KAZAMIN TAKU

11

by @hafnancy

Banyi tsammanin ganin k'ofar gidan abud'e ba, amma ganinsa abud'en ya bani tabbacin an farga da fitar tawa kenan, hakan yasa na danna kai ciki atsorace gabana na bugawa da sauri sauri, hango Addah da nayi shine ya tsananta bugawar zuciyar tawa, da hanzari nayi nufin komawa don bana jin zan iya jure Fitinar Addah acikin daren nan.."in kika kuskura kafafunki suka taka waje saina tsine miki! idan yaso sai ki k'arashe lalacewar kibi duniya!"...cak! Na tsaya na maida kafata ciki na dire, babu abunda yafi daga hankalina kamar furucin daya fito daga bakin Mahaifiyar tawa, ayadda kuma ta fusata d'in nan ina da tabbacin sosai zata iya aikata abunda ta fad'a, ina kallo Adnan ya mik'a mata abu amma ban san ko menene ba, naga dai ta b'oye hannunta abaya...


"Wai jira kike in sake bud'e baki ince miki ki karaso ko me kike nufi ne?" Maganarta ya katsemun tunani, ahankali na soma motsawa, jikina na d'an rawa tsabar tsoron daya mun katutu, ina dab da karasa inda take sai kawai naga ta zabura ta shammaceni, ba sai kawai naji saukan dorina kota ina ajikina ba, Na shiga ihu da kururuwa ina tsalle tsalle, Addah sai surutai take tana cigaba da dukan nawa"ki gayamun wani shaid'anin ne yake hure miki kunni awaje da har ya iya zuwa ke kuma kika sa kafa kika fita acikin daren nan sabida kin isa kuma zaman kanki kike, wallahi sai ayanzu ne nake sake gasgata zancen da Ubaida tazo mana dashi, ashe da gaske d'in ke me fuska biyu ce, Rahama Allah ya isa tsakanina dake don kinci amanar tarbiyyar dana bata tsawon lokaci ina baki, zakiyi magana ko kuwa sai jikinki yayi tsami tukun ?, nace dawa kika fita amota?, kuma uwar ina kuka je ?"


Sakina da karajin Addahn tasu ce ta farkar da ita daga dan baccin daya saceta ne, ita ce ta fito aguje ta rik'e bulalan hannunta tana bata hakuri"Addah dan soyayyarki da ma'aiki kiyi hakuri ki rabu da ita wallahi Ya Rahama ba 'yar iska bace, kuma ni nayi imani har ga Allah babu namijin da zata yarda ta fita dashi acikin daren nan baya ga Uncle Yusuf kuma kema kin san da cewa Uncle Yusuf ko kusa bai yi kama da fasik'i ba, bazai so ya lalata d'iyarki kuma d'iyarsa ba.."...Addah ta katseta cikin karaji"akaramin tinaninki ko.?, hhmmm Sakina har yanzu ke d'in yarinya ce kankanuwa adan haka kona zauna ina baki labarin duniya da kaidinta babu abunda zaki fahimta aciki watakila sai nan gaba, dan haka sakarmun hannu kafin zuciya takai mun wuya in mommokeki.."


Da sauri ta sakar mata hannun tayi dakin Papa da gudu tana kiran sunansa tana kuka, ita kuma Addah ta cigaba da dukan Rahama.


****

Abdiel ne kwance ya kasa bacci sabida hayaniyar da yake tasowa daga makobtan nashi, cike da zafin rai yace"God! Who are this people disturbing my peace?, wasu irin mahaukata ne wa'ennan kowa na kwance yana hutawarsa su kuma suna can suna rigima acikin tsohon daren nan ?, nifa shiyasa kwata kwata bana kaunar arewa sabida sun cika abubuwa irinta dabbobi, dole ce kawai tasa nake zaune cikinsu kuma da zarar na kammala abunda ya kawoni zan ware abuna ne" Tashiwa yayi ya jawo system d'insa ya Fara aikinsa don ba baccin zai iyayi ba da wannan hayaniya tasu.


