Page 2
*ABIN DA CIWO*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 2.
Bayan yaya Kamalu yayi parking sai ga matan dake gidan da yara sun zo sun zagaye motarsu suna faɗin oyoyo tare da yin guda, Sameeha dai fitowa tayi tana kallon ikon Allah wanda a yadda suka tsara ba zasu sanar da sauran dangi yau ne dawowarsu ba har sai an kwana biyu kafin za a faɗa tare da gayyatar su walima da suka shirya yi, yadda taga suna ta yi mata sannu yasa ta saki fuska tana amsawa, bayan sun shiga cikin falon ne suka ganshi kaca kaca anci abinci da ruwan gora da lemukan gora an zubar wani gurin an zubar da ruwa yayi dama dama falo dai ya fita hayyacinsa, ga cushing da suke sababbi anci abinci akai duk an zubar, cabar mamaki da haushi yasa Aminu bai tsaya a falon ba ya wuce zuwa falonsa ya buɗe ya shiga ciki ya zauna a cushing, kana ya cire hular kansa ya tallabo fuskarsa da hannu bibbiyu, sai ga su Yaya Alhasan sun biyo bayansa suna balbale faɗa, Sameeha itama ta shigo ciki da yara sannan su Hauwa suka biyo su suka tsaya cirko cirko suna sauraren faɗan da Alhasan ya ke yi musu akan yadda suka mayar da gida kamar ana hidimar biki ko suna, har murhu suka dasa a tsakar gida suka yi girki, Yaya Alhasan ya dubesu yana cewa.
Da izinin waye kuka zo gidan nan kuka dasa shagali kamar za a tarbi amarya, wannan ai hauka ne da rashin hankali, fisabilillahi ya dace ace Aminu ya dawo yaga gidansa haka. Ina ce mun tsara sai bayan kwana biyu za a faɗawa dangi lokacin walimar da za a yi na dawowarsu.
Yaya mu wlh munyi ne dan suga tsantsar murna da farin cikin dawowarsu da muka yi, ba da wani nufu muka yi haka ba, kuma In Sha Allah yanzu zamu gyara ko ina..
Cewar Hauwa, Kamalu ya daka mata tsawa.
Ai na tabbatar ke ce kika yi shelar sun dawo saboda bakinki ba farsa kamar radion daya samu matsala, rarara haka kike, shiyasa ni inyi sirri da ke Allah ya kyauta, ke kuma wa kika tambaya da kika kwaso jiki kika zo.
Ya kare maganar akan matarsa Sa'a da sai raba ido take dan tabbas su suka shirya abinsu ba tare da mazan sun sani ba, Hauwa itace shugaba sai Laure data karfafa lamarin, Laure ce ta yi magana cikin jin haushi.
Haba daga taya murna sai cibi ya zama ƙari, mu munyi abinmu domin Allah ne da kuma zumunci amma baku yaba ba sai kushewa. Hauwa kun ga ku zo mu tattara mu tafi tunda suma wanda muke damonsu basu ji daɗin ganinmu ba, hmmmm ba shakka Aiziki kashi tun kafin abu yayi nisa an fara nuna mana wariyar launin fata, to Allah ya horewa kowa.
Dama ai ke girman jiki gareki amma da kina da hankali ke ce zaki hana wannan haukar da kuka shirya, amma kika biye su kuka aiwatar da abin takaici.
Cewar Alhasan cikin zafi, ƙanwarsu Salma ce tace cikin fuskar tausayi.
Dan Allah yaya kuyi hakuri yanzu zamu gyaran gidan. Anty Sameeha fatan kun dawo lafiya.
Lafiya lau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya, yaya Laure yaya Hauwa anty Sa'a dan Allah ku yi hakuri ni sam banga laifin da kuka yi ba, ku rabu dasu yaya, kuma nayi murnar wannan tarba da kuka yi mana dan soyayya ce ta kawo haka, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.
Dalla rufe mana baki munafurcin banza.
Cewar Hauwa data katseta ta wuce fuuu kamar guguwa, suma sauran suka bi bayanta bayan Laure ta sakar mata wata uwar harara suka fice. Sameeha sauke ajiyar zuciya tayi ta koma ta zauna tana bawa su Yaya hakuri akan subar maganar haka komai ya wuce, ita sam bata ga laifin su ba tunda mai kaunarka shine zai tarbeka da farin cikinsa, duk da a cikin ranta ba haka bane amma dole ta nuna kawaici dan tasan faɗan suna yi ne saboda ba zata ji dadin faruwar abinda suka yi ba, Aminu ma nuna musu yayi komai ya wuce, nan suka yi salama da su suka wuce, suna fita Aminu ya rufe kofar falonsa da key dan sam baya son hayaniya ya shige bedroom ɗinsa ya bar Sameeha da yara a falo itama tana mamakin wannan rashin lissafi da suka aikata mata sai dai ta san da biyu suka yi, kuma taji daɗin yadda su Yaya Alhasan suka kwarkwance musu ko banza ba zasu kara yi mata wannan shisshigin ba.
