13
by @hafnancy
"Tabbas yaya bakayi karya ba Son Rahama nake. Kuma So na aure nake mata, Na dad'e ina kokarin b'oyewa gudun kar ya bayyana dan nasan in kuka sani abun baze tab'a muku dad'i ba, Sai dai ance kamar yadda alamomin 'K'i' basa boyuwa to haka zalika alamomin 'so' suma basa boyuwa, Zanso ace in mallaketa amatsayin matata ta sunna...''
Nan take Papa ya hada uban gumi duk da sanyin Ac na motar dake bada iska hakan be hana zufa tsastsafo mishi ba yace"Anya Yusuf kanka daya kuwa ? shin ka manta matsayinka ne awurin wannan yarinyar da har kake Tunanin kasancewa da ita a inuwar aure ?"
Idanunsa daya kada yayi jawur ne ya runtse Sai ga wasu sabbin hawaye masu Zafi sun zubo masa, Bayan hannu yasa yana sharesu yace"ina Sane kuma Zan iya bugan k'irji ince Zuciyata batayi kuskuren sonta ba. Yaya in har zakamun adalci kaima kasan akwai aure tsakanina da Rahama! amma ana barin halak dan kunya ne Sai dai ance muddin kaga zaka cutu to karka biye ta kunya ka aikata abunda Zuciyarka keso, yaya dan girman Allah karku hanamin Rahama, Ka Fahimtar da Addah Halima cewa ba wani abu bane in 'yarta ta Aureni "
Sosai Tausayinsa ya darsu aran Papa, kwarai ya kwana da Sanin cewa akwai Aure tsakanin Rahama da Yusuf, Ita Rahamar ce ma ko kadan bata da masaniya akan hakan, amma shi Rigimar Halima ce kawai bayaso.
Fesar da ajiyar Zuciya yayi yana"Yusuf Na Fahimceka sosai amma da zaka bi shawarata ne da kayi hakuri, Nasan da Aure atsakaninku Tunda bani na haifeta ba sannan kaima din ni dakai ba ciki daya muka Fito ba, hasalima iyayenmu ba daya ba, Kaga kuwa akwai halartacciyar aure tsakaninka da Rahama! sai dai ni Rigimar Halima ce banaso, Kai kanka ai kaga yadda take mana hauka data gano kuna kaunar juna.
ina ga an kai ga yin auren ? Allah kadai yasan abunda zata aikata. kayi hakuri ka janye Tunda aurenka da Rahama zai zamo tamkar bayyanar sirrinta da take rufewa ne wanda ko kusa bata son 'yar nata ta sani."
Haka dai papa ya cigaba da lallashinsa akan ya hakura ya janye Yusuf dai jinsa kawai yake amma baya Tunanin Zuciyarsa zata iya hakura da kaunar Rahama.
Papa na Sauka Yusuf yaja mota sai gidan rediyo, ko acan din ma kasa maida hankali yayi awajen aikin haka ya dauki permission ya taso yayi musu karyan baya jindadi ne.
UMAR
Be bata lokaci awajen Zalihat ba, Nan suka hau tsaren tsarensu na yadda zaa had'a kayan Lefe, Nan take yayi mata transfer d'in dubu dari shidda yace asiya tsadaddun kaya da akwatuna sannan ta nemi mutanen da zasu kai kayan Ranar alkhamis, yanaso ne ayi komai atsare kar arusa masa plan. Be wani bata Lokaci awajenta ba ya nufi wurin aiki.
YUSUF
Yana fita daga gidan Rediyo tun be karasa gida ba Rahama keta nacin kiransa shi kuma yaki dagawa don jin muryatta kadai Zai iya kara tada masa da hankali. abangaren Rahama kuma kasa zama tayi hankalinta yakai kololuwar tashi ganin Uncle Yusuf yaki daga kiranta tasan dole ne yakasance cikin Fushi da abunda Addah tayi Masa.
Ta rasa mafita hakan yasa ta nemi Ameerah awaya duk da dai ayanzu dole mutuncin dake tsakaninsu zai samu rauni sabida al'amarin daya kunno kai amma hakanan kawai taji tana son magana da ita Tunda Uncle yaki daga mata waya kuma tasan aiki be isa yasa yaki dagawan ba.
Ameera na dagawa tace "ya akai na kirana da safiyar Allahn nan ne me son k'anin mahaifinta?
ko kadan banyi mamak'i ba dan ko abunda yafi hakan tamun batayi laifi ba.
