɓe a ɗaki kamar munafuka" Zaytuna ta faɗa game da jan tsaki. Ba wanda ya tanka mata.
Ba ƙaramin rikici suka yi da Azra ba kafin ta amince ta fito, tsoron Zaytunah fal aranta. Jiki a sanyaye ta saka room slippers ta biyo Azra hannunsu riƙe cikin na juna.
Good Morning Uncle ta faɗi bayan ta iso wajen, karatun wani magazine yake yi jin muryarta ya sa shi ɗagowa ya kalleta sannan ya amsa gaisuwar.
Ai bata gama zama da kyau ba muryar Zaytunah ya bigi kunnenta " amma Naziha, kin yiwa kan ki adalci kuwa, tun da safe kina laɓe a ɗaki kin ƙi fitowa, gashi aiki ya min yawa a kitchen Saratu na shirya yara, ke kuma kin naɗe kan gado kina barci, ai ko ba komai dai ko dan kara kya fito ki taya ni wani aikin" ba Ziha kaɗai ba hatta Yamin da Yassar maganar ta basu mamaki.
Da ƙyar Ziha ta iya haɗa kalmar "I'm sorry Anty" idanunta suka ciko da hawaye.
" kin zo cin arziƙi gidan mutane amma ba za ki iya yi mana aiki ba, sai dai ayi ki zauna ki ci, bayan nan ma sai an kira ki kafin ki fito tsabar rashin hankali"
"Aunt Zayt....." kafin ya ƙarasa maganar Sajid ya ɗaga masa hannu alamar yai shiru.
Ya kalli Zaytunah ya ce " ban kawo Ziha gidan nan don ta yi aiki ba, idan aiki na miki yawa ƙofa buɗe ta ke ki nemi 'yan aiki su dinga taya ki"
" but my one....."
" enough Zaytunah" ya faɗi da kakkausan murya...
Haka dai aka ƙare cin abincin kowa da abinda ya ke tunani. Suna gamawa Ziha ta fara tattara wajen, ganin Sajid na wajen ya sa Zaytunah bata ce komai ba.
Suna shiga kitchen Zaytunah ta sa hannu ta kamo kunnen Ziha ta murɗe sosai tana faɗin " wato ke 'yar iska ce ko, ba kya jin magana, duk warning ɗin dana miki a banza"
Muryar Yassar da ya ke kiran Ziha ya sa ta sake ma ta kunnen tareda mangajeta ta fice daga kitchen ɗin.
Saratu da ke gefe tana ganin komai ta ƙaraso wajen Ziha ta dafa kafaɗarta tace " ki yi haƙuri" Ziha ta girgiza kai ta ce " nagode Baaba"
**
Tunda suka gama da Bank inda aka buɗe wa Ziha account suka wuce shopping, irin kaya masu tsada da su Yassar ke siya har sai da ta tsorata, komai designer su ke siya, har sai da tace wa Yassar su haƙura haka ya isa. Yassar yai dariya ya ce " Uncle Saj is filthy rich, kuma shi ya ce mu sai duk abinda mu ke so"
Kaya kaɗan ta ɗauka nata dan komai ta ɗaga ta ga kuɗinshi da yawa sai ta ajiyeshi. Yassar yai ta ɗiba mata kayan da ya ga zai dace da ita, har su takalmi da jaka.
Bill ɗinsu ya kama 450k. Ziha ta zaro ido ta ce a rage kayan sun yi tsada da yawa... Yamin ya ce " 'yar ƙauye kawai" wannan shine maganarsa ta farko gareta tun fitowarsu daga Bank. "Allah Yamin it's too expensive, kayan sawa kawai"
Yassar ya tintsire da dariya ya ce " waya gaya miki mun gama siyayyar ai da saura, yanzu wani wajen zamu je muga kalar tasu hajar"
Ta ma rasa mi za ta ce musu su gane almabazzarancin da suke yi, ta dai bisu da ido kawai.
Aƙalla sun je manyan malls uku sunyi siyayyar da ta kai 1.6M kafin suka wuce wani restaurant suka ci abinci daga nan suka tafi yawon ganin gari. Dama Abuja baƙonsu ne dan wannan ne karo na farko da suka taɓa zuwa. Iya kacinsu Taraba da Lagos sai Kano da suka je sau ɗaya da Alhaji tun kafin su koma Lagos da zama.
