Page 4
*ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 4.
Najwa tana fita Zaidu ya mika mata fararen leda guda biyu ta amsa tana washe baki da godiya, suka yi sallama ta shiga gida ta zube ledan gaban inna ta zauna tana dubawa, ledar farko kayan tea ne a ciki sai leda na biyu kuma gasasshiyar kaza ce dankwaleliya da kuma cips da kwai da miyar albarka a cikin wani foil paper daban, Najwa taja numfashi tana sauke shi a hanlaki tare da haɗiye miyau.
Allah ya shiryeki Najwa ya rabaki da cutar kwaɗayi, dan na kula shine kawai yake damunki, na tabbatar ke ce kika saka shi wannan siyyar da ba shiri saboda nayi tuwo maƙiyinki.
Kai innata koda na roƙeshi ɗan uwana ne fa, kuma matsayin wa yake a guna ko ba soyayya akwai ƙauna ta jini.
Hmmm ni kwashe kayanki ki tafi da shi ɗakinki kafin babanku ya shigo, kin san dai baya son irin wannan abin.
Ai da sauri ta miƙe ta kwashe ledanta ta fice dan ta san babansu bayi da wasa, inna ta bita da cewa.
Saura ki cinye baki aje min ba.
Dariya Najwa tayi ta shiga ɗakinta tana gyara zama ta soma cin kazar nan kamar mayunwaciyar zaki. Najwa kenan ga sani ga shagala take ta kenan, yarinya ce mai natsuwa da iya shiga ta mutunci, dan bata saka gyale hijab ne har kasa da safa, nikaf ne sai in zata islamiya take sakawa, shekarar da ta wuce ta kammala secondry bata cigaba ba dan babansu bayi da ƙarfi kuma ma irin mutanen nan ne masu ra'ayi bai yarda tayi boko da ta wuce secondary ba, mazan ne dai suke da garantin cigaba sai dai gabaɗayansu ma sunƙi mayar da hankali ga karatun boko, babbansu Junaid bakaniken mota ne sai mai bi masa Abdullahi ustaz ne yana koyarwa a islmaiya, sai kuma na uku Sadiq tela ne sannan Najwa da yanzu take makarantar haddar alqur'ani tun bayan yin saukarta da shekara biyu da ya wuce, ta haɗa izi ashirin da biyar. Ance mutum tara yake mai cika goma ba to gaskiya itama ta samu naƙasu a fannin yawan buri, tana mugun son rayuwar masu kuɗi da wayewarsu, duk da tana da tarbiyya sosai amma bai hana ta nuna maitar son kuɗinta a fili ba, idan aka ce hidima ta masu kuɗi ne aka gayyaceta to ba karamin bashi muhimmamci take yi ba, shiyasa ko a makaranta kawayenta yaran masu kuɗi ne, sai ta tabbatar da akwai kumbar susa kafin take bada kofar ayi abota da ita, kuma tun tana karama da wannan aƙidar ta taso wataƙila dan ko su talakawa ne yasa take kwaɗayin haka, saboda duk danginsu babu masu kuɗi sai dai masu ɗan rufin asirin Allah, yanzu ne dai da Sameeha ta fita zakka a cikinsu ta zama musu zakaran gwajin dafi, shiyasa Najwa take mugun sonta har hakan yasa ta yanke amincewa da auren Zaidu saboda hakan ne kaɗai zai ƙara mata kusanci da ita kuma ta riƙa shiga cikin masu kuɗi, dan a ganinta Sameeha tana da kawaye masu kuɗi sosai, sannan ta samu gidan kashe kwaɗayinta tunda ta san basa rabo da kaji da kayan daɗi, addu'arta Allah yasa Sameeha tana da sakin fuska da son mutane duk da tasan halinta a da ba tada matsala, amma kila yanzu kuɗi ya sauyata dan wasu in sun samu rana basu iya shanya ba.
