Mutum Mugu Ne

38

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*

                     38


Tamkar biki ake yi, haka kowa ya yi shiri na gani na faɗa. Kowa ka gani da zubin kwalliyarsa, abin birgewa shine dukkansu Allah ya musu baiwar kyau. Hajiya Zaytunah ke shige da fice cikin 'yan uwa tana bada umarnin mi ya da ce da kuma abinda za'a yi, shigar ta kaɗai abin kallo ne tun daga jewelries ɗinta zuwa lace ɗin da ta saka ɗinkin gown.

Tun da sassafe Naziha ta yi wanka, da shike duk girkin da za aci a wajen ordering ɗinsa aka yi, shi yasa ba wani aikin da za su yi. Saratu ne ta tayata zaɓar kayan da za ta saka, cikin kayan da suka siyo da su Yassar ta zaɓi wani Anarkali gown ta saka baƙi mai adon golden a jiki ta saman rigar, gyalenshi baƙi da golden ta yane kanta da shi, cikin takalman da Yassar ya zaɓa mata ta sami mai kalar golden sai dai ya na da tsini sosai, ta ja tsaki ita dai ta san ko da wasa ba ta taɓa gwada tafiya da takalmi heel ba, har za ta maida shi wata zuciyar ta ce there's no harm in trying, Thank God yana da igiya, ta saka tana gwada tafiya Saratu na ma ta dariya, kasancewa duka gidan za su tafi har maigadi yasa dole kowa ya fito, tuntuni an fara wuce wa asibitin. A hankali ta ke takowa ta fito, daga ɗaki ta tsaya ba kowa a falon tana jiran Saratu ta fito su fita wajen gidan, tun da baƙi suka zo Sajid ya cire facial recognition a ƙofar falon yanzu kowa ya matso kusa da ita za ta buɗe da kanta.

Wani ƙaramin yaro ta gani da ba zai wuce shekara biyu da rabi ba yana saukowa daga stairs ɗin da gudu. "Marzuƙ ka yi a hankali kar ka ji ciwo" wa ta farar ma ta ta biyo shi da sauri, kallo ɗaya ta mata ta ganeta, ƙanwar Sajid ce Nadia da ta taɓa ganin hotonta a laptop ɗinsa. Yaron ya zo ya ɓuya a bayan Ziha yana dariya. Nadia ta ƙaraso ta ce " oya zo nan na ce"

" ina kwana ma" Ziha ta gaisheta

Fiskarta sake ta amsa ma ta gaisuwar tareda cewa " yi haƙuri hankalina yana kan Marzuƙ ne, an tashi lafiya, ya kwanan baƙi, sannunmu fah kunata ɗawainiya da mu tun jiya"

Ziha ta yi murmushi kawai, tun daga sama Azra ta fara kiranta Nazzy, Nazzy. Ta na saukowa ta zo da gudu ta rungumeta ta ce " i miss you Nazzy"

Nadia ta taɓe baki ta ce " Lah ashe ke ce Nazzy da ta ke ta bani labari tun jiya, Allah Sarki, what's the name please?"

"Naziha" ta amsa ma ta

"Oh no! ke ce yarinyar da ta taimaka wa Ya Saj a Lagos, nice meeting you dear" ta miƙa ma ta hannu suka gaisa. Tare suka fita daga cikin gidan, Ziha ɗauke da Marzuƙ da ya maƙale mata. Motoci uku ne a waje motar da Sajid zai tafi sai ɗaya da zata ɗauki Nadia, Azra da ɗanta Marzuƙ, ɗayar kuma Saratu da maigadi za ta ɗauka. Motar da Saratu za ta shiga Ziha ta nufa. Nadia ta kirata " zo mu tafi a wannan 'yar Albarka" ba musu ta je ta shiga suka tafi, ta yi mamakin yadda Nadia ta sake jiki da ita tana ta zuba ma ta surutu kamar sun jima da sanin juna. " fatan dai Zaytunah ba ta muzguna miki ?" Tambayar da ya sa ta yi ƙaramar ajiyar zuciya sannan ta ce "Anty Zaytunah is nice"

"Lah ba wani ɓoye-ɓoyen da za ki min dan na san halin Zaytunah sarai, na zauna da ita na san abinda za ta iya yi, kin ga idan Zaytunah tana takura miki feel free ki gaya min, ni zan ɗau mataki akai, da ma ba yau muka saba rikici da ita ba, kin gannin nan lokacin dana ke budurwa ma ban barta ba balle yanzu, ranar sunan Azra sai da na mata kankat a gaban mutane, kin san a haukarta sai da ta dena kiran sunan Azra saboda ni na ce wa Yaya ya saka sunan, ban san ma ya aka yi ta huce ba har ta ke kiran sunan yanzu"

Haka Nadia ta dinga ma ta hiran rikicinsu da Zaytunah har suka isa farfajiyar asibitin.

Sajid da Zaytunah ne fitan ƙarshe a gidan, suna fita ya sa remote ya locking gate ɗin da duk sauran ƙofofin gidan. Sai da suka fara tafiya ya tuna kwana biyu bai saka Ziha a ido ba tsabar yadda ayyuka suka masa yawa.