Hannu nasa na share hawaye ina"Anty Meera an tashi lfy "
"Sumul nake! ko dama kira kikai kiji ance miki bakin cikinku keda Yusuf ya kasheni ? toh Rahama Ameera htana raye kuma cikin koshin Lafiya duk ku gama haukarku ku dawo cikin hayyacinku don aure bazai taba tabbatuwa atsakaninku ba sai in zaku nunawa Duniya cewa ku d'in Jahilai ne haihuwan gaba da fatiha... "
Hawaye nake sosai, duk wani kalamin data furta na dukan ilahirin Zuciyata, sai dana gama sauraronta sannan nace"Ameera soyayyar da mukewa juna nida Uncle Yusuf ba yin kanmu bane Allah ne ya jarabcemu da shi, sannan mu bamu ce miki aure zamuyi ba kamar ta bakinki da kika ce aure bazai taba yuwuwa atsakaninmu ba to haka d'in ne, yanzu dai ki Taimaka mun in samu ya daga wayata ina ta kiransa amma yaki daga...."
"kutumar bura ubanki! shegiya tsinanniya 'yar macce Ni zaki Rainawa hankali ? Rahama kanki daya kuwa ? Wannan wani iri abu ne dan kin ga ina shiru na maida abun wasa shine zaki nemi raina mun wayau. agabana jiya kika nuna baro baro kina son saurayina Ƙanin Mahaifinki, ban dauki wani zafi ba na dauka jarabta ce ta ubangiji amma abun be isheki ba Shine zaki daga waya ki kirani duk duniya ki rasa wanda zaki lallaba ya shawo miki kan Yusuf sai Ni rahama ?
dan kin ga nayi shiru na kyaleki ban dau mataki ba ? wallahi kin jawa kanki koda zanyi yawo ne da zani ahannu sai na rabak'i da Yusuf wallahi yau dole ne ya zaba ko ni ko Ke in zai iya aurenki tunda wanda zai so wanda ba muharraminsa ba ai komai ma zai iyayi Kuma ayanzu na gane cewa sonki da Yusuf keyi ba laifinsa bane kece ke cusa kanki gareshi ta karfi da yaji, ya Allah ka aurad damu da wuri kar ka jarabemu da ganin masifa irin wannan dan rasa mijin aure ne ya jawo miki hakan, ki jira kiga irin matakin da zan dauka Tunkiya kawai "
Kit ta kashe wayar.
kuka nake sosai kamar raina zai fita gabadaya sai nake jin kamar duka mutanen duniyan sun juya mun baya ne. ban tab'a jin haushin rashin aurena da wuri ba sai ayau amma kuma ba yin kaina bane haka Allah ya tsaromun.
Yanzu har a idanun mutane sabida sabani yadan hadamu shine suke mun kallon ni nake cusa kai ga mazajensu ? ina kok'arin buga misali ne akan Ubaida da ita Ameeran da suka goranta Min har suke ganin kamar ni nake Tura kai ga mazajen nasu.
sak'o na aika masa ganin kona sake k'ira ba dagawan zaiyi ba "Uncle inka huce dan girman Allah ka nemeni muyi magana Addah tana neman bada aurena cikin gaggawa ga Umar Juma'ah mai zuwa."
Yusuf ya iso kofar gida kenan sai ga sak'on Rahama ya shigo wayarsa jiki na rawa ya kashe motar ya fara karantawa dakyar yakai karshe sabida yadda hankalinsa ya tashi ainun Burinsa kawai ya latso ta.
Gumi sai tsasstsafo masa yake amma bai damu ba ya kirata bugu daya ta daga gami da rushewa da kuka tana"Uncle Yusuf kaki daga wayata Addah ce ke kokarin bada aurena ga Umar abunda dama nakeson in gaya maka kenan please kabar Fushi dani ban maka laifin komai ba kazo ka tayani bata hakuri dan Allah ta janye ban sonshi ko kadan "
Wani irin huta ne yaji ya dauke masa hawaye masu zafi suka cicciko masa idanu, arayuwarsa be taba tunanin Addah Halima zata iya aikata iri iren abubuwan da take musu ba sai gashi ta shayar dasu madarar mamaki.
"Shi Umar d'in har yanzu yana cikin Gidanku ne ?" ya furta da rawar murya.
Nace nima cikin dakusasshiyar muryar"be jima da barin gdn ba itama Addah ta Fita ban san inda taje ba "
Runtse idanu yayi da yake jinsu suna masa har wani irin yaji yaji yana"Zaki iya fitowa ki sameni ta kasan layinku please bazaki dad'e ba in kinzo kawai ki shiga mota "
"Uncle ina tsoro kar in sake samun wata matsalar da Addah muyi magana kawai ta waya dan Allah " Na ida magana ina kunshe sabon kukan da yake neman kufce mun, kuka ya riga ya zamemun sabon dab'ia, yanzu akullum sai na zubar da hawayen da baa iya kirgawa.