***
Washe gari da wuri Najwa ta shirya ta tafi gidansu Zaidu, ta samu har sun gama shiri zasu tafi Zaidu ne ma ya tsayar dasu akan su jirata ta ƙaraso, Najwa ta gaishe su cikin girmanawa kana Sameeha ta ce su wuce dan akwai aiki a gabansu, suka fito Zaidu ya tare sumu napep biyu, Sameeha da yaranta sai Najwa da Ikram a dayan napep ɗin tare da kayanta dan zata kwana biyu a can har sai sun gama kimtsa gidan.
Suna isa bakin gate suka sauka dama Zaidu ya sallami masu napep tun kan su taho, Abi ya buga gate mai gadi ya buɗe yana ganinsu ya shiga yiwa Sameeha sannu da zuwa ya buɗe musu ƙofa suka shiga, tun daga farfajiyar gidan Najwa take karewa gidan kallo tana faɗin masha Allah tana maimaitawa, har suka isa ƙofar shiga falo Sameeha tayi amfani da key ta buɗe musu ganin ba motar Aminu tasan baya nan, suna shiga Najwa ta zube a cushing tana sauke numfashi da wani irin tsantsar murna wanda ya bayyana a fuskarta, saboda yadda falon ya tsaru yayi matular burgeta da hango kanta dama itace ce mamallakin gidan, sam ta kasa danne farin cikin tana cewa.
Alhamdulillah Masha Allah La Kuwwata Illah Billah, Anty Sameeha kin dace da gidan duniya saura na lahira, wlh gidanki tamkar irin gidajen da muke gani a cikin fina-finai, ya tafi da imanina Allah ya sakamu a danshinki, ni kam kamar in dawo nan gabaɗaya da zama dan wlh ba karamin kankaro mini mutunci zai yi in kawayena suka ganni a nan.
To Najwa ai ga ɗaki nan sai ki kwaso kaya ki dawo mu cigaba da zama.
Ai wlh Baba bazai barni bane kawai amma da sai na dawo, ko da yake ko hutu na riƙa zuwa ina buga hotunan da zan riƙa posting a status, ko ba komai muma muna da gida mai kyau.
Allah ya kyauta miki Najwa ke dai har yanzu ba zaki bar wannan shegen ƙarya da buri ba.
Cewar Ikram tana balla mata hararar wasa, Najwa ta miƙe ta yi tattaki ta isa inda Ikram ke tsaye ta dafa kafaɗarta tana cewa.
Ke me za a fasa ai ina nan akan bakana, dole in yi kwaɗayin kuɗi domin cikin talauci na taso, da ace na gaji arziki ba zanta magana irin haka ba, ki barni na faɗa koda a iya baki ne na dai furta, kuma kuɗi abin so ne ba wanda baya son jin daɗi.
Naki dai yayi yawa wlh, yanzu na tabbatar da kin ci sunanki wato ga sani ga shagala.
Faɗi ki kara 'yar uwa.
Kun ga, ku bar wannan taƙaddamar ku zo ku fara aiki bana son Abban Amra ya dawo bamu ci karfinsa ba, Ikram ina ga ke zaki shiga kitchen ne ki ɗaura mana shinkafa da miya ki gyara kaza biyu kiyi mana peper chicken.
Cewar Sameeha tana fitowa daga ɗakinta data shiga aje jaka, Najwa tayi wani shewa tana rawa da wakar.
Ewe gidan masu kuɗi gidan daɗi, za muci kaza zamu kaza.
Allahu yahadiki Najwa.
Cewar Ikram, Najwa tace Ameen wa iyyaki tana kalkale dariya, motsa kofa da suka ji ne yasa suka mayar da hankalinsu ganin waye zai shigo, sai ga Aminu ya bayyana cikin tsadadden shadda da hula akansa yayi matukar kyau, wani irin sumar wucin gadi Najwa tayi numfashinta har ɗaukewa yayi ya dawo, nan take taji kirjinta yana wani bugawa da sauri da sauri ga kanta daya yi mata wani girr, tunda take bata taɓa ganin Namiji daya tafi da imaninta lokaci ɗaya ba kamar wannan da ya shigo, ana cewa so farad ɗaya a ganin farko to tabbas ta tabbatar da hakan yana faruwa dan kuwa nan da nan ta faɗa cikin wani kogon bege da mafarkin samunsa a matsayin miji, sai dai kalmar data ji yaran suna Abba oyoyo yasa ta farka daga kogon tunanin data faɗa ta tsaya sororo tana kallon ikon Allah jiki a matuƙar sanyaye.