Motarsu ce isowar ƙarshe wajen, suna fitowa Zaytunah ta sa hannu cikin nasa ta na murmushi suka taho a haka.

Ziha na gefen Nadia ɗauke da Marzuƙ ta ji Nadia ta ce "ji min fitsaranci, wai ita daɗi miji, tafi kowa iya soyayya, mtsww "

Ziha dai ba ta ce komai ba saboda hankalinta ya tafi kan Sajid da ta ke ganin kyau da ƙuruciyarsa ya sake fitowa.

Alhaji ne ya gabatar da addu'a sannan Sajid ya kama hannunsa tare suka yi Bismillah suka yanka ribbon ɗin da ke jikin ƙofar. Wajen ya ɗauka da tafi wasu kuma suka yi kabbara. Idon Zaytunah ya ɗan kaɗa saboda duk plans ɗinta wannan rana bai wuce hotunan da za'a musu yayin da Sajid zai haɗa hannu da nata ya buɗe asibitin ba, sai gashi hannun Alhaji ya kama. Har ta rubuta irin sharhin da za ta yi a ƙasan hoton gashi Sajid ya ruguza ma ta plans, Allah da Alhaji ba sirikinta ba ne da ta make hannunsa, zuciyarta na raya ma ta " I deserve this moment more than anyone"

Gaba ɗaya jama'a aka kutsa kai cikin

*SAJIDA HOSPITAL AND CENTER FOR NEUROSURGER*

Ko wani lungu da saƙo an duba, daga nan aka shiga bayyana tsare-tsaren asibitin tareda gabatar da ma'aikatan wajen tun daga likitoci zuwa cleaners da masu gadi. Daga litinin zuwa jumu'ah na satin farkon buɗe asibitin duk wani aiki da ya danganci ɓangaren neurosurgery kyauta za ayi shi sauran ɓangaren kuma za a biya 50% na kuɗin.

Manyan mutanen da ke wajen suka tofa albarkacin bakinsu sannan aka fara refreshment cikin farfajiyan asibitin.

Marzuƙ ta biyo da gudu cikin asibitin kar yai ɓarna dan yaron gagara gareshi, abinka da rashin sabawa da heel tana cikin sauri ta ci tuntuɓe ta yi luu za ta faɗi ta ji an riƙeta " careful pretty" muryansa ya doki kunnenta suna haɗa ido ta ganeshi Dr Jamal Yusuf ɗaya daga cikin gynaecologist da aka kira ɗazu. Maimakon ya sake ta sai ya sake riƙeta gamgam ɗaya hannunsa yana shafar bayanta zuwa hips ɗinta, irin kallon da ya ke mata da kuma shafar jikinta da ya ke yi yasa ta yi saurin fizgewa daga jikinshi.

"Naziha!" Ya daka ma ta tsawa, magana suke yi da Dr Carson amma yana hankalce da abinda ya faru ganin Dr Jamal ya fara wani abu daban ya sa shi yi mata tsawa babu shiri.

Suna haɗa ido da shi ta ga tsantsar ɓacin rai tattare da shi, da ƙarfi ya ce mata "follow me " ba musu ta bi shi. Office ɗinsa ya shiga itama ta bi shi cike da tsoro.

" what the hell happened out there?"

Shiru ta yi idonta a ƙasa

" ba kya ji na ne, kina ganin ina ki ka barshi ya ke taɓa miki jiki?"

Muryanta na rawa ta ce " I'm..... so....sorry uncle tuntuɓe na yi...."

"And so what kin yi tuntuɓe, does that gave you the audacity to hug him? Uban wa ya saki saka heel in the first place......"

" Ya Saj lafiya" muryan Nadia ya sa shi yin shiru. Bai ce mata komai ba ya fice a office ɗin.

Ta ƙaraso wajen Ziha da take zubda hawaye ta ce "Naziha mi ya faru ne wai?" Da ƙyar Ziha ta iya tsayar da hawayenta ta gaya ma ta abinda ya faru, wani ƙayataccen murmushi Nadia ta yi sannan ta ce " kiyi haƙuri ba laifinki bane, stress ne ya mi shi yawa shiyasa yai miki tsawa"......


.....KADUNA......


Zaune suke a wani restaurant dukkansu biyu kowa da abinda ya ke tunani, a ɓangaren SY tunanin risk ɗin da ya ɗauka na haɗa hannu da Nazira ya ke yi while ita kuma abu biyu ta ke tsoro, kar SY ya hanata muradinta na ganin bayan Alhaji Kadi ko kuma ya zama ta ɓata lokaci wajen bin plans ɗin SY daga baya ta yi nadama.

Ya tura mata doguwar envelop gabanta ya ce " wannan shine plans ɗin da na tsara, idan kin je gida ki duba da kyau abinda ba ki gane ba sai ki kira ni"

" shikenan abinda za ka ce?"

"What else do you want me to say? tsohuwar 'yar bariki kawai Allah wadai da halinki"

A fusace ta tashi ta nuna shi da yatsa ta ce " ya isa haka nagode da cin mutunci, amma ka sani babu wanda ya wuce jarrabawar Ubangiji duk min muninta" daga haka ta ɗau jakarta ta bar restaurant ɗin ba tareda ta ɗauki envelop ɗin ba.