Kwantar da murya yayi yace"Rahama in kina sona ki Fito gani ata kasan layin ina jiranki " Kit ya kashe yana kok'arin daidaita parking don suna kan wayan ne yake tuk'in har ya karaso kasan layin gidansu Rahamar.
Bin wayar nayi da ido ayayin da nake ji ana kara ninka min son K'anin mahaifin nawa. in dai har wannan itace kaddarata arayuwa ta son k'anin mahaifina to zan karbeshi da hannu bibbiyu dan ni koda kaunarsa kawai Allah ya barni besa nayi aure ba tabbas zanyi Farin ciki.
_"Rahama in kina sona ki Fito gani ata kasan Layin ina jiranki."_ Tuna maganarsa yasa ban san sanda na dakko doguwar hijabina na zura akan wandon aikin asibitinmu ba wanda dama ban kai ga ciresa ajikina ba.
Da sauri na Fito na kulle koina kana na boye makulli a inda muka saba boyewa sannan nayi Fitowata. Ina bud'e kofar gida ina saka kafafuna awaje idanuna dana Addah ya harmutse cikin na juna gabana yayi wani irin mummunar Faduwa, ko baa fada ba daga gidan babbar aminiyarta ta Fito Maman Hawwa.
Wani irin Kallon Tsana ta jefo mun tun kan ta kariso tana"Dan ubanki ina Zaki ? ashe bana miki iyaka da waje har sai randa kika bar gabana ba ? Rahama kina wasa dani ko ina zaki ?" Wani irin jarumta ne naji kawai yazo min ban san sanda na saki malalacin tsaki na sake kofar ta rufo da karfi ba, ban damu ba nasa kai ta hannun haguna na mika kai tsaye har zuwa inda zan sami Uncle akarshen layin.
ina jin Addah na biye dani abaya tana kiran sunana cike da mamakin Kalar Rashin kunyar dana mata abunda ban taba yi ba, ko juyowa in saurareta banyi ba sai ma kara sauri nayi kuma still bata dena bibiyata ba, Koda na Lura itama saurin take zabgawa dan ta cin min sai na had'a da gudu harna sha kwanar layin, Acan na hango motar Uncle apake, da gudu na karasa na bude gaba na shige ina"Uncle dan girman Allah ja mota mubar nan ga Addah nan biye dani kuma in ta cin mana tasan kaine aciki akwai matsala "
Ina fadin hakan ne ina waiwayenta ta cikin motar, shi kansa Uncle Hankalinsa atashe ya waiga yana kallonta dab take da karaso wa.
"Uncle kaja Uncle Kaja mu tafi " Na furta ina me rushewa da kukan Tausayin kanmu duka.
Kamar jira yake in bashi kwarin gwiwa, Atsiyace ya figi motar kiris ya rage ya kaɗe wani yaro, Ina Kallonta kamar zatai hauka don nasan ta gano cewa motar Uncle Yusuf ce, Kuma nasan sosai zatai nadamar mantawa da tayi ta rabani da wayata kamar yadda taci alwashi don tayi seizing communication atsakanina dashi.
ADDAH
Ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta bisu ta shake Yusuf har lahira kowa ma ya huta, komai Rahama zatai mata ko kadan bazata taba ganin laifinta ba laifin Yusuf za tana gani, shine take ganin ya taimaka wajen lalata mata tarbiyyan yarinya don bata yadda wai hakanan yake Tare da Rahama ba, Allah ne kadai yasan abunda suke aikatawa in sun keb'e don shakuwarsu da juna ta zarce misali, haka dai shaidan ya cigaba da kawata mata zuciya.
"Allah ya isa tsakanina dakai Yusuf, bazan taba yafe maka ba don kaci amanata " Ta furta tana sharar hawaye ayayin da zuciyarta ke suya. Juyawa tayi ta fara takawa gida ganin mutane sun fara maidata abar kallo, akan hanya ta katso Maman Hauwa awaya ta kora mata bayani dake dama tasan kwanan zance.