Abban Amrah ashe baka yi nisa ba na ɗauka ba yanzu zan ganka ba.
In koma kenan bakya buƙatar ganina a yanzu.
Ni ɗin banza na nace ka koma.
Cewar Sameeha tana dungurin kanta, suka saka dariya ya karaso falon ya zauna a cushing yana cewa.
Kewarku yasa na taho yanzu dan wlh jiya nayi kwanan kaɗaici, gashi gobe da sassafe zan wuce Abuja ana nima na.
Wayyo daga dawowarmu ko hutawa baka yi ba, ni dai ina burin naga ranar da zaka aje aikin nan ka dawo ka zauna guri guda.
To ya za ayi Meeha ai duk wanda ya tara iyali dole ne ya fita nima.
Ina kwana yaya.
Lafiya lau Alhamdulillahi Ikram ya karatu ana ta taɓawa.
Ikram ta amsa da lafiya lau kama ta wuce kitchen dan ɗaura girkin da Sameeha ta sakata, sai a lokacin ne Najwa ta sauke raunannen ajiyar zujiya ta ce.
Ina kwana.
Lafiya lau ya amsa sai ya miƙe yana duban Sameeha.
Baƙuwa muka yi ne?
Eh ɗiyar Gaggo Zulai ce wanda nake faɗa maka ita kenan mata 'ya mace. Ai in gaya maka ma haɗin gida za muyi musu Zaidunmu ne zai aureta.
Kai masha Allah Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu, idan kin gama basu aikin ki zo ki tayani shirya kaya dan ina ganin sati biyu zuwa uku zanyi a Abujan nan dan wlh akwai ayyyuka rututu da suke niman shan kaina.
Wayyo ni Sameeha har sati Uku, ina tunanin sati guda zakai ka dawo gaskiya bazan yarda ba.
Ta faɗa tana fuskar shagwaba, Aminu yayi dariya ya wuce zuwa falonsa Sameeha ta bi shi tana yi mishi mitar kwanakin sunyi yawa, Najwa da kamar an daskarata a gurin ta bisu da ido tana jin wani irin damuwa da kuma haushin Sameeha daya ɗarsu mata a zuciya nan take, sosai taji haushin faɗa masa da tayi wai zata auri Zaidu, sai ta koma cushing ta zauna tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tunda take bata taɓa jin yanayi irin wannan ba akan wani ɗa namiji ba sai akan Aminu, wanda har numfashinta da zafi yake fita, jikinta ya ɗauki ɗumi da shiga tashin gankali, ga koshi ga kwanan yunwa ita taga samu taga rashi, dan tasan ko mutuwa zata yi Mijin Sameeha ya haramta a gareta dan tasan babu ta yadda zata yi ta mallakeshi a matsayin miji, dole ne ta lallashi zuciyarta ta samawa kanta lafiya, sai ta miƙe tana kokarin yaƙi da shaiɗan ta wuce kitchen wajen Ikram.
Sallamar Hauwa yasa Sameeha fitowa daga falon Aminu, cikin sakin fuska ta ƙarasa falon tana yi mata sannu da zuwa ta nuna mata gurin zama, Hauwa ta zauna suka shiga gaisawa sai bayan sun nisa ne Hauwa tace.
Ina Aminu ko yana babban gida ne?
Yana ciki yana haɗa kaya gobe zai tafi Abuja.
Ohh aikin kenan ba zama, dama nazo gurinki ne mu tattauna.
Ina jinki yaya Hauwa amma kafin nan bari na kawo miki abin motsa baki.
A'a yi zamanki ba na bukatar komai dan a koshe nake.
Sameeha ta koma ta zauna dan harta miƙe, Hauwa ta cigaba da cewa.