**

Turus! tayi akofa ganinsa Zaune abakin gado ya buga tagumi da duka hannayensa, sosai abun ya bata gingimemiyar mamak'i tace"Papa ashe kana jin Addah nata dukan Ya Rahama shine koka fito ka ceceta ahannunta ?"..shiru babu amsa haka kuma yaki dagowa ya kalleta, hakan yasa tayi tunanin ko yayi nisa cikin tunani ne..asanyaye taja jiki zuwa gabansa ta tsugunna tasa hannu ta tab'oshi, murya ashaqe tace"Papa magana fa nake maka..."....bai bari ta dire numfashi ba yace"ina jinki, koba magana kike akan Halima da d'iyarta ba?, to shawara zan baki Sakina amatsayina na mahaifinki, daga yau sai yau ki cire hannunki alamarin Halima da d'iyarta Rahama kamar yadda nima na tsame hannayena daga ciki, naki kawai ido.."....Cike da mamakinsa tace"ban gane in tsame hannayena daga cikin lamarinsu ba, haba papa wani irin magana kenan da ko kadan batta da dadin ji akunne ? yanzu kai hakan ba suyi wa labbanka nauyin fad'a ba ?, in cire hannuna acikin matsalar dake tsakanin mahaifiyata da kuma yar'uwata kamar yadda kaima ka tsame, to papa in har kai zaka iya jure ganinmu kullum cikin tashin hankali to ni bazan iya ba, gaskiya banji...."


"Ke tashi ki bani wuri karki sa in sauke haushina akanki, kinji na rantse da assamadu ko kashe Rahama Halima zatai bazan tanka ba, ban sani ba ko kina kallo na sake daura wani sabon alwala dazu bayan ta gama ci mun mutunci akanta, to kamar yadda na daura sabon alwalan nan to ina mai tabbatar miki haka nayi rantsuwa akan na tsame hannuna daga lamarin Rahama! ayau Halima ta nuna mun iyakata akan d'iyarta! Kuma ta sake tuna mun da cewa banda iko akanta.."


Da tsantsar mamak'i Sakina tace"kamar ya ?, dama ashe Uwa takan fi iko da ya'yanta akan Uba?, ban tab'a cin karo da hakan ba sai agidanmu.." murmushi papa yayi yana girgiza kai kan yace"to ayau kinji, alamarin Rahama Halima ta fini iko da ita, amma akan lamarinku keda Muhammad Adnan na fita iko akanku, ina fatar k'wak'walwarki ta dan fahimci wani abun..?"...kai ta kama tana kokarin nazari kan maganganun nasa amma ta kasa gane komai, ko don kasancewarta yarinya karama ne shine bata sani ba, 17years gareta, tace"Papa wallahi kuna sake jefamu cikin rud'ani, ayau d'in nan gabak'i daya kun bawa k'wakwalwanmu aiki wajen tunane tunane amma kwata kwata mun rasa gano tudun dafawa, shin me yake Faruwa ne ?, me kuke b'oye mana ne da har kuka kasa bayyanawa sai jefo mana maganganun kuke adunkule ?"


Mik'ewa Papa yayi ya rab'a ta gefenta yana k'okarin wucewa waje"kiyi hakuri Sakina in lokacin daya dace ya karato sosai zaki fahimci abunda ya shige miki duhu amma duba da yadda lamura suke kokarin sauyawa watakila abunda ake gudu yana iya bankad'owa kowa ya gani anan kusa kuwa." Tashiwa tayi tabi bayansa tana sharar kwalla, alokacin da suka fito sun tarar Addah tabar kilar Rahama bayan ta gaya mata wanda ya sauketa amotar, tana ganin fitowar papa ta nufeshi da sabon masifa, ta cakumo kwalar rigarsa abunda bata tab'a gigin yi ba, hakan da tayi ba shi kadai abun ya bawa mamak'i ba hatta da yaran nasu, Cikin dacin rai take magana"Abdulmalik ina son ka gargad'i kaninka, gargad'i da kakkausar murya akan ya nesanta kansa da d'iyata in ba haka ba shari'ah sai ta shiga tsakanin al'amarin nan, ai dama na gaya maka amma kaki saurarata, har zaunar dakai nayi don muyi magana ta fahimta kaki bawa zancen nawa muhimmanci, hasalima maidani shashasha kayi, nace amanta da batun wai yana matsayin k'anin mahaifi agareta, wallahi soyayya bai san wannan ba, yau da gobe idan shak'uwarsu ta wuce misali mai yiwuwa ta koma soyayya, abunda naso ka fahimta kenan awannan lokacin amma kaki, ni kuma da nake ta kokarin son na dauki mataki akai sai kayi saurin takamun burgi, yanzu ga irinta nan abunda ake gudu ya faru, gata nan da bakinta take gayamun da gaske Son uncle d'in nata take ko kunya bata ji.."