Tun safe da suka fita sai ƙarfe takwas na dare suka iso gida gaba ɗaya a gajiye suke, kaya niƙi niƙi suka shigo da su driver ya biyosu da sauran, a falo suka taradda Sajid da yaran suna kallo, wanda a zahiri Sajid zaman jiransu yake yi, Azra ta sha kuka har ta yi baccin dole, tuntuni ta ke roƙon Sajid ya kai ta wajen Nazzy yace mata basu dawo ba.
Bayan sun shiga da kayan, Yassar ya kawo masa ATM ɗinsa yace "Uncle mun gode"
Sajid ya karɓi ATM Card ɗin ya ce "banason yawon dare, next time ku dawo gida da wuri"
"Ok sir" Yassar ya faɗa yana sara masa kamar wani soja.
Sai da ta yi sallan Maghrib da Isha sannan ta fito falo rigima ta samu Azra da Zaytuna ke yi, Zaytunah ta zo ɗaukan Azra ta kai ta ɗakinta sai ta farka, ta yi ƙirmisisi ita ɗakin Ziha za ta kwana, Zaytunah kuwa ta ƙi. Sajid na zaune yana kallo bai tanka musu ba.
" ina wuni Anty" Ziha ta gaisheta tareda yaƙinin ba za ta amsa mata ba. Hakanne kuwa ya faru ta ɗago ta zabga ma ta harara sannan ta cigaba da yiwa Azra magana " Azra my love, you have to sleep in your room, with all your favourite teddies and toys kin ji"
" No!, I'm sleeping at Nazzy's room only" Azra ta faɗi da ƙarfi. Itama ɗin ta haɗe rai tace " you better obey what i said or I'll slap you" Azra ta yi ƙoƙarin fincike hannunta ta gudu amma ba hali saboda riƙon da Zaytunah ta mata. Ganin za ta ɓata mata lokaci sai ta sunkuceta ta haura sama da ita, sai wutsil wutsil take yi tana kuka amma Zaytunah ba ta ajiyeta ba sai da ta kaita ɗakinta sannan ta direta akan gado tareda daka mata tsawan da ya sa ta firgice har ta saki fitsari. Tuni ta haɗiye kukanta ta koma tana ajiyar zuciya. "Marar kai kawai , ana nema miki kariya kina yi wa mutane kuka" sai da za ta cire ma ta kaya sannan ta lura har fitsari ta yi, ta shiga da ita bathroom ta mata wanka sannan ta shiryata cikin kayan bacci mai kyau, ta shimfiɗata kan gadon sannan ta tofa mata addu'a ta fito.
......
Bayan haurawan Zaytunah sama, ta ƙaraso wajen Sajid ta tsugunna ta fara yi ma sa godiya. Ya ɗaga ma ta hannu alamar ya isa haka, shiru ne ya biyo bayan hakan, kusan minti biyu sannan ya juyo ya kalleta ya ce " Ziha bana son yawon dare, na san laifin su Yassar ne amma ki kiyaye, bana son ki dinga wuce maghrib a waje"
" I'm sorry Uncle" ta faɗi still tana kallon ƙasa.
" za'a buɗe Asibiti nah ranan Saturday, so gidan nan zai cika da baƙi, try and adjust idan sun zo, don't worry family na ne kawai za su sauka anan, sauran a hotel za su sauka"
" Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya" ya amsa da amin ta ma sa saida safe ta shige ɗakinta. Ita kam mamaki ya bata bai ji haushin kuɗin da suka kashe ba sai dan sun yi dare a waje , lallai Allah ya buɗe wa wasu taskar arziƙi, #1.6Million ya tafi a yini ɗaya amma ko a jikinsa.
Ba ta jima da bacci ba ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofarta, ta taso da sauri ta zo ta buɗe, Uncle Saj ne ɗauke da Azra ba tayi bacci bama yace " she'll sleep here" Ziha ta matsa ma sa ya shigo da ita ya shimfiɗata kan gado ya tofa ma ta addu'a ya mata peck a goshi sannan ya fito.....
Bai samu Zaytunah a ɗakinsa ba, dan haka ya wuce banɗaki kawai.
" Wallahi Sady ina cikin tashin hankali, kwana biyu da yarinyar nan ta yi a gidana gaba ɗaya na takura, i hate her. Wai har account my one ya sa 'yanbiyu suka buɗe mata yau"
Daga ɓangaren Sady haƙuri ta ba ta tace za ta san yadda za su yi idan ta dawo.
"You better come up with a good plan, dan ko ta halin ƙa-ƙa yarinyar nan sai ta bar min gida" da haka ta kashe wayar. Ta sake feshe jikinta da turare ta wuce ɗakin mijinta...