Dama na zo ina yi miki tunin abinda kika sani ne, akan sanin Aminu ɗan dangi ne, kuma rashin zamanku a nan kaduna yasa duk ba ayi saboda dake ba, dan haka ina so ki saki jikinki da mutane, ki shiga cikinmu a dama zumunci dake dan in kika ce zaki ware kanki wlh ba zaki ji daɗin mu'amala damu ba, dan na kula baki son mutane bakya so a raɓeki.
Hmmm yanzu Yaya Hauwa maganar kenan da ya kawo ki.
Eh itace ta kawo ni sannan in sanar dake gobe zan aiko miki da 'yar aiki wacce Laure ta samo miki, dan wannan gidan naki saida me tayaki aiki in ba haka ba kar ki zo ki fara tara datti gida ya lalace.
To ni nace muku ina buƙatar 'yar aiki ce? Sannan ma in zan nima 'yar aiki dole sai ku ne zaku kawo mini? wannan wani irin son kai ne da shiga hurumin da ba naku ba, to ki koma ki faɗawa Lauren bana son 'yar aikin dan baku isa ku ce zaku yi iko da abinda yake matsayin ikona ba.
Rashin kunya zaki mini Sameeha.
Hauwa ta faɗa da ƙarfi tana dukan kirjinta, Sameeha ta kalleta da kyau.
Idan haka kika ɗauka to shi na miki, wlh baku isa ku juyani ni da gidana ba ko wacce taje taji da matsalar gabanta, haba ni kaɗai ce wacce take auren ɗan uwanku da zaku sakani a gaba, tun ina Lagos baku barni da ƙananun munfurcinku ba gashi na dawo nan zaku dasa miki iko to wlh uban kuturu yayi kaɗan.
Ke Sameeha yaya Hauwan kike faɗawa haka?
Cewar Aminu daya fito falon wanda yayi daidai da lokacin da Sameeha take faɗa mata magana, sai Yaya Hauwa ta fashe da kukan munafurci tana faɗin.
Ni zaki zaga kici mituncina daga gyara ka yanka to ai bazai zama sauke mu raba ba.
Ta miƙe a fusace tana goge hawaye zata wuce Aminu ya dakatar da ita.
Dan Allah yaya Hauwa ki tsaya. Ke Sameeha ki bata hakuri ko na sassaɓa miki, baki isa ki wulaƙanta mini 'yar uwa ba kinyi kadan wlh, nace ki bata haƙuri!
Ya faɗa a tsawace, Sameeha da hawaye ya cika mata ido dan wlh Abin da ciwo matuƙa azo har gidanka anima takaka sannan ace ka bayar da haƙuri, tace cikin damuwa.
Kiyi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba In Sha Allah.
Ba shakka Sameeha daga abin arziki kin mayar da shi abin tsiya, ai wlh kinyi da 'yar halak dan zan baki mamaki, ba zan sake kawo miki magana irin wannan ba kuma zanje in isar da sakonki ga Laure cewar kince baki son 'yar aikin da ta samo miki.
A'a yaya Hauwa dan Allah kiyi haƙuri kuma na amince a kawo mana 'yar aikin, Sameeha ki kaɓeta tunda sunyi ne dan su kyautata miki, kuma dama dole zaki samu mai taya ki aiki ga kuma zaman gidan zai miki ba daɗi ke kaɗai in yasa sun tafi makaranta.
To Abban Amrah Allah ya kawota da alkhairi.
Daga haka ta juya tana share hawayen daya zubo mata a kuncinta ta shige ɗaki, Su Najwa kuwa da suka fito suka tsaya a kofar kitchen komai ya faru akan idonsu, dan haka suna ganin Sameeha ta shige ɗaki sai suka koma ciki, Ikram tana ƙananun surutai akan abinda Hauwa ta yiwa 'yar uwarta, Najwa dai tsaki take ta ja dan damuwarta daban ba wannan ne a gabanta ba, dan yadda ta ƙara tozali da Aminu wutar soyayyarsa ƙara ruruwa ta yi a zuciyarta.
Cakwakiya! To muje zuwa...
Ummu Sultan da Samha ce