"a iya sanina macen kwarai bata taɓa cin ƙwalar rigar mijinta, Halima ki cigaba da gwada mun kalar haukanki, ki kuma cigaba da cin mutuncina agaban idon ya'yanmu, Ni kuma zan cigaba da zuba miki idanu har inga iya gudun ruwanki kafin in dau mataki, sakarni banza jahila kawai.." yasa karfinsa ya tunkud'eta tayi taga taga zata fad'i amma bakinta bai rufu ba ta cigaba da zage zagenta, bai sake biye ta kanta ba yayi hanyar waje, ko ina zaije acikin tsohon daren nan oho? Amma gara masa kwanan waje daya tsaya maganganun Halima masu suka su sanya zuciyarsa bugawa..


Izuwa yanzu lamarin Addah yabar bani mamak'i sai papa duba da yadda lokaci guda kawai yayi fancakali da al'amurana, hakan na nuni da cewa ya soma gajiyawa da duk wani abunda ya shafi rayuwata kenan...cikin karaji na daga murya nace"papa ko kaima ka soma gajigawa da lamarin d'iyar taka ne ?, ku sani bani na dorawa kaina wannan kaddarar ba, haka kuma bani na zab'awa kaina irin wannan haguguntacciyar rayuwar ba, Allah ne da kansa ya zabamun, kuma ba don baya sona yayi hakan ba, a'a sai dan ya gwada cikar imaninmu duka domin kuwa jarabawa ce agareni, haka zalika kuma d'in jarabawa ce agareku ku iyayena, to shin meyasa bazaku taimakamun wajen cinye wannan jarabawar ba ?, papa watsi da kake k'ok'arin yi da al'amurana shi yafi mun komai ciwo fiye da hukunce hukuncen da Addah take dauka akaina, mahaifina dan girman Allah karka juyamun baya, kuturu, makaho, bebe, gurgu, ko kuwa mai kowacce irin nakasa ko wanda ya hada duk wa'ennan nakasosin kana iya had'ani aure dashi, daga yanzu nina hakura na baku zab'in mijin aurena wanda dama can hakkine akanku ku iyaye daku zab'awa ya'yayenku abokan rayuwa na gari....."


"a'a Rahama bani da wannan ikon domin mahaifiyarki bata dorani akan wannan matsayin ba, abunda kawai zan iya tayaki dashi shine du'a'i..." yana gama fadin hakan ya kada kai yayi gaba abinsa ba tare daya bani damar sake magana ba.


Sosai maganganun nasa suka tsaya mun arai, kwata kwata na rasa gane abunda yake nufi, maganar mama ne ya katsemun guntun tunanina"karki wani dami k'wak'walwarki da tunani dan bazaki fahimci komai ba, amma abunda kawai zan iya ce dake shine, maganarsa tana akan hanya, dan haka karki daukeshi wawa, soko wanda baya da katabus agidansa, ina so ki sani idan har al'amarin daya shafeki ne, to Abdulmalik yakan kasance mai rauni kuma mai sanyi, amma akan abun daya shafi Sakina da Adnan yakan zama mutum mai zafi kuma mara tausayi, nasan ke kanki kin fahimci hakan tun ba yau ba, kuma ki kan cika fam da mamakin hakan, kuma nasan tambayoyi kan cika miki ciki aduk sanda hakan ta faru.."


Tabbas Addah tayi gaskiya, nakan addabi kaina da tambayoyi, shin meyasa mahaifina baya hukuntani aduk sanda na aikata ba daidai ba sai dai ya jira mahaifiyata ita d'in ce ta hukuntani ?, Shin yafi sona ne acikin ya'yansa ko kuwa ?, amma ai ance yadda zaka nunawa dan daka haifa so shine ta hanyar nuna masa kuskurensa aduk sanda ya aikata ba daidai ba, rashin kwab'a yakan jawo yaro ya lalace kuma wannan ba so bane, kuma abun mamak'i laifi kalilan kannena zasu aikata kaga ya dau zafi, awasu lokutan ma har sai kaga ya shigesu da bugu amma ni zan iya rantsewa sau daya tak! Ya dakeni arayuwarsa tunda nayi wayau kuma sai da mahaifiyata ta nuna tsantsar bacin ranta akan hakan wanda tun asannan ko fad'a bai sakemun ba, ina tsammanin wannan yana iya zamo dalilin dayasa ya tattara al'amurana ya watsar tunda ya lura Addah bataso yana tankawa, kadan ne kawai yake saka baki.