"Amma wallahi wannan yaron anyi dan banza shege la'ananne! wallahi Halima kece ke ɓata mana lokaci in ba haka ba ni da an bi ta nawa ne da tuni ko an shafe babin dan iska aduniya , mu haukatashi yashiga duniya sai dai wani Yusuf din bashi ba wallahi "
Addah tace arude"aa Maman Hawwa ni bana son na cutar da kowa, ko k'yank'yaso ban taba kashewa ba balle akai ga batun zaluntar dan adam, Yusuf bai mun komai ba ni kawai hadin ne bai mun ba akwai haramci aciki."Azafafe maman Hawwa tace"har sai yaushe ne zaki daina zama kina cigaba da tarar hawayenki akan Yusuf da Rahama ? ki zauna kiyi Tunani tun kafin lokaci ya kure miki, kin san nice mutum na farko ma dana fara ankarar dake sanda na lura shakuwarsu tana neman zarce misali amma awancan lokacin kika nunamin kar inji komai babu abunda zai faru, sai gashi ayau hasashena ya tabbata gaskiya, Halimatu Sadiya ki tashi tsaye ina tsoron kar halittun nan biyu suzo su saki hauka, Abdulmalik me rauni ne akan Rahama bazai iya taimakonki ba nice kawai zan iya baki taimako Halima ki Tashi daga wannan dogon baccin"
muryatta na rawa tace"Maman Hawwa ban k'i ta taki ba amma kibari inje in sami babbar yayarsu da maganar in taki daukar mataki akai ne sai musan abunyi amma ki tayani adduar Allah yasa shi Umar ba guduwa yayi ba ya dawo adaura musu auren ko ayaya ne suje su karata acan, aurenta da Umar shine kwanciyar hankalina don nasan hakan ne kawai zai kawo karshen wannan matsalar kinga rabuwarsu dole bayan ta auri Umar, dole ita da Yusuf zasu hakura da junansu Tun kafin duniya ta farga da sanin halin da ake ciki na wannan abun kunyan."
Cike da tausayinta Maman hauwa tace"To shikenan Allah ya mana maganin matsalar in kin dawo sai ki kirani inji yadda kukayi da ita "
"Ba damuwa "
nan sukayi Sallama Addah bata shiga gida ba tayi wajen Yaya Fad'ime wanda babban yaya take awurinsu Yusuf.
RAHAMA
Kifa kaina nayi asaman cinyata ina rera kuka me taba zuciya, ina jin hannun Uncle akaina yana lallashina ayayin da hannunsa dayan ke kan sitiyari, fadi yayi da rawar murya" Rahama kibar kuka Allah zai kawo mana karshen wannan matsalar insha Allah, Dago ki kalleni habibty "
Jin sunan daya ambatoni dashi akarshe yasa na dago kai ina kallon cikin k'wayar idanunsa, hada idanu danayi dashi yasa naji wani sonsa na kara yawa azuciyata, ban san na shagala da kallonsa ba sai danaji hannunsa akan fuskata yana sharemun hawaye yana" abar yi mun asarar waennan hawayen dan ni kadai nasan tsadarsu agareni i love you so much Rahama ban san meyasa mahaifiyarki bata san mu kasance tare ba " yana fadin hakan ne ayayin daya sunkuyo yana kai min light kiss a lebb'ena.
Karon Farko dana ji wani irin sabon alamarin da ban taba jin irinsa ba, Nan take jikina yadau rawa, bakinsa yakai kunnena yana min rad'a"Am sorry i know i'm not suppose to do that, Na kasa controlling kaina ne domin labbunan suna daukar hankalina ne da yawa "
ya ida magana yana sakar mun lallausar murmushi daya kusan sumar dani nan zaune, kuma har zuwa wannan lokacin na kasa Furta komai, ko hawayen ma sun bar zuba idanuna sai kallonsa suke.
"duba gabanki kiga inda muka zo"
dasauri na daga kai ina kallon gabana, agigice na maida kallona gareshi ina "meya kawomu Dan'Zaki Foods babban ma'aikata ? me muka zo yi ?"
"wa muka zo gani dai yakamata kice"
ya bani amsa yana murmushin yak'e,
yace"Wurin Umar muka zo ayi sulhu domin koyarwar addininmu ne yin sulhu tsakanin musulmi da musulmi waenda suka sami sabani, amma akace in sulhun taki yiwuwa ana iya yakar juna in akwai zalunci da cutarwa, dan haka ki sani ko kwantawa akasa Umar yace inyi ya takani kafin ya hakura ya janye to zanyi amma ya guji mikewata in har yaki ya janye kudirinsa akanki "
Yana maganar nan ne idanunsa na kan gate d'in ma'aikatar, be kai ga danna horn ba aka bude masa kofa ana daga masa hannu "barka da zuwa yallabai " shigewa yayi ciki ya nufi inda ake parking, Nidai gabana cigaba yayi da faduwa dan ban san makomarmu ayau ba tunda mune muka dauki kafa muka kawo har inda Umar yake. da uncle ya shawarceni daban bashi shawarar muzo ba.....