39
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
39
Tsaki yai sannan ya ɗau envelop ɗin ya fita shima.. da ya fito bai ganta ba, ya san ta riga ta samu abin hawa ta tafi.
.....tunda ta shiga Keke ta ke zubda hawaye da ta san cin mutunci da zai mata kenan da ba ta zo ba. Da ƙyar ta samu ta tsaida hawayenta lokaci guda ta haɗe rai ta ce aranta " duk min rintsi ni ce da nasara".
Washegari ta je gidan marayu ta ci sa'a Hajiya na nan, neman aiki ta ce wa Hajiya ta zo yi ko wani iri ne, Hajiya ta ce ta je ta dawo washe gari za ta duba maganar. Tana fitowa ta yi kiciɓis da SY da ke shirin shigowa, harara ta watsa ma sa ta wuce.
Washegari da ta dawo Hajiya ta ɗauke ta aiki a ɓangaren rijista na yaran da aka kawo ko aka tsinto, cike da farinciki ta yiwa Hajiya godiya, ta ce za ta fara aiki yau. Hajiya ta kira wata staff ta ce ta nuna ma ta inda za ta yi aiki.
Ƙarfe shida za ta dinga tashi amma saboda tana so ta yi bincike ta fake da kula da yara har ƙarfe tara na dare. Office ɗinta ta koma ta shiga ta fara binciko tsofin record tana dubawa ganin abin dayawa sai ta fara snapping ɗinsu.
"Za ki kwana kina dubawa ba za ki ga komai ba" ta yi saurin ture file ɗin gefe jikinta na rawa. "Matsoraciya kawai, a hakan za ki yi bincike" ganin SY ne tsaye akanta ta hararareshi ta ce "babu ruwanka da ni, abin da na ga dama zan yi" ya girgiza kai ya ce "tattara kayanki ki zo mu tafi" ta ɗago da niyyan hararansa amma sai ta tsorata da yanayin kallon da ya ke mata, ta kasa yin abinda ta yi niyya. Sake maimaita maganansa ya yi a karo na biyu, ta ja ƙaramar tsaki sannan ta fara tattara files ɗin ta maida su yadda suke.
Shi ne ya fara fita kafin ta bi bayansa. Suna fita daga gidan marayu ta ja ta tsaya ta ce "Malam ban gane mi kake nufi da ni ba fah, ka yi naka aiki na yi nawa mi ye na mini shishshigi" bai ko juyo ya kalleta ba ya cigaba da tafiya. Ta yi kwafa ta shiga tsallaka titin wa ta mota da ta zo wucewa da gudu ta bigeta.
Innalillahi....ya maimata lokacin da ya juyo ya ga ita mai motar ya kaɗe ya ƙarisa wajen da gudu, har mai motan ta fito ashema mace ce sai ihun Jesus ta ke yi.
Ta zubar da jini sosai saboda rauni da ta ji akai, bayan an gama mata ɗinki aka saka ma ta ledar jini. Kallon yadda ta koma lokaci guda ya yi, tausayinta ya kama shi, ala tilas dole ya kwana da ita a asibiti duk da kuwa akwai tarin abubuwa da ya kamata ace ya yi a wannan dare. Kada ta farfaɗo babu kowa a wajenta.
Ba ta farka ba sai ƙarfe biyar da rabi na safe, bayan ta tabbatar a gadon asibiti ta ke hankalinta ya tashi musamman da ta tuna cewa zai iya yiwuwa Allah ya ɗau ranta a accident ɗin da ta yi, nadama ya cika ta, hawayen danasani suka fara zuba a idanunta saboda yanzu da ace ta mutu kenan ta tafi ba tare da Abba ya yafe mata ba.
***
Fitowarsa daga masallaci zai koma asibitin ya dubata kafin ya wuce gida ya hango ta tana zaune kan dakali, ya ganeta sarai dan haka ya nufi inda ta ke da sauri sai da ya iso dab da ita ya ga wannan mutumin wanda ya ke tunanin escort ɗinta ne a tsaye a gefenta.