Papa na fita waje ya latso Uncle Yusuf awaya yana dagawa bai jira yayi wata magana ba yace"idan ka taso daga aiki gobe ka biyo gida ina son ganinka." Yana gama fadin hakan ya katse.


******


Tun adaren jiya da Umar ya koma gida suke ta rikici da Ubaida, ko kadan bata sarara masa ba hakan ya sake Fusatashi yayi mata dan iskan dukan daya sata baccin dole da ko kadan batayi niyyar yinsa ba, shidda saura na safiya ta farka tana mik'a da salati, bin dakin ta shiga yi da kallo ko'ina ahargitse hatta standing mirror d'inta sai da suka fasashi, ahankali ta mik'e tana jan jiki sabida ba karamin tsami jikin ke mata ba, ta dad'e bata ga azzalumin namiji kamar Umar ba wanda ko kadan besan darajar 'ya mace ba, fadawa bandak'i tayi ta sakarwa kanta ruwa, ta dan jima tana duddurza jikinta sannan ta dauro alwala ta Fito, matsar da wasu kayan tayi gefe ta shimfid'a dadduma, nan tayi kabbara ta fara sallah...Sai kusan bakwai saura ta fito bayan ta gama kimtsa dakin don adakin nata ne akayita yak'in kasancewar nema yayi ya haik'e mata adaren jiyan bayan ya dawo, shine ta hanashi suka shiga kukuwa, dan shi Umar mutum ne wanda duk iskancinsa baya tab'a kusantar Zina, idan ya kwaso bukatarsa zuwa yake ya huta ajikin Ubaida, be dauketa abakin komai ba illa Sex machine d'insa, shiyasa ya kwadaitu da Rahama sosai yake jin kota halin kakani kayi ne sai ya mallaketa domin su zamar masa biyu, ababen hutawarsa da kuma kau da damuwa, acewarsa kenan...shi kwata kwata ko tausayin Ubaidar ma ba yayi da ba wani cikakken lafiya gareta ba, Umar dan Kumurci ne na gaba ba baya ba....