***
Laure da Hauwa.
Suna fita tsakar gida suka sanar da 'yan uwa cewar zasu tattara su koma family house ɗinsu dake unguwar dosa, sai su cigaba da hidimarsu saboda dama jiran dawowarsu suke yi su koma can, suka saka aka yi shara ciki da waje aka yi mofin kitchen da falo gida ya dawo hayyacinsa duk da ba wani gyara ya samu mai kyau ba, suka kwashe murhu da tukunya suka saka a baron da aka ɗauko shi dan daga can babban gida suka ɗauko, saboda Umma ta siya musu tukwane da kuloli saboda sha'ani, Laure takan ba da hayarsu a bata kudi, kuma ba wanda ya hanata dan saboda gadara da take a gidan kuma ba umma balle Abba a raye, haka suka tattara da yara suka wuce ba tare da sun yi musu sallama ba, da yake ba wani nisa sosai a tsakaninsu wasu a kafa suka tafi babban gida, wasu kuma suka tari napep ya karasa da su, Laure da Hauwa sune karshen tafiya suka jera a kasa suna yi suna surutu cike da takaicin abinda su Alhasan suka yi musu, Hauwa ta mele baki tana cewa.
Ni Sameeha tafi bani haushi, ai da taso karemu lokacin da yaya Alhasan ya fara magana sai tayi kokari ta tare shi, amma sai da suka kare mata cin mutunci kafin ta iya saka baki.
Ni kin san miye ma? na kula da shi tunda suka shigo wani gani gani take mana da kallon raini ita matar Alhaji, wlh yarinyar nan nan gaba Allah kaɗai yasan iskanci da wulakancin da zata yi mana, dan haka ni zan kama kaina dan bazan bari raini ya shiga tsakaninmu ba.
Haba Yaya Laure wane ita? ai uban kuturu yai kaɗan, kuma bata isa ta hana mu zuwa gidan ɗan uwanmu ba dan a sama ta same shi wlh, in kuma ta kawo mana wargi sai nayi sanadin da tabar gidan mu aura masa wacce muke so.
Allah yasa Aminu kar ya baku kunya dan naga yana mutuwar son Sameeha kamar ta gama da shi.
To na nawa kuma, ko kin mance mahaifin mamanta malami ne ai tuni aka kafe sunan Aminullahi a allon ƙarfe, sai yadda tayi da shi dan an wanke an bashi ya sha.
To Allah ya kyauta amma in tasan wata ai bata san wata ba mu zuba mu da ita.
Yauwa yanzu naji batu ai sai dai muga bayanta ba dai mu taga karshenmu ba, wlh yadda na tsani mutuwata haka na tsani ganin Sameeha a gidan Aminu tunda ta nuna mu bamu isa da ita ba. Amma gobe In Sha Allah zan dawo gidan na ja mata layi dan nan ba Lagos bane, mun dawo kusa da juna komai da zata yi yana kan idonmu.
Hmmm har kin tuna mini da batun yar aikin da kika ce na samo, jiya agent ɗin ta kira ni ta sanar dani an samu.
Yauwa yaya Laure zamu je kuwa tare, dan mu ga yarinyar kuma mu ɗaurata a hanyar yadda muke so, kinga kenan zamu rika jin labarin duk abinda ke faruwa a gidan.
Cewar Hauwa tana wani sha'umin murmushi, sosai suka cigaba da fito da hassadarsu akan Sameeha, bayan in an tsaresu ba su da wani hujja da zasu faɗa laifin da Sameeha ta yi musu, kawai daibbakin ciki daular da take ciki suke yi kuma sun kasa juyata kamar yadda suka so.
***
Sameeha.
Sai da ta tabbatar da sun fita kafin ta fito falon ita da yara, sai ta fita tsakar gida taga sun gyara gidan amma akwai sauran inda ya dace a share sannan akwai inda ya kamata a saka ruwa a wanke, ba zata iya wannan aikin a ranar ba sai dai ta bari zuwa gobe in Allah ya kaimu tayi. Babban gida ne da aka zuba masa kudi aka kerashi yadda ake son ya kasance, falo biyu ne a gidan falon farko shine na Sameeha da ɗakuna guda gudu, ɗaya na ta ɗaya na Abi ɗaya kuma na Amrah, sai guda ɗaya extra saboda baƙi, sai katon kitchen da store a ciki an zuba komai na buƙata sannan akwai bayi ɗaya a falon duk da a ko wani ɗaki da bayin, sai falon Aminu da yake madaidaici da ɗakuna biyu, ɗaya bedroom ɗinsa ɗaya kuma ya aje muhimman takardunsa wato study room da kuma kayan motsa jikinsa, an zuba komai dai na buƙata. Sannan can bayan gida akwai BQ guda biyu da bayi da kitchen sannan akwai bishiyoyin mangoro da gwaiba har da gwanda da lemu, yar karamar garden dai da rumfar shan iska da kujeru, sai parking space a nan farfajiya an ajera mota uku a ciki, ɗaya na Aminu ɗaya na Sameeha hotuwar nashi da yake hawa ya bar mata sai ya saya sabo, sai na ɗaya na kai yara makaranta, ga kuma ɗakin me gadi a bakin gate komai dai gwanin sha'awa. Sameeha da ta koma falo sai ta aika Abi ya amso key ɗin ɗakunansu dan duk suna rufe, kuma key yana hannun yaya Alhasan sai da suka zo ne ya bawa Aminu su, da ace su Hauwa sun samu key ɗin da fa sun gama ganin sirrin gidan da komai yadda zasu ji daɗin karaswa, tana tsaye sai ga Aminu ya fito daga falonsa tare da Abi, da murmushi ta kalle shi tana cewa.