Sallama ya musu mutumin ya amsa amma ita Nana kallon titi kawai take yi. "yau ma biyoni har nan ka yi kenan?" ya faɗi yana kai kallonsa ga mutumin.
" ba bu nasara a tsarin da ka shirya, idan ka cigaba yarinya za ta rasa ranta kuma kai ma za ka jigata, shawara gareka kai haƙuri, saura lokaci kaɗan abokinka ya bayyana kuma komai zai zo ƙarshe" tana gama faɗin haka ta fara wasa da wasu duwatsu guda biyu.
"Ke wa ya gaya miki babu nasara a plans ɗina?" Ya tambayeta ba tareda tsoro ba.
Nana ta ɗago ido ta kalleshi kallon da sai da ya sha jinin jikinsa, sai yau ya kalleta ido cikin ido. Idanuwanta sun nuna ranta ya ɓaci sosai. Ba tace komai ba ta tashi ta fara tafiya. Sai da suka ƙule ma sa da gani sannan ya iya motsawa daga wajen. Da ƙyar ya iya shiga asibitin saboda yadda jikinsa ya yi sanyi.
Lokacin da ya shigo ɗakin ya tadda Nazira tana kuka har da sheshsheƙa, jikinsa ya sake yin sanyi musamman da ya tuna abinda Nana ta faɗa masa.
Ya ƙariso wajen gadon ya zauna gefenta kaɗan ya ce " ya jikin na ki?" Sai a lokacin ta iya ɗaga ido ta kalleshi duk da wani raɗaɗi da kanta ke mata saboda buguwar da tayi an ɗaure mata goshi zuwa rabin kanta da bandeji.
Ta mayar da dubanta ga ƙafarta na hagu da aka ɗaure shima dai dai wajen gwiwa, ta fara tunanin anya kuwa za ta iya takawa da ƙafar?.
" ki dena kuka zai sa mi ki ciwon kai" ya kamo hannunta ɗaya ya riƙe zuciyarsa na sake tuna ma sa abinda Nana ta faɗa
" idan ka cigaba yarinya za ta rasa ranta"
Wannan maganar shi yafi damunsa. What if da gaske ne idan ya saka Nazira cikin plans ɗinsa za ta mutu. Ya kau da tunanin ta hanyar cewa Nazira "Likita ya ce ba wani internal injury a kanki, so you'll recover quickly, zan tafi gida ba zan jima ba, zan dawo tareda sister na she'll be staying with you idan ba na nan" ta gyaɗa ma sa kai kawai, har ya tashi daga kan gadon zai tafi sai kuma ya juyo ya tambayeta " mi kike son ci?"
Ta haɗiyi yawu da ƙyar sannan ta ce "anything will do" ya amsa da "Ok sai na dawo" haka ta bi bayansa da kallo har ya fita tana tunanin sudden change of attitude ɗinsa
"It's because you look vulnerable Nazira" zuciyarta ya amsa ma ta.
Ko da Shabbir ya je gida ya sanar da Umma abinda ya faru ta tausaya wa Nazira sosai. Wanka yai sannan ya shirya suka tafi asibitin tareda Umma da Amina. Bayan sun isa ya sanar da Nazira zai zo ya dubata da rana daga nan ya je ya samu likita dan jin update akanta, Likita ya tabbatar masa nan da kwana huɗu zuwa biyar ma za su iya sallamanta.
Jollof ɗin shinkafa ne da ya ji kifi a ciki da kuma tea and bread suka kawo mata, ba laifi ta ci sosai musamman da ta ga Umma tana da kirki.