Hangoshi tayi zaune adining yana kari, had'awa kansa kakkauran shayi yayi amug, gefensa kuma bread sandwich ne wanda ya dawo dashi adaren jiya, da sauri sauri yake karin don ya kammala ya Fita aiki, amma kafin nan yana da kudirin fara biyawa gidansu Rahama domin ya cika manufarsa akanta, sosai yayi mata k'yau yana sanye da black suit da wandonsa ma black, sai cravat neck tie d'insa purple, Siririn kasumbar nan tasa agyare, Umar ya hadu ta ko'ina sai dai halin kumurcinsa ne yasa ba'a ganewa, Wani irin daddad'ar kamshin turarensa ta 'Eternity For men' ne kawai ya dume Falon...Lumshe gajiyayyun idanunta tayi gami da sakin ajiyar Zuciya ta dumfari inda yake, Kallo daya yayi mata kana ya dauke kansa ya jawo wayarsa ya hau latse latse, alokaci daya kuma yana me cigaba da karinsa, akai ta tsaya masa ta kama kwankwaso sai wani irin girgiza take wanda ze tabbatar maka da cewa lallai rigima take ji...bai ce da ita kala ba har aka share kusan dakik'u biyar, can ya mik'e rike da tissue ahannu yana share bakinsa sannan ya dauki briefcase d'insa da makullin mota, se kuma waya, had'e rai yayi yace"kaucemun ahanya " baza'a kauce ba kayi mun hukuncin daka saba yi " ta furta idanunta na tafasa tsabar bala'i...Murmushi ya saki gami da daga hannu yana karkada mata makullin hannunsa" Ubaida ki shiga hankalinki don ban shiryawa haukarki da farar safiyar nan ba, ki bani hanya in wuce in ba so kike in sake kumburar miki da Fuska ba..." cakumo kwalar rigarsa tayi babu wani tsoronsa kuma atattare da ita tace"Umar ka dade baka kasheni bama amma wallahi na rantse da Allah ayau saika sawwakemun donna gaji da zama da azzalumi, macuci kamarka, maganar gaskiya mahaifina ya cutamun daya hadani zaman aure dakai ! Sam banyi sa'an uba ba, da irin mahaifina amatsayin uba gwara in fito duniya amatsayin shegiya wacce ba'a ma san takamammen ubanta ba..." kuka yaci mugun k'arfinta, jikinta ya mutu lakwas data tinano ko wanene mahaifin nata, bushewa da wani irin mahaukacin dariya Umar yayi, cike da rainin wayau yace" Sai ayau kika dawo hankalinki kenan...? ai gwara dani, ni d'in dan kumurci ne, shi fa...? ya kasance ne dan zaki me ruri, Ubaida tunda na bud'e ido nayi wayau ban tab'a cin karo da wani d'a namiji wanda akewa lakab'i da Wuta da kankara kamar mahaifinki ba, kifi me tarin ya'ya kenan don shi karan kansa yana yawan gayamun cewa shi besan iya adadin yaransa aduniyan nan ba, ke kiji fa...? Sannan sai ki zauna kina tunanin akan halin ko in kula da yake nunawa akanki...? yana da tarin ya'yan da ba lallai ma ya sake tunawa dake ba, ni addu'ata ma ayanzu be wuce kar Allah yasa be had'a cakwakiya ba, kar Abu yazo ya kasance kuna komawa kuna auran junanku Baku sani ba tunda abun aduhu yake, gwara kawai ki lallaba mu zauna da dad'i ba dad'i, zancen saki kuma da kikemun kinji nace Allah bazaki saku ba don muddin na kuskura na sakeki to tabbas arziki'in da nake tattalawa awajen mahaifinki zaizo karshe....Ubaida ki lallashi zuciyarki akan tayi hakuri don bazan taba fasa abunda na kudurta araina bane, Muddin ina raye saina auri kawarki Rahama !.."


Yana gama furta hakan ya hankadata tayi gefe zata fad'i, da sauri ta dafe kujerar daya tashi akai, hakan yasa bata ida kai k'asa ba, shi kuma yasa kai yabar gidan, sai zage zage take tana rusa kaya tare da cin alwashin ganin bayan Rahma koda kuwa zatayi yawo tsirara ne, acewarta da zama da wacce ta gama sanin kusan dukkanin sirrukanta amatsayin kishiya gwara azabar kabari.


 *(wa'iyazubillahi! Sister's wallahi kaso 70 acikin labarin nan true life ne, Ku muje zuwa karku bari abaku kabari)*


Yana fita kai tsaye unguwarsu Rahma ya nufa bayan ya kira Zalihat awaya yace taje gidansa ta karashe masa aikinta na k'arshe akan Ubaidar. Yana danno hancin motarsa layinsu Rahama adaidai lokacin shi kuma Abdiel yake fitowa daga gidansa da tashi motar, ganin Sakina ta fito gida ne yasashi paka motar ya fito ya nufeta da sauri yana fadin"Excuse me dan Allah ina son magana dake " 



waigowa tayi tana kare masa kallo dan bata tab'a ganinsa a unguwar ba, can ta karasa wajensa, daga can nesa kuma Umar ya paka tashi motar yana kallonsu ji yike kamar yayi tsuntsuwa yaje yaji dalilin dayasa Abdiel tsayar da Sakinar.


Daga can kasan layi kuma motar Uncle Yusuf ce ta kunno kai, don daga baya yayi Tunanin gwara ya fara zuwa yaga yayan nasa suyi magana don in yace sai ya jira har ya tashi aiki kafin yazo tofa hankalinsa bazai tab'a kwanciya ba. Shima dai kamar Umar bai karasa kofar gidan ba, daga nesa ya paka yana kallon bak'uwar Fuska ta Abdiel da Sakina.


*Littafin KAZAMIN TAKU paid book ne, domin samun cikakken labarin sai abiya N500 kacal Via 0249313050, Hafsat Mustapha, GTB.

*Shedar biya ta wannan lambar ***.*




#Vote

#Comment &

#Share

#HAFNAN💋