Cikin kwana biyun nan Ziha ta fahimci abu guda, shine Zaytunah ta tsaneta, kuma ba ta son zamanta a gidan. Yamin da Yassar ke ƙoƙarin ƙwacanta daga tuggun Zaytunah, habaici da zagi kam idan da suna tsiro a jikin mutum da yanzu sun kai tsawon rake a jikinta.
Yau Alhamis ake shirin tarban su Alhaji mahaifin Sajid kenan, Zaytunah da kanta ta gyara musu ɗakin da zasu sauka, tun safe ta ke shirye shirye ita da Saratu da 'yan aikin gidansu biyu da ta ce Mommy ta turo mata. Sau ɗaya da ta je kitchen dan taya su aiki Zaytunah ta daka ma ta tsawa ya sa ta koma ɗaki ba ta sake fitowa ba, ta zauna tana karatun wani novel mai suna 'Catcher in the rye'.
Ƙarfe uku Sajid ya je airport ya ɗauko su Alhaji, su biyar suka biyo jirgi sauran da mota suke tafe shi yasa basu iso ba. Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya fara cika da 'yanuwa, sau ɗaya Ziha ta fito ta gaida Alhaji da Ummi wanda shima cikin ribibi ne ba wanda ya wani damu da ita, haka ta wuni tun breakfast ɗin safe bata ci komai ba, kunya da tsoron fitowa take yi. Har ƙarfe goma na dare tana jin hiransu a falo sai dai ba ta san mi suke faɗa ba dan mafi yawanci da fulatanci suke magana.
Yunwa ya turnuƙeta ta kasa barci, sai juyi takeyi akan gado. Chan ta tuna akwai chocolate da suka saya ranar da su 'yanbiyu, ta yi sauri ta buɗe drawer ta ɗauko packet ɗin, ta buɗe ta fara ci sai da ta cinye fiye da rabin packet sannan ta ajiye ta shiga bathroom ta tari ruwa a tap da hannunta ta sha ta yi naƙ. Sai lokacin ta iya yin bacci, ta san yau kam ba lalle Azra ta zo su kwana ba...
Washegari da sassafe ta fito ta taradda Saratu na gyaran falo dan haka ta ce ta kawo ta taya ta, ba ta hanata ba ta bar mata falon dan akwai ayyuka dayawa a gabanta. Ƙarfe bakwai Zaytunah ta fito ta shiga kitchen, kafin ta zo Saratu da sauran matan biyu sun kusa haɗa aikin, ta taya su suka ƙarisa haɗa komai. Ko kunyar fulani nan Zaytunah ba tayi ba, matsayinta na matar ɗan fari, da kanta ta kaiwa sarakananta breakfast ɗinsu a falon Sajid, tare suke da Sajid ɗinma ana ta hira.
Wannan karon ta samu abinci ta ci sosai saboda har ɗakinta Saratu ta kawo ma ta. Zuwa ƙarfe huɗu wasu baƙin suka iso, gidan ya sake cika. Shigowar Zaytunah ɗakinta ya sa tayi saurin tashi daga kan gadonta agigice ta ce " i...ina wuni Anty" Zaytunah ta ja tsaki ta ce maza- maza ki tattare kayanki ki koma ɗakin Saratu, 'yanuwan masu gida za su sauka a ɗakin nan. Jikinta na rawa ta shiga tattara kayanta ta zuba a akwati ta yi ɗakin Saratu dasu. Zaytunah na tsaye har ta gama kwashe kayan nata duka, cikin zuciyarta ta ce ko baƙi sun tafi kin koma zama da Saratu kenan....
Tun da ya fita da safe bai zauna ba, yana can yana tarban baƙi abokanansa na nan Nigeria da na ƙasar waje da suka samu zuwa ciki harda Dr Ben Carson ɗaya daga cikin manyan neurosurgeons da ake ji da su a duniya. Ƙarfe shaɗaya na dare ya shigo gidan, tun yana haurawa yake jiyo muryarta ana hira, fiska sake ya shiga falonsa...." oyoyo babban yaya" ta taso da gudu ta rungumeshi.
"Ke wai har yanzu ba kya girma ne"
"Allah Ya Saj ka bari na mori ƙarfina, har yanzu ji na nake kamar 'yar shekara bakwai " gaba ɗaya suka tintsire da dariya. Nadia kenan autansu, ba ta jima da isowa ba dan jirginsu ƙarfe tara na dare ya sauka daga Michigan state, USA