***
Zaune ya ke cikin gidan AY ya saka plans ɗinsa a gaba yana kallo, initially plan A ɗinsa kenan wanda ya ke tunanin in dai ya yi amfani da shi akwai 75% chance na samun strong evidence a kan Alhaji Kadi, amma for the first time in his entire career yana tsoron aiwatar da plan ɗinsa, normally in dai ya yi mapping plan haka ba ya taɓa chanjawa, amma yanzu yana shakkan abinda zai aiwatar duk da yana da plan B amma it's not as strong as the first one, chances ɗin samun nasara kaɗan ne.
Zuciyarshi ta shiga debating, wani ɓangaren na bashi shawaran ya ignoring maganan Nana yai abinda ya yi niyya da zaran Nazira ta samu lafiya, wani ɓangaren kuma na cewa a'a kada ya salwantar da ɗiyar mutane saboda plans ɗinsa.
Sallamar da ya ji a ƙofa ya sa shi tashi da sauri ya nufi ƙofar yana mai amsa sallamar tareda cewa "waye ?" Muryan nan da ya jima da kamawa ne aka amsa ma sa da cewa "Idan ka buɗe za kaga ko waye ne" ya buɗe ƙofar ba tareda tsoro ba. Ya rasa mi yasa ba ya iya haɗa ido da wannan bawan Allah, ba ƙaramin kwarjini mutumin ya ke masa ba, normally idan yana magana da mutane ya kan duba ƙwayar idonsu dan ya karanci wani abu, amma wannan mutumin bai isa ya duba cikin idonshi ba sai ya ji tsikar jikinsa na tashi.
Bayan mutumin ya zauna sai SY ya ce "Bawan Allah har yanzu ban fahimce ka ba, ban kuma fahimci Madam ɗinka ba"
Yai murnushi ya ce "ka zauna Muhammad ɗan Yunusa, na san za ka fahimceni idan ka ji labarin da ke tafe da ni" SY ya zauna opposite da shi.
Mutumin ya nisa ya ce " shirinka shine ka cewa Nazira ta yi cikin ƙarya sai ku sanar da jami'an Alhaji Kadi a sakata cikin lissafin jariran da gunki zai tsotse, kai kuma sai kayi amfani da wannan dama ka....."
" enough!" SY ya faɗi cikin tsawa " how did you know my plans? Mi ye nufinka game da ni?"
Murmushi mutumin ya sake yi sannan ya ce "na ga kamar ranka a ɓace ya ke zan dawo wani lokacin idan zuciyarka ta yi sanyi" da ga haka ya tashi ya fita ya bar Shabbir dafe da kansa da ke sara masa.
Bayan sallar Azahar ya je asibiti, bai tadda Umma ba amma ya samu Amina awajenta, itama ɗin cewa yai ta je gida ta huta.
" kin ci abinci?" Ya tambaya bayan Amina ta fita daga ɗakin ta gyaɗa ma sa kai
" Hey listen to me, na duba wayarki banga numbar iyayenki ko 'yan uwanki ba and they need to know you are here"
Ta sauke nannauyan ajiyar zuciya gami da goge ƙwallan da ke shirin zubo ma ta. "Allah Sarki Abba na " iya abinda ta faɗa kenan.
" ba su san kina nan ba ko?"
"wani uban ƙwarai ne zai san 'yarsa za ta je wani gari ɗaukan fansa kuma ya barta"
Ya ɗan cizi gefen lips ɗinsa sannan ya ce "tell me your story, ya aka yi 'yar'uwarki ta haɗu da Alhaji Kadi?"
Tambayarsa ya sa ta tunowa da Waheeda, tuni kuka ya ƙufce mata musamman da ta tuno irin mutuwar walaƙanci da ta yi. Kuka take yi sosai, da farko ya barta saboda ya san ta tuna da sister ɗinta ne, amma ganin kukan ya fara yawa ga kuma condition da ta ke ciki ya sa shi tashi daga kujeran da ya ke ya zo ya zauna gefen gadonta ya riƙo hannunta duka biyu ya ce " ya isa haka, ki dena kuka, you can tell me all about yourself later"
A hankali ta sassauta kukan har ta zo ta yi shiru, still yana riƙe da hannunta lokaci zuwa lokaci yana matsa yatsunta.
Shiru ya ratsa ɗakin ba abinda ke motsi sai ƙaran juyawar fanka. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta fara karanto ma sa labarinta tun daga farko har ƙarshe, lokacin da ta tsaya da magana ba ta ankara ba ta ji ya rungumeta dama a rigingine ta ke da filo, sosai ya matseta a jikinshi yana faɗin "I'm sorry Nazira, I didn't know you went through this much cruelty" muryanta ya ji tana cewa "zafi, kai na namin zafi" ya cireta daga jikinshi yana faɗin "sorry dear" duk da tana cikin baƙin ciki amma sai da ta ɗan murmusa.
Yanzu dole ya haƙura da plan ɗin nan dan ba zai iya saka Nazira cikin wani tashin hankalin da ya wuce wanda tasha a baya ba, infact idan aka sallameta daga asibiti zai mayar da ita Bauchi, she deserves to be with her Dad not out there seeking revenge, musamman ma da ke bata da wani ilimi a fannin bincike komai zai iya faruwa da ita. For the first time da tausayin mace ya sashi cikin zulumi kenan, ya yi mata alkawarin zai yi duk abinda ya kamata dan ganin asirin Alhaji Kadi ya tonu.
Da ya yi sallar Isha sai ya wuce gidan AY dan nan ne wajen aikinsa yanzu, ya riga ya yi wa Nazira sai da safe saboda Amina ce zata kwana da ita. Da mamakinsa ya kalli ƙofar gidan sa ya ga wannan dai mutumin nan ne zaune a ƙofar gidan yana jiransa.
"yanzu abin ya koma jirana ka keyi"
Mutumin yai murmushi ya ce " tunda zuciyarka ta yi sanyi zan iya ba ka labarin da ka ke son ji tuntuni"
" da zai fi kam" SY ya faɗi yana buɗe gidan.
A hankali mutumin ya taka zuwa wajen da SY ya manna wasu takardu ajikin bango wanda yawanci strategies ne na yadda zai solving case ɗinnan sai wasu kuma daily activities ɗinsa ne da ya rubuta.
"ina son mutum mai tsari" ya cigaba da cewa "sunana Abdulwahab, iyayena sun zo daga wajajen sahara zuwa wannan yanki ɗaruruwan shekaru da suka shuɗe. Mahaifina attajirin ɗan kasuwa ne kuma ya yi tsawon rai sai dai Allah bai bashi yawan 'ya'ya ba, 'ya 'ya biyar Allah ya bashi biyu sun rasu agabansa, sai ya rage ni dana kasance auta da yayyena ma ta biyu wanda dukkansu sun yi aure, mahaifina yana sona sosai, duk wani jin daɗi na rayuwa na samu. Lokacin da mahaifina ya kwanta rashin lafiya yai jinya sosai har kaman ba zai tashi ba. Watarana muka fita yawon zaga gari saboda ya ƙara samun ƙarfin jiki, wani ƙaramin gari a yankin Borno muka isa ƙofar wani dattijon malami yana bada karatu, abin ya bawa mahaifina sha'awa ya ce mu zauna muji karatun, nan muka zauna a wajen mahaifina yai sha'awan ina ma ɗansa zai zama malami kaman wannan dattijon, da ke ya tashi da kasuwanci bai samu damar yin karatun addini sosai ba, kuma nima a lokacin ba wani karatun na yi ba. Bayan an tashi muka koma gida Mahaifina yace yana so na fara karatu a wajen Malam Ibrahim. Na ce "Baba ta ya zan dinga zuwa ɗaukan karatu bayan ba ganina ya ke yi ba, idan ban gane ba ina son na yi tambaya ya za'ayi kenan?" Mahaifina ya ce kar na damu, washegari muka yi shigar mutane muka tafi gidan Malam Ibrahim, Mahaifina ya masa bayanin ya kawoni ne yana so na koyi karatu Malam yai na'am dani daga nan na fara ɗaukan karatu a wajen Malam. Hakan ya sa na san ko wanene Malam Ibrahim.
Malam Ibrahim irin mutanen nan ne da Allah ya musu baiwar ilimi da karama, a gaskiya iya zamana da Malam na gane Malam ba ƙaramin mai tsoron Allah bane, yana da yawan ibada ga haƙuri da yawan taimako. Allah ya jarabceshi da rashin haihuwa amma hakan bai sa Malam ya gaza wajen ibada ba, asalima hakan ya sa shi ƙara ƙusanci da Allah. A shekaransa hamsin da ɗaya lokacin ya na da yara sama da saba'in da ya raine su har sun girma wasu sun yi aure, yawancin yaran 'yan uwansa ne ko agolan da matansa suka kawo ko kuma marayu. Alqasim ya kasance cikin agolan gidansa, mahaifiyarsa ita ce matar Malam ta huɗu wanda mijinta ya rasu ya barta da marayu biyar, lokacin Alqasim ne autan ɗanta yana da shekara uku lokacin da Malam ya auri mahaifiyarsa.
Duk cikin yaran da Malam ya kula da su ba wanda ya ke so kamar Alqasim. Hakan ya tsananta masa wajen koyar da shi karatu. Da Alqasim ya fara girma sai ya zamana kwata-kwata ba ya son karatu, amma haka Malam ya tursasa ma sa dole sai ya yi, lokacin da ya cika shekara sha tara Malam ya ma sa aure saboda yana tunanin haka zai nutsar da shi.
Lokacin da na fara karatu a wajen Malam da kwana uku matar Alqasim ta haihu wajen haihuwa kuma Allah ya ma ta rasuwa. Ranar suna Malam ya sa ma ta suna Khadija, ta sha addu'a sosai wajen Malam hakan ya sa ta taso da basira da kuma tarin hikima, yayar mamanta ke shayar da ita amma kullum ana kawota wajen Malam saboda yana sonta sosai. Nana Khadija itace ɗiya ta farko a gidan Malam da aka sata makarantar boko tana shekara biyar, tunda aka yayeta aka maida ta gidan Malam, ko yaushe tana maƙale da Malam tun tana shekara biyu da rabi Malam ya lura da baiwa na saurin ɗaukan karatu da Allah ya mata. Daga nan Malam ya fara koya mata karatun addini sosai.
Mahaifinta Alqasim tun rasuwan matarshi ya ce wa Malam zai yi nisa da gida saboda ya samu nitsuwa, Malam ya ce ba matsala amma ya dage duk inda ya je ya dinga karatu. Nan Kaduna Alqasim ya taho bisa shawaran wani abokinsa, ya sauka gidan Malam Zakariyya saboda yawan labarinsa da ya ke ji. Malam Zakariyya babban Malami ne da sunansa ya ɗaukaka a duniya, ya kasance cikin malamai wanda ake musu ganin waliyyai.
Saɓanin Malam Ibrahim da ba a wani san shi ba saboda irin malaman zauren nan ne da ba kowa ya san da su ba, amma akwai su da tarin ilimi. Zaman Alqasim gidan Malam Zakariyya ya sa ya raina Ilimin Malam Ibrahim ya ke ganin Malam Zakariyya ya fishi komai dan haka ya sha zamansa a wajen Malam Zakariyya yana ɗaukan karatu a hankali kuma yana cusa kanshi wajen Malam ɗin har ya zamana yana ɗaya daga cikin wanɗan da suka fi kusa da Malam.
Sai bayan ya shekara biyar a wajen Malam Zakariyya kafin ya je Borno dan ya ga ɗiyarsa da kuma mahaifiyarsa. Anan Malam ya gane wasu canji daga halayen Alqasim har watarana ya buɗi baki ya ce masa wai ya je ya nemi ilimi dan har yanzu bai kai ya kira kansa da malami ba a gaban Malam Zakariyya. Malam murmushi kawai ya yi sannan ya ce idan Allah ya yarda zai cigaba da neman ilimi duk da dama ba wai ya zauna haka ba ne, kullum cikin karatu ya ke.
Da ya koma Kaduna sai Malam Zakariyya ya haɗashi aure da ɗiyarsa hakan ya ƙara masa daraja da ɗaukaka. Bayan shekara uku Malam ya fara rashin lafiya gashi babban ɗan Malam da ake ganin zai gaji Malam ya rasu shekaran da ya gabata. Malam ya ja labule da Alqasim a turakarsa.
" ka na son daraja da ɗaukaka ko?"
Alqasim ya amsa da "na'am Malam"
"Ka na son karama da walittaka ko?" Nan ma ya amsa masa da na'am.
Malam ya tallafo ya ce ma sa ya matso da kunnensa, nan Alqasim ya matsa kusa da shi Malam ya gaya mishi sirrin komai. Alqasim ya zaro ido gami da rufe baki. Malam yace "idan ka san ba zaka iya ba kada ka fara dan abinda ya kashe ɗana Musa kenan, taurin kai ya ƙi yin abu ɗan ƙanƙani da aka umurceshi".
Tunda Malam ya faɗa wa Alqasim sirrinshi nan ya shiga ruɗani ko ya yi ko kar ya yi. Amma ɗan daraja da girma da mutane ke ba shi na matsayin sirikin Malam ya sa ma sa girman kai, ƙarshe zuciyarsa ta amince masa da komai jin yanzu fa idan Malam ya rasu shine zai hau matsayin Malam na yanzu.
Ba ayi wata biyu ba Malam ya cika nan aka shiga cikin baƙin ciki sai dai daga baya hankalin kowa ya koma kan Alqasim saboda shine wanda Malam ya kira a matsayin magajinsa a masallaci, hakan ya faru ne kuwa bayan Alqasim ya tabbatar da amincewa da dukkan sharaɗin da aka buƙata.
Daren kwana casa'in da rasuwan Malam Zakariyya da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare Alqasim yai sujudi wa ɗaya daga cikin manyan baƙaƙen Aljanu da suke makusanta wajen shaiɗan. Ga abinda aka bayyana ma sa lokacin
" 'yarka tana da daraja, ɗaukaka, karama da duk abinda kake buƙata, za ka yi amfani da darajarta, idan ka yi hakan zai ja maka farin jini da ɗaukaka mai girma domin an halicceta mai yawan ilimi, basira da ɗaukaka. Abu ɗaya muke so zamu aureta dan haka daga yau har ƙarshen rayuwanta babu mai aurenta. Haka nan duk lokacin da ta ke jinin haila zamu dinga saduwa da ita ta baya ta jikinka" daga haka baƙin Aljanin ya ɓace.
Lokacin da Alqasim ya zo ɗaukar Nana Khadija Malam Ibrahim ya tafi aikin hajji dan haka ba wanda ya hana shi. Shekaran Nana goma sha ɗaya tana aji biyar a makarantar firamare. Sai dai Nana ba ta fara jini ba sai da ta cika shekara sha uku a duniya, haka nan duk wata Sheikh Sidi Alqasim ke faɗa ma ta ta baya hakan ya nakasar da ita ta dena girma ta koma tamkar mai taɓin hankali, tana ganin abubuwa da dama wanda ni ba zan iya cewa ga yadda aka yi ta ke gani ba" ya nisa kafin ya ce " wannan shine labarin Nana"
Shabbir da tuntuni hawaye suka fara gangaro ma sa yai ƙarfin hali ya ce " Mi yasa? akan duniya, duniya da zamu bari, duniya da kowa zai mutu ya barta, ɗaukakar banza ta wofi" AbdulWahab yai murmushi ya ce " kaɗan kenan da ga halin mutum, ba da safe Nazira ta gaya ma ka nata tarihin ba. Haka mutane suke, akwai mugaye acikinku wanda sun fi wasu Aljanun hatsabibanci da mugunta"
" but why? Mi ya jawo haka?"