Allah yasa bamu tasheka a barci ba.
A'a idona biyu tunda na shiga nake amsa waya kin san harkan aikinmu ba hutu, amma gaskiya gidan nan sai kin kira su Ikram sun zo sun tayaki gyara dan sam bai gyaru yadda ya kamata ba.
Eh dama na bari gobe In Allah ya kaimu sai nayi aikin yanzu me zan ɗaura maka kaci, dan mu muna da abincin tarba da ummanmu ta yi mana, kasan can zamu kwana.
Eh da yake ni ba ɗan umma bane dole a ware ni, to nima dani zaku tafi in cika cikina a can in yaso sai na wuce can babban gida in kara gaisawa dasu Yaya, ƙila ma na kwana can.
Abban Amrah na isa nace kai ba ɗan umma bane, kawai banyi maka tayin zuwa ba ne dan baka ce zaka ba.
To yanzu nace zani Madam Meeha matar Aminun Alhaji Ado.
Sai ta kwashe da dariya yaran suna taya ta shima dariya yayi sai ya wuce ya buɗe ɗakinta suka shiga suna wow wow kamar motar asibiti, an zuba funitures masu tsanani kyau da burgewa wanda suka yi oder daga company MG Furnitures wanda show room ɗinsu yake Freetime house kusa da asibitin giwa kan titin Ali Akilu. Zaku iya tuntuɓarmu a nan *** domin karin bayani akan ko wani irin kaya da kuke muradi.
Bayan sun gama ganin ɗakin Sameeha haka suka fito suka shiga ganin ɗakunan dake falon har zuwa kitchen komai yaji an zuba kuɗi kuma buƙata ta biya, bayan sun shiga store ne suka tadda an buɗe buhun shinkafa ɗaya an ɗiba, ga kuma mai dake galam da aka diba shima, Aminu ya buɗe freeza da aka zuba musu kaji ɗanye gyararru da ganda da kifi. Ya ƙirga kajin yaga guda takwas madadin guda goma sha biyar da yaya Kamali ya faɗa masa an zuba a ciki, ya juyo fuskarsa cike da ɓacin rai.
Amma wlh Hauwa da Laure sun wuce gona da iri, na tabbatar sune suka yi wannan aikin, ashe abincin da suka dafa namu suka ɗiba, na ɗauka taya murnan nasu da gaske ne da suka cika mana gida suka ɓata, gaskiya dole na taka musu burki dan bazan jure wannan cin kashin ba.
Haba Aminu in rai ya ɓaci hankali ke nimoshi, 'yan uwanka ne fa suka ci abincin nan, arziki ne ma ayi maka irin haka, idan ba suna ganin kai nasu ba ne taya zasu yi haka, ni dan Allah karka yi musu magana faɗar da su Yaya Kamalu suka yi musu ya isa kar kazo kayi magana su mayar da abin wani iri.
To amma fisabilillahi ba zasu iya faɗa mini za suyi abu ba sai dai kawai mu dqywo mu tadda gida kaca kaca, ashe ma abincin gidan suka ɗiba suka yi wannan wandaƙar, duk lemuka da ruwan dana siya mana wanda zamu jima muna amfani dasu shi suka kwashe suka shanye, wannan ai haukane da mugunta..
Kayi hakuri dan Allah kuma kayi musu uzuri na tabbatar ba zasu sake yin haka, Abi da Amrah kuje ku ɗauko hula da hijab da jakata mu wuce gidan umma.
Ta kare maganar akan yaransu, sai suka fice da sauri ita kuma ta mayar da kallonta gurin mijinta.
Dan Allah Abba Amra komai ya wuce kuma bai dace kana irin wannan maganar a gaban yaran nan ba hakan ba tarbiyyarmu bace.
Wlh raina ne ya ɓaci amma zan kiyaye, mu je gidan Umma dan naga la'asar ta kawo jiki.
To tace masa sai suka fito, yaje inda motarsa take ya cire mata riga ya budte ya shiga ciki ya kunna ya kawota tsakar gidan, suka shiga gabaɗaya mai gadi ya buɗe musu gate suka fice.
Ummu Sultan da Samha ce.