"son zuciya Muhammad, son zuciya shine silar komai"
Ya goge hawayensa ya ce " mi yasa ka ke bibiyata toh? Kuma ina Malam Ibrahim yanzu?"
"Lokacin da Malam ya dawo ya tarar an ɗauke Nana ya ji baƙin ciki sosai amma ba yadda ya iya saboda Alqasim mahaifinta ne, lokacin da na je Kaduna ziyara wa Nana saboda mun saba da ita sosai tun tana yarinya na tarar da abinda ke faruwa sai dai ba abinda zan iya yi akai saboda gidan Sheikh cike ya ke da baƙaƙen Aljanu, idan nace zan saceta ma ba zan kai ko ina ba za su halakani ganin haka na tafi wajen Malam na bayyana masa ko ni wanene da kuma abinda na gani, abin mamaki Malam ya jima da sanin ni ba mutum bane kuma ya jima da sanin ɗaukakan Malam Zakariyya ba daga Allah bane. Na tambayeshi abinyi ya ce min addu'a, bayan shekara goma da na sake komawa wajen malam shine ya ce min wai idan aka samu jarumi marar tsoro da zai iya auren Nana kuma ya sadu da ita zata dawo hayyacinta sai dai zai iya fuskantar barazana daga wajen Aljanin da yai wannan aiki amma kuma Allah ya fi ƙarfin kowa. Da na tambayi Malam ko ya san wannan jarumi sai ya ce min na roƙi Allah ya bayyana min shi, tun daga lokacin na fara istikhara har zuwa shekarar da ya gabata da Allah ya fahimtar da ni kai ne wannan jarumi. Amsar tambayar ka ta biyu kuma shine tabbas Malam na nan da rai sai dai ya samu matsalar ido saboda tsufa ba ya gani yanzu dan yanzu shekarun Malam casa'in da shida a duniya"
Shabbir yai ajiyar zuciya yana tunanin abin yi ƙwatsam wayar sa ta shiga ringing ya ɗauka dan ogan sa ne, bayan sun gaisa ya ke ce mishi an buƙaci ya resuming aiki gobe gobe saboda wani aikin gaggawa da zai yi a Abuja.
"Allah shine mai tsara komai kuma shi zai taimaka mana, ka je Abujan, Allah kaɗai ya san hikimar zuwanka" da wannan Abdulwahab ya mishi sallama ya tafi. Tafiyar AbdulWahab ya jima yana juya wannan al'amari, shin wai son duniya zai sa ka nakasar da rayuwar ɗiyarka? shi ya san ana asiri dan neman kuɗi bai san maluntaka ma har abin ayi asiri bane.
Ƙarfe goma ya isa asibitin har sun yi bacci ya tasheta saboda ya san yanzu ne lokacin da yake dashi gobe da sassafe zai wuce Abuja. Da bacci a idonta amma lokacin da ya ma ta maganar idan an sallameta Umma za ta maida ta Bauchi sai hankalinta ya tashi. "ni ba zan koma Bauchi ba, ni sai na cimma burina akan ganin ƙarshen Alhaji Kadi"
"Za ki yi abinda na faɗa Nazira" ya daka ma ta tsawa wanda ya sa Amina ta farka.
" I forbid you from going anywhere near Alhaji Kadi or his properties, da kin mutu a hatsarin jiya fa? so stop this nonsense and go back to your father. Ni da ya ke aikinmu ne zan dage na tona asirin Alhaji Kadi, amma ke ba abinda za ki iya yi" da wannan ya ajiye ma ta kuɗi akan gado ya fice daga ɗakin ya barta tana zubda